Free chapter · Read without an account

Page 1

by Sumayya Usman · JADEEDA

*JADEEDAH*

         (It's a story of two love birds who are so different from each other ) 
STORY & WRITTEN BY :
 (*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin 
        MENE NE ABIN YI ?
        KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*

***
***
Yabo da Godiya ga Alla
Alhamdulillah! Ina miƙa godiya ga Allah (SWT) da Ya bani damar rubuta littafin  Jadeeda. Ina roƙonsa da saƙo da ke cikin littafin ya isa inda ake buƙata, ya taɓa zukata, ya zama darasi da amfanin rayuwa. Allah Ka saka da alkhairi. Amin.
Sai jinjina ga Yah Abba (Abba Writer),Yah Aliyu (Al'uskun waƙa), Sadeeq Rufa'i(Abu Julaibeeb),Safiyya Muktar Garba da kuma Members na YOTA musamman Excos ɗin su, Allah yai riƙo da hannayensu ya ɗauka su,ya basu nasara a duk cikin abinda suka sa a gaba,ba zan manta da irin gudunmawar da su ke bani ba akan duk abinda na zo masu da shi, Allah ya biya ku da mafificin Alkairi 



Wannan labarin k`irk`irarren labari ne duk abinda ki ka gani a cikin sa wanda yai dai-dai ko kamanceceniya da wani abu to bisa arashi ne,ban gina wata kalma wadda ta shafi duka `bangarori biyu da zan yi magana akan su ba batare da hujjoji akan haka ba.
Wannan page naku ne massoya na  Allah ya bar mu tare forever and ever
BOOK 1 
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
[01/07/2025] 

PAGE 1 ❤🔥
       FREE PAGE

                 Bismillahi Rahamanir Rahim
"Ummie Maryama dan Allah kiyi haƙuri ki bar ni in yi zamana anan wallahi tsoro na ke ji ,ji na ke kamar da zaran na fita zan ci karo da Baba Ƙarami na tsaye ya na jiran na fito ya hukunta ni",ta ƙare zance ta na mai share hawayen da su ke ta faman  kwaranya a kyakyawar fuskarta.
       " Haba  Hibbah ki kwantar da hankalin ki mana,domin tuni Baba Ƙarami ya tafi Masallaci don gabatar da Sallahr Azuhur kuma kin dan ba zai dawo dan yanzu ba,ke kuma kin ga tun safe ki ke a cikin ɗakinnan ko kayan barci fa ba ki samu kin sauya ba".
   "Ni dai ki bar ni a haka ban ƙi ba ma in kai tsawon sati a cikin wannan Bedroom ɗin ba muddin hakan zai sa in tsira daga faɗa ko hukuncin Baba Ƙarami ,sosai na ke jin tsoran haɗuwata da shi,ban san me zai faru ba in hakan ta kasance".
"Ba wai zan faɗar ma ki da gaba ba ne ko in sagar ma ki da gwuiwa ba ne ba, A'a amma kin sa ni kuma ni ma na sa ni ,dole ce haɗuwar ki da Baba Ƙarami ke ba ma sh ƙadaii ba har da Baba Malam ,da sauran Yayyen ki sai sun neme ki duk iya zille-zillen da za ki yi ma hakan".
" Innalillahi wa'ina ilaihirraju'una Ummie Maryama na shiga uku ,Ni yanzu ina zan sa kaina da rayuwata ,ko ɗaya ba na son haka ta kasance domin ban san me zan fuskanta ba a haɗuwata da su".
"ki yi haƙuri amma duk tsoranki da hakan sai ta faru domin ta hakan ne kawai za a iya samo hanyar da za a warware wannan rikitaccen al'amari da ya shigo cikin Gidannan ".
" Ummie Maryama ba zan iya ba Zuciyata ba zata iya ɗaukar hakan ba ,a yanzu ma haka ji na ke kamar zata tsaga ƙirjina ta fito waje ta tarwatse,saboda tsoro da fargaba".
      Sai da Ummie Maryama ta sa ki wata gajeriyar dariya kana ta ɗora da cewa,"Kin ga har kin ba ni dariya sai ka ce ba  Hibbah  da na sani ba duk ina dakakkiyar zuciyar da jarumtar da na san ki da ita ?".duk ta ana yin haka ne don ta ɗan kwantar mata da hankali.
  Ka sa cewa da ita komi ta yi sai Ummie Maryama ɗin ce ta ɗora da cewa ,"Komi yai farko zai ƙarshe ,yanzu haka wani al'amarin ne babba ya ke tunkaro ki shiyasa Allah ya jarabce ki da wannan ƙaddarar don haka ki daure kuma ki jajurce har zuwa sanda za ki cinye wannan jarabawar kin ji Hibba".
" Ta ya ki ke ganin haka za ta kasance tun a yanzu na sare zuciyata ta karye ba na tunanin zan iya cin nasara a cikin wannan lamarin mai cike da rikici,Sarƙaƙiya tare da ruɗarwa ba".
"Ban san ki da irin wannan halin ba,duk da nasan cewa kin sa ni cewa saurin sarewa ko miƙa wuya ga lamarin da ba kasan me Gobe zata haifar ba,babban kuskure ne,dan haka ki kwantar da hankalin ki zo mu je yanzu ki yi wanka daganan  ki ci abinci".
   " Ni ba na jin yunwa ko kaɗan, sunan abinci ma ba na son inji an ambata".
"Hakanan za ki daure ki ci ko da one cup na tea ne"," Ni dai a'a Ummie Maryama,ba zan iya cin komi ba a halin da na ke a ciki yanzu".
"Oh ba ki so wannan lamarin ya zo ƙarshe ba kenan ba,domin ba shakka na san wata cutar ce za ta kama ki kin ga anyi ba ai ba kenan ko,gara ma ki haƙurƙuntar da kan ki da zuciyar ki ki samu ki ci wani abun", da haka dai Ummie Maryama ta samu ta shawo kanta har ta amince su ka fito tare da nufin ta je tai wanka ta ci abinci.
Suna isowa Parlour su ka iske Mama Hadiza,Umma Maimuna,Umma jamila,Umma Hafsat da kuma Baba Asabe zazzaune da dukkanin alamu suna tattaunawa akan abinda ya faru ne.
Zaraf Umma Maimuna ta miƙe ta nufe su tana mai cewa,Yauwa Ummien Jaheed,sannu da ƙoƙari kin samu kin shawo kanta ta fito kenan ?".
Cikin girmamawa ta ta bata amsa da cewa," Eh na samu ta fito wai ko ta samu ta ci wani abun ko ya ya yake,tunda ba yanda za ayi mutum ya zauna da yunwa,daga nan sai ta samu ta yi wanka".
"Ai kamata yai ta fara cin abinci in yaso sai tai wankan daga baya kamar zai fi", Cewar Umma Jamila.
Hannun Hibba Ummie Maryam ta ja ta nufi Dining area ɗin da ita ta na mai cewa,"To bari ta fara cin abincin sai tai wankan daga baya".
Wermars ɗin da ke jere akan dinning ɗin ta fara buɗe mata tare da tambayarta me za ta zuba ma ta.
Cikin muryarta wacce ta ke fayyace halin da ta ke a ciki ta bata amsa da cewa," Ki ba ni ruwan Lipton kawai ma ya isa".
Sake baki Ummie Maryam tai ta na kallon ta kafin ta ce da ita,"A'a ba za ki sha ruwan Lipton tsuran shi ba,ina laifin ki in baki Tea ko in haɗa maki Black bhazar Coffee ne,Wanda zai ɗan riƙe mi ki ciki",ta kai ƙarshe zancen ta na mai haɗa mata kakkauran Black bhazar Coffeen ta haɗa mata harda Madara ta miƙa mata ba dan Hibba ta so ba ta amsa ta fara kai shi bakinta tamkar ta na shan magani,nan da nan zufa ta fara tsatstsafo mata ,idanuwanta sun yi ja tamkar hawaye za su zubo daga cikin su.
"Amma Mama Part ɗin Baba Asabe zata koma da zama ko,kafin wannan lamarin ya ɗan yi sauƙi ko ?",Ummie Maryam ta tambaya.
Kasa cewa komi Mama Hadiza tai,sai ma miƙewa da tai ta bar parlour ta nufi hanyar Part ɗin ta ba tare da tace komi ba.
Hakan ya sa jikin su Umma Hafsat yai sanyi,sai Umma Maimuna ce ta fara katse shirin da cewa," Kema ai kin san ba zata furta kalma ko guda ɗaya akan wannan zancen ba,sai dai mu zauna mu yanke abinda ya kamata akan hakan".
Kwalkwal idanun Hibba su kai nan da nan hawaye su ka fara rige-rigen sauka akan fuskarta,da sauri ta kai hannunta saman fuskarta ta na mai share hawayen sakamakon jin hayaniyar shigowar JAHEED yaro ɗan kimani shekara takwas,turus ya ja ya tsaya a tsakiyar Parlour ya na mai rarraba idanunsa akan mutanen da ke cikin falon
Cikin muryar yarinta ya fuskanci Ummie Maryam da tarin tambayoyin da suke a zuciyar shi da kuma ƴar ƙaramar kwakwalwarsa,"Ummie me ya samu Momynah na ga idanunta da hawaye,waye ya bige ta, ko kum ba ta da lafiya ne,ko dai Baba Asabe ce tai ma ta faɗa?".Wacce shigowar Baba Asabe cikin parlour kenan 
"Kai wannan Yaro dama haka ka ke ban sa ni ba,to ta Allah ba ta ka ba,ahir ɗin ka ka kiyaye ni,ta ya zaka kwaso wannan gingimemen sharrin na ka ka ɗora shi a kaina,ban ji ba ban gani ba,to ni Allah na tuba meye nawa a cikin wannan lamarin ai sai dai gani ko hange daga ne sa".
Ko ta kan Baba Asabe bai sa ke bi ba,ya nufi inda Hibba ta ke ya fara share ma ta hawayen da su ke zubo ma ta tare da cewa," Momynah me ya same ki ki faɗa min inji,nima ina jin kamar in yi kuka hawaye sai ƙoƙarin zubo min su ke sakamakon ganin kina kuka,hankalina duk ya tashi ?",
Sai da Hibba ta haɗiye sabon kukan da ya taho ma ta kafin ta ce da shi,"My son ba abinda ya same ni,ba ni da lafiya,idona ke ciwo shiyasa ka ga hawaye na zuba daga cikin".
Sake baki da idanu yai yana kallon idanunna ta da ta ce suna ciwo har ya,na kai hannunsa ya na ɗan taɓa su a hankali  tare da cewa,"To ai Momynah ban ga ciwon ba  ko dai wayo ki ke son yi min ?".
Buɗe baki tai da niyar ba shi amsa ta kasa sakamakon tsananin firgitar da tai na ganin shigowar wanda ta ke jin tsoro ba ta tsaya ba har sai da ta kai ƙarshen jikin bangon Parlourn ta makure ta na mai jiran tsanmanin abinda zai faru.
     Baba ƙarami ne ya shigo,bin ta da Ido kawai ya ke,Zuciyarsa cunkushe da tarin bak`in cikin abun kunyar da ta ke k`ok`arin janyo mu su kai tsaye fuskarta shi ke bayyanar da halin da ya ke a ciki,daga ƙarshe kauda kan shi yai akan ta alamun kamar bai son ya cigabada da kallon ta ya ce da ita,"Ki zo babban Parlour Baba Malam na jiran ki,in kin so za ki iya sake tserewa a karo na biyu".yana kaiwa nan ya bar cikin parlourn.
Hannu bibbiyu Hibba ta ɗora a saman kata tare da fara sakati da sallallami gami da cewa,"Na shiga ukuna yanzu ya zan yi ina zan sa kai na ",duk ta rud`e sai faman tsalle-tsalle ta ke,ta rasa wani abu guda ɗaya mai muhimmanci da ya kamata ta aikata.
Umma Hafsat ce ta riketa gam gami ɗan ɗaga sautin muryarta ta ce da ita,Ke ki natsu mana,wannan ruɗun da tashin hankalin da ki ke ba zai haifar ma ki da ɗa mai Ido ba,gara ki natsu ki tsaya ki fuskanci abinda ke gaban ki,tun da can ba ki san da zuwan wannan ranar ba sai yau ,sai yanzu za ki zo ki tashi hankalinmu ki tashi hankalin ki akan me?".
Baba Asabe ce ta anshe zance da cewa," Yauwa ƴar gari kuma ƴar albarka faɗa mata gaskiya man wata ƙila ta manta ita ce sila kuma ummul'aba'isin faruwar duk abinda ya ke faruwa a cikin Gidannan a yanzu"....
"Haba Baba Asabe bai kamata ku rinƙa faɗar irin wannan kalmomin a irin wannan lokacin ba,ba ku ga halin da ta ke a ciki ba ne ba?".
" Ke ar ja can ba ni wuri,yo Allah na tuba da ke da ita ai duk kanwar ja ce,kwaryar sama ce ke bugun ta ƙasa,ina zargin ma kina da sa hannun cikin faruwar wannan lamarin "....
Umma Jamila ce ta saurin dakatar da batun da cewa," Haba Baba Asabe wannan abinda ki ke bai kamata ba, ku bar mu mu ji da abinda ya ke damun ma na,sai ku tsuro da wani sabon rikicin  da zai sa ke dagula ma na lissafi ".
Hankakin Hibba ba ƙaramin ƙololuwar tashi ya sa ke yi ba,yau gidan su ne a ke wannan hayaniyar,Wanda a tarihin ba ta taɓa jin labari ko ganin iri hakan ta faru ba,duk da kasancewar Gidan na su babban Gida ne,ko Mahaifinta Baba Malam  matan shi huɗu da yara Aishirin da biyar,ba ta taɓa ganin hakan ta faru ba sai yau kuma wai akanta.
Muryar Mahaifiyarta Mama Hadiza ta ji ta na mai bata umarnin akan ta wuce ta je ta amsa kiran da ake ma ta tun kafin ta iskota nan inda ta ke, ranta ya sake ɓaci.
Jikinta ba kwari ,Zuciyarsa sai faman tsananta bugu ta ke ta nufin hanyar Babban Parlourn ,ji tai daga baya an riƙe ƙafafunta,a sanyaye ta waigo domin son ganin waye ya riƙe ta.
Jaheed ne fuskarta shi da hawaye shaɓe-shaɓe ya ce da ita," Momynah zan bi ki,ki tafi da ni,ina so in ba Abbahna haƙuri kar ya yi maki faɗa ko ya bige ki,in ya so ni yai min faɗa,tunda na ga alamun kamar duk sun daina son ki".
Sai da ta share wayen saman fuskarta kafin ta ba shi amsa da cewa"Kar ka damu Yarona ba abinda Abbanka zai yi min yanzun nan zan dawo"...
Cikin yarinta ya fara tsalle ya na direwa tare da cewa shi bai yarda ba sai ya bita,duk irin lallashin da za tai mai ta yi ma shi amma yaƙi amincewa daga ƙarshe sai Ummie Maryam ce ta zo ta ja shi su ka bar wurin ba don ya so ba,ita kuma ta nufi Parlourn wanda ta na shiga ta ji ƙirjin ta yai wani irin matsanacin bugawa ta sake shiga cikin mafi tsananin ruɗuu da tashin hankalin......

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.