Free chapter · Read without an account

9&10

by Aisha Abbakar · SAHAAR

SAHAAR

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.

BY

MOM MUHSEEN

🅿️9&10

ONE YEAR LATER

Shekara guda tazo ta wuce kamar wasa a cikin wannan shekarar guda abubuwa da dama sun faru,masu dad'i da marasa dad'i cikinsu hadda karatuna wanda na fara shi bada jimawa ba,wannan shekarar ta farko nasha wuya mai sunan wuya saboda gaskiyar magana itace kaina bayaja,zan iya cewa ma na mance taya ma ake karatun,tun daga fara daukar lectures na gane banda wayau idan kuma har banyi wasa ba komi na iya faruwa da karatun saboda rashin ganewa ta, na cire kunya girman kai da tsoro na fara neman yadda zanyi na tsira da mutuncina, da farko na saka Jidda gaba na hana mata sakat inhar na dawo gida,bamu da wani abunyi sai wannan karatun duk wasu lectures da aka mana nayi recording nayi jotting,haka zamu tattauna ta wayar mun dai in gane na ganewa in bar na bari,a lokacinne na fahimci cewar karatun dai ba sauk'i bane,dan danan na fara zuk'ewa ina rama a tsaye babban damuwar shine ban iya fahimtar turanci sosai,kamar yadda bazan iya yin dogon sentence mai kyau ba,anan aka lalota daga tushe weekend banda hutu working days ma ban huta ba,Anna tana iya wuni bata ganni ba abinci sai nayi da gaske inci,duk don inajin tsoron cikin aji na wulakanta ko kuma azo jarabawa in kwaso C.O

Jidda tamun namijin kokari Ba kad'an ba,sai kuma tazo tatafi camp hankalina ya tashi sosai har ta fahimta, tace dani "Ba fa a jimawa anayi just 3 weeks ne na fito,amma kafin nan zan ma Hammah UH'AIMID magana shine ke gida time to time sai ki ringa zuwa duk abunda ya shige miki duhu zai baje miki shi har ma fiye dani"

Bance mata komi akai ba amma ni nasan bazan je d'in ba,saboda yanzu wani shan murr yake tashe dashi ko hanyar dana bi baya kallo, inzan gaida shi baya ansawa sai kawae na daina ma gaidashin, tace "Anti Jamila ba bangaren ta karanta ba aida na hadaku,amma duk da haka itama kina zuwa lokaci lokaci kina zama da ita kuna aikin tare"

A raina nace gara-gara ita,a haka tatafi tabarni cikin damuwa,rannan zamu C.A hankalina ya tashi na rasa waxan tun kara ya kara mun haske akan abunda zan karanta,duk da nayi iyakar kokarina amma inaso in kara fahimta sosai, yammacin lahadi ne gobe monday zamuyi C.A d'in sai na wuce cikin gidan wajen Anti Jamila, Oga Fauzan yayi tafia kwana kin nan baya zaune,amma yana kirana a sabuwar wayar daya siya mun kafin ya tafi,mu gaisa sosai ya tambayeni ko akwai matsala ince masa komi lafia,daga haka sai muyi sallama.

Baya tsallaken kwana biyu bai kirani ba,Ina jin dad'in kulawarsa gashi baida girman kai a natse yake komin sa cikin natsuwa, karka had'a da wasu banda fad'in rai na gado ba abunda aka iya.

Tura k'ofar dakin nata nayi naga bata nan,na fito ina saukowa daga stairs d'in,Wata Laraba mai cikin masu aikin take itama tace mun, "Yawwa daman Jamila ke neman ki tana lambu,tace kitai da kayan karatunki"

Dad'i ya kamaani daman kuma tare dasu nake,nai maza na bi ta wata hanya da zata sadani da can bayan gidan,inda lambun yake shuke shuke ne masu kyau a wajen,ga ni'ima wurin da kamshin itatuwa ga tsuntsaye suna shawagi suna kuka mai dad'i, inbacin kar in zak'e da babu inda zan ringa zaka ina karatu sai can,to ina ta taka tsan tsan da komi saboda gudan wulakancin uwargida,wadda har yanzu bata hkr da karatun da nake ba a cewar ta kaskantatta irina bata dace da karatu ba.

Ina ta tunani na har na iso wajen, Ina isowa na fahimci ba ita d'aya bace saboda ga laptop d'in Oga Uhaimid nan bud'e da wasu takaddu sai mug d'in coffee,ita kuma tana kishingid'e tana danna wayarta.

"Ya kika toge nan,karaso nan"

Kafafuna kamar ba zasu iya isar dani ba na isa na tsaya gefe, "Anti Jamila Laraba tace.......iskar dana zuk'a ta hancina ya iso mun da tabbacin yana tafe a wajen,kamshin sa shine ID card d'in sa na nuna cewar shine a tafe, shiru nai na had'iye maganata.

"Zoki zauna, muga kayan karatun tukunna Uhai yana available duk abunda ya shige miki dubu zai baje miki shi,Jidda mukai waya dazun tace kuna da C.A in taimaka miki"

Yak'e nayi Ina cewa, "Ai daman karatun nake kika kirani,"

Zama yai ya cigaba da abunda yake, na had'iye abu a wuyana nace "Oga U'haimid ina wuni"

Wani dak'ik'in kallo ya watso mun, ya cigaba da aikin sa hankali kwance, Anti Jamila tace "Uh'ai Sahaar na gaidaka"

"Ta rik'e kayanta bana so"

Ta kallan tana cewa, "kin masa laifi ko?"

Girgiza mata kaina nayi,ta jawo hannuna muka zauna inda take shi kuma yana gabanmu muna facing d'insa, "Mugani kayan katatun"

Ta ansa tana dubawa harda wadanda na rubuta da kaina abubuwan dana karanta daga jiya zuwa yau, tace "Da kyau Sahaar da alamun dai zaki dage sosai,amma akwai gyararraki cikin nan bari ya gama sai ya miki, Ina dawowa"

Tatashi tabarni dagani sai shi a wajen,jinai kamar ina cikin keji tare da zaki ko kura na kame jikina waje guda ko motsin kirki na kasa, kusan minty goma da barin ta wajen naji yace, "Ina shi Ogan naki?"

Dago kaina nai ina kallon shi, ya sakar mun harara na maida kan k'asa bance komi ba, "Halan baki da baki?"

"Aa kayi hkr"

"Ina shi Ogan naki?"

Ina wasa da biron hannuna nace a sanyaye, "Yayi tafia inji Jidda"

Wani dan iskan murmushi yai yana ta danna laptop d'insa da yatsa d'aya kamar baya so, "shiyasa kike neman mai koya miki karatu?miyasa shi bazai tsaya ya koyar dake ba tunda shine ya dauki nauyin ilimin?"

Har raina mgnr ta tsayan a zuciya, na runtse idona kamar na yab'a masa bakar magana,amma nasan bazan shaa ba, sai na zab'i da inyi shiru kawae na matsu ta dawo kila in tsira daga wadannan tambayoyin da bakaken maganganun nashi........"Saboda kin samu daurin gindi har kinyi kaurin wuyan da baki iya gaidani ko"

Girgiza kaina nayi kamar k'adangare, "Kayi hkr,naga idan na gaisheka baka ansawa.........yaushe kika gaidanin ban ansa ba,kenan ma karya nake ko?"

"Aa wallahi,bana nufin karya kake amma wallahi nasha gaidaka baka ansawa"

"Naji,amma yanzu bazan miki wani karatu ba sai radda kika gaidani na ansa,tunda bana ansawa in kin gaidanin"

Nai shiru kamar in tashi ince to nagode,amma nasan magana ya fada mun don yaji mi zance, "kinji ai ko?"

Na kalleshi kad'an nace "To kayi hkr zan gyara"

"Yaushe?"

Ya fada yana tsareni da idanu, "Daga yau"

"Ohk to inajinki fara daga yau d'in"

Ni dariya ma yaso bani amma banyi ba, kaina kasa a hankali can ciki nace "Ina wuni Oga Uhamid"

"Ni bana jin abunda kike fad'a,speak louder"

Na sake fad'in, "Ina wuni Oga Uhamid"

"Waye yace miki Uhamid sunana?"

Ya salam,wannan mutum da azaba yake, "To ya zance?"

Karkace kai yayi yana kallona har na d'an sauke kaina k'asa, sannan yace "kije ki tambayo"

Sai na yunk'ura zan tashi, yace "Not now,zauna"

Na zauna ya gama iyayinsa sannan ya ce na bashi ya gani, hand out da sauran su na aje masa, ya jima yana dubawa kafun ya kalleni inata luliyar biro, "Ashe da rabon za'a kab'oki karon farko"

Gabana ya fad'i sosai,yanzu fa Anti Jamila ta yaba mun amma shi yana cewa za'a kadani, "Wlh Ina bakin kokarina"

"A hakan?"

Ya fad'a yana tusa takaddun yana kallo, kafun ha duban sosai yace "Kallan ni nan"

Na d'ago ina kallon fuskar shi, "Inhar kina son kiyi achieving goals naki saikin canza tsarin karatunki,makarantar da kike bata son wasa zak'wak'wuranci take so da zafin nama,duk wannan wasan kwaikwayone idan exam d'inki tazo ta semester d'in nan,"

Maganarsa ta ratsani kuma tabbas Jidda tana gaya mun cewar mkrntar dole ma ka iya karatu dole ka dage, ban sake tabbatarwa ba sai yanzu,jikina yai sanyi sosai kaina k'asa duk nayi la'asar, cikin sanyin jiki dana murya nace "Ina ta bakin kokarina wallahi"

Har cikin ranshi yaji ta bashi tausayi,sai ya gyara zamanshi yana kallona cikin taushin murya da yakan jima baimun mgn da ita ba yace,

"Zainab"

Kallon sa nayi sosai da mamakin jin ainahin sunana bakin sa,banda haka ma ban tab'a jin ya anbaci sunana ba na boyon da na zahirin sai yau, "Kina so ki koyi yadda zaki iya karatu?"

Cikin sauri na jinjina masa kai, "Eh Ina so"

"Ohk,zan koya miki amma da sharad'i"

D'an fiddo idona nai ina kallon shi, "Bari kallona haka"

Na sauke kaina k'asa bance komi ba, "Kin yarda zaki biyani idan na koya miki?"

"Oga Uhamid......U'HAIMID" ya katseni da fad'i exact yadda sunan yake, na jinjina kai Ina cewa "Banda abun biyanka a yanzu,amma ka fad'i koma miye zan kokari in tara"

Dariya ma ta bashi sai ya gimtse bai ba, yace "aje mgnr pending we talk later"

Nan take naga sauyin salon karatu daga irin wanda nakeyi har wanda Jidda ke mun,jikina ya kara sanyi saboda abun bana ragwaye bane,sai na natsu sosai natsuwar da zan iya cewa babu malamin da nake ma ita sai shi,natsuwar da ko gaban Anna bana yinta sai idan salla nake ina gaida ubangijina, Anti Jamila bata dawo wajen ba sai daf magariba, fruit ta aje masa tana zama a wajen tana taya mu,kusan ma da ita akai ta darasin, cikin abunda bazai gaza awa biyu ba naji kwakwalwata tana chaji sosai,zuciyata tana samun karfi da kuma kwarin guiwa,ban tab'a tunanin zan samu irin wannan saukin daukar karatun ba,sai gashi naje nayi C.A lafia lau cikin question biyar na ansa hud'u naci uku na fad'i biyu,ni a haka murna nake na dawo Ina gaya ma Anna da murnata, itama taita tayani tana sake cewa in dage sosai,saidai tsoro da fargaban fad'anta yasa na kasa gaya mata kokarin Oga Uhamid akaina,da kuma alkawarin cewar zai zama malamina akodayaushe kuma a ko ina.

Daman munyi dashi kullum karfe tara zamu na zama can lambu,weekend kuma da yamma bayan munci abincin dare nida Humaira nake gaya mata yadda mukai dashi jiya, tace "Don Allah karki bashi kunya mutanan nan suna sonki sosai,suna nufinki da alkairi kidage sosai Sahaar"

"Insha Allah zan ba marad'a kunya Humaira,saidai ban San miyasa yakejin haushina akan taimakon Oga Fauzan ba"

Murmushi tayi tace "kedai ki fuskanci abunda ke gabanki,koma miye watarana zakiji"

To na bita dashi saboda ban fahimci maganarta ba,na tafi wurin na zauna jiransa ba dad'ewa sai gasu shida Anti Jamila,Hannuwan su had'e dana juna suna tahowa cikin takun su mai kyau,suna kama sosai kuma sun dace da juna,wannan dad'ad'iyar kauna ce tun ba yanzu ba zan iya cewa nidai haka na wayi gari na gansu suna son junan su sosai,ko ina suna tare kuma duk inda zasu tare sai idan wajen aikine,shima baka rabasu a waya,Ina ta tunani har suka iso wajen.

"Sahaar naga fuskarki da fara'a miye labari?"

Na saki murmushi sosai nace "Anti naci C.A d'ina anyi ta over ten naci six"

"What!"

Naji ya fad'a da d'an sauti yana kallona, fizgar takaddar yai yana kallo yana gama wa ya tillo mun abuna, ranshi ya b'aci ainun yace "Kina nufin duk whlr dana sha jiya sakamakon kenan?to bazan whlr banza wlh"

Ya juya fuuuu zai bar wajen,hankalina ya tashi sosai Anti Jamila tai saurin rik'oshi tana cewa, "Come down Baby,ka yaba mata ko yayane sai ta kara dagewa.......karma ta dage wlh bazan tsaya ina bata lokacina ba,kinsan awa nawa muka dauka da ita jiya kawae akan darasi d'aya?"

"Duk da haka ai ba zaka had'a kwalwarka da tata ba,kayi hkr pls"

Hawaye suka zubo mun na takaicin kaina,tabbas awannin da muka kwashe jiyan yaci ace na cinye ma C.A d'in,jikina yai sanyi zuciyata ta karye matuk'a sai na kama kuka kaina cikin guiwata,saboda kawae na sadakar bazan iya wannan karatun ba,banda kokarin da zan iya yin jami'a, sassauta fad'an yai jin ina kuka Anti tace "kagani ko,ba dad'i sai ka karye mata kwarin guiwarta"

Shiru yai yana zama cikin kujerun dake wajen, ta shiga lallashina tana ban baki har na hakura da kukan, tace "wanke fuskarki ki natsu ki saurareshi"

Naje ga famfo na wanke fuskar sosai na dawo na zauna inata sauke ajiyar zuciya, ba wanda yace komi cikin mu tsawon lokaci,sannan yace "dole fa ki fuskanci abunda ke gabanki,dole saikin zabure,dolene ki tsaya tsayin daka ki fahimta kuma ki gane abunda nake doraki akai,inba haka ba ni gaskiya zan hkr da koya miki karshe a koroki ni ba ruwana,bani kika ba kunya ba wanda ya saki mkrnta shikika kunyata"

Kwalla ta cika idona nace da rawar murya, "kayi hkr Oga Uhamid,zan dage"

Lumshe idonsa yai sautin muryar ta mai karkarwa ya ratsa masa kunne, yaji wani abu ya soke shi amma na dake yana cewa, "Da yafi"

Bamu tashi ba ranar sai shabiyu ko bacci ka banaji kwata-kwata,don jinai ya mun wata allurar zaburarwa,har muka rabu raina ba dad'i saboda ina ganin kamar na kunyata shi.

*********

Daga wannan rana na ban kuma yadda na fad'i ba,duk abunda zai koya mun saina tabbatar ya zauna daram a kaina,sannan tun daga lokacin duk wani malami dazai lecture na daina fargaba, zan iya gane duk wani turanci dazai har ya fita,nima ina jefa nawa inhar presentation ya taso na cire tsoro kunya da fargaba,karatun nake baji ba gani wannan ne ya jawo wata irin shak'uwa tsakanina dashi,ba kuma shak'uwa ta fira ko labari ba,aa shak'uwa ta sakewa in Ina gabansa sabanin da banda sukuni saboda yar tsamar dake tsakanin mu,har takai zai iya fahimtar kuzarina ina da lafia ko akasin hakan,kuma yana gane miye yake damuna more especially idan Mp d'ina ya taho,sai kurin inga ya siyo allura ya taho mun da ita,kuma yayi mani a cinya ba tare dana bud'e jikina ba,har Jidda ta dawo shima Oga Fauzan ya dawo daga tafia da yai kan harkar kasuwancin su.

Lokacin saura kwana kad'an mu fara jarabawar semester farko,alhamdulillah zuwa yanzu komi ya soma zuwa mun da sauk'i,amma duk da haka ban daina daukar karatu daga Oga U'HAIMID ba,abunda na fahimta tun dawowar Oga Fauzan shine wani miskilanci U'haimid ya dawo dashi fiye dana baya,har gabana yakan fad'i idan Oga Fauzan ya kirani suna tare ji nake kamar in zura aguje,rannan yace na kawo masa takadduna yagani da C.A din da mukai ya gani,suna tare a falon Ammi firar kasuwanci suke kamar akwai share na Yallab'ai da U'haimid cikin kasuwar su Oga Fauzan shiyasa nake yawan jin suna tattaunawa akai.

Ya yaba sosai ba kamar yaga duk tambayar da ya mun ina bashi ansa sosai, yace "Dole na miki kyauta mai tsoka don ki kara maida hankali,amma waye da wannan kokarin Sahaara?"

Na danyi murmushi na dago zan bude bakina,muka hada ido dashi wani kallon kashedi daya mun sai na hadiye mgnr, nace "Jidda da Anti"

"Aiko sun kyauta,amma na dauka Hamman ku zai shige miki gaba tunda ya tab'ayin course d'in,"

Shiru nai bance komi ba, ya sake cewa "Bro ka ringa kama mata pls"

Wayarsa ya ke dannawa baice uffan ba,Oga Fauzan yace "ki ce ma Anna da Yamma zamu fita dani dake da Jidda kuyo siyayyar duk abunda kuke buk'ata"

"To zan gaya mata angode.......shiiiit,karna sakejin godiya kiyi mun addua kawae"

"Allah ya biya maka dukkan buk'atun ka Oga fauzan"

Yai murmushi yace "To amin nagode"

Daga haka na fice daga falon Ammin har ina hard'ewa,wajen Humaira na fara tsayawa nake gaya mata, Tace "Masha Allah,Allah ya biyasa da aljannah amma anya wannan d'awainiyar kuwa Sahaar?"

Na yatsina fuskana nace "Ban gane ba?"

Dariya tayi tace "Aa ba komi Allah jishemu alkairi"

Kafin Anna tabarni saida tai ta kafa mun dokoki,har raina ya b'aci na cire doguwar riga abaya dana sanya nace na fasa zuwa sutai kawae, daker ta shawo kaina na tafi ni bansan tsoron da take ba, bana jin a raina Oga Fauzan zai cutar dani,U'haimid kan shi da muke samun sab'ani bana masa wannan zargin,dukda cewa bansan miye a ransu game Dani d'in ba.

Ova U'haimid ke jan motar shi yana gaba nida Jidda Anti Jamila muna baya, time to time nida ke tsayarsu mukan had'a ido dashi ta madubin tsakiyar motar, har gobe ina mamakin kalar idonsa idan ransa a bace yake suna canza wa sosai,sai nake ganin sunfi kyau ma idan ransa ya b'aci,uffan baya cewa cikin firar Jidda da Oga Fauzan Anti Jamila ma kadan kadan take sa baki,nima shirun shine abunda naga yafi mun nida ba yar gida baa.

Har mukayo siyayyar muka dawo uffan banji wanda yace ma komi ba,sai Oga Fauzan da Anti Jamila shima ba wata doguwar mgn bace, munsha kaya sosai Jidda ta zab'armun duk abunda ta dauka shi ta daukar mun, Anna taje ta Masa godiya har da Ammi.

"Hadiza ai Sahaar qanwar sa ce,duk abunda ya mata kamar nauyin ne ya sauke ki daina damun kanki da sai kin gode mana,amma ban hana ki masa addua ba"

Duk yadda naso zuwa daukar karatu wajen sa ya hana mun damar,idan naje inda yake zama sai yace aiki yake har rannan na iske shi dakin sa,yana bud'e k'ofar na ganshi daga shi sai towel ai ban san sadda na b'acewa ganinsa ba, daga ranar na hkr na ringa yi nida Jidda in tana free har muka fara exam,lokacin ne Yallab'ai yace Oga Fauzan ya fiddo mata a sanya auren shi shida Oga Uhaimid.

Mom muhsen✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.