Free chapter · Read without an account

19&20

by Aisha Abbakar · SAHAAR

*_SAHAAR_*

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.

BY

MOM MUHSEEN

🅿️.....19&20

Wannan kalmar tashi ta karshe ta dabaibaye mun zuciya babu second ko awa dazai wuce bata zo a raina ba, wai MATAR AHMAD to uban waye ahmad d'in?ganin nai tunani na niyyar zautar dani dole nai watsi da duk abunda ya shafe sa na cigaba da karatuna, bayan kwana biyu Hamma F yazo office din wani malamin mu na iske shi nida Feedo muka je,bayan sun gaisa ne tace Bari ta jirani waje, bayan fitar ta ne ya tsura mun ido sosai har na tsargu na sadda kaina nace, "Hamma Ko nayi maka wani laifin ne?"

Girgiza kanshi yai yana cewa, "Kina kokarin yi dai,naga kin rame duk karatunne haka?"

Murmushi nayi nace "Kasani ai Hamma"

"Duk da haka bai kamata ki rame haka ba,kamar wadda ke cikin damuwa"

Kallonshi nai shima d'in kamar ya fad'a, fuskar sa ba walwala sosai, nace "Ban da damuwa Hamma komi nakeso kana yi mun har ma wanda bance inaso ba,amma kaima ai ka rame d'in kuma ban saba ganin fuskar ka haka ba"

Relaxing bayansa yai yana kara narke fuskar sa, "Banda natsuwa ne kwata kwata Sahaar"

Sai naji gabana ya fad'i,nace "Hamma miye yake damunka,dazun daman kace wai Ina niyya maka laifi saboda me to?"

Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa, "Kina boye mun wani abu ne,wanda ya kamata na sani sannan ayyuka sun mun yawa company banda lokaci sosai,ko abinci sai nayi dagaske nake ci,shiyasa na rame"

Na sauke numfashi a hankali ina wasa da yan yatsuna, kamar bazan ce komi ba sai kuma na dago naga yana kallona, "Hamma kayi hkr pls"

Yatsina fuskar sa yai yana cewa calmly, "Why are u saying that?"

"Naji kace ina boye ma wani abune,sannan baka samun huta da sauran su shiyasa nace kayakuri"

Siririn murmushi yai yace "to ai dole nayi aiki kinga mgnr inyi hkr bata taso ba,hkr ya zama dole kawae mataimaki Zan nema shine kawae,"

"Sannan ai kema kinsan kina boye mun abun ko?"

Shiru nayi bance komi ba,shima yai shirun zuwa can yace "Ko zaki zama mataimakiya ta?"

Zaro idona nai "Wace ni Hamma ai bankai ba wallahi"

"Aiko kin kai kuma zaki gani bada jimawa ba"

Na b'ata raina "Aa nidai bana so"

Ya d'an zaro idonshi yace "ba kya so?"

Rufe bakina nai Ina murmushi "To na yafe nake nufi..........wayata dake cikin jikka ta dauki ruri,wata fad'uwar gaba ta sameni,jikina yai sanyi na kasa ma fiddo wayar inajin kuma yana kallona da idanunsa masu kaifi, "Ki dauki kiran mana"

Girgiza kaina nayi "Aa......Ai....ba....ba wayana bane na Feedo ne"

Murmushi yai yace "to ki je ki kai mata mana"

Na mik'e da sauri na fita daga office din,tana can cikin wata brander na mik'a mata jikkata, "ki dauka kice bana kusa,wlh in Uhaimid mayene da yanzu babu sauran Sahaar"

Me feedo zatai ba dariya ba, tace "Karfa a samu matsala"

Ina tafiya nace "matsalarsa ce wannan"

Duk kuma da nasan cewar ni nafi kowa shiga matsala indai Oga Uhamid ne,

Ina shiga na ganshi ya d'age kanshi sama idanun lumshe, na zauna Ina cewa "Hamma baka da lafia ne?"

Bude idanun yai yana kallona dasu sun lumshe sosai sun sauya launin su, muryarsa ba kuzari tayi sanyi yace "Banda lafia Sahaar"

"Kaje asibiti mana,ba kyau zama da ciwo Hamma"

Guntun murmushi yai yana cewa, "to zaki rakani a dubani?"

Gabana ya fad'i sosai nace "Ai kagani yanzu yamma tayi kuma......ba zaki rakani ba kawae zakice"

Girgiza kaina nayi nace "To kayi hkr muje d'in"

Koda muka fito naje nace ma Feedo, "ki kashe wayar nan don Allah karma ya dameki,Zan raka Hamma F asibiti"

Tace "Adawo lfy amma Ina jiye miki fitinar wannan Ogan naki"

Koda muka dauki hanya tukinma kamar bayaso haka yakeyi,munyi shiru mu dukan kowa da kalar tunanin da yake a ransa, hankalina bai tashi ba saida naganmu cikin asibitinsu,zuciyata ta soma bugawa da sauri da sauri nace "Hamma Ko na jiraka a mota"

"No,miye amfanin rakiyar to?"

Kafafuna kamar zasu kayar dani,tsoron mizaije ya dawo nakeyi zuwa yanzu Oga Uhamid lamarinsa tsoro yake bani matuk'a,Office d'insa muka je zuwa lokacin KO ina najikina tsuma yake,lokaci zuwa lokaci yana kallona sosai kamar yana son fahimtar wani abu, baya cikin office din sai ya kirasa a waya, ba a dauki dogon lokaci ba sai gashi ya shigo,bai ma kula dani ba ya shigo yana cewa, "Wannan zuwan fa?Ina haramar tashi ma"

Kalloni Hamma yai ganin na gaza natsuwa waje d'aya sai juye juye nake cikin kujerar, Ina ta tsifar yatsuna naji yace "Sahaar tace nazo asibiti a dubani banda lafia..........Kutumar uba!!! Idanuna na xaxxaro waje Ina kallon shi jin abunda yace, ahankali ya jiyo yana xuba mun idanunsa,sosai naga wani abu lokaci guda tatttare dashi amma cikin yan seconds komi ya b'ace, sai ya fad'ad'a murmushinsa yace "Kai yanxu sai wata tace maka kaxo a duba ka,to kaida ita waye ciwon yafi damunsa?"

Langab'ewa yai cikin kujerar dake gaban table d'insa yana cewa, "I think ta fini damuwa da ciwon,tunda ita ta matsa muzo a dubani ko Sahaar?"

Ihune kawae ban kurma ba,saboda na gama fahimtar miye yakeson isarwa,Hamma so yake kawae na mutu a wajen,miyakeso ince? Eh ko Aa? Wlh banda wannan ansar,tashin hankalin dake zuciyata kad'ai ya isan.

"To waye zai mun bayanin ciwon,insan abunda Zan iya maka"

Uhaimid ya fad'a yana bud'e laptop d'insa hankali kwance yana daddannawa, "Ai ba zata iya mgn ba kunya takeji"

Mik'ewa nai nace "Hamma bari najiraka a mota"

Ban saurari meye zaice ba na wuce k'ofa kawai,amma kafin in fice naji muryarsa cikin kunnena, "Da dai kin dawo Hajia,Ina xakije bacin kin kawo mun patient,kuma ga dukkan alamu kece ciwon nashi"

Saurin girgixa kaina nayi suna neman d'imautani, "Aa ko d'aya ni kawae na rakoshi ne,banda alak'a da rashin lafiyar sa Shima kuma ya san hakan"

Na fice daga office din har ina had'e hanya,wlh bacin banda ko a si ga hannuna baxan jira shi ba,miye ma'anar wannan abun?ya suke neman su maidani yar Teddy wasan yara?kwalla ta cika idona "Ya suke so inyi ne wai?"

Cigaba yai dadaddana laptop d'insa zaka rantse har ga Allah yana yin fuskar sa haka abun yake har cikin zuciyarsa, babu wata alamar damuwa ko bacin rai akan kyakkyawar fuskar sa,tunda ta fita ba wanda ya sake magana cikin su,saida Fauzan ya gaji da shirun yace "Kamun Bp pls"

Bai ce komi ba ya tashi ya dauko abun awon ya zauna yana mashi,cikin yan mintoci yacire yace "Normal"

"But inajin ciwon kai,kirjina yana zafi zafi"

"May be ulcer ne"

Uhaimid ya fad'a cikin basarwa, "Bari na rubuta allura sai a maka"

"No barshi inkazo gida saika mun ka taho da ita........bazan dawo da wuri ba da ka tsaya kawae na maka"

"Yanzu kace kana shirin tashi fa" Fauzan ya fad'a yana kallon shi da son fahimtar wani abun, "I'm forget ina da bakon da xai zo nan da minti talatin"

Kira yai ya bada aka anso allurar yai masa sannan ya bashi wani maganin,har yakai k'ofa zai fita Uhaimid yace "I advise u ka ringa cin abinci, sannan kabar neman abunda babushi"

Jujjuya maganar yai a ranshi sai ya juyo yana cewa, "Thank you bros, kaima ina baka shawara ka daina Hidden d'in abu yana da illatarwa"

Daga haka ya fice daga office d'insa,yana jin wani iri a ransa ya gama fahimtar komi,yanzu neman mafita kawae shine ya rage masa bazai sanya ba sai yaga abunda ya turewa buzu nad'i,har muka iso makaranta ni dashi ba mai magana,na masa sallama na wuce Hostel abuna.

Wannan daren yadda yaga rana haka ya ganshi,idanunsa sun soye kamar soyayyar amaro ko ruwa ya kasajin zai wuce ta halshensa balle ya ratsa ta mak'oshinsa ya jik'ashi saboda bushewar da yai, shi za'a azo har office d'insa a ci masa fuska? Suzo har gabanshi su nuna masa iyakarsa,shin wai miye tattare da yarinyar da har yakejin wannan bala'in akanta, bazai iya tuna rana ko lokacin da wanna masifar ta same ba,abunda ya sani shine tun tana kwaila bata da komi jikinya ya samu kanshi da jin tsananin tausayinta,yana jin tashin hankali idan yaga Mommy ta sata kuka har hakan ya hadda sa masa rashin cin komi a wuni,wannan abunne yake girma kullin safia baisan kuma dalilin girman nashi ba,a lokacin da yake niyyar aure da wacce kowa yake kallon itace DUNIYARSA, taya zai iya watsama Jamila kasa a ido,wacce taso shi tun suna yara mitsi mitsi komi nashi ita ke masa daga assignment homework da duk abunda na whl ne ita keyi masa, tun jamila bata tafasa ba take fad'in UHAI NE MIJINA MOMMY wannan mgnr itace ta girma cikin zuciyar Mommy kuma ta dasa masa hakan a zuciyarsa,saboda kullum fad'i take baka da mata sai Jamila AHMAD, ita ce wadda zata bauta maka ta soka so na Allah ba zalinci ko cutarwa acikinsa,kullum k'ara cusa masa ita take har wata zuciyar ta ansa tayin saboda samun farin cikin dukan sun,kwatsam k'addara ta jefo musu SAHAAR cikin gidansu gashinan tana niyyar farrak'a tsakaninsa da d'an uwansa wanda ba a tab'a jin kansu ba tun suna yara, Duk abun Mommyn shi bai yarda ta shiga tsakaninsa dashi ba,haka Ammi yana mutuntata yana bata girma sosai,shin idan har ya bari SOYAYYAR yar aiki tayi galaba kanshi ta farraka musu zumunci yayi adalci kuwa? Fauzan bashida ko budurwa hasalima ana tsokanarsa da cewa tsoron yan mata yake,shima yasha fad'a masa hakan saidai yai dariya yace in lokaci yayi zayi budurwa a huce masa gori,sai kuma Allah ya jarance sa da son abunda ya girma yana sonshi shima,kuma har ana shirin aurensa amma hankalinsa tunaninsa yana kanta,miyasa bazai iya barwa Fauzan ba???

Wadannan tunanu kan sune suka faurauci baccin sa natsuwarsa da kwanciyar hankalinsa,ya kwana baiyyi bacci ba don samo ma kanshi mafita,jinta yake kamar ranshi koya yayi tunanin hkr da ita yabar masa sai yaji wata guguwar tashin hankali tana samun shi,kanshi ya sara masa yaji yana masa wani irin ciwo,a haka ya kwana cikin asibitin ya wayi gari bayan ya samar ma kanshi mafita wadda aganinsa itace alkairi.

*******

Sati guda bayan nan muka kammala exams d'inmu hankali kwance, har lokacin Anna bata dawo ba nai mugun matsuwa ta dawo, ranar da muka gama exam d'in jinai kamar kar in koma gidan,saboda shirun Uhaimid ba yana nufin shirune na lafia ba,wlh har cikin kashin raina nasan akwai wata a k'asa,sannan shima Hamma F bai sake zuwa ba bai kuma kira ni ta wayar feedo ba,ni da zasu cigaba da hakan xanfi samun natsuwa,duk sadda na tuna zuwanmu asibitin nan da Hamma F hankalina yana tashi, haka na dawo gida cikin zullumi da tunanin mizai biyo baya.

Anshiga hidimar biki ka'in na na'in ko da wasa ban sanya Oga Uhaimid idona ba,kuma yana gidan har aiki yana zuwa kasancewar Anna bata nan yawancin ayyukanta duk kaina suka dawo,duk yadda Ammi taso janyeni wajenta Uwargida ta tare hanyar gudun rigima da zubar da girma yasa Ammi ta sanya mata ido,haka nakeyin aiki kamar jakka idan na kwanta bayana kamar zai balle saboda ciwo, kuma asuba nayi zan tashi nida sake Kai kafad'ata k'asa kuma sai wani daren,ga aike kasuwa indai za'ai aike uwargida bata tausaya mun tace ni zanje,kuma mashin zanje inhau ga driver ta hana ya kaini,saboda tana so ta nuna ma yan uwanta da sukazo nidin baiwarta ce haka zatai ta wulakanta mu nida su Humaira,tana zaginmu tana kiranmu gidadawa.

Abun ya zamar mana jiki haka muke kullum,ranan Anna ta dawo farin ciki kamar me jinai duk damuwata ta yaye, ranar muka kwana tana bani kabarin can gida da taje.

Anti jamila da qawayenta nan dakunan k'asa suke ta hidimarsu,an shirya event Kala Kala da yake Jidda na makale dani komi ake ciki saitazo ta bani labari,an fitar da anko kala biyar Jidda tace Ammi duk tayi mana nida ita, "Haba dai ni inata aiki ina zanga lokacin saka anko,aida Ammi bata wahalar da kanta ba"

"Wlh indai aka fara event dole sai kinje ai Daddy ya hana a sanya ki aiki irin haka"

Saidai in girgiza Kai kawae saboda banson in fadi wani abu na daban,kullum tana tare damu a kitchen ko can baya inda muke aiki, ko bayan magariba dakin Humaira acan muke firar.

Anyi kwallon amarya da ango a ranar ne zance na sashi idona tun waccen ranar,amma baima nuna yagannin ba har aka tashi,sannan akayi fulani day a ranar ne muka had'u da Hamma f, shine ma ya dawo damu gida nida Jidda,yana ta janmu da fira kamar komi bai faru ba,bayan ya sauke mu sai ya tsayar dani yace "Sahaar baki tausayina ko?"

Na sunkuyar da kaina Jidda ta kalleni ta kalleshi sai ta kumshe dariyar ta tace, "Hamma banfa tafia ba"

Dak'uwa yai mata yace "lab'e kike mun?xan sab'a miki Jidda"

Ta hade hannunta alamun ban hkr, "Allah ya huci ran Hamma na, Sahaar ki tausaya masa ke kam.........ganin zai biyota yasa ta watsa aguje tana dariya,har nima ta bani dariyar sanye nake da kayan fulanin wanda kowa ya ganni saiya tanka,saboda yadda suka mun kyau ainun daman kuma fulanin ce ziryan ba sirki.

"Kinga yadda kikai ma kayan nan kyau kuwa?"

Kunya naji saboda babu mayafi jikina,aboye jidda ta jani mukaje ban sanar da Anna ba don hanani zatai, "Har yanzu rashin lfy nake ban warke ba,"

Bakina nauyi yayi mun na kasa cewa komi,salon da yake mani magana dashi yau ya girmi tunani na, "Pls kice wani abu........saiga motar OGA UHAIMID nan ta tsaya daidai inda muke, dan danan naji hankalina ya tashi,kamar in zura aguje na daskare tsaye gaban motar Hamma F ya sani gaba da idanunsa suna huda fatar jikina, shida Anti Jamila ne suka fito ta zagayo tana rik'e da hannunsa,sunyi kyau sosai sbd duk cikinsu ba wanda bayaji da kyanshi saboda duk jini daya ne, kunya tsoro fargaba suka dabaibaye ni sadda Anti Jamila ke cewa "Sahaar keda Fauzan ne anan?"

Bakina na rawa nace "Sak'o zai bani Anti"

Shi kau kamar baya ganin mu,wuce mu kawae yai baice mana uffan ba, bayan sun shige ya kallan yana cewa "Tsoron miye kikeji don angamu tare?"

Girgiza kaina nayi nace "Hamma kowa zai zargi akwai wata alak'a tsakanina dakai,bacin kuma.........kallon dayake mun yasa nai kasa da idona inajin nauyin mgnr, "Bacin kuma babu komi tsakaninmu ko?"

Na daga masa kaina da sauri, "Ke kike ganin ba komi,amma ni nasan akwai komin"

"Hamma zanje ciki Anna bata san na fita ba," duk don in dakatar dashi daga fad'in wani abu........idan ma kin tsere yanzu,next time bazaki tsere mun ba daman kinyi mani alkawari zaki ban labarin matar BAffanki"

"Watarana zan baka Hamma saida safe"

Nai saurin barin wajen zuwa dakin Anna.

*******

Atakaice dai har aka kammala hidimar biki mgn ta fatar baki bata kara had'ani dashi ba,tun ina dojewa haduwa dashi saboda gudun abunda xai faru har na sake jikina,saboda dai naga kamar babu wani abu da yai niyya yi mani,tunda har dakinsa zanje Inkai masa abinci kalmar tak bata fita bakinsa akaina har in fito,haka zalika akwae radda Anti jamila tace in bishi zan anso mata kayanta wajen tela wlh har muka isa na anso ya dawo dani kanan ya wuce inda zaije,ci kanki baice mun ba na samu relief a zuciyata,amma kuma can kasan raina inajin akwae wani abun saboda duk wanda yasan shi ba haka yake ba yanzu, koda bashida sakin fuska amma baya zama sukuku da rashin walwala irin wannan, rannan safiyar daurin aure inaji Baba uwani ta na cewa, "Wannan aure dai kamar dole,ban tunanin Oga Uhaimdi yana son Jamila"

Anna tace "Kedai ba ruwanki idone naki kibar abunda ba ruwanki uwani yafi dadin kallo Allah ya sasanta iyakarta kenan."

A ranar daurin auren ce Hamma F ya tona mun abunda ke cikin zuciyarsa wanda ya kasa hkr ya kasa jurewa, tura takai bango ya sanar dani, bazan mance wanan ranar ba,an dauki Anty don kaita gidanta shi kuma yasa Jidda ta nemo masa ni, yace dole saina shiga anje dani Jidda tace "Hamma motar nan tafi karfina Bari in nemi wata"

Murmushi yace "gara da kika taimakeni jeki maza"

Duk ban fahimta ba har saida tatafi da kanshi ya bud'e mun gaban motar na zauna, ankon wata tsadaddar atamfane jikina anyi mun gown da ita mai masifar kyau,tahau jikina duk wani sirrim kyau ta fiddo mun dashi, duk ya susuce duk inda nayi bina yake da kallo, koda muka dauki hanya sai ya sauya hamyar zuwa gidan amaryar, ya kaini wani guiden kamar wata duniya ce mai ni'ima da tsari an kawata wajen da abubuwan da zasu ba masoya jin dad'i da more soyayyarsu,kuma wurin duk samari da yan mata ne sai wasu mata da miji da yaransu har suka burgeni, drinks aka kawo mana da snacks,nidai ko ruwa jinai bazan iya sha ba duk a rud'e nake, "Sahaar kiban lbrin Matar Baffanki"

Na sadda kaina yayin da yake mik'o mun lemu a cup mai sanyi, "Kayakuri Hamma bazan iya shan komi ba"

Na fada kamar zan masa kuka, "miyasa ba zaki iya sha ba?kina gudun na saka miki wani abu har na cutar.........Wallahi ko kad'an bana tunanin wannan,kawae......kawae dai na takura ne anan d'in"

Ya aje lemun yana rungume hannunsa yace "Shikenan bazan matsa miki ba,kiyi hkr na kawoki nan bada neman izininki ba,anan d'inne nake tunanin yayi daidai kuma ya dace da abunda nake fatan kafuwarsa"

Wlh duk kwane kwanen sa na gama fahimta,kamar ince masa don Allah karka furta komi kabaeshi a ranka,gabana faduwa yake gani nake idan na kwafsa masa fa,idan na kasa bashi abunda yakeso fa?har yanzu bazan iya tantance miye nakeji a raina game dashi ba,ba kuma don baikai ba hasalima duk wacce tai sa'ar samun shi dole a taya ta murna,haka duk wadda ta rasa samun irinsa ta shimfid'a tabarma azo mata jaje,kawae nid'in ce ban gane miye nake ciki ba,banma san ya akejin so ko soyayyar a zuciya ba.

"Inso samune ki ban lbrinki"

Ya fad'a yana kallona da sanyayyun idanunsa,ta cikinsu kad'ai duk wanda ya kallai zai shaida cewar ya kamu da soyayya, na sunkuyar da kaina ina wasa da yan yatsuna, "Labarina bashida dad'in ji Hamma,bansan miyasa kakeso kaji ba"

"Na fahimci baida dad'in ji d'in tun ranar dana kiraki da zainab kikai kuka,amma inaso inji insan wacece Sahaar,kuma miyasa aka saka miki Sahaar ma'anarsa batai ba,ked"in kinfi gaban Sahaar domin duk wanda ya kalleki zai shaida zubin baiwar kyau da zati da Allah ya miki,suna mai ma'ana kika cancanta dashi"

Kwalla suka ciko idona muryata tayi sanyi sosai ina tuna Inna Sahura wadda naci sunanta na asali watau ZAINAB, "Don dai ka dage amma ban shirya sake tunawa da waccen rayuwar ba Hamma,saboda rayuwa ce ta k'unci da bak'in ciki da rad'ad'in ciwo da bana fatan sake tunawa da ita, amma kafi karfin sanin abu wajena ince maka Aa,don haka zan sanar dakai wacece ZAINAB SAHAAR"

*KUN SHIRYA JIN WACECE SAHAAR? MUJE NEXT PAGE GOBE IN ALLAH YA NUNA MANA*

MOM MUHSEN✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.