Free chapter · Read without an account

BABI NA HUDU – Faɗuwar Asiri a Gida

by Sa’adatu Ahmed · Zuciya Mai Rauni

🖋️ Zuciya Mai Rauni


© Sa’adatu Ahmed (Hamdeyerh)


⸻


🧕🏽 BABI NA HUDU – Faɗuwar Asiri a Gida


“Zuciya bata da lissafi… ta fi kwalkwali saurin amincewa.”


Wata rana da rana ta kusa faduwa, Alhaji Bashir ya dawo gida da fuskar da ke nuna cewa akwai sabon labari mai zafi a cikin zuciyarsa. Yana shigowa falon, ya zauna a babban kujerar fata yana tsaye da hannunsa a cinya.


“Ke Maryam,” ya kira sunana ba tare da kallo ba.


Na tsaya a bakin kofa, hannu a bayana, zuciyata na bugawa da karfi kamar karar guguwa.


“Waye Usman a rayuwarki?” ya tambaya a tsawace, muryarsa cike da izza.


Na runtse ido. Tsawon lokacin da na kwana ina boye wannan soyayyar, ban taba tunanin zai kai nan ba.


“Baba…” na fara, murya na rawa.


“Ki daina yi min karya!” ya dura da tsawa. “Kin raina ni kenan? Kin raina gidan da ya raina ki?”


Hajiya Nafisa ta shigo da sauri daga dakinta, “Don Allah Alhaji… ka saurareta…”


“Na gaji da wannan rainin hankali!” ya ce yana daga murya. “Na ce kar ki kusanci malamin Islamiyya, amma har yanzu kina aika saƙo da wasa da sunan gida! Ina ruwanmu da talakawan mutane?”


“Me talaka yayi wa rayuwa?”

“Ko a cikin soyayya sai an lissafa kudi?”


Na fashe da kuka, na durƙusa a ƙasa. “Wallahi bana da wani buri sai na rayu da wanda zuciyata ta zaba…”


Shiru ya biyo bayan maganata. Sai dai shigowar Hadiza – ‘yar uwar mahaifina – ta girgiza zaman.


“Ni na faɗa masa,” ta ce da murmushin cin fuska. “Ina jin kunya akan irin tarbiyyar da Maryam ke nunawa. Ki ji tsoron Allah!”


Na kalle ta cikin hawaye. “Ke kika haifeni?”


Ta watsa min kallo. “Ba sai na haifeki ba kafin in gaya miki gaskiya.”


⸻


🌑 Daren da Ya Cika da Duhu


A daren nan, babu wanda ya yi bacci. Hajiya Nafisa ta shafe lokaci tana kokarin kwantar da hankali, amma zuciyarta da tawa duk suna karyewa.


“Ki tsaya da zuciya,” ta ce tana shafa bayana. “Wannan ba ƙarshen komai bane. Wata rana zaki gane cewa zuciyar da ta so da gaskiya, ba ta faɗuwa ba.”


⸻


💌 Usman a Gefena


Washegari Amina ta kawo mini sakon Usman.


“Ki tsaya da gaskiyar ki, Maryam. Karki yarda kowa ya kashe miki burinki. In ki na so, to zan tsaya dake har ƙarshen hanya.”


Na fashe da kuka, amma ba na kuka saboda rauni.


Na kuka saboda ina jin ƙarfi ya fara tashi a cikin zuciyata.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol