Free chapter · Read without an account
BABI NA GOMA SHA BIYU – Na Zabi Soyayya
Washegari gari bai gama wayewa ba, sai gaban gidan Alhaji Bashir ya cika da hayaniya. Ango da iyalinsa sun dawo da ’yan tsaronsu da lefe irin na attajirai. Ana shirin ɗaura aure a rana ɗaya, babu biki, babu lokaci, komai a guje.
Maryam tana daki zaune kamar dutse, zuciyarta na bugawa kamar ana buga ganga. Goggo Hajjo na kokarin shiryata da kyar.
“Maryam, ki tsaya lafiya. Wannan ba lokacin kuka bane,” in ji Goggo Hajjo tana kokarin taje mata gashi.
Amma Maryam ta mike tsaye, da idanu cike da hawaye, da zuciya cike da shiri.
“Goggo, da rai nake ciki, amma zuciyata ba raye take ba. Ban yarda da auren nan ba.”
“Amma fa kika ce ki na jira Usman… har yanzu bai zo ba.”
“Zai zo,” ta ce a hankali, tana kallon tagar da rana ke fitowa ta ciki. “Zai zo. Idan har yana sona kamar yadda nake sonsa, zai dawo…”
⸻
🚗 Wanda Aka Jira Ya Iso
A kofar gidan, motar bas ta tsaya. Usman ya fito da jakarsa a kafada, da ƙamshi na karatu da natsuwa. Tunaninshi ya cika da tambayoyi — shin har yanzu Maryam tana jira? Shin har yanzu soyayyarta bata gushe ba?
Ya kalli harabar gidan, sai wani yaro ya ce masa:
“Wai kai ne Usman?”
“Eh.”
“To ana shirin ɗaura auren Maryam yau!”
Idanunsa suka cika da firgici. “Yau?”
“Eh, yanzu haka ana jiranta ta fito.”
Usman bai tsaya ba — ya ruga da gudu zuwa cikin gidan, zuciyarsa kamar ta fashe.
⸻
💔 A Gaban Idan Duka
Maryam ta fito cikin shigar amare, amma idonta ba walwala. Kafin ta karasa, sai ga Usman ya shigo da sauri yana haki.
“Maryam!”
Gaba ɗaya suka juya.
Idon Maryam ya haɗa da nashi. Idon da ya sha wahala. Idon da ya kunshi begen soyayya.
“Don Allah ku dakata!” ya ce da murya mai ƙarfi. “Ba za a ɗaura auren nan ba! Ban zo nan da hannu babu ba!”
Ya zaro wata takarda daga aljihunsa. “Ina da aiki a Zaria yanzu. Kuma zan iya kula da Maryam. Ba da dukiya ba — da ƙauna, da mutunci, da gaskiya.”
⸻
😢 Juyin Halin Mahaifa
Alhaji Bashir ya kalle shi da mamaki. “Wato kai ne Usman?”
“Ni ne. Kuma ko da fatar kujera ce za mu zauna, zan kasance da ita har abada.”
Maryam ta fashe da kuka. Ta gudu ta rungume Usman. “Ka dawo! Wallahi ka dawo!”
Alhaji Bashir ya yi shiru, ya juyo ga matashin attajiri.
“Mutum na iya kawo kuɗi… amma ba zai kawo zaman lafiya ba. Zaman aure da soyayya suke, ba da bank account ba.”
Ya juyo ga Maryam. “Ki yafe min ’yata.”
⸻