Free chapter · Read without an account
FANSAR MACE
5 & 6_*🦋FANSAR MACE🦋*-
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
NIDA PATIENT DINA
ASHE ZAMUGA JUNA
ƊAYA CIKIN BIYU
MAKIRIN IKO
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
Ina masu son tallata hajarsu?,masu son a yi musu tallar kayan sana'ar su domin samun kostomomi, to Kar ku yi ƙasa a guiwa ku garzaya ku Kira wannan layin *** Mrs isham domin a tallata muku hajar ku.❤️😊
5 & 6
A hankali ta buɗe idanunta ta ga yanda falon yake ci da wuta, Dr Sagir da su Mommah har wuta ya soma kona su. dakyar ta iya tashi tsaye tana kallon fuskokinsu tana kuka,tana riƙe da cikin ta inda aka harbeta se zubar da jini yake ta nufi inda gawan Zaid yake amma se kayansa kawai ta gani alamar shi kam wuta ya riga da ya cinye gawarsa.
“Allah ya jikan ku iyayena da ƴan uwana. wallahi se na ɗau fansar kisan gillan da aka muku”
Ta faɗi hakan tana nufan dakinta dakyar take iya taka kafarta. tana shiga ta ga nan ma wuta ya na ci a dakin kayayyakinta da su laptops din ta duk sun kone. pillow ta ɗaga ta ɗauki jakan da Dr ya bata ta fita ta kofan baya,titi ta nufa tana tafiya jiri na ɗibanta. Wata tsuhuwa ce da ta fito domin yin bara saboda lokacin har karfe uku ya wuce ta hango Alisha da sauri ta nufe ta
“ ke kuwa yarinya me ya same ki su waye suka miki haka?”
“Dan Allah ki taimaka min ki ɗauke ni daga man. zan baki ko nawa ki ke so matukar zaki ɓoye ni,zan baki daga daga abinda yayi million daya har zuwa dari “ ta na faɗin haka ta suma zata faɗi tsohuwar ta yi saurin riƙota. Tana ƙarewa anguwar kallo. Mutane sun fara fitowa suna kiran taimako saboda yanda wuta ke cinye gidan se ihun mutane ke tashi babu wanda ya ankara dasu. Da sauri matar ta bar gurin da Alisha.
Gari da ya waye labari ya karaɗe ko Ina kancewa gobara ya tashi a gidan Dr Sagir Lelewal ya kashe sa da matar sa da yaransa. Sosai aka cika da alhinin mutuwar Dr da iyalansa,mutuwarsa tabbas ya taɓa zukatan al’umma saboda mutum ne me taimako. Talakawa sun yi kuka sosai da wannan rashi haka aka zo aka kwashi tokansu aka yayyafa ruwa aka musu sallah aka binne su. Yan uwan sa da suke kumo sun zo zaman makokin dan uwan su. sosai suka yi kuka saboda wannan babban rashi ne da aka yi. Haka social media ya yaɗu da labarin mutuwarsu ana saka hoton Dr da kuma Zaid saboda ba kowa ne yasan Alisha ba. Haka aka yi ta zaman makokinsu batare da zargin komai ba saboda babu wanda yasan gaskiyan abinda ya faru se Allah.
CI GABAN LABARI
“Wayyo dan Allah kar ka kasheni,ni fa me gadi ne kawai a wannan gıda. Ka taimaka ka yi min rai ina da iyali kuma da ni kaɗai suka dogara. Ka rufan asiri kamar yanda Allah ya rufa maka.” Mai gadi ya gama wannan zance cikin tsananin tashin hankali domin kuwa bindiga ce a kansa kunama ce kawai baa harba ba,wanda ke riƙe da bidigar kuwa yana sanye ne da bakaken kaya, daga sama har ƙasa se wani iriyar fuska da ya sanya. A gefe da su kuwa gawan me gidan ne da wannan makashin ya kashe se matar me gidan da ya liƙewa baki da gam se kuka take yi tamkar ranta ze fice yabar jikinta saboda ganin mijinta kwance ƙasa matacce,a dayan gefen kuwa ɗan jaririnsu da be wuce wata bakwai bane ke ta tsalla ihu amma babu halin uwar ta ɗauke sa.
Kallon me gadin makashin ya yi kafin ya sake gyara bindiga akan sa yana kokarin harbawa kenan aka fara kiraye-kirayen sallah asuba tare da soma jin sahun takun mutane wannan dalilin ne yasa ya daki me gadin da gindin bindigar akai nan take ya faɗi ya suma shi kuma makashin ya sanya bindigar a aljihunsa na baya sannan ya fice a farfajiyar gidan yana me bin kofar baya da gudu cikin saa kuwa ya bar area batare da kowa ya gansa ba.
“Dan Allah driver ka hanzarta wannan irin tafiyar da ka ke yarinyar nan zata iya haihuwa a motar nan matukar baka yi sauri ba.”
“In sha Allah Hajiya zamu isa asibitin nan da wuri”
Cewar driver yana ƙara gudu kamar yanda ta basa umarni.
“Washhhhhhh,Innalillahi zan mutu. Dan Allah Hajja hauwa ku cire min abinda ke cikina in ba haka ba zan mutu dan azaba. Wayoooo ni Maryam yau karshe na yazo.”
“Haba ke kuwa se ka ce akan ki aka fara ciki da haihuwa maryam, a ce kina naƙuda amma ba za ki dinga wa kan ki fatan alkairi ba,to babu kyau ki dinga addua kawai.”
Cikin azaban naƙuda maryam bata ko kula ta ba se ma yarfa hannu da take yi kawai tare da dafe maranta da ta ji yana mata barazanar rabewa biyu.
Duk irin gudun da driver yake shararawa fa hakan be sa hajja hauwa ta yi shuru ba gani take tamkar a hankali yake tafiya saboda yanda maryam ta kiɗima mata hankali da sambatun wahala.
Waro ido Driver ya yi lokacin da idon sa ya sauka akan inuwar mutum a tsakiyar titi ya tsaya kamar gunki ya ki matsawa. sa'ke sitiyarin motar ya yi cikin mamakin abinda ya gani ya juya ga hajja hauwa yana faɗin
“Hajiya kin ga mutum a tsakiyar titi”
Watsa mai harara ta yi cikin masifa ta ce “ehhh Kwarai yau na yarda baka da hankali labaran,waye ze tsaya akan wannan titin a irin wannan lokacin dal….”maganar makale mata a baki ya yi lokacin da ta ankara da driver labaran fa ya sa'ke sitiyarin motar ne a yayinda ya juyo gareta yana mata magana. cikin tsananin tashin hankali ta soma rafka salati domin shine kawai mafita saboda ta riga da ta hango mutuwa ƙarara da idon ta.
“Innalillahi wainna’ilaihi rajuun labaran yanzu saboda kana son ka kashe mu shine ka sake sitiyarin motar ?”
Ta faɗa tana dukan kirjinta hatta maryam da ke naƙuda se da gabanta ya faɗi lokacin da ta ji abinda hajja hauwa ta furta.nan ta ji ɗan cikin ta ya yi wani irin juyawan da se da ta koma ta kwanta bata sanı ba.
Cikin gaggawa labaran ya dawo hayyacinsa ya yi hanzari wajen ganin ya riƙe sitiyarin amma fa lokaci ya kure masa saboda wani haske da ya dauke masa ido nan suka bugi abinda bazasu iya cewa ga sunan sa ba. nan motar na su ya dinga juyawa akan titi dan ma Allah ya taimake su ba su bugu da gungumen icen dake gefen titin ba.
Gaba dayan su suman yan mintuna suka yi sanadiyyar fargaba da suka shiga se bayan wasu mintuna tukun suka dawo hayyacin su, inda kowa ya hau duba jikin sa amma babu ciwo, hakan yasa suka hau godewa Allah.
Buɗe murfin motar ya yi ze fita hajja hauwa ta hau cewa
“Labaran ina kuma zaka mu da zamu godewa Allah sannan mu ƙarasa asibiti”
“Hajiya na ji mun buge abu shine nake son ganin menene wannan kar ya tare mana hanya”
Kai ta gyada masa shi kuma ya fita a motar,kamar wani mara gaskiya Labaran ya fara tafiya yana dube-dube saboda shi de ba baya ba inde wajen tsoro ne to ze iya lashe lamban yabo.
A gaban motar na su yaga mutum kwance alamar de su ne suka yi sanadiyyar hakan. cikin tsoro-tsoro ya tsuguna ya sa hannu a fuskar da yake rufe da abu, ya yaye sa nan yaga matashiyar budurwa kwance gefen kanta na zubar da jini,hannu ya sa a hancinta ya ji tana numfashi sama-sama da gudu ya isa motar yana kwankwasa glass din gefen hajja hauwa zugewa ta yi tana mai kallon lafiya,saboda ganin sa da ta yi a wani irin yanayi.
“Ya aka yi kuma?”
Murya na rawa ya ce “Hajiya wallahi mun yi kisan kai wayyo mun shiga uku”ya ƙarasa maganar yana ɗaura hannun sa akai
Kallon shi duk suka yi a firgice da sauri ta ce “Labaran kamar ya kisan kai?me kake nufi da kisan kai wa mu ka kashe?”
“Hatsarin da mu ka samu yanzu ashe ita muka buge tana nan kwance cikin jini “da sauri ta buɗe ta fito tana me faɗawa maryam da kar ta je ko ina.
Ko da suka isa inda matashiyar take babu ɓata lokaci suka kamata suka sanyata a motar suka shiga suka nufi asibiti.
Karfe hudu da rabi dede suka shiga asibitin ZAINAB BURKACUWA suna shiga kuwa nurses din da suke night duty suka tare su tare da wucewa da Maryam labor room ita kuma matashiyar suka nufi Emergency room da ita. Zama Hajja Hauwa ta yi tana girgiza kai ta rasa ta ina zata fara addua kawai take yi a ranta Allah ya fito da dukan su biyu lafiya.haka yake a bangaren labaran driver shima zama ya yi ya buga uban tagumi kamar wanda aka wa mutuwa.
Se karfe biyar aka fito da jariri aka kawo mata tare da mata albishir maryam ta haihu lafiya ta haifo ɗa namiji.
Murmushi ne ya subuce mata lokacin da ta yi arba da jikanta me tsananin Kama da Uncle din sa wato ƙanin mahaifin sa saboda babu abinda ya bari na sa.
Kallon doctor ta yi ta ce “to ita kuma wancan baiwar Allah fa??”
“Gaskiya ba domin ku din kun zo a mawuyacin hali ba da gaskiya ba za mu taɓa wancan yarinyar ba. saboda case ne da se police sun sa hannu wannan ya kasance doka,amma yanzu ana bata taimakon gaggawa kuma Alhamdulillah komai na tafiya dede saboda bata wani raunata sosai ba”
“Allah ya maka albarka yaro. ni na sanı kuma kun yi kokari yanda ku ka cece rayuwar yarinyar nan Allah ya saka muku.”
“Ameen hajiya “
Dakin da aka mayar da Maryam ta nufa ta zauna a gefenta tana kwantar da yaron a jikinta tare da kura musu ido.
Bayan ta idar da sallah asuba ne tana kan sallaya bata motsa ba ta aika labaran driver ya je ya ɗauko mata wayar ta. Nan ta fara kiran yan uwa da abokan arziki tana sanar da cewa maryam ta haihu.
Kafin 7:00am an fara zuwa asibiti inda kowa ya zo yake taya maryam murnan sauka lafiya,tare da yaba kyau da yaron ya yi nan aka soma shirye-shiryen komawa gida da mai jego.
Shigowa wata nurse ta yi ta dubi hajja Hauwa ta ce “Hajiya yarinyar ta farka”
“Masha Allah bari ina zuwa”
Kallon ta duk suka yi banda maryam Wata babban mata ta ce
“Hajja hauwa wata yarinya kuma ake magana akai ?”
“Wallahi Adda jiya a hanyar mu na zuwa nan mun haɗu da hatsari inda muka buge wata yarinya,shine yanzu suke sanar da ni ta farfaɗo mu je mu dubata “
Babu musu duk suka rufa mata baya ko da shigan su dakin da take, samun ta suka yi ta haɗe kai da guiwa ta dukunkune jikinta da bakar doguwar hijabi tana kuka ƙasa-ƙasa.kan ta da ta bugu an naɗe mata shi da bandege ga dogon gashinta dake zube a gadon bayanta.
Sallama suka yi suka shigo duk suka tsatstsaya,hajja hauwa ta zauna a kusa da ita tace
“Yarinya sannu ko!.. mune muka buge ki jiya bisa tsautsayi fatan zaki yafe mana kuma ki bamu damar mayar dake ga iyayen ki?”
Sautin kukan ta ne ya ƙaru ba tare da ta ɗago kai ko ta kula su ba ta ci gaba da rera kukanta. Kallon juna suka yi ganin bata ce komai ba hakan yasa Adda ta zauna a gefenta ta ɗaura hannunta a bayan ta
ta furta
“Yi hakuri yan mata kin ga baki da lafiya ki yi hakuri da wannan kukan ki ɗago mu yi magana dan Allah kin ji ko?”
Jin tana haɗa ta da Allah ne yasa ta ɗago black beauty face din ta a hankali da kumburarrun idanunta ta dubesu tana kuma dukunkunewa gu daya tana musu kallon tsoro saboda ba ta san su ba,murmushi duk suka yi ganin yanda take musu kallon tsoro.
“Kar ki ji tsoron mu,mu ma mutane ne kamar ke,ya'ya sunan ki?”
Sukunyar da kanta ta yi ta soma wasa da yatsunta a yayinda hawayen ke ci gaba da zuba a idon ta. Da siririyar muryarta ta ce
“ALISHA”
Ta faɗi sunan a taƙaice.
“Suna me dadi. ke din daga ina ki ke ?ko de anan cikin Gombe kema ki ke tare da iyayen ki?” Hajja hauwa ta mata tambaya,a madadin ta bata amsa se ta fashe da kuka tana rungume guiwowinta da hannayenta.
Fahimtar da suka yi yawan tambayoyin da suke mata ne yasa take kukan yasa suka sauya maganar ta hanyar faɗin
“Shikenan dena kukan tashi mu tafi gidana, in yaso in kin samu sauki se mu yi magana kin ji ko?”cewar Hajja Hauwa
Gyada mata kai ta yi kawai without saying a word,. riƙeta Adda ta yi ta taimaka mata ta miƙe suka fice a dakin suka nufi filin fakin din motar. inda motar biyu yake jiran su shiga suka yi suka bar asibitin.
Kai tsaye anguwar ARAWA suka nufa,horn driver yayi a bakin gate din matsagaiciyar gıda me kyau. buɗe gate din me gadi ya yi duka motoci biyun suka shiga. gida ne flat me kyau de de zaman mutum daya zuwa biyu ne ba wai wani babba bane yana da tsari sosai. Fitowa suka yi suka nufi kofar falon inda Hajja Hauwa ta buɗe suka shige. Adda da maryam da wasu mata biyu suka shiga daya daga cikin dakuna uku da suke ciki. Inda Hajja Hauwa kuma ta nufi wani bedroom room da Alisha . Dakin babu wani tarkace katifa ce six by six akan gado,se wani wardrobe,gefe kuma wasu akwatuna ne guda biyar a jere. ga kofar da ze sadaka da toilet Dakin ya haɗu sosai.
Tunda suka shigo dakin kan ta a ƙasa, sannan kuma yatsun damanta tana amfani dasu wajen wasa da zoben azurfa dake hannunta na hagu.
Murmushi Hajja Hauwa tayi bayan ta karanci Alisha na wasu mintuna ta fahimci yarinyar tana da matukar kunya,miskilanci,da kuma tsoro haɗe da rashin son hayaniya sosai.
Fuskarta a sake ta ce “Alisha...wannan dakin ƴata ce Yusra ita ce yar auta ta,yanzu tana abuja taj e hutu gurin dangin mahaifinta,za ki kasance a nan dakin na ta kuma sanan kasancewar ba ki da kaya zaki iya amfani da kayanta.”
Kai kawai Alisha ta gyada mata tana tsaye ƙiƙam ta ki motsawa,saboda yanda take jin ta a takure.
“Ki yi wanka yanzu zan zo miki da abinci da kuma maganin ki.“ tayi maganar tana ficewa a dakin.
Bayan fitanta ne Alisha ta ɗago kyakyawar fuskarta ta ƙarewa dakin kallo, ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe manyan idanunta da suka kumbura. A hankali ta taka har izuwa bakin kofar sannan ta danna key ta zare dogon hijabin jikinta ta ajiyesa a kan gadon a tsanake. Masha Allah Alisha kyakyawa ce sosai kasancewar ta doguwar mace me karancin shekaru,kuma baƙar mace son kowa ƙin wanda ya rasa tana da doguwar fuska me ɗauke da manyan fararen idanu me zagaye da zara-zaran gashin ido,se dogon hanci da ɗan ƙaramin bakinta da ya kasance pitch color,idan muka kai duba izuwa goshinta ɗauke yake da kwantaccen saje da ya sake bayar da damar ɗawata kyakyawar fuskar na ta,se gashinta da ya kasance dogo me tsantsi wanda ya ke zube a bayanta,Alisha kyakyawa ce ajin farko se de daga yanayinta zaka fahimci akwai miskilanci ,domin daga yanayin ta zaka fahimci tana da matukar sanyi kuma sannan mara son hayaniya ce ga kalar fuskar tausayi. Jikinta na sanye da English wears riga da skirt hannu ta kai tana me taɓa bandeging kan ta nan ta ji zafi ya ratsata domin ta ɗan bugu akan dogon tsaki ta ja.
“Aikin banza kawai “ tayi maganar tana zama akan gadon wayanta dake vibrating ne ta zaro a cikin breziyarta keypad ce tana fito dashi ta ga me kiran nata ‘Inna ta’
“Hello inna kin tashi lfy?” Ta yi maganar kamar bata so
A bangaren inna kuwa cike da damuwa ta ce “Ayyah Alisha na Ina ne inda ki ka tsaya har yanzu ba ki dawo ba? Hankalina sam ya gaza kwanciya, shin kin yi abinda ya kai ki kuwa?”
Murmushi tayi yanda ta ga Inna hankalinta ya tashi
“Nayi. Wasu ne suka buge ni a hanyata na dawuwa gida bayan na binne kayan aikina, amma zan dawo soon” batare da ta jira amsar inna ba ta kashe wayarta.
A can dakin me jego kuwa hira suke yi “Adda har yanzu Sameer be dawo bane da baze zo ya mayar da matarsa dakinta ba ko be san dacewa ta yi yaji bane?”
Ajiyar zuciya Adda ta sauki ta dubi gwaggo Indo da tayi magana “ Wallahi yanasani sarai ni ban san menene matsalar Sameer ba”
Hajja hauwa da yanzu shigowanta ta samu guri ta zauna “Ai Sameer ba ze taɓa canzawa ba wani lokacin ji nake kamar bani ce na haifesa ba. Halin uban sa ya ɗauko. Ni wannan jaririn yafi min shi kuma Maryam bazata koma gidan sa ba”
“Ah ah Hajja Hauwa bazaa yi haka ba dan Allah. Wallahi nasan yanzu in ya san ta haihu ze nutsu inde ya san ya zama uba ze dawo hayyacinsa “cewar Adda.
“Hmmm Sameer fa baze canza ba,ya ɗauko dabi’un ubansa wanda a gaba za su yi danasanin wannan mummunar halin nasu. Kullum ina gode wa Allah da ya rabani da Modibbo Ɗan gaske. gashi tunda na rabu dashi nake rayuwata cikin kwanciyar hankali. Yanzu Haydar ba ɗanki bane Adda? Ko kuma ba ƙanın Sameer bane? Meyasa shi be zama shashasha irin Sameer ba. Wallahi kullum ji nake dama a ce Haydar ne ɗa na ba Sameer ba”
Hajja Hauwa ta gama magana cike da masifa.
Gwaggo indo ne tace “kiyi hakuri be kamata kina fushi da yaron ki ko da yaushe ba,ke de kawai ki dinga masa addua “
Maryam dake riƙe da jaririnta kanta a kasa duk abinda suke cewa bata ɗago kan ta ba.
Adda ne ta dubeta “Maryam ki yi hakuri da halin Sameer in sha Allah ze shiryu da izinin ubangiji”
“To Adda. Ina uncle Haydar?”
“Yana can gida bari in kira sa” ta ɗau waya zata kirasa Kenan ta ga ‘Mrs Hashim zakewa’ na kiranta ɗagawa ta yi bakinta ɗauke da sallama yanayin fuskanta ne ya sauya
“Innalillahi wainnailaihi rajuun,kulli nafsin za'ikatul mauut”
Duk kallon ta suka tsaya yi dan jin waya rasu bayan ta gama wayar ne Hajja Hauwa ta tambaye ta “Adda waya rasu?”
“Matar Hon. Hashim zakewa ce ta kirani take sanar dani daren jiya wani ya shigo har gida ya yi wa mijinta Hashim zakewa kisan gilla yanzu haka ana zaman makoki”
Gaba daya dakin ne ya kaure da salati sosai mutuwar Hon Hashim zakewa ya taɓasu, domin Hon Hashim Zakewa aminin mijin Adda ne wato Hon Modibbo Ɗan gaske.
“Allah yaji kansa. Bari in je in kaiwa yarinyar nan abinci kar in bar ta da yunwa “ Hajja Hauwa tayi maganar tana sawa Alisha abinci sannan ta fice
Kwankwasawa tayi Alisha dake tsaye ne ta koma ta zauna tana “a shigo”
“Sannu yarinya ga abincinki da magani, kin ji ni shuru wallahi rasuwa aka mana “ tayi maganar tana zama kusa da ita.
Cikin sanyin murya ta ce “Allah sarki waya rasu haka?”
“Hon Hashim zakewa ne,wai wani makashi ya shiga gidan sa ya masa kisan gilla”
Ta ƙasan ido ta kalli Hajja hauwa da kyau “Allah sarki amma ku meye haɗin ku dashi ?ko ɗan uwan ku ne?”
Girgiza kai Hajja Hauwa ta yi “ah ah ba ɗan uwan mu bane. Hashim zakewa aminin tsohon mijina ne wato Hon Modibbo Ɗan gaske nice uwar gidansa,se kuma wannna matar da mu ka zo gurinki tare ita ce matar sa ta biyu. Amma ni yanzu mun rabu dashi “
Tunda take magana Alisha ta tsareta da ido tana kallon ta kwakwalwarta se juya maganganunta take, wato de yanzu ta shigo cikin ahalin Ɗangaske batare da sun san ta ko ta san su ba lamarin ya matukar bata mamaki kuma ya mata.
Cikin son shan cikinta domin ta lura da Hajja Hauwa akwai surutu irin mutanen nan ne da ake Kira faɗi baa tambayeka ba
“Kenan wacce ta haihu ƴar ki ce?”
Dariya tayi “ ah ah ba ƴata bace surkata ce. Mata ce a gurin babban ɗana Sameer Modibbo Ɗan gaske”
What a coincidence 🔥🔥🔥🔥🔥🔥
(Da ni da ku duk mun girgiza 🤭😳 Allah baya bacci cikin ruwan sanyi Allah ya wurgata cikin su)
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍