Free chapter · Read without an account
23
by Rufaida Umar · ALWASHI
ALWASHI
23
GODIYA
Assalamu alaikum yan uwana, ina yiwa kowa fatan alkhairi. Ina kuma godiya bisa bibiyar labarina da ku ke yi. Daga kan yan uwana marubuta har da ku makaranta, Allah ya bar kauna fisabilillah. Ameen. Ƙofar gyara ko shawara a buɗe take ta wannan lambar ***. Nagode.
***
'Salma kina ji ko? Kar a sake a takurawa yarinyar nan, duk abin da take buƙata a yi kokarin samar mata. Baƙuwarmu ce don haka har yaran nan a ja musu kunne su yi haƙuri mu lallaɓa ta domin mahaifinta yana kokari matuƙa wurin kyautata mana idan mun haɗu a London. Ke shaida ce."
Mami wacce tun a safiyar ranar da Nihla ta kwana a ɓangarenta Abban ya kira ta waya ya jaddada mata wannan kashedi a kanta, a yanzun da take zaune Afrah ta kawomata ƙorafin ita dai a kai Nihla din tsohon ɗakin su Yayarsu Mardiyya dake ɓangaren saboda bambancin ɗabi'unsu, a cewarta wai Nihla din ba ta ƙaunar yin sallah kan lokaci, kwananta biyu amma ta kula kuma ga shi nan inda ta cire kayanta nan za ta bar su ba ta ɗauke ko tsinke. Kashedin can na Abban ne ya dawo wa Mamin a kwanyarta. Ta sauke ajiyar zuciya ta dubi Afrah dake ta ƙunƙuni lokaci guda kuma tana ɗaura ɗankwalinta na uniform din islamiyyarsu a gaban madubin Mamin.
"Haƙuri za ku yi har ta kammala hutunta Auta. Kamar yau ne sati biyu zai cika ai."
Jin haka Afrah ta ƙara tura baki.
"To amma Mami har fa takura mana take da tambayar wai ina Yaya Areef, dazu da safe da ya shigo ya fita ba ta nan har ce mana ta yi wai mu yi mata rakiya ɗakinsa su gaisa. Sai Sis Benazir ce ta ce mata kin hana mu zuwa ɓangarensu shi ne fa ta haƙura."
Nan ma Mami kallon Autarta tayi cike da nazarin zancen, koda dai dama bai kamata ta yi mamakin buɗewar idanun Nihla ba tunda haka ta taso ta girma, babu abin da take nema a duniya ta rasa, komai da take buƙata iyayenta na mallala mata. Ita dai ba za ta so suruka irinta ba. Ta kula ma Areef din bai san tana gidan ba, a zatonsa har ita aka fice don ba ya wurin aka yi shawarar ta zauna.
"Wuce ku tafi suna jiranki, zan duba yiwuwar maida ta ɗakin su Mardiyyar."
Sai lokacin Afrah ta yi murmushi sannan ta yi wa Mamin sallama ita kuwa ta bi ta da addu'ar neman tsari da ma sa'a a karatu sannan ta ƙurawa hanyar da yarinyar da ta bi da idanu, duka duka shekarunta ba su wuce sha bakwai tana kokarin shiga na takwas, idan an koma hutu za ta tafi aji na biyu a jami'ar Alƙalam, tabbas ita ma Afrah akwai sangarta a tattare da ita amma sun ci karo da irin na Nihla wacce babu alamun ma ta damu da karatun addinin.
Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta jawo waya, ita sai a sannan ta tuna ba ta ji ɗuriyar ɗan nata ba tun safe da ya fice daga gidan yace yana da uzuri.
***
Zaune yake a falon Haj Maimuna tare da Fareed, shiru ne kawai ya ratsa falon bayan sun ji bayanin da ya fito daga bakin Haj Maimuna cewar ita fa ta jima ba ta ga Sameera ba don koda ta tambayi wacce ta haɗu da ita wato Maman Muneer, wato Haj Nabeela, ta ce mata su din ma wayar gari kawai suka yi suka ga ba sa unguwar gaba ɗaya. Kuma hatta a wayoyinsu ba sa samun su. Abin ya ba su mamaki ainun. Jin wannan ya sanyayar da gwuiwar Areef.
Ga Haj Maimuna sai ta ji tana zargin kodai Areef din son Sameera ya ke yi? Don haka ta ce,
"Wai neman me kuke ta yi wa Sameera haka ne Areef? Ko neman iri ku ke?"
Maganar ta daki Areef, sai ya rasa ma yanayin da zancen ya jefa shi, Fareed kuwa da ya san komai sai ya yi dariya kawai ya waske da fadin,
"Hajjaju kenan, bari mu je lokaci yana ja."
Ta jinjina kai, to da alama dai Areef din sonta yake, yanayinsa da ma na maganar da Fareed ya yi sun tabbatar mata da zarginta. Ah lallai dole su Sameera su yi ɓata dabo, wayasani ma ko wani baƙin asirin suka ƙulla da ya sa Areef haukacewa a nemansu yanzun, to ita kam ma sai ta ji mamakin yadda duk kusancinsu da Salma ba ta taɓa yi mata batun ba koda wasa, asalima akwai sadda ta ke jajanta mata cewar ta je gidan Haj Nabeela abokiyar kasuwancin nata take ce mata Sameera sun bar unguwar kuma ba labarinsu, ban da Allah ya kyauta babu abinda tace. A lokacin ba ta wani dauki hakan a komai ba tunda ai tunaninta ma ba zai ba ta ba, abin da kitsone kawai ya haɗa? To tun shi ba su ƙara batun da Salma ba sai yau din da Areef ya zo mata da zancen. To ko dai dama saboda soyayyar Sameerar ne ya bar ƙasar? Alamu sun nuna iyayen nasa ne ƙila suka ƙi, kuma dama ai ko ita ba za ta yi murna da hakan ba ko ba komai ga ɗiyarta Nazeefa da take kwaɗayin samun mijin aure kamarsa. Sai ta ji gwara ma da aka yi hakan, gwanda da Sameera din suka ɓace a unguwar, hakan a yau sai ta ji ya yi mata daɗi.
Suka yi mata sallama tana musu tayin abincin rana amma suka ce suna sauri, Areef na shiga mazaunin kusa da direba ne wayarsa ta yi ƙara. Ganin sunan Maminsa sai ya ɗaga, sallama ya yi mata ta amsa cike da kulawa.
"Na ji ka shiru ne ban ga ka shigo neman abinci ba, ko ba ka dawo ba?"
"Eh Mami ina tare da Fareed ne. Zan ci a gidansa, muna tattauna batun kasuwancinmu, sai yamma zan dawo in sha Allah."
"To Allah ya nuna mana."
Ya amsa da amin daga nan suka yi sallama, kwantar da kai ya yi yana tuna abin da Haj Maimuna ta ce da su.
'Maganar Sameera ba ta taɓa haɗa mu da Salma ba ai tun bayan da na haɗa su da ita. Nemanta ku ke?'
Wannan zance ya ba shi mamaki, meyasa Mami da Abba suka nuna mishi dagaske ana binciken inda Sameera take har alhalin ba su ko taɓa tuntuɓar Haj Maimuna kamar yadda Mamin ta faɗamasa ba? Ransa ya ji yana zafi, meyasa iyayensa suke ƙoƙarin danne tarin laifukansu, sun manta rayuwar ba iyaka duniyar nan ba ce? Sun manta da wani wuri da ake kira Lahira inda kowa zai tafi?
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!" Ya furta a fili cike da ƙunar rai, idanunsa tuni sun kaɗa. Anya alhakin waɗannan bayin Allahn zai bari ya ji daɗin duniyarsa? Ji yake da wane idanun ma zai kalli iyayen Sameerar nan har ya nemi afuwarsu? Sameera fa? Za ta karɓi tubansa?
"Areef, ya dace ka bar takurawa rayuwarka da tunanin abin da ya wuce, ƙaddararka ce. Ka aikata ne ba a hayyaci ba, please ka share komai ka yi aure ka yi rayuwarka. Allah shaida ne ka yi tuban da ake so kuma kana kan yi. In sha Allahu watarana sai ka ga Allah ya haɗa ka da ita. Amma for now you have to stop.."
"No Fareed, i can't. Ba zan taɓa samun nutsuwa ba idan ban ga Sameera ba. I don't know how i feel about her." (Ban san ya nake ji ba a kanta)
Ɗan murmushi Fareed ya yi ya dubi Areef din kafin ya ce,
"I think it's more than just seeking her forgiveness." (Ina ganin ba neman gafararta kaɗai kake buƙata ba)
Areef shi ma kallonsa ya yi kawai ya kauda kai, babu wanda ya ƙara magana, Fareed na tuƙinsa cikin nutsuwa da tunanin wannan al'amari, shi har aka yi aka gama bai taɓa ganin wannan Sameerar ba.
"No, it's not what you think, so just forget it." (A'a, ba abinda kake tunani ba ne, don haka a bar maganar)
Fareed ya ƙara dubansa karo na biyu kafin ya maida hankali ga titi lokaci guda ya yarfa hannu da ɗaga ƙafa, daga haka bai ƙara uffan ba har suka ƙarasa gidansa. Matarsa Aisha ta musu tarba sosai don dama tuni ta shirya musu lafiyayyun girke-girkenta. Sam ba ta da son jiki, ba ta yarda kuma ƴar aiki ta yi wa mijinta hidima ba. Ga tsafta da kwalliya. Gidan sai ƙamshi yake, ita kanta ta ci adonta tsaf da ɗan lulluɓinta na medium veil a kanta. Ɗan ƙaramin cikin da ke jikinta ya ƙara mata kyau madadin muni.
Areef na son tsafta da ƙamshi, hakan yasa ya tabbatar amininsa ya yi dacen samun matar aure. Bai bar gidan Fareed ba sai da suka yi sallar la'asar kafin su rako shi har farfajiyar gidan da Aisha. Fareed ya miƙa masa muƙullin motar don dama shi ya zo da ita ya dauke shi suka fita.
Huɗu da mintoci ya shiga gidan nasu, bai zarce ɓangaren Mami ba don a gajiye yake wannan yasa kai tsaye ɓangarensa ya tunkara. Sai da ya ɗan huta kafin ya yi wanka ya ɗora alwala wanda hakan kusan ɗabi'arsa ce, zai wahala Areef ya zauna babu alwala. Ya zura doguwar jallabiya da silifas dinsa ya fita zuwa ɓangaren Mamin.
Sallamarsa ce ya sa Nihla saurin duban ƙofar falon, ji ta yi numfashinta na kai da komo ta fisgo shi da ƙarfi, ƙirjinta ya shiga bugu. Farar jallabiyar ƙal take, ta yi wani irin kwanciya a jikinsa wanda hakan ya fiddo da ƙirarsa na ɗa namiji. Ta kai duba ga damtsen hannayensa da ke a waje, ga gargasar da ya yi wani kwance luf a fatar hannayensa. Takun da yake yi kuwa sai ya ƙara fiddo kwarjininsa, babu ko ɗigon murmushi a fuskarsa amma ta kuka hatta da ɗaurewar fuskar ma kyau take masa. To ina ga kuma ya murmusa? Ta sauke ajiyar zuciya tana ƙara narkewa a kan kujerar da take ciki, ta kasa ko ƙifta idanu a kansa.
Benazir da ke hankalinta na ga Yayan nasu tana gaida shi, ba ta ko kula da Nihlar ba. Gareshi kuwa, kallo ɗaya ya yi mata a fisge sai ko na biyu don ya tabbatar ɗin ita ce ɗin ba ta tafi ba, da ya tabbatar ita ce sai kawai ya kauda kai bai ƙara na ukun ba, cikin ransa tsaki ya ja na wannan banzan kallon ƙurillah da take mishi wanda tuni ya karanci shu'umancin dake yawo a cikin nata ƙwayoyin idanuwan.
Ga Nihla kuwa, kallon da ya yi mata sai ya kara sukurkuta ta.
"Mami fa?"
Ta ji muryarsa karo na farko tun shigowarsa falon domin ba ta ji sautin muryar a lokacin amsa gaisuwar Benazir ba. Zumbur ta riga Benazir magana.
"Ina wuni Bro Areef."
Ba tare da ya ɗauke idanu kan Benazir da yake jiran amsarta ba ya ɗan ɗaga hannu da gyaɗa kai, a hankali ya motsa pink lips dinsa.
"Lafiya."
"Tana ɗakinta."
Daga haka ya yi gaba, Nihla ta bi bayansa da kallo, sai a sannan Benazir ta dube ta tana ɗan murmushi.
"Wannan kallon fa?"
Ita ma murmushin ta yi da ya fi kama da yaƙe a wannan karon, jikinta ne ya soma sanyi ganin yadda bai ko damu da ita ba, bai ma tambaya ya ji dama ba ta tafi ba? Kawai ya amsa mata kamar wata baƙuwar da bai taɓa tozali da ita ba.
"Yana da wuyar sabo." Ta furta ga Benazir. Ita kuwa dariya ta yi. Ya yi daidai da shigowar Afrah falon daga kicin sanye da riga da wando sakakku, ta dunƙule gashinta da manyan ribbons, hannunta riƙe da bowl wanda ta dafo indomie da sardine da ya ji haɗi, sai ko lemunta na gwangwani pepsi. Zama ta yi saman kujera ta naɗe ƙafafunta, za ta soma ci kenan Areef da Mami suka fito daga ɗakin. Fuskarsa har lokacin ba walwala, abin da ke cin ransa bai wuce na rufe shi da iyayensa suka yi da cewar suna bincike akan inda Sameera take ba.
Gefen Afrah ya zauna yana karɓar bowl ɗin, ita kuwa ɗan turo baki.
"Ba ki da aiki sai cin indomie ta ya ya za ki yi ƙiba?"
"Ato, faɗamata dai, wannan soyayyar da Auta ke yi wa Indomie na rasa irinsa nikam." Cewar Mami sadda take zama a kujera mai zaman mutum ɗaya. Ta dubi Nihla da murmushi saman fuskarta ta ce.
"Nihla ina fatan babu wata matsalar ko?"
Nihla da ke duban Areef sai ta ɗan murmusa.
"Babu Mami, just ni ban san me na yiwa Bro Areef ba."
Duka suka dube ta har Areef din, Afrah kusan harara ta watsa mata ma wanda basu kula ba.
"Me ya yi maki? Areef wani abu ya haɗaka da ita ne?" Cewar Mamin bayan ta maida dubanta ga Areef ɗin. Ya basar tamkar bai ji ba yana mai miƙawa Afrah bowl dinta.
"No Mami kawai ba ya son kulani ne, ban san dalili ba."
Maganar Nihla ta sa Mamin maida hankali kanta.
Shi kuwa miƙewa ya yi.
"Mami bari na je masallaci na dawo."
Kafin ta amsa ya soma tafiya, itama ba ta tsaida shi ba jin ana kiran sallah.
"Nihla ba haka bane, yayan naki ba shi da magana ne sosai. Haka halittarsa take, ba kya ganin su ma ƙannen nasa ba wani jan su yake ba? Ganinsa ma wuya yake saboda ba kasafai ya fiye zama ba yana da harkokinsa."
Afrah ita haushi ma ta ƙara ji da Mamin ta tsaya yiwa Nihla bayani, a gefe guda kuma ta ji daɗin yadda Yayan nata bai wani ji ɗarr da kyawun Nihlar ba ballantana a kai ga ya ji yana sonta.
"Ok Mami, na fahimta. But please ki ce ya dinga sakarmin fuska. Ni ma sister dinsa ce fa."
Murmushi Mamin ta ɗan yi.
"In sha Allahu zan masa magana. Yanzu ku je ku yi sallah ko?"
Daga haka ta miƙe ta nufi hanyar ɗakinta. Ita kuwa Afrah ta ƙara nannaɗe ƙafafunta ta cigaba da loma kasancewar ba ta da sallar, Benazir ta yi ɗaki. Nihla ta dubi Afrah, kamar ta yi magana sai ta fasa, ta kula yarinyar ba wani maraba take da ita a gidan nasu ba. Ganin yadda Areef din ya kula da Afrah din yasa ta fahimci kamar ya fi son Afrah din akan Benazir din can, ƙila idan ta samu karɓuwa wurin Afrah din ta samu itama ya dinga kulata. Sai ta mike ta bi bayan Benazir din don gabatar da sallar, ta kula gidan ba sa wasa da lokutan sallah. Ita kuma hakan ya zama tamkar matsi ga rayuwarta don wani lokacin ma sai ta haɗa salloli babu abinda ya sha mata kai. Kuma koda Momi Inayah ta nemi tsawatarwa idan abin ya yi yawa, Daddy Affan na taka mata burki da cewa har yanzu ita din yarinya ce ta kyale ta za ta daina zuwa gaba.
***
MAIDUGURI...
Zuwan Gwaggo Samha da danta Alh Mu'az Haruna Zango gidan ya sa kowa cikin murna da nishaɗi.
Laila koda ta fito zuwa falon Yakumbo don ta gaisa da su, ta yi mata ƙuri tana kallo, dattijuwa sosai da za ta haura shekaru saba'in a duniya sai dai kyawun jikinta da ma lafiyar gani da Allah ya ba ta ya ɓoye wannan shekarun, ɗanta dake zaune a gefe wanda koda zai girmi Mama bai fi da shekaru biyu ba ko ɗaya, shi ma ya sha manyan kaya abin sa. Kallo ɗaya za ka yi wa Gwaggo Samha ka gane jinin Kawu Barhim ce tsabar kamannin da suka yi.
Ta ƙarasa ta durƙusa a gefen ƙafafun Gwaggon wacce ta tsura mata idanu tana hango fuskar masoyinta na farko a duniya a kan Lailar,(Fuskar Hammad). Shi ta fara so irin so na haƙiƙa sai dai kuma kuskuren mahaifinta Kawu Barhim ya sa Hammad ya guje ta ya zaɓi auren Khalisat mahaifiyar Mama.
Yanzun da Laila ke durƙushe a gabanta tana gaida ta, sai ta ji wannan ƙauna da soyayyar da ta yiwa Hammad ya dawo sabo fil amma a kan Lailar. Ta kamo hannunta tana murmushi ta amsa gaisuwarta.
"Wannan dai tawa ce Kubra, ni za ki bar wa ita mu wuce Kano ko?"
Mama ta yi dariya.
"Idan har haka kike so Gwaggo, ai kai da kaya duka mallakin wuya ne."
Murmushin Gwaggo Samha ya faɗaɗa, ta ƙara duban Maman.
"To na san su Yakumbo ba bari za su yi kema na ɗauke ki a nan ba, amma nasan ba za'a hana ni Laila ba."
Dariya aka kara yi. Laila kuwa ta wiaga ta gaishe da Alh Mu'az. Ya amsa fuska a sake shima. Nan aka hau hirarraki, can bayan ma an bar zancen Gwaggo ta ƙara gyaran murya.
"Kubra fa ba wasa nake ba, dagaske zan
wuce da Laila wurina."
Wannan ya sa duk suka dube ta.
Women Of Words Writers.