Free chapter · Read without an account

Matar Khalees

by Nusaiba Ibrahim Rimi · Matar Khalees

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy_bee

Page 15

Ranar suna an sha shagali,yaro ya amsa sunan Mahmud,sunan mahaifin Deeja, amma Mima ta ɓoye sunan da Affan,anyi hidima sosai,mai jego ta sha ado cikin manyan kaya kala-kala ita da jaririn ta, wasu ita ta siya,da yawan su kuma siya mata akayi,don daga gidan professor Ismail an kawo mata sama da kala ashirin kayan fitar suna,banda na jaririn ta ma,ga su Aunty Bintu,hidima dai sai son barka

Har da umaima akazo suna,sarai sun gane cewa leƙen asiri tazo yiwa Nadiya,don haka Deeja ta zage gayu da facaka iri iri,mai make-up din da tayi mata lokacin bikin mijin ta da nadiya ita Aunty Bintu ta sake ɗauko mata,ga sutura masu asalin tsada da ɗinki mai kyau,ga adon gold abin sai son barka,ga cima kala-kala sai wanda Mutum ya zaba,ba umaima ba kaɗai,hatta da lubaisa sai da ta raina kanta

Umaima bata wani dade a gidan sunan ba ta tafi gida,tana komawa ta kirawo Nadiya ta shaida mata abinda ya faru a gidan sunan, Nadiya taji takaici sosai don so tayi ace Deeja ta wulaƙanta,amma wai umaima ke sanar mata yadda Deeja ya haska kuma ake tarairayar ta a wajen sunan,don haka tace

"Ƙyale ta umaima, alƙawari fa na ɗauka,sai na rusa mata farin ciki,zata san cewa da ni Nadiya gagari kowa takeyi,sai na nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane,sai na sanya ya ɗora hannu aka na rasa mafita,don wallahi sai na sauke mata wannan ji da kan nata,sai tayi data sanin zuwa duniya"ta ƙarasa cikin ɗaukar alwashi da ɓacin rai

"Wallahi ina bayan ki,ke dai kawai ki shirya,dole mu komawa boka"a cewar umaima

"Ai haka za'ayi kawai,don naga alama tana ɓata min aiki,kuma idan nayi mata baya kama ta"

Umaima ta jinjina kai tana fadin"wannan ai mei sauƙi ne,tunda kin gama da wanda take taƙamar ai shikenan"

"Ke dai bari kawai umaima,duk da na raba su harkar gaban ta kawai takeyi,ko kaɗan bata da damuwa,kuma ya kasa kataɓus akanta"

"Keep on trying, watarana zakiyi nasara"a cewar umaima,tana mai ƙarfafa mata gwiwa"

"Har sai kin faɗa?ai na riga na gama yanke abinda zanyi mata na samu ta fita daga rayuwa ta"

"Okay!to Sai na jiki"suka kashe wayar

Taro ya tashi lafiya, hankalin Deeja ya kwanta sosai,don yadda aka tarairaye ta aka nuna musu kulawa ita da jaririn ta ya sanya ta kuma sakin ranta,rashin damuwa da al'amarin ta da Khalees yakeyi kwata-kwata baya danun ta,don ta sani ba yin kanshi bane,kuma bata taɓa fashin saka shi a adduoin ta ba

Gyara sosai aunty Bintu tayi mata,ga ƙara wayar mata da kai da takeyi, kullum cikin tofe ɗan ta da adduoi kala-kala take,kuma dare da rana bata gajiya da yiwa mijin ta addu'a,tare da addu'ar Allah ya bayyana mata yayyen ta,tana son zuwa Yola amma fargaba ta hana ta

Watan ta guda amma har lokacin bata koma gidan auren ta ba,sai dai ta koma bakin aikin ta,Affan kuwa yayi kyau yayi ɓulɓul abin shi,kamannin shi da Khalees sun ƙara fitowa sosai

Zaman Deeja a gidan Aunty Bintu ya taimaka ƙwarai wajen tafiyar da kaso mai yawa na damuwar ta,ta nutsu sosai tana aikin ta,tana son komawa makaranta don ƙaro karatu amma tana tsoron tunkarar Khalees da batun,don haka taga gwara ta haƙura kawai,har sanda al'amura zasu daidaita

Don haka ta cire damuwar komai a ranta,ta riƙi aikin ta da yaron ta sosai

Watanni biyu suka shuɗe,Deeja tayi kyau tayi haske sosai,a lokacin sati biyu ya rage su Aunty Bintu su tafi kasar Syria,don haka Deeja ta fara shirin komawa gida

Ranar da zata koma Aunty Bintu ta aika aka gyara mata ɗakin ta,nadiya na zaune tana jin kiɗa sai ga su intisar sun shigo da sallama

Su shida ne,intisar,ilham ƙawar intisar sai masu aikin Aunty Bintu su huɗu

Sheƙeƙe ta kalle su sannan ta zare airpiece ɗin kunnen ta tana kallon su a wulaƙance,cikin isa da gadara tace "ku kuma fa?daga ina?"

Intisar ta kalle ta sama da ƙasa tace"yi haƙuri,ba wajen ki muka zo ba,kin gane?"tana gama faɗin haka tayi wucewar ta ciki,suma sauran suka biyo bayan ta

Nadiya ce ta biyo bayan su tana faɗin"maza maza kuzo ku fice min daga gida,matsiyatan yara kawai"ko kallon ta basuyi ba suka wuce suka kama aikin su

Basu juma sosai ba suka koma gida,suka zayyane wa Auntyn Abinda Nadiya tayi musu amma suka mayar da ita mahaukaciya,sukayi ta dariya

Da yamma su Aunty Bintu suka raka Deeja gidan ta tamkar masu kai amarya, nadiya ta tsorata sosai ganin dawowar Deeja,ganin Deejan babu alamun damuwa a tare da ita ya firgita Nadiyan,amma sai tayi tsammanin ko ta san da tafiyar da Khalees yayi ne, kasancewar Khalees yaje wata seminar a Abuja jiya,Kuma bazai dawo ba sai bayan sati uku

Su Aunty Bintu suka gama abinda ya kawo su suka tafi, Nadiya na ganin sun tafi  sai tayi azamar shigowa

Deeja na zaune tana shayar da Affan Nadiya ta shigo,kallo ɗaya tayi mata ta ɗauke kanta,don ta san ko ma menene ya kawo ta ba na arziki bane,don ko sallama batayi ba. Nadiya ta dube ta a wulakance tace

"Ai dole ki ɗauke kanki,don ni na baki damar shigo min gida har zan shigo in da kike ki ɗauke kai,wato kinji labarin miji na baya nan ko?hakan yayi kyau,amma ki shirya karɓar tanade tanade da nayi miki......."

Karatun Alkur'ani Deeja ta sanya,ta janyo airpiece ta saka a jikin wayar ta toshe kunnuwan ta dashi hakan ne ya tilasta wa nadiya ficewa daga ɗakin tana jan tsaki,a ranta tana ayyana ko me zatayi sai tayi don ganin ta kuntatawa Deeja

Daga lokacin ya zamana kowa harkar shi yakeyi,sai dai Nadiya ta tsani ta buɗe idanu taga Affan,ta tsani yaron tsana mafi munin,don haka ta sha alwashin sai taga bayan shi,har da uwar tashi ma

Har da zan ɗauki hutun ma'aikata na yau nima,kawai sai nayi tunani na fasa😁😉

Ayi min afuwa biki mukeyi shiyasa akaji ni shiru

#Nusy_bee

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.