Free chapter · Read without an account

9: Takaran gaskiya

by fatima muhammad bello · TUDUN ADAMA

Tashera ta lura a bayan ta kawo karshen adeela, nata karshenne zezo, seta kallo gumza tayi mata signal. Gumza ta sulale jiki ta fice daga dakin batareda an gantaba.
"Oho! Haba! Nide nayi mamakinda ta fito daga wurin buyanta ta dosa jangwale bayan kowa na guduwa dagashi. Wato jawo miki shi tayi donya lahantaki!" Paipai tace tana kallon tashera.
"Amma shine kikazo kika kawo karan cewan itace keda laifi bayan a zahiri kece me laifi!" Sintura ta bayyana.
Bakin tashera ya bushe, canta kalla sarauniya wadda a yanzu ta canza kallonda take mata ya zama na tuhuma.
"Sarauniyata.........."
Sarauniya hubba ta daga mata hannu. "Gaskiya kawai nakeso tashera!" Ta hade rai.
Tashera ta sunkuyar da kai. "A halin yanzu ba abinda zan iya cewa akan abinda paipai ta bayyana. Tsakaninada adeelane maganata."
Kowa yaji mamakin kalamanta akayi jigum ana son a fahimci meke tsakaninta da adeela?
Sintura ta tunzura da cewa yanzu hukunci ya koma kan tashera, karyarriyar soja. Kuma kowa na bukatan a yankeshi yanzun nan!
"Bandamu!!!"
Kowa ya kallo kofan ana mamakin su waye.
Kwalafara, misau da dareja suka shigo suka tsaya gaban sarauniya. 'Yanmatan takaran mulki. Ana ji dasu ana saurarensu. Amma kowa yaji bala'in mamakin abinda sukace a yau. Gumza ta biyo bayansu.
"Kwalafara, meye dalilinku nakin amincewa a hukunta wannan karyarriyar sojan?!"
Kwalafara ta kalla tashera sannan ta maida kallo ga sarauniya. "Sojace me jarumta da bajinta. Akan karyar wannan kwaro za'a karyata soja a gaskata lebura!"
Misau ta matso gaba. "Aita gaya muna komai. Wannan kwaron bata sonta da alkhairi ko kadan. Batason kwarin tudun adama da alkhairi. Burinta taga ta durkushe tashera damu baki daya amma muddin muna nan, bata isaba wallahi!"
"Rayuka nawa tashera ta ceta, inma wani abune taga wannan kwaron nason cutar dasune shiyasa taga gwara su biyu su cutu akan kowa ya cutu. Shiyasa ta kauda jangwalen daga sauran kwarin."
Kan adeela ya harba. Kaji wani zance fa! Ya suke juye gaskiya ne akan wadda itama takaran mulki takeyi?!! Kai! Da wani abu a kasa.
Kowa ya fara tunani ana kallon tashera da jarumta. Duk wanda ze salwanta rayuwarshi dana wani mugu don ganin mugun be cimma burinshiba ai jarumine.
"Me zesa adeela taso cutarda kwari? A kira wadanda suka santa zasu gaya muku wacece adeela da kirkinta da taimakonta dason ganin lafiya da cigaban tudun adama. Shiyasa ta....." Sintura ta tsaida bakinta kafin ta fasa kwan gameda shigan takara na adeela.
Jaguwa ta kallo sintura. "Shiyasa tayime?"
Kallon adeela sintura tayi, adeela ta daga mata kai. Tabata go ahead ta fallasa.
"Adeela nason ta shiga takaran mulkin tudun adama."
Shiru. Can tashera, gumza, su kwalafara da wasu leburori dake wurin suka fashe da dariya. Lallai adeela da dogon buri take. Wai tanason zama sarauniya! Sarauniyar tudun adama!! Suka sha dariyarsu.
"Wasu zai basu dariya amma kudurinta kenan. Me wannan kudurinne ze cutarda kwari?"
Sarauniya ta kalla adeela da kyau. Ta tuna wannan kwaron itace bayan haihuwarta aka gano baza tayi kwarin zama daya cikin yaran sarautaba. Shiyasa ta jefata cikin leburori.
An kyankyasota da siririn jiki, cikinma wani tababbe kaman baze budeba. Ba wanda ma yasha zata rayu don dukta fi sauran kwarin kyankyasanta rashin girma.
Amma kalleta yanzu, tayi girmanta, cikinta yayi tsawo yana girma ita kanta tayi tsawo Kuma daga ganin yanda jikin yake, akwai alaman ita lafiyayyace zata iya daukan ciki. In banda bugu da gajiya dake tareda ita, zata iya yin takaran. Gashi ta kusa kamo tashera wurin girman jiki.
Abinda ta gane a rigimansu shine, tashera tayi ikirarin ganin adeela nason cutarda kwari shiyasa ta bada wannan mugun shawaranda yayi sanadiyan rasa rayukan kwari. Ta amshe ma adeela wahalanda tayi.
Hukuncin shine koran abada daga tudun amma kuma saboda 'yanmatan sarauta sun sama tashera baki, yanzu hukunci ya canza.
"Me kuke bukata yanzu?" Sarauniya ta tambayesu.
Adeela ta kalla tashera taga tana murmushin mugunta. Zasu kulla mata wata tsiyan kenan.
Kwalafara ta kalla adeela ta maida kallo ga sarauniya. "Muna bukatan takaran gaskiya don nunawa tudun adama karyan wannan kwaron da kuma nunawa tudun gaskiyan tashera."
Tabdi! Takaran gaskiya wahala da hatsari gareshi. Da farko de 'yar takaran ta farko zata bada gwaji uku na ra'ayinta. Sannan ta biyuma ta bada nata. In aka gwada gwajin, se sarauniya ta zaba kwara uku kawai ta bada a matsayin takaran da zasuyi. Sanin adeela da tashera, bazata bada gwaji me saukiba. Amma bari taji nata gwajin.
Gwajin tashera ta farko shine. Gwajin bajinta, zasu kara itada adeela aga wayafi wani karfin jiki dana zuciya. Inde a karfin jikine, adeela batadama dama amma in ana zuciyane, adeela ba kwaro bace me tsoro.
Na biyu shine gwajin atisaye, don gano jajirtan kwaro da juriya. Adeela akwai naci akan abu, in tasa kanta to seta yishi. Kuma tanada jure abu komin wahalanshi ce taci nasara. Na uku, gwajin gudu, don iya tserema hatsari. Dama adeela ba bayaba wurin gudu harna tsiya kuwa. 
Duk wadannan gwajin na sojojine saboda haka yayima adeela dadi donba duka za'a daukaba tunda ita ba sojaceba.
"Munji naki gwajin. Kefa?" Para ta kalla adeela.
Sintura ta matso gaba. "Sarauniyarmmu, adeela ta samu rauni saboda dukanda tashera tayi mata. Inma zatayi takaran, zefi dacewa a barta ta farfado tukunna."
Hakane. Ka'idan takaran kenan. Se duka 'yan takara suna cikin koshin lafiya za'a iya aiwatar dashi. Sarauniya ta gyada kai.
Para ta kallo adeela. "To amma ke bamuji naki gwajinba?"
"Yanzu kaina ciwo yakeyi, bayan na warke, zan fada muku nawa gwajin a rananda za'ayi takaran gaskiyan."
Hauka takeyi ta fada musu gwajinta kafin a fara takara, tashera ta nema rigakafi! Ba dama! Hm, dama tasan inda tashera takeda rauni, wannan zatayi amfanida ta kasara matar. Bade mugunta takeji dashiba? Zataga abinta!
Amma har yanzu wani abinda ya daurema adeela kai. In tashera tana daga cikin 'yan takara, ai zata zamo masu kwalafara cikas. To meyasa suka goya bayanta? Kota musu alkwarin wani abune?
To inma alkawarinne waye zewa wani? Wazeci alfarmar wani? Sufa 'yanmatan sarautane itafa? Dole ta bincika ta gano meke faruwa kafin su kara daureta batada madafa. Tanada kwarinda zasu mata bincike su gano makarkashiyanda tashera dasu kwalafara ke kullawa.
Haka nan aka kira hisu, me bada magani ta tafi da adeela dakin magani don kula da lafiyanta harta warke. Kowa ya watse aka bar sarauniya da manyan tudu su cigabada tattaunawa.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.