Free chapter · Read without an account
15: Bayyanan gaskiya
Duk ilahirin jama'an tudun adama sun hallara a katoton fagen wajen tudun domin gudanarda takaran gaskiya. Adeela na tsaye tareda tashera a tsakiyan fagen, kwari sun zagayesu. Gangaren tudun sarauniyace da shugabannin tudun a gefe. Ga yaran sarauta gefenta tareda masu kula dasu.
Sintura na tsaye tareda nata yaran ta kallo jera wadda take tsaye ta dayan bangaren tana kulada nata yaran sarautan. Suka hada idanu, jera ta kauda idonta daga sintura ta kallo tashera.
Tashera ta kalleta ta mata murmushi. Ta kallo tseela ta dan murmusa mata. Tseela ta lurada murmushin be kai zuciba abin ya bata mata rai. Ashe ita kadai keta kidinta da rawarta kuwa donko tashera amfanida ita takeyi.
Idanun tashera suka diran kan wadda taso kamawa amma abinya faskara saboda kawai bat, ta bacene a tudun. Bompai taga ta fito daga cikin taron kwari ta tsaya tana kallonta, kafan daya a daure inda ta karya mata da icce.
Kallon tsana ya bayyana a fuskan tashera ta kallo jera. Nufinta zatasa a kama bompai se jera ta zauna tareda sojojinda zasu fake bompai din. Jera ta kalleta ta kauda kai. Mamaki ya bayyana a fuskan tashera se kuma ta dake.
Ta kalla binturai. Nufinta binturai ta kamo bompai a.......binturai ta linke hannayenta a kirji, nufin ba abinda zatayi. Hakan yasa tashera taji wani luuu. Meke faruwane? Bade suna mata tawaye bane? Meyasa zasuyi mata haka?
Kallonta ya koma kan kwalafara, tayi mata murmushi. Ta kallo dareja, ta gyada mata kai. Suna tare kenan. Bari ta gama da takaran nan se taji dalilinda zesa wata karamar soja kaman binturai zata ketare magananta!
Shiyasa tafi son gumza duk cikinsu tafiyi mata aiki yanda ya dace. Waima ina take? Tashera ta hango pitinau gabanta ya fadi. Kenan......to amma idan gumza bata cika aikinba ina ta shigene duk lokacin nan?
Adeela ta kallo pitinau da sintura sukayi kallon kallo, ta maida idanunta kan zimba daga nan ta kallo binu sukayi kallon kallo. Ta kalla tashera taga ta dan rude. Abin ya bata dariya da mamaki.
To dama me take tunani inta yada na kusada ita? Ko in na kusada ita suka gano gaskiyanta? Yau zata gane kawayenta sun gano bakin rayuwarta. Karyanta yau ze kare!
Suruttai se tashi sukeyi tsakanin kwari. Sunyi mamakin jin wai a yau a tudun adama ne za'ayi takaran gaskiya don samo gaskiyan soja akan lebura! Wannan abu da mugun mamaki yake.
Soja na kulada lafiya da zamantakewan kwarin kowane tudune. Lebura kuma ta tabbatar ciyarda kwari tudu da kulada yara da aiyukan tudu gabadaya. In an bukaci ayi takaran gaskiya, to lallaine an samu tangarda.
Wato ko an samu karyayyiyar soja, 'yar damfara kenan, ko an samu karyayyiyar lebura. To amma kowa yasan tashera, ita fitacciyace me gaskiya, rikon amana, kare rayukan kwari da kaunar hada kan kwarin tudun gabaki daya, yaushe za'ace itace karyayyiya!
Ga wadanda suka san adeela sunsha mamakin wai da ita za'ayi takaran. Adeela kwaroce meson jama'anta wadda zata iya yin komai don ganin ta kyautatama jama'anta. Ba'a taba kamata da wani mugun haliba, ga iya taimako koda abin yafi karfinta. Ta yaya akayi ta kare a wannan yanayi?!
Para ta daga hannu, kowa yayi tsit. "Na tabbatar dayawa daga cikinku se yau kuke jin abinda ya faru tsakanin tashera da adeela. Labari yazo muku cewa adeela tayi sanadiyan rasa rayukan kwari da suka fita samo ma sarauniya zaki. To haka muma yazo muna.
Amma musawanda adeela tayi tareda hujjoji daga paipai da wasu yaran tudu yasa mukazo ga wannan yanayi. A saboda haka, yau za'ayi takaran daze bayyana muna gaskiyan wannan rikitaccen lamarin."
A wancan lokacin anji gwajinda tashera ta bukaci ayi. Bayan dogon nazari, sarauniya tace tunda adeela ba soja bace, cikin gwajinda tashera ta kawo daya kawai za'a dauka. Wato na ukun, gwajin gudu. Domin kuwa kowa na gudu, ba soja ba lebura. Shine yayi daidai ayi gwaji da.
"Adeela ki sanar damu gwajinda kike bukatan ayi domin sarauniya ta zaba wanda zakuyi." Para tace.
Adeela ta kalla tashera kallon yau kin kade. "Gwajin cin gizo, gwajin shan zuma, gwajin samo kafan fara."
Wuri yayi tsit. Wanne irin gwajine haka?! Hala de adeela wasada kwalkwaluwarsu takeyi? Menene haka? Kota dade bata sha zuma ba, bataci gizo bane shiyasa ta kawo wannan zancen? Shugabanni suka kallota cikin jin haushi. Wannan ai rainin hankaline.
Ganin fuskokin kwari kowa ya kasa gane dalilinta na zaban wannan gwaji, adeela ta bayyana musu. Ita leburace kuma ta kware wajen samo abinci. Sojoji nacin duk abincinda suka kawo. Saboda haka, gwajin cin gizo da shan zuma aiba abu bane me wahala ga dukkansu. Ze nuna karfin jikinsu wajen jure kowane irin abincine zasuci.
Tashera taji gabanta ya fadi, bade adeela ta gano asirinta bane? Shiyasa ta rattaboda zancen nan? Amma taya za'ayi tasan haka? Tanata kallon adeela cikeda tunani.
Adeela ta tunatar musu da cewa dama ta koka musu da cewa itace ta samo kafan faran amma tashera ta amshe. Kowa akaki yarda da ita a lokacin, to yau se tasheran ta nuna bajintarta wurin iya samo kafan faran.
Hakane, sarauniya ta gaskata. Dumu ma ta amince tunda tasherace ta kawo mata kafan faran. Ina lebura ina iya samo kafan fara ai hatsarin yayi yawa. Amma soja meji da karfi ita zata iya samo kafan ba matsala.
Sarauniya ta amince ayi gwajin gudu, gwajin shan zuma da gwajin samo kafan fara. Nan fa tashera ta rikice. Tayi saurin kallon adeela taga ita bata damuba.
Ai dole tashera ta shiga damuwa don duk abinda adeela ta bukaci ayi ze mata illa a jiki. A sha zuma! a samo kafan fara!! Ai ita.......
Para ta sanar musu da cewa, tunda sarauniya ta amince da gwajinda 'yan takaran suka kawo, se a fara dana shan zuma don gwaji na biyu dana uku zasu hadene, donko da sun samo kafan faran ai dole suyi gudun rai.
Nan take fira me kulada abinci ta iso tareda wasu leburori mata biyu masu rikeda kokon zuma. Suna isowa ta umurcesu dasu mikawa 'yan takaran. Adeela ta karbe ta shanye ta maida kokon ta kallo tashera.
Kallon kokon tashera tayi ta kalla adeela. Meyasa adeela ke kallonta hakane? Ta karba ta kalla zuman se murmushi kadan ya sauka a lebenta. Ta kurbe ta mikama leburan kokon ta kalla adeela.