Free chapter · Read without an account

17: Yafiya

by fatima muhammad bello · TUDUN ADAMA

Dole sarauniya da jama'an tudun adama su nemi yafiya daga wurin adeela na rashin yarda da rashin mutuncinda suka mata. A yaude sun gano cewa tashera makaryaciyace, munafukace, muguwace.
Sunyi matukar mamakin wannan al'amari. Ba'a taba samun soja karyayyiyaba se a wannan karon. Haka bayan mutiwarta kwari suka dinga fitowa bada jawabin halayen tashera.
Sarauniya da shugabanni abin har daure musu kai yayi da sukaji abubuwanda takeyi a bayan idonsu. Suka Yi hamdala da mutiwarta donta zama annoba.
Aka kira adeela a dakin sarauniya tareda shuganni. Adeela ta shigo ta tsaya gaban sarauniya.
"Adeela, kin zamo abin alfahari a tudun nan. Anso aci amanarki a miki rashin adalci a koreki daga tudun nan amma kika ki yarda kika kuma nuna jajircewa wurin samun gaskiya.
Muna godiya da kika bayyana muna gaskiyan ki kuma kika bayyana muna karyar tashera. A dalilin haka, ni sarauniya hubba na amince da ki shiga takaran sarauniya."
Adeela ta murmusa cikin jin dadi. Yau bakin cikinta yazo karshe. Yau mafarkinta ya zamo gaskiya. Yau kudurinta ya kusa cika. Ba me mata bakin ciki bame hantararta. Hanya sumul.
Bompai, tseela da jera suka shigo suka tsaya gefen adeela.
"Muna neman yafiya ki adeela. Muna kuma neman alfarmar daga gareki ki samu cikin manyan sojojinki."
Abin mamaki. In aka taba cema adeela ranan me kaman ta yau na zuwa aise ta karyata. "Na yafe muku kuma na amince ku zama na hannun damana."
Murna ta bibiyesu sukayi godiya suka fita. Sarauniya ta kalla unnurnu. Itace me kulada 'yanmatan sarauta.
Unnurnu ta kalla adeela taga eh ta dace da inda akeso a sata. "Adeela, daga yau kin zama 'yar takaran sarautar mulkin tudun adama. Sarauniya ta amince a bude miki daki don shakatawa kafin takaran."
"Godiya nake sarauniyarmu."
Dumu ta kalleta tana kesa bajintarta. "Gaskiya adeela da bamuga yanda kika samo kafan fara me raiba da bamu yarda ke kika samoshiba."
Jaguwa ta gyada kai don adeela ta bala'in burgeta. "Kin nuna muna kin kece tunaninmu. Kece lebura me karfin soja!"
"Lallai da munyi hasaran shugaba kamanki da munyi nadama."
"Ina so in inyi amfani da wannan daman in roki yafiya daga ke adeela." Sarauniya tace.
Adeela tayi mamaki, yafiya na biyu kuma daga sarauniya! Me tayi mata da take neman yafiyan?
Lokacinda sarauniya ta haiho kwayaye, kwan adeela shine mafi girma daga sauran. Akayi zaton za'a kyankyasa kwaro mafi girma ta zama sarauniya ba takara.
Yana faruwa idan aka samu kwai me girma aka kyankyasa. Seta zama sarauniya ba me ja mata cikas. Dukda akwai sauran yaran sarautan, su suna nan ne in case wani abu ya faru da ita. Har sa mata suna tayi adeela, wato alkali kenan don ita zata mulka tudun adama da gaskiya da rikon amana.
Amma se akayi rashin sa'a bayan kyankyansata seta fito a karama, tayi tamoji kaman wata tsohuwa, in fact itace mummunan tsutsanda ba'a taba yiba a tahirin tudun adama.
Duk zaton arziki da akayi akanta ya zube. Zuciyoyin sukayi sanyi, haske ya dishe. Ba yanda sarauniya ta iya illa ta maidata gefen leburori. Dukda haka tana sa a dubata in bata mutuba don gaskiya ko numfashinta ba daidai bane.
Amma da yake tanada sauran rayuwa, ita kanta sarauniya seda abin ya bata mamaki da taji uwar kulawa da adeelan, shafatuo ta gaya mata cewa tsutsar da shiga rayuwa ta uku.
Rayuwar kiyashi ta kasu kashi hudune kafin su girma. Kwai, tsutsa, tsaka-tsaki sannan se su girma su zama kwari. Kenan adeela tana tsaka-tsaki!!! Taje da kanta don ganin ikon Allah.
Seko gata cikin koshin lafiya dukda de batayi wani girmaba. Sarauniya ta kesa aikin shafatuo tace mata ta cigabada kulawa da adeela da kyau. Tana kyautata zaton akwai wani babban al'amarine jingine da kwaron.
Aiko batayi karyaba domin haka adeela ta fita daga rayuwa ta uku ta zama kwaro. Sarauniya tana sha inta zama kwaro ta fara girma domin tanada structure din yaran sarauta amma se aka samu akasi. Dole aka barta a matsayin lebura.
"Duk laifinane sarauniyata!"
Kallo ya koma ga wata tsohuwa data shigo tana dingishi. Tace sunanta inya, itace take karban haihuwan sarauniya. Da aka haiho adeela taso abata ta kula da ita kafinta shiga rayuwa ta biyu.
Se akaba shafatuo. Tun daga lokacin se tsanar shafatuo da son ganin batayi nasaraba wurin kulada kwan ya shiga ranta. Tayita rage abubuwa daga cikin abinci da maganin adeela.
Shiyasa takiyin girman daya dace tayi. Hakan yayima inya dadi donko daga baya dole yasa aka tura adeela gefen leburori ita kuma inya kwanda ta kulada ta zama soja, tashera.
Furta sunan tashera aka gano inda ta samo asalin mugun halinta, wato daga wannan inya dinne! Kowa na mata kallon kiyayya da kyama. Ashe sumin tabi sukaji, ga gagarumin labari na zuwa.
Inya ta kudurama tashera a ranta cewa seta zama wata babba a tudun adama. Shiyasa ta jajirce wurin jawo jama'a da nuna bajinta a tudun tunda ba yanda za'ayi ta iya zama sarauniya seta kama abu na gaba da ze yiwu, shugaban sojoji.
"Tabdi!" General para ta furta. Waita zama shugaban sojoji. Kenan tayita kashe jama'a ba kabkabtawa.
Ta tursasama tashera tsanan adeela da son ganin ta tabe a tudun saboda daga baya ta lura adeela na budewa da girman jiki, kenan yana samun abubuwa tanaci. Inta cigabada budewa haka zata koma asalin jikinta kuma zata koma asalin matsayinta, sarauniya ba takara.
Yaushe inya zata bari shafatuo tayi nasara afi fifitata akanta? Shiyasa tasa tashera ta dinga takurama adeela, ta tabbatar ba'a ba adeela abincin gina jiki sosai, ta addabeta da rayuwarta a tudun adama.
Da hakan beyiba, inya tacema tashera tasan yanda zatayi tasa a kori adeela daga tudun, wanda hakan ya kawo karshen tashera. Inya ta kalla adeela tace ta yafe mata ta gafarta mata tayi kuskure.
Babban kuskure ma. Wato inyace tayi sanadiyan rashin girman adeela! Tasa akaki bata abinci me gina jiki, tasa tashera ta tsaneta tana takura mata, duk hakan be ishetaba seda tasa tashera koran adeela daga tudu!
Shine take son adeela ta yafe mata wannan babban zunubin data aikata!! In fact kowa yaji takaicin abinda inya tayima adeela saboda bakin cikinta da mugunta. Inma adeela ta barta sukama bazasu bartaba don batada wurin zama a tudun adama.
"Nina yafe miki amma ina rokon sarauniya data hukuntaki daidai da hukuncin tudun adama."
"Haka ya kamata!"
"A hukunta muguwan!"
"Babu wurin irnki a tudun nan!"
"A bisaga laifinda kika aikata inya, na tarema adeela wuri a tudun adama, Mun koreki daga tudun adama. Ki hada yanaki yanaki kibar tudun yanzunana!"
 
Adeela ta fito daga cikin dakin sarauniya, murmushi bayyane a fuskanta. Yanzu ta gamada tashera da mukarrabanta. Sauran takaran gaba.
"Muna rokonkibdaki gafarta munanki yafe mana."
Waigowan adeela taga kwaron nan ce data mata duka lokacinda ta fito motsa kafa. Ai dama tace zasu dawo neman gafarta sun ganin kaman wasa takeyi.
"Komai ya wuce."
Sukayi godiya kawunansu kasa sukayi gaba. Aka murtsuke adeela cikin runguma da ihun murna tasankare. Ashe pitinau ce da sintura suna murnan ganin komai ya warware.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.