Free chapter · Read without an account

CHAPTER TWELVE

by Rahinat Hussein (R.Hussain) · TAEESH

Dan na zo cin arziki gidanki shi ne kike korata, me na tsare miki, saboda Allah" ta kuma rushewa da kuka.

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun me ke faruwa ne haka?" ce war Malam Ali, ya na ɗaukar TAEESH, " alkur'an yaya Ali kawai don ta ga na yi maka wanki shikenan ta zo hau ni da faɗa, don na yi maka wanki aibu ne?" Ali ya kalli A'i cike da ɓacin rai, ya ce" laifi ne don ta wanke min kayana, kinsan za ki ji kishin kika sa ƙafa ki ka fice gantali" A'i da tun ɗazun ta kasa magana, sai yanzu ta ce "wallahi Malam ban aibata Wasila ba, hasalima ita ke faɗa min baƙaƙen maganganu, amma don Allah ka yi haƙuri" ta ƙarasa maganar zuciyarta na karaya, kawai daurewa take yi ne.

Ali ya ce" banason shashanci, sai ka ce wasu ƙananun yara me ye abun gori, to ina ma abun yake har da za ki na yi wa ƴar'uwata gori akan sa, kin bani mamaki A'i ban taɓa zaton haka daga gare ki ba" sai lokaci Wasila ta tsaya da murza ido, ta kama bakin zanin da take matsar hawayen ƙarya da shi, ta soke a ƙugu ta ce" bakomai ai akwai Allah, kuma alkur"an duk kaidin da makircin mace bata isa ta raba hanta da jini ba". Ya isa haka Wasila banason zancen, kun yi sallah ma kuwa?" kai A'i ta zirgiza alamar a'a, ta ɗauki buta ta nufi randa ta zuba ruwa.

Wasila ma ta ɗauki ɗayar butar ta nufi banɗaki.

TAEESH ya tisa a gaba ya hau yi mata wasa, tana ta ƙyalƙyala dariya, shima sai dariyar yake yi, yana tsananin son TAEESH, fitilar da suke amfani da ita, wacce take kwalba ce da kalanzir ɗ sai lagwani sili ɗaya A'i ta ajiye musu. Abinci ta kawo ta ajiye, ganin ko kallonta bai yi ba, yasa jikinta duk ya yi sanyi, a hankali ta ce" kawo ta nan ka ci abincin" a dakile ya ce" barta kawai tare zamu ci da ɗiyata" zama ta yi a gefen tabarmar ta ce" don Allah Malam ka yi haƙuri ko me Wasila za ta ce min, ba zan ƙara kula ta ba, bare har ta kaimu ga sa-in-sa, ka gafarce ni malam. Ya ce " ai ya wuce dama ni fitar ce ta ƙona min rai sai magariba sannan ki ka dawo haba, don Allah ki kiyaye ɓacin raina" ta ce" hakan ba za ta sake faruwa ba in Allah ya yadda" take komai ya wuce, yau faten doya da wake ta yi musu, tare da TAEESH su ka ci, duk abin nan da ke faruwa akan idon Wasila, tana jikin labulen ɗakinta tana kallonsu, ƙwafa ta yi gami da cin alwashin sai ta auri Ali, kuma sai ta kori A'i da TAEESH daga gidan.

Washe gari tamkar babu abin da ya faru, da fara'a A'i ta ce" Wasila yau Inna ta zata zo me ya kamata mu dafa mata?" taɓe baki Wasila ta yi sannan ta ce" yo ni me ye ruwana, in yi magana ki sake haɗa ni da ɗan uwa na ya kore ni, hmmm don ma mai fahimta ne" A'i ta ce" kinga Wasila ni ba tashin hankali nake nema ba Allah ya baki haƙuri" rarrafowa TAEESH ta yi, ta ja farantin shanyar barkonon da A'i ta yi ta zubar, da sauri A'i ta nufi wajen, ta na faɗin " oh-oh-oh ni Aisha, wannan ta'ari naki TAEESH ya ishe ni, ni kenan ba dama na ajiye abu a ƙasa, Allah ya raya min ke" Wasila kuwa da take zaune ta na sana'ar ta-ta na sakace, ta cire tsinken da take sakacen ta ce" ba dai ku masu tausayi ba, kuna riƙon shegiya wacce ba tada asali, ai alkur'an ita za ta yi ajalinku a dai juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe ato ka ji".

A'i ba ta tanka mata ba, saboda yanzu ƙiris Wasila take jira, ta haɗa mata gobara a wajen mijinta, A'i ta ɗauko wake ta surfa shi, sannan ta wanke, sanin Innarsu na son alala, leƙawa zaure(soro) ta yi don samun yaron da zai kai mata markaɗe, Safwan ta hango ya manno da tayarsa yana garawa.

Kiransa ta yi, ta na faɗin " yauwa ɗan albarka zo ka kaimin markaɗe, kawo tayar taka na ajiye maka" karɓar tayar ta yi, ta bashi naira talatin, ya ɗauki markaɗen ya tafi.

Babu layi sosai, nan da nan ya dawo, godiya ta yi masa, ta ba shi alewa yana murna ya ɗauki tayarsa ya tafi. Nan da nan ta gama dafa alalan ta zubawa Wasila nata a kwano ta miƙa mata ɗaki, Wasila ta na ta bacci, don bata taya A'i aiki sai bacci, ko cangal bata yi a cikin gidan.

Sallamar su Inna ta jiyo, "assalamu alaikum" da murna ta amsa "waalekumussalam, sannun ku da zuwa, a'a amarya har da ke" Rabi (autarsu) ta yi murmushi tana faɗin " ai gidan na zo, na ji Inna ta ce za ta zo gidanki shine na biyota" ɗaki suka shiga, TAEESH na gado baje tana bacci, Inna ta kalleta ta na faɗin " kai Allah ya kyauta wannan taurin kan na Ali, duba ki gani ba su da niyyar mayar da ƴar nan" Rabi da ke da son yara, ta ce" kai Inna ai alkur'an ko ni ce bazan mayar da ita ba, kyakkyawa da ita, ai ba laifin ta ba ne, ita me ta sani ma a duniya" ke dalla rufe min baki, ai ke da A'in duk ɗaya marasa zuciya" ta ƙasara da galla mata harara.

Ruwa da alalen A'i ta kawo musu, ta na gaishe da Inna, zama ta yi tana ta washe baki don murnar ganin mahaifiyarta, Wasila ce ta fito, jin hayaniyar su yasa ta san baƙin sun iso, da sauri buguzu-buguzun ta nufi ɗakin A'i, ta ɗage labulen ta shiga bin su da kallo, sannan ta ce " baƙi kika yi, hannunku da zuwa" Inna ta ce" ina wuni" Wasila ta amsa "lahiya lumi, ta saki labulen ta juya, Rabi ta ce" Yaya Ai wacece wannan?" A'i ta ce "ƙanwarsa ce ta zo, daga garin Dumama take" amma ba ta da hankali ko ya...Ka fin ta ƙarasa magana muryar Wasila ta karaɗe ɗakin "Uwarki ce mahaukaciya.........

CIROMA UBAID FAM

Gaba ɗaya iyalan nasa suna turakarsa, Hajiya Binta, Hajiya Nafisa, Hajiya Sadiya, kowacce sai faman sannu ranka ya daɗe take yi, Abubakar da Dawud na tsaye, "ka samu Dr. Salim ɗin?" ce war Abubakar, Dawud ya ce" har yanzu bai amsa ba, i think ba ya kusa da wayar" Abubakar ya ce" mu tafi asibitin kawai" Ciroma Ubaid ya ce" a'a ba sai an je asibiti ba, ai cikin nawa ya lafa, na samu sauƙi ku tafi kawai" Hajiya Binta ta ce" haba ranka ya daɗe wana irin mu tafi, to kuwa dole a sanarwa da mai martaba halin da ake ciki" yunƙurawa ya yi zai tashi, da sauri Abubakar ya kamashi, jingina ya yi da fuskar royal bed ɗinsa. "Kar wanda ya kira ɗan uwa na ya tayar masa da hankali" Usman autansu ne ya shigo, yaron bai fi shekara bakwai ba, ya ce" Abba ba ka da lafiya?" murmushi Ciroma Ubaid ya yi, ya na kiran yaro da hannu, gadon ya hau, Ciroma ya ce" eh amma na samu sauƙi, ya mai martaba yake, ka je fadar?" Usman ya ce" a'a ai daga school muka dawo, Abba Khadija ta yi faɗa a school, kuma ta yi zagi, wayar Dawud ce ta hau ringing. "Dr. Salim ne" ya faɗa yana picking call ɗin "hello afuwa ranka ya daɗe wayar tana office ne, na fita duba marasa lafiya ne" Dawud ya ce" ka zo gida ka duba Abbanmu" Dr. Salim ya ce" subhanallahi me ya same shi, gani nan- gani nan zuwa ranka ya daɗe" ya faɗa yana harhaɗa papers ɗin da ke kan table ɗinsa, ba tare da ya jinkirta ba, ya bar kmc hospital.

"yauwa ai gara ya zo, amma a zauna da cuta" ce war Hajiya Sadiya, a hankali Ciroma Ubaid ya ce" kun yi waya da Yayanku?" Abubakar ya ce" eh Abba, Allah ya ƙara maka lafiya" ma sha Allah, ce war Ciroma, ina so na ɗan huta ku je daga waje" gaba ɗayan su, suka tashi, suna yi masa fatan samun lafiya, Usman ne ya sauka ya ce" Abba Allah ya baka lafiya" murmushi ya yi, yana shafa kan yaron yana amsawa da amin ya Allah.

Cikin ƙasa da minti ashirin Dr. Salim ya iso, ɗauke yake da brief case ɗinsa a rataye a kafaɗarsa, dogarai ne suka ga zuwansa hakan yasa suka san akwai abin da ke faruwa a cikin gidan. Gaisawa su ka yi sama-sama ya shige ciki, darect ɓangaren Ciroma Ubaid ya nufa, iso akai masa ya shiga, duk suna parlor har da ƴan matan wato su Fa'iza, Aisha, Zainab,Abida, da Khadija , duka su biyar ɗin, yana shigowa, ya zube don kai gaisuwa ga iyalan, Hajiya Binta ta ce" tashi-tashi mu je ka duba shi, tun jiya bai yi bacci ba, kuma yaƙi yadda mu kai shi kmc hospital ɗin" tana maganar suna nufar turakar Ciroman.

Zaune yake da cazbaharsa kamar kullum, don mawuyaci ne a ga hannunsa babu carbi, da sallama suka shigo.

"Allah ya taimake ka, ya ƙara maka maka lafiya, me yake ciwo?" ce war Dr. Salim, Ciroma Ubaid ya ce" ciwon ciki ne, kuma Alhamdulillah na samu sauƙi" Dr. Salim ya ce" ranka ya daɗe, ya kama a yi scanning don musan wana irin ciwo ne, meye yake causing ɗinsa" Hajiya Nafisa ta ce" wannan gaskiya ne, ranka ya daɗe" Ciroma Ubaid ya ce" to shikenan bari na fito sai mu tafi.

Cike da farinciki suka ce a fito lafiya, suka bar cikin turakar. Bai daɗe ba ya fito, sanye yake da blue ɗin shadda da farin rawani, da farin takalmi irin na sarakai, duk abin da yake yana yi ne cikin ƙarfin hali, don cikin ya matsanta masa.

"lafiya bajimi na mijin zaki, Allah ya kare gabanka da bayanka ɗan sarki jikan sarki, gaba salamu baya salamun" dogarai sukai ta kirari ga Ciroma Ubaid, kawai hannu yake ɗaga musu, Dr. Salim ya shiga motarsa, su kuma suka shiga ɗaya daga cikin motocin da ke harabar gidan. Daga shi sai Abubakar, sauran suka koma ciki.

Tunda aka zauna a fada, Sarki Suhaid yake jiran ganin shigowar ɗan uwansa Ciroma, har akai sallar azahar bai ganshi ba, kasa jurewa ya yi, ya ce" lafiya kuwa banga Ciroma ba?" take sallama ya ce" Allah ya baka nasara yanzun nan, bayan na fito daga masallaci na ji sarkin gida yana faɗin sun tafi asibiti tare da likitan da ya zo duba shin ma.

Hankali sarki Suhaid ne ya tashi, take ya fara shirin miƙewa, da sauri dogarai suka miƙe gami da baza babbar riga, suka kare sarki, " a tashi lafiya ɗan toron giwa, Allah ya bawa Ciroman Hauren Giwa lafiya mai amfani, Allah ya taimaki Sarki mai adalci" sai da suka tabbatar ya tashi, sannan suka matsa, a hankali ya ke takunsa, ya na faɗin " a fito da abin hawa, za mu je asibiti, kafin ya rufe baki, tuni an fito da mota mai tsada, duka bayin da ke harabar gidan suka dinga zubewa suna kai gaisuwa, yana shiga mota ɗaya daga cikin driver's ɗin gidan ya ja, wata motar ce ta rufa musa baya, Shamaki, da Matawalle, daTuraki har da ɗan Maje ne a ciki.

Daga bayansu kuma motar Dogarai ta rufa musu baya.

Da gudu Batula ta shiga sashin Fulani Rahama ta na kishingiɗe Ruƙayya na yi mata yankar farce, a gaban Fulani Rahama ta zube ta na faɗin " ranki ya daɗe, mai girma Ciroma ne ba lafiya, an ce yana asibiti, yanzu nan mai martaba ya tafi can.

"Innalillahi wa' inna ilaihirrajiun, me ya same shi haka?" Batula ta ce " wallahi bansani ba, Allah ya ba ki nasara" addu'a ta yi masa da fatan Allah ya ba shi lafiya.

A ɓangaren Fulani Tagabas kuwa ta na jin labarin rashin lafiyar Ciroma Ubaid, murmushi ta yi, tana fatan ina ma ya mutu, don burinta ne a ce Ubaid ya riga Sarki Suhaid mutuwa, duk da tasan shi yana da magada.

Fulani Zaitun na jin labari, ta nufi sashin Fulani Tagabas, cikin tashin hankali, tana zuwa taga hankalin Fulani Ta gabas a kwance, ta ce" Fulani shin ba ki da labarin Ciroma yana kmc hospital?" Na sani, sai me kuma.............

Zinariya ce✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.