Free chapter · Read without an account
Chapter three
Iyalan Gidan BABA
Rtd Brigadier General Isa Saleh, wanda kowa ke kira Baba, tsohon babban jami’in soja ne da ya yi fice a Rundunar Sojan Najeriya. Sananne ne sosai — mai iko, daraja, tarbiyya, da suna da ya wuce iyakokin kasa.
Shi cikakken Hausa-Fulani daga jihar Adamawa ne, kuma ya gina rayuwarsa akan tsantsar disiplini da gaskiya.
A lokacin aikinsa, ya shugabanci manyan ayyuka, ya yaƙi rikice-rikice a Arewa maso Gabas, ya yi muhimman wakilci a ƙasashen waje.
Yanzu da ya yi ritaya, yana zaune cikin Adamawa tare da matansa biyu — Maami da Aunty, da ’ya’yansa guda bakwai — dukkansu maza da mata, manya da kanana, wasu sun yi aure wasu ko suna makaranta. Dukan su kuma suna koyi da halayensa masu ƙarfi.
Sai dai kuma, komai bai dawwama ba.
Watanni biyu da suka gabata, Baba ya fadi da safe — daga baya aka tabbatar da cewa ya sami “mild stroke.”
Tun daga wannan rana ne komai ya canza. Ko da yake hankalinsa yana nan lau, lafiyarsa ta jiki ta raunana sosai. Yana buƙatar kulawa da taimako daga likitoci da iyalansa.
Yanzu yana rayuwa cikin kwanciyar hankali da iyalansa, yana kokarin murmurewa, amma zuciyarsa cike take da abubuwa da yake son kammala kafin lokaci ya kure.
*********
Hajiya Karima Saminu Gidado, wadda kowa a gidan ke kira da Maami, ita ce uwar gida kuma matar fari ta Brigadier General Isa Saleh.
An haife ta cikin zuriyar soja, domin mahaifinta shi ne General Saminu Gidado, sanannen soja daga Adamawa wanda ya taɓa rike manyan mukamai a zamanin baya.
Maami ta taso a gidan soja, ta kuma auri soja, yanzu tana rayuwa a matsayin matan tsohon soja — daga karshe kuma ita ma tana da dabi’un soja.
Komai nata tsari ne, da disiplini, mai karfi.
Ko da yake ba ta taɓa aiki a hukumance ba, Maami tana kasuwanci sosai — tana shigo da kayan sawa daga Dubai da Turkey, tana da sunanta a kasuwa, kuma ta kafa gida mai cike da tarbiyya da nutsuwa.
Ta haifi yara guda hudu —
Colonel Junaid Isa Saleh (ɗan fari)
Dr. Salima Isa Saleh
Commander Hakeem Isa Saleh
da ƙaramar su, Bilkisu Isa Saleh
'Ya'yanta sune manyan cikin gidan. Ita da su suna da wata irin wayewar kai da ta bambanta su — saboda irin yadda Maami ta rainesu da tsauri da ƙauna.
Maami ba 'yar wasa bace. Idan ka yi sa’a za ta yi maka dariya, amma wanin zubi kuma, harararta kaɗai sai ya sa ka gyara zamanka.
Ta fi karfin nuna damuwa a fili, sai idan Baba yana cikin jinya ko damuwa — za ka gan ta tsaye hankali tashe.
*******
Hajiya Barrister Amina Gwadabe, wadda kowa ke kira da Aunty, ita ce mata ta biyu a gidan Brigadier General Isa Saleh. Duk da cewa ta zo bayan Maami, ta daidaita da ita cikin zaman lafiya da mutunci — kuma hakan ke karawa gidan kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Ba ‘yar talakawa bace. Ta fito daga babban gida — mahaifinta shi ne Alhaji Shamsu Gwadabe, attajiri kuma babban ɗan kasuwa a Arewacin Najeriya.
Bayan kasuwanci, yana da karfi sosai a fannin siyasa — dattijo ne da ake ji da maganarsa har a fadar gwamnati.
Barrister Amina Gwadabe ta karanci lauya, kuma ta yi practice a shekarun baya kafin ta koma gida gaba ɗaya. Duk da cewa yanzu ba ta fita aiki sosai, zuciyarta da tunaninta har yanzu na cikin doka da tsari.
She speaks softly, but carries herself with class and influence.
Ta kasance ‘ya ta biyu kuma ta karshe a gidansh.
Yayarta yanzu tana zaune a London tare da mijinta da 'ya'yanta.
Aunty ta haifi yara uku:
Bello Isa Saleh
Firdaus Isa Saleh
da Nabil Isa Saleh
'Ya'yanta su ne ƙaramin rukunin gidan,
*****
Colonel Junaid Isa Saleh, wanda kowa ke kira da Colonel J. Saleh, shine ɗan fari a gidan Baba.
Shi ne babban yayansu, kuma tuni ya kafa sunansa a rundunar sojojin Najeriya da matsayin soja mai daraja da kima.
A halin yanzu yana da shekaru 38 — but he doesn’t even look it.
Sai ka rantse cewa yana early 30s dinshi ne — young-looking, attractive, sexy, very tall and extremely well-built.
Mutane suna cewa “he’s huge like his father, but finer and calmer.”
Even with all that physical attraction, Junaid ba mutum bane mai jiji da kai ko almubazzaranci ba.
He’s a modest man, mai tsoron Allah kuma mai mutunci.
He's known for his discipline, silence, and strong values. Yana da ƙa’idarsa — he doesn’t bend easily. Maganar Junaid ba ta da second version.
He’s highly principled, shi yasa har yanzu bai yi aure ba. Yana ganin cewa yawancin matan zamani basu da kunya ko mutunci, kuma yana son mace mai tarbiyya da nutsuwa.
Best friend dinsa — Captain Fahad, da ƙaninsa Commander Hakeem kullum suna yi masa dariya suna kiransa da:
“The Old fashioned man”😂
Junaid yana da lafazin Turanci mai kyau sosai, da wani ɗan Hausa-English blend a cikin accent dinsa — which makes him sound unique and sweetly northern.
Despite being a soldier, he stays off social media completely.
Bai son show off, kuma he believes dignity is in privacy.
He’s also a philanthropist in silence — yana tallafa wa mutane ba tare da hayaniya ba.
A halin yanzu Junaid yana Libya — on a military assignment.
Ya shafe watanni tara a can tare da abokin amanarsa Captain Fahad, kuma sauran wata uku kawai ya rage ya dawo gida, daman shekara daya zai yi.
A can yake tunanin rayuwa da kuma maganar auren da mahaifinsa ya matsa masa akai.
********
>Yan’uwan Colonel Junaid Isa Saleh
Dr. Salima Isa Saleh – “Doc Sali”
Salima ce second child a gidan Baba. She’s already married with three children.
Tana aiki a matsayin Chief Consultant a Army Barracks, Yola, kuma she’s one of the most respected doctors in military medical service.
Since she became a certified doctor, Baba ya hana wani likita ya tabuka masa komai sai ita — except if it’s a specialist case.
She’s very close to her big brother Junaid, and ta daɗe tana yi masa maganar aure — amma bai taba sauraren ta ba.
---
Commander Hakeem Isa Saleh – “Commander H.”
Hakeem yana da shekaru 34 — shi ne third born kuma Navy officer ne.
Yana aiki da rundunar sojojin ruwa na Najeriya a matsayin Commander.
He’s very lively, energetic and social — party boy of the family.
Gashi handsome, kuma yana da rauni wajen mata.
Ya yi aure da wuri — yanzu yana da yara biyu.
Junaid kullum yana yi masa faɗa akan halayensa, amma bai dai na ba. In dai party ne da mata toh Hakeem oga ne..
---
Captain Bilkisu Isa Saleh – “Captain B.”
Bilkisu itace kawai mace cikin ’yan gidan da ta nace itama sai tayi soja..
Tana da Captain rank a rundunar soja, kuma tana da aure da ’yarsu guda, Baby Zee (Zainab).
Saboda busy lifestyle na ita da mijinta, Baby Zee yawanci tana zama ne a gidan Maami da Baba.
Bilkisu is reseved, tough, kuma very focused.
---
Bello Isa Saleh
Bello shine ɗan fari na Aunty — kuma na biyar cikin siblings. A halin yanzu yana Terminal 5 a NDA Kaduna — yana shirye-shiryen zama officer.
Bello is lively, playful, amma he takes his military dreams seriously.
Baima cika zuwa gida ba — NDA life is tough!
---
Firdausi Isa Saleh – “Baby Firdaus”
Firdausi a yanzu haka tana karatu a Base University.
She’s studying Medicine kuma kullum tana cewa:
> “I want to be like Dr. Sali.”
She’s brilliant, pretty and the quietest of Aunty’s kids.
---
Nabil Isa Saleh – “Nabi Boy”
Nabil shine ƙaramin gidan — last born.
Yana da shekaru 17, kuma yana karatu a Nigerian Military School (NMS).
Sai ka ce miniature version of Colonel J. Saleh — serious face but kind hearted.