Free chapter · Read without an account
Page 25
*KARAGAR MULKI*
STORY & WRITTEN BY
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
*YOTA*
BOOK 1
"Ya ke `yata kuma abar K`aunata,wannan zubar hawayen ya isa haka,domin kwata-kwata bai kamace ki ba,ba zan ji dad`i ba in har ki ka cigaba da zama a haka,Kar ko da wasa ki d`auka matsalar ki bata da magani,kuma kar ki kuskura ki cilla kan ki a cikin wuta kuma ki sa ki yi tunanin Masoyinki na hak`ik`a ne zai zo ya ce-ce ki,aikata hakan ban-ban kuskure ne,ya ke ruhina kuma kyakyawar Gimbiya ta mai kyakyawar fuska mene ne ya sa na ji kin yi shiru ko dai kalamaina ba su d`ebe mi ki kewa gami da sanya ki farin ciki nr?",sai da ta gyara kanta da ke saman cinyarsa sannan ta ce"Shin zai iya kasancewa d`iyar kirki mai neman albarka ba ta buk`atar kalami ko zance daga bakin Kawunta,Ya kai Kawuna Ishmal shin ko da wasa ka ta`ba tunanin rayuwata za ta juye izuwa wannan munmunan yanayin, cikin tsananin duhun da ko tafin hannuna ba na iya ga ni ?", hannunsa ya sa ya na mai shafa kanta alamun rarrashi tare da cewa," Ina fatan dai ba waccan matsalar ba ce ki ka d`auka ki sa a cikin ranki ba ko ?,Na riga da na yi mi ki alk`awari da izinin Allah komi runtsi da tsanani ni da kaina zan jajurce wajen ganin na kawo k`arshen ta","A'a ba haka bane ba na dai san na yi kewanka matuk`a,na kwashe tsawon lokacin ina dakon gami da son ganin ka a kusa da ni,zuciyata a cunkushe ta ke,na san zama da kai ne kawai zai d`an iya yaye min wani kaso daga cikin abinda ke damuna","To in haka ne mene ne ya ke damun ki har yai silar jefa ki cikin wannan halin ya ke d`iyar `yar'uwata",sai da ta numfasa gami da sauke ajiyar zuciya mai k`arfi ta ce da shi,"Na kasance na yi shiru da harshe na ne saboda ina jin idan na yi magana kamar za a GeA na kwafsa ko kuma wani yai tunanin ko ba ni da hankali ko ma ace na samu matsala a kwakwalwata ",yanayinsa ya nuna ya kad`u da jin zancenta,har sauri ya ke wajen cewa,"Gimbiya Junainah fad`amin abinda ya ke faruwa,Zuciyata da gangar jikina sun k`agauta da son jin ko mene ne abinda ke shirin jwfaa min ke cikin wannan halin"," Ina ji a jikina tamkar zamowarta ko kassncewarta Uwa mahaifiya a gare ni tamkar zunubi ne,ko kuma wani laifi na aikata da aka jarabce ni da ita a matsayin Uwa a gare ni tunda".....da sauri ya sa hannunsa ya a toshe mata baki ,ya hanata damar da zata idasa fad'ar abinda ke a saman bakinta,"Kull d`in ki kar ki kuskura ki sa ke fad`in irin wannan zancen domin hakan zunubi ne da zai iya Jan ragamar ki izuwa wuta aranar gobe alk`iyama",tashi ta yi zaune yanda za ta fuskance shi sosai ta ce da shi"Haba Kawuna Ishmal ka manta ita d`in ko wace,ta kasance muguwa ce,ta na zaluntar talakawanta,ta ci hak`in su,ta kwace mu dukiyoyinsu da kayan abincinsu,ta kan kashe duk wanda ta so,ba tare da duba girma ko k`ank`antar laifin da ya aikata ba,ta taka hukunci ko dokar k`asar,kai har dokar Allah ma ba ta bari ba balle wata dokar k`asa a gaba ki d`ayan ta ba wani abun alkairi a rayuwarta,MULKINTA kuwa ya koma tamkar na fir'auna,mene ne abin alfari ko tunk`aho da mutum zai yi a duniya in har me irin wannan halin ta kasance Uwa mahaifiya a gare sa ?",sai da Ishmal ya sauke wata a jiyar zuciya,sannan ya gyara zaman sa gami da kamo tafukan hannunta ya rik`eta ya na mai cewa da ita,"Duk na ji kuma na fahimci duk abinda ki ke son ki fad`a min amma wannan ba shine abinda za ki rik`a har ya zame mi ki linzamin da za ki yanke ma ta hukunci ba,idan ki kai duba a baya ai ba haka ta ke ba ,ko iya tsakanin ni da ita ba irin wannan rayuwar mu ke gudanarwa ba,balle a kai kan soyayya kulawa da jitiwar da ta ke tsakaninki da ita,a baya ita mace ce mai jink`an talakawanta gami da jin tausan su,jarumar mace ce wacce a ka buga da ita a kowanne fannin a ka barta,ban ta`ba ganin abinda ta nuna ma soyayya a rayuwarta kamar ke ba, da akwai shak`uwa da fahimtar juna a tsakaninmu da ita,domin ko Malikat Juwairiyya mahaifiyarmu ta kan ce ni da ita tamkar `yan biyu mu ke ba a jin tsakanin mu ko da wasa ,ke hatta da abinci d`ayan mu bai ci sai tare da d`an'uwansa,in k`arshe mi ki labari hatta da mahaifinki marigayi ni ne na za`ba ma ta shi a matsayin mijin Aure, shi d`in abokina ne kuma mutum mai amana,hak`uri da kawar da Kai",ya d`an tsahirta gami daruntse idanunsa alamun abinda zai fad`a ya na Sosa ma sa rai da zuciyarsa, "Sai ga shi lokaci guda komi ya sauya ni da na kasance abokin hira da shawatar na zama ni ne babban mak`iyi a gareta,ya zama tsakanina da ita kullum cikin rigima da fito na fito mu ke ,har ta Kai na Zama ni ne babban abokin gabarta,k`arin tashin hankali a gare ni shine Malikat Juwairiyya ta juya min baya duk abinda zance ko in aikata a wurin su a matsayin kuskure ne daga k`arshe `yar'uwata kuma k`anwata ta kai ni kurkuku gidan gyaran hali a ka kulle ni har na tsawon watannin shidda,ba tare da tayi duba da matsayina na yayanta ko kassncewarta d`an Sarauniya kamarta ba,shin wannan labarin ba abin da mutum zai zauna ya sa nisan hankali da tunaninsa a ciki ba be ba?",ya kai k`arshe zancen da alamar tambaya a kan Gimbiya Junainah.
" Na san wasu kad`an daga cikin labarin da ka bada to amma ni a cikin sa ban ga abun mamaki ko na tsaida hankili a tattare da shi ba","Hmmmm har yanzu ke yarinya ce Gimbiya Junainah shiyasa da akwai abinda ba zan iya sanar da ke ba amma kiyi sa ni Mahaifiyarki na son ki da k`aunar ki kawai dai da akwai wani nannad`ad`d`en zare da ya nannad`e rai da zuciyarta gami da zama silar kauda kai daga duk wani abinda da a baya ta ke, Kai tsaye dai zan ce da ke Mahaifiyar ki na cikin halin k`ak`anikayin da ta ke da buk`atar addu'ar ki ,har ma da kulawa da soyayyar ki ta hakan ce kawai zata iya dawowa asalin yanda mu ka santa a baya","Ta ya hakan za ta kasance ya kai Kawuna Ishmal ko ka manta ni da ita ba mu ta`ba iya zama wuri d`aya da ita balle har mu sha inuwa guda a tare,a kullum kuma a ko da yaushe ba na iya d`aga idanuna in sauke su a cikin nata domin jin tsoran abinda idanuna ke gane min,tamkar dodo ko Aljana haka Ni ke ganinta,gashi kuma da zaran na ganta sai ciwon da ke barazana da rayuwata ya tashi ,haka kazalika itama ta na jin tsoron ta zo inda na ke don gudun kar wani abu ya same ni,alhalin ba za ta iya taimaka min da komi ba"...."Mene ki ka ce ,ki na so ki ce da ni ki na ganinta da wata siffa ta daban ba wacce kowa ke ganinta ba","Kwarai da gaske a duk lokacin da na ganta a gabana tamkar kwarangwal haka na ke kallonta ,hannayenta d`auke da zara-zaran farata su na kawo min cafka da niyar za su hallaka ni,wannan tsoro da firgicin da na ke shiga shine ya ke zama sula ko sanadiyar motsawar ciwon da ke bibiyar rayuwata ","Innalillahi wa'inna ilaihirraju'una wannan lamarin ba k`aramin lamari ba ne ba,amma ina zuwa"," Ina kuma za ka ka tafi ka bar ni bayan na fara samun sauk`i ne a sa'adda ka dawo cikin rayywata ?","Zan je na shirya tafiyar gaggawa ne domin da akwai wani abokina a sa'adda muna yara an ta`ba jifanshi da munmunan asiri kwatankwacin irin wannan da ki kai min bayani,an aikata ma sa haka ne domin a nason a hana shi gadar KARAGAR MULKIN mahaifin sa,a kasa rashin jituwa a tsakanin sa da iyayensa sannan a duk sanda ya had`a Ido da Mahaifinsa sai ya fad`i k`asa sai suma, dole sai dai a ka fitar da shi daga Masarautar ya je can yai rayuwarsa,ya cigaba da yawan duniyarsa da ga bisa ni ya had`u da wani tsohon malami ya karya wannan siddabaru,Zan dangana da wurinsa gami da yi masa bayanin halin da ki ke a ciki ,bazan dawo ba har sai na samu makarin cutar da ke damun ki",......katse shi tai tana mai k`ara rik`e hannunsa da ke cikin nata ta ce,"A'a ban yarda ba ,Babu inda za ka ka tafi ka bar ni,wata k`ila ma akan hanyarka ta tafiya wani abu ya sameka,ba zan lamunci hakan ba kuma bazan ta`ba yafe ma kaina ba in har wani abu ya same ka a ta dalilina",jawota jikinsa yai ya na jijigata alamar lallashi tare da cewa,"Kar ki damu ya ke `yata ba abinda zai faru da ni kuma wannan ita kad`ai ce hanyar da zamu warware wannan rikitaccen al'amarin,Mahaifiyar ki na buk`atar taimako,ke ma kina buk`atarta a kusa da ke ,kina son soyayyar Mahaifiyarki ta dawo ni ma kuma ina son alak`ata da`yar'uwata ta dawo kin ga kenan ba zamu samu damar hakan ba har sai mun shirya fuskantar komi da ka iya biyo baya,shin ki na tunanin za ki iya k`are rayuwar ki ba tare da Mahaifiyar ki ta asali ta dawo ba ?,ni dai nasan ina son k`anwata,`yar'uwata kuma Sarauniya K`asar BAIBAH ta asali ta dawo yanda ta ke a baya","Ni kai na zan so duk abinda ka fad`a ya kasance amma kai kan ka ba ka da tabbacin akan da gaske asirin a kai mata,ko-ko ta can za ne dan rad`in kan ta,na kwashe tsawon mako shidda ina kwance ko numfashin arzik`i ba na iya ja,amma ba ta ta`ba zuwa inda ba ke ba,halin da na ke a ciki bai fameta ba kwata-kwata bana agabanta MULKINTA kawai ta sa a gaba,,a `yan k`alilan kwanakin da ka yi da fitowar ka daga kurkuku sai ga shi na warke har ina cin abinci ina magana,saboda addu'o'in da ka ke ma ni shin yanzu idan ka tafi waye zai maye min gurbinka ?","Kar ki damu ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai same ni idan kuma dan ruwan addu'ar da na ke rubuta ma ki ne,sai in rubuta mi ki wani wadatacce wanda zai ishe ki ki yi ta sha har in dawo, tunda duka-duka tafiyar ba za ta wuce ta mako biyu ba","Amma kuma Kawuna "...." Shhhshhhhshhhh kar ki ce komi in sha Allah wannan tafiyar za ta za ma alkairi a gare mu baki d`aya, zan ce lafiya kuma in dawo lafiya shifa Sarkin k`asar Abokina ne na fad`a mi ki ,har a cikin Gidannan a wannan Masarautar mun yi rayuwa da shi, da na je idan zan samu malamin da ya karya asirin da ke jikinsa kawai zai fad`a min ni kuma inje mu taho tare da shi zuwa nan kuma dad`in gushi zan ta fi da Dakaru ba ni kad`ai zan ta fi ba","Shikenan na amince amma ba wai dan na so ba ,kawai dai don ba ni da yarda zan yi ne sheyasa kawai","Kar ki damu shalelena, ni dai abinda na ke so da ke ki kula min da kanki ki rik`a shan maganin ki akan lokaci har zuwa san da zan dawo,idan kuma ki na da buk`atar wani abun ko in wata matsalar ta ta so kai tsaye ki tunkari abokina Malam Musa, zai tsaya tsayin daka akan komi ki ka je masa da shi ","To in sha Allah na yi ma ka alk`awari zan yi yarda ka ce,amma ba na tunanin wani abu zai faru ko ka manta ina tare da Malikat Juwairiyya, kasan ita d`in haihuwa ta ne kawai ba tai ba amma ta na jura gami da fuskantar ko wacce irin rayuwa ko wahala a ta dalilina","Yauwa na ji dad`in hakan kuma ina godiya sosai da sosai game da amincewar da ki kai sai na dawo",ya k`are zancen ya na mai yi mata sumba saman goshinta,tare da mik`ewa ya nufi hanyar da za ta sada shi da d`akinsa domin ya fara shiryawa ya tafi.
*St
*Afuwan ba Editing*