Free chapter 路 Read without an account
Page 5
馃挒馃挒馃挒LAILAH馃挒馃挒馃挒
STORY AND WRITTEN BY
AISHA MA'ARUF(GIMBIYA AYSHU)
ELEGANT ONLINE WRITER'S馃摎
Page 9-10
___________________Lailah nada lectures kuma na safe,bayan ta gama tayi wa Mama sallama ta wuce,bayan minti 20 suka isa,ba bata lokaci ta shiga cikin hall,karfe sha biyu suka gama lecture,cafteria suka nufa ita da wata yar ajin su,sha biyu da minti arba'in da biyar suka bar cafteria zuwa masallaci dan suyi sallah,bayan sun fito suka nufi hall.daya da rabi daid-dai malamin ya shigo ya rubuta musu test sannan yace minti ashirin kawai ya basu,bayan an gama yasa class rep ya hada mishi papers din,bayan kowa ya gama harhadawa ya bashi,lecture ya fara,uku da rabi dai-dai ya fita bayan ya kwashi test script da handout din shi,bayan ya fita a ka fara watsewa dan an gama lecture na ranan.
Bayan Lailah ta fito ta tadda driver dan dama ta gayamai lokacin da zai zo, back seat ta bude ta shiga,direct gida suka nufa,yana gama gyara parking ta fice abin ta tare da mai a huta gajiya,zaune ta tadda Mama hannun ta rike da Al-Qur'ani tana karantawa,gaida ta Lailah tayi,Mama ta amsa dai-dai tana kulle Al-quranin dake hannun ta tace"ya test din,da Alhamdulillah Lailah ta amsa ta manna wa Mama peck a goshi,toh ga abincin ki a cooler,ki je ki watsa ruwa sai ki zo kici abinci,"am full first luv, bari anjima",da toh Mama ta amsa,"daki Lailah ta nufa,bayan ta gama cire kayan ta ta shiga bathroom,wanka tayi tare da alwala dan lokacin la'asar ya kusa",bayan ta fito ta shafa lotion ta dan shafa powder kadan,tasa lip gloss,Kiran sallah da ta ji ne ya sata mikewa ta nufi drawer ta dau kayan da za ta sa,bayan ta gama shiri ta shifida darduma tasa hijab dinta ta tayar da sallah bayan ta idar ta danyi addu'an da ake bayan an idar da sallah,sai tadan kwanta dan ta huta,barci yayi awon gaba da ita,ba ita ta tashi ba sai 6:00pm,tana tashi tayi addu'ar tashi daga barci ta miki ta linke darduman ta cire hijab din ta ta shiga bayi,brush tayi ta fito parlor,ta samu babu kowa,kitchen ta shiga ta dauko abincin ta ta ci,bayan ta gama ta shiga kitchen dan daura abincin dare,ruwa tasa a tukunyya ta daura a gas,ta debo wake ta gyra dai-dai ruwan ya tafasa,ta wanke ta zuba,tasa kanwa kadan ta kulle,kayan miya ta gyra, kafun bakwai ta gama girki,shinkafa da wake jelof ta dafa,da cos low,sai water mellon and cocumber juice,jera coolers din tayi kan dining taje tayi sallah,bayan isha'i suka ci abinci,lokacin kwanciya nayi su kabi lafiyan gado.
Washe gari Saturday,tun karfe goma duk suka gama shiri zasu gidan yayan Daddy su sada zumunci,mota duk suka shiga,da kanshi Daddy yayi driving,a cikin 1 hour suka isa,danna door bell Lailah tayi,Mum ta amsa daga ciki ta bude kofan tace a'a manyan baki zuwa ba sanarwa,ta fada tana rungumar Lailah,"surprise mu ka muku,cewar Mama",naga alama kam,ina sauran mutanan gidan cewar Abba bayan sun gaisa da Mum,su twins na sama,Abba da Muhammad kuma sun fita,kwala ma twins kira Mum tayi,ba bata lokaci suka sauko,bayan sun sauko su kaga i Daddy da family shi ne,da gudu suka nufi Mama suka rungume ta,kun ki girma har yanzu,dariya su kayi hadi da cewa we miss u Mama,"ba wani miss,ku da ba ku zuwa inda nake",noooooo! Mama ba haka bane,school ne wlh,amman za muzo insha Allah,da Allah yasa Mama ta amsa,suka amsa da Ameen,barin Mama su kayi suka rungume Lailah da Husna,a tare suka gaishe da Daddy,ya amsa da twins dina ya kuke,ya school,lfy lau Daddy,ya aiki,da Alhamdulillah Daddy ya amsa yace"yaya fa,wlh ya fita,bai ma jima da fita ba,bari ma na kira shi,da toh Daddy ya amsa,sama Mum ta haura dan ta dau wayar ta,kiran Dad tayi,bayan ya daga tace ga Alhaji karami da iyalan shi,ahhhhh! shine ba sanarwa,ga ninan dawowa yanzu insha Allah,da toh Allah ya tsare Mum ta amsa,bayan kaman minti ashirin Dad ya iso,gaisawa su ka yi,Dad yace zuwa babu notice,i da na san da zuwan ka da ban fita ba,gaida shi Mama tayi kafin su Lailah,amsawa yayi tare da tanbayan su ya karatu,da Alhamdulillah duk suka amsa tare da tanbayan shi ya Aiki,da Alhmd Dad ya amsa yana mai sa musu albarka,hira su ka fara,kitchen Husna da twins suka shiga dan taya Mama da Mum girki,abinci kala uku da local drinks suka hada,bayan sun gama girkin aka zuba a cooler masu daukan ido,daukan cooler twins su kayi suka nufi dining area suka jera,bayan sun gama kwashewa su Mama suka fita parlor suka ga babu kowa,"ko sun fita ne,cewar Mama",da wiya fita suka yi dan banji karar kofa ba,bari dai na duba sashen Alhaji,ki shiga daki na ina zuwa,da toh Mama ta amsa ta amsa,part din Dad ta nufa,tun kafin tayi knocking taji dariyan su sai kawai ta juya ta koma dakin ta,a zaune ta tadda Mama gefen gado da waya a hannun ta alaman yanzu ta gama waya,shine baki shiga wanka ba cewar Mum,da a'a babu komi Mama ta amsa,haba hajiya haka za muyi da ke,nanma fahh....... kaman gida ne,ba haka ba ne,ban zo da wasu kayan bane,indai kaya ne matsalan ki toh karki damu,ina da wani sabo zan baki kisa,tohh ya na iya dake,wanka ta shiga bayan ta fito Mum ta nuna mata lotion din da zata shafa da turarurruka tace ga kayan nan saman gado nima bari na shiga na fito,to a fito lfy.
A bangaran su Lailah bayan su Mum sun fita suka yi wanke-wanke suka share ko'ina,bayan sun gama dakin twins duk suka shiga suka wasa ruwa kayan twins Lailah da Husna suka sa,bayan sun gama shiri su kayi sallah,bayan sun idar suka zauna suna hira,mum ce tazo ta kira su tace su fito parlor,a dining suka yada zango,husaina tayi serving din su,suna cikin ci su kaji sallaman Abba da Muhammad,amsawa duk su ka yi,dining su ka karaso suna gaida iyayen su,su twins da Lailah suka gaishe shi,ya amsa yana kallon Lailah,ita ko kallon shi ba tayi ba ta cigaba da cin abincin ta,gaida twins da Lailah yayi,Husna kuma ta gaida shi,kujera suka ja suka zauna,Mama tace Lailah ta yi serving din su,"mikewa tayi ba dan ta so ba ta zagaya bangaren da suke tayi serving dinsu",Abba sai kallonta yake kasa-kasa,tana gamawa ta koma ta zauna ta cigaba da cin abincin ta,bayan sun gama ci duk su kaje parlor,su Lailah suka kwashe kwanonin suka kai kitchen,Hussaina da Husna suka wanke suka gyara kitchen,Lailah da Hassana parlor suka koma,tun da Lailah ta zauna ta fara chart da friends dinta,Abba ko shima rike wayar shi yayi yayi kaman ya na anfani da shi,amma duk hankalin shi na gun Lailah,duk mosinta akan idon shi,abinda bai sani ba shine ashe Daddy da Dad na lura dashi tun dawowan shi,murmushi kawai suka yima junan su,"nikam nace wannan murmushin ko meh ma'anar shi",karfe hudu mazan suka fita zuwa masallaci Mama da Mum suka shiga dakin mum su Lailah suka shiga na twins bayan sun idar parlor suka dawo karfe biyar su Daddy suka ce zasu wuce,Dad yace da wuri haka,'yamma yayi Alhaji sai wata rana,zamu zo insha Allah",sai na ganku twins,"soon inshsa Allah",daki Mum ta shiga ta dauko ma Mama da yaran ta tsaraba,kin amsa Mama tayi,sai da Mum ta nuna bacin ranta kafin ta amsa tayi mata godiya,wani laida Abba yaba ma Lailah taso taki amsa,ganin sun hada ido da Daddy ne yasa ta amsa ta mai godiya,suka raka su har parking space,daga musu hannu suke har suka fice daga gidan,a hanyyar su ta komawa Daddy ya siya musu taraba suya da bread da fruit da kayan flour sukaje gida,6:15 suka kai gida,parking Daddy yayi suka fita,daukan laidodin su kayi zuwa cikin gida,a fridge Lailah ta saka laidan Fruit din dake hannun ta,ajiye laidan flour da ke hannun ta Husna tayi kan dining,Mama ta shiga da Wanda ke hannun ta dakinta ta ajiye ta fito,dakin Daddy ta shiga ta hadamai ruwan wanka ta ciro mai kayan da zai sa,bayan ya shiga wankan Mama ta fice daga dakin ta wuce nata dakin,wanka ta shiga kafin a kira sallah,daki duk su ka nufa dan su dan watsa ruwa kafin lokacin sallah yayi,a na kiran sallah daddy ya tafi masallaci su Mama su kayi nasu a dakin su,bayan sun idar Lailah da Husna suka hada abinda za'a ci a dining,slicing fruit din Lailah tayi a small tray tasa a fridge kafin lokacin ci yayi,bayan sun gama hada komai suka je su kayi sallah,bayan sallan isha'i sukaci abinci 10:00pm suka kwanta.
ko wani lecturer ya kammala test din shi,saura sati biyu su fara exam Lailah sai karatu take ba kama hannun yaro.
Yau Tuesday suna da lecture da safe kuma sir sa'ad ne zai fara shiga,sauri take dan ta kusa makara,7:25 ta gama shiri,takwas suke da lecture,bayan ta gama tayi wa Mama sallama shap-shap,7:45 takai school da sauri ta shiga cikin hall ta zauna tana duba littafin da za su yi a lolkacin,8:00,Ya shigo ya fara musu revision bayan ya gama yace who is "khadija muhammad ibrahim",ji tayi kaman kirjin ta zai fashe tsabar tsoro,cikin in-in na tace am the one sir yace meet me at my office,"ok sir",nan a ka fara kallon-kallo a da kananun magana a aji,fita yayi Lailah ta bi bayan shi,office ya shiga ya zauna jiran ta,bayan kaman minti biyar yaji tayi knocking,"shiru yayi kaman bai jiba",kara knocking tayi amman still shiru,"sai da ya gama jan aji kafin ya bata izinin shiga",shiga tayi bakin ta dauke da sallama tace am here sir,"shiru yayi kaman baiji ba",sai da tayi minti goma a tsaye kafin ya nuna mata kujera a lamun ta zauna,"bayan ta zauna ya kalle ta yace mai ya hanaki rubuta test dina",da sauri ta dago ta kalle shi tace I wrote the test sir,"but I can't find it",wlh I wrote the test sir,ta karasa maganar ta idan ta na tara hawaye,"so u mean am lieing to u",da sauri Lailah tace no Sir tana share hawayen da ya dan gangaro kan cuncin ta tace"am sorry sir",you can go,"kin tashi tayi tace am sorry sir,pls give me another one to write or make up test",shiru yayi bai ce mata komai ba,"magiya ta fara mai akan ya mata make up test ko kuma ya mata oral question,ta kai tsawon minti sha biyar ta na mai magiya amman ko a jikin shi",hasali ma yi yayi kaman bai san da zaman mutun ba,"da dai ya ga da gaske take ba tafiya zata yi ba sai yace"am done with u pls,u can leave,use the door",kin tashi tayi ta cigaba da rokon shi,"i said go,am done with u,don't allow me to repeat my words okh,ya karasa maganar da tsawa",i batasan lokacin da ta fashe da kuka ba ta hada hannayen ta biyu tana rokan shi,"a zuciyar shi yace wow she's so pretty even when she's crying",u are disturbing my ear's pls u can leave,kneel down tayi tana rokon shi idan ta na zubda ruwan hawaye,"yi yayi kaman bai san da ita ba amma duk abinda take yana kallon ta ta kasan ido",sai da ta share tsawon minti ashirin tana abu daya kafin yace"what did u want me to do now",sir pls give me another questions to answer or oral test pls,"shiru yayi daga baya kuma yace meet me tommorow by 8:00am,koda minti daya kika yi latti to that's all u are done with the test,da sauri tace Okh sir,am greatful,"u can go",tashi tayi tana share hawayen idan ta,"bayan ta fita yayi murmushi ya daga wani file ya dau wani paper yana kallo yana murmushi",ba paper kowa bane face na test din Lailah wato "khadija Muhammad Ibrahim",bayan ya gama kallon script din ya bude jakan laptop din shi ya saka paper a ciki.
Lailah na fita daga office din shi tasa handkerchief ta share fuskan ta da kyau ta wuce,ko da ta isa aji ta iske wani lecturer a ciki,karfe hudu suka gama lectures din su na ranar,sallah taje tayi,bayan ta dawo ta samu driver har ya karaso,gaida driver ta kafin ta bude front seat ta shiga,amsawa yayi yana tanbayar ta ya makaranta,tada motar yayi ya nufi hanyar fita daga makarantar,shi ko sir sa'ad na cikin motar shi yana kallon ta,sai da suka fita a makarantar kafin ya tayar da motar shi ya fita.
Washe gari Wednesday bakwai da minti hamsin(7:50)yayi wa Lailah a kofar Office din shi,tayi knocking har sau uku amman shiru,kokarin bude kofan tayi taji a kulle,jingina tayi da bango tana jiran zuwan shi,"ba shi ya karaso ba sai bakwai da minti hamsin da bakwai(7:57),gaida shi tayi da ladabi ya amsa ba tare da ya kalle ta ba,bude office din yayi ya shiga,bin bayan shi tayi bayan tayi sallama,nuna mata wurin zama yayi ta zauna yace can we start,"yes sir",rubuta questions din yayi ya mika mata,"amsa tayi ta mai godiya sannan ta fara amsawa",jawo laptop din shi yayi kaman yana dannawa amman duk karyace domin hankalin shi kaffffff!........na kan Lailah,"duk mosin ta akan idon shi tayi shi",bayan ta gama ta bashi ya bata izinin tafiya ta fita,"dago paper yayi yana kallan rubutun ta da answers din,girgiza kai yayi alamun tayi dai-dai,bude jakan laptop din shi yayi ya saka a ciki yana sakin wani irin kayatatten murmushi....................................................
Ku biyo ni dan karanta cigaban wannan labarin nawa mai taken "LAILAH".
Comment
And
Share
BY GIMBIYA AYSHU馃挒馃挒馃挒.