Free chapter 路 Read without an account
page 10
馃挒馃挒馃挒LAILAH馃挒馃挒馃挒
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AUSHU馃挒馃挒馃挒
ELEGANT ONLINE WRITER'S馃摎
PAGE 19-20
____________________"Cute lips and they are pinkish in color",ohhhhhh! God was wrong with me,Sa'ad wake up, what the hell is wrong with you hannu biyu yasa ya rike kan shi,daga baya ya kulle laptop din ya ajiye,kwantawa yayi ya ja duvet ya rufe jikin shi ya bar kan shi a waje yayi addu'an barci,duk da haka bai daina tunanin ta ba,hakanan ya hakura ya cigaba da yi har barci ya kwashe shi,a cikin barcin ma mafarkin ta yake wai gasu a wani lambu mai cike da fararan fure suna soyayya,ta rike flower shima ya rike tana bin shi suna tsere sai dariya suke gwanin ban sha'awa,dai-dai tazo zata kama shi kenan ya farka da addu'ar tashi daga barci,duba lokaci yayi gaga 2:00am,kuma ko daya kwanta 11pm ya wuce,toilet ya shiga ya dauro alwala ya dawo ya tada sallah nafila,ba shi ya kwanta ba sai karfe 3am.
Washe gari kiran sallan farko a kunnen shi ya tashi da Addu'ar tashi daga barci,sauka ya yi daga kan gadon ya yi mika yana hamma kafun ya shige toilet ya yi wanka hadi da brush sannan ya yi alwala ya fito daure da towel a kunkumin shi daya kuma a hannun shi,goge gashin kan shi yake da tsauri,bayan ya gama ya dan shafa lotion ya fesa turare,drawer ya nufa ya dauko jallabiya baki da farin hula,cinkin minti biyu ya gama shiri,ba karamin kyau yayi ba,dama gashi fari,sai ya fito kaman wani balaraben makkah,ya hadu over,na bari ku kiyasta da kan ku,yana gamawa ya ji ana kiran sallah,charbin shi da azkar da wayoyin shi ya dauka ya fita,ba shi ya dawo ba sai karfe 7:00am,direct part din shi ya nufa,ya shiga ya ajiye abubuwan dake hannun shi,ya cire jallabiyan da hula ya hanga,bude drawer yayi ya dauko suit baki,na cikin shi kuma pink da neck tie mai ratsin baki da fari ya aje saman gado,fita yayi a dakin ya wuce main parlor gidan,shiga yayi da sallama,salame dake goge-goge ta amasa hadi da gaishe shi ya amsa,upstairs ya nufa zuwa dakin mummy shi,knocking yayi a kofar dakin ta.
Kai tsaye Mummy ta ce"shigo salame".
Murya a sanyaye ya ce"it's me mummy",okh son shigo,na zata salame ce,shigowa yayi ya zauna kan kujera ya gaishe ta ta amsa tace"ya ka tashi".
"Alhamdulillahi mummy,Daddy bai dawo ba?".
"Ehhhhh!,amman kila ya dawo yau,kasan yanayin aikin shi".
"Ehhh! Mummy,bari naje na shirya".
"Okh a fito lafiya".
"Ameen mummyna,thank you",daga nan bai zarce ko ina ba sai part din shi,shiryawa yayi cikin kayan daya ajiye kan gado bayan yayi wanka,ba karamin kyau ya yi ba,gaske naga matan makarantar na roller mishi,ashe dai da abin da suka gani,yanzu naga zahiri, gyra gashin shi yayi ya shafa oil,sai ya kwanta luf-luf kaman na baby gwanin ban sha'awa,ya fito tsaf da shi,sossai ya yi kyau,jakar laptop din shi ya dauko ya bude sai yaga papers a ciki,murmushin gefen baki yayi ya dau laptop din shi yasa a ciki ya kulle ya hanga jakan a bayan shi ya kara fesa turare kafin ya fita ya kulle part din shi,gun Mummy ya koma yayi break,bayan ya gama ta rako shi zuwa kofar parlor ta mai Addu'a ya fita,direct school ya wuce.
Lailah na gama shiri ta yiwa Mama sallama,Addu'a Mama ta yi mata kafin ta fita,yana shiga makarantar sai ga motar su Lailah,parking yayi ya bi motar da ido,fitowa ta yi sanye da dogon hijab har kasa kalan pink,tayi kyau sossai,ya rasa mai yasa yake son kallon yarinyar da tunanin ta,har wani natsuwa yake samu idan yana kallan ta,kallon ta yake har ta bace mishi,ajiyar zuciya ya sauke ya jingina da kujerar motar,yace"meke damuna, was wrong with me"SA'AD MUHAMMAD ALIYU",daukan jakan laptop din shi yayi da wayoyin shi ya fito ya kulle motan,tafiya yake majestically kaman baiso,Lailah na shiga da minti 10 aka fara paper,karfe hudu suka gama exam ta wuce gida.
Yau suke last paper su,bayan sun gama first paper ta zauna karkshin wani bishiya tana karatu,karfe biyu suka shiga hall,bayan sun gama ta fito ta tsaya tana jiran driver har tsawon minti sha biyar amman bai zo ba,wuri ta naima ta zauna tana latsa waya,ba jimawa ta kara wayar a kunne,bayan an daga ta gaishe shi ta ce"lafiya har yanzu baka karaso ba?".
"Wlh tire ce ta yi faci,yanzu ma haka ina wurin gyara,amman dazaran an gama zanzo insha Allahu".
"Toh shikenan Allah ya kawo ka lafiya".
Fitowar Sa'ad ke da wiya ya hango ta zaune a karkashin bishiya,har ya wuce sai kuma ya tsaya, juyowa ya yi ya dawo in da ta ke zaune.
Dagowa ta yi dan ta gawa ke tsaye a kan ta,gaban ta ne ya yi mugun faduwa,fuska ba yabo ba fallasa ya ce"mai kike a nan?".
Murya na rawa ta ce"driver nake jira".
"Yaushe zaizo?"
Girgiza mishi kai ta yi alamun bata sani ba sannan ta ce"tire ce ta yi faci a hanyar shi ta zuwa,amman yana wurin gyara ya kusa karasowa",ta karasa maganar ta muryar ta na rawa.
"Okh,tashi na sauke ki".
Kai tsaye ta ce"thank you sir",gaban ta ko sai bada karan fat..fat yake,bata san suna kebewa sabida ba karamin rudani zuciyar ta ke shiga ba.
"Bana san musu,do what i said",ya fada tare da barin wurin ya nufi wurin motar shi.
Mikewa ta yi a hankali ta bi bayan shi kamar wacce ba ta da lakka a jiki,bude front sit ta yi ta shiga,tuni student din dake harabar wurin suka hau kus-kus,kowa na son sani ainayin alakar dake tsakanin su,masu son shi kuwa tuni kishi ya motsa.
Suna cikin tafiya ta ji ya ce"ke baki magana ne?".
Juyowa ta yi ta kalle shi taga yana kallan gaban shi,cikin rashin fahimta ta ce"bangane ba".
Kallan ta ya yi sannan ya dauke kai ya ce"baki iya hira ba?".
shiru tayi tana tunanin abinda za ta ce mishi,sam bata cikin natsuwar ta,ta matsu ya isa gidan su.
Jin ta yi shiru ne yasa shi fadin"uhummm".
Murya a sanyaye ta ce"ba nida abin cewa".
Kai tsaye ya ce"ki nema".
Shiru ta yi tana wasa da zoben hannun ta.
"Ina jin ki".
Shiru ta yi har lokacin tana wasa da zoben hannun ta.
Murmushi ya yi,kunyyar yarinyar na daya daga cikin abinda yake birgeshi da ita,har suka kai bata yi magana ba,suna isa ta yi wuf za ta fita ya danna lock,tana jin yasa lock ta saki salati a zuciyar ta.
"Ina zaki baki ban lbr na ba unnnn".
Shiru ta yi tana jin nunfashin ta kamar zai dauke,cikin rawar murya ta ce"ni banda abin cewa fahhh?"..
"Kohh,ashe zamu kwana a nan yau kenan".
Zaro ido ta yi gaban ta na gaduwa.
Murmishi ya yi ya ce"kina tantama ne?".
Girgiza kai kawai ta yi har lokacin kan ta a kasa.
Murmushi ya yi ya danna lock din motar.
Kamar kiftawar ido ta balle marfin motar ta fice tana mai godiya kanta a kasa, sannan ta juya tana tafiya,bin ta ya yi da ido har ta shiga gate din gidan su,hannu biyu yasa ya rike kan shi yana sucking lips din shi"ohhh!God mai ke shirin faruwa da ni?,mai nake yi haka?,mai yasa nake jina daban idan muna tare?, y am I feeling different?",wani bangaren zuciyar shi ta ce"so ne",cikin sauri ya ce"Allah ya kiyaye kaman wanda yaga mugun abu,wannan ba soyayya bace,kawai dai yarinyar nada hankali ne,haka ya yi ta sakar zuci har ya bata lokaci mai tsawo ba tare daya ankara ba,ringing din waya shi ne ya dawo da shi,lalabo wayar ya yi da sauri ya duba yaga my Everything,picking ya yi yana murmushi ya ce"hello mummyna",yes! "son kana Ina yanzu?".
"Ina hanyya Mummy".
"Okh! ka siyo min fruit".
"Insha Allahu mummy",ajiyar zuciya ya sauke bayan ya kaste kiran,kallon gate din gidan ya yi kafin ya ja motar shi ya tafi,a hanyyar shi ta komawa ya siyanwa mummy fruit ya wuce gida,yana isa ya danna horn aka bude gate gaisawa ya yi da mai gadi kafin ya shiga ciki yayi parking,jakar shi ya dauko da wayoyin shi sai laidan fruits,parlor ya shiga da sallama ya sami mummy a parlor,zama ya yi kusa da ita yace washhhh! mummy na gaji,ya fada tare da kwantar da kan shi a kafadar ta,shafa kan shi ta yi ta ce"ayyyah my son sannu koh ya aiki".
"Lfy lau mummyna ga fruits din bari na dan watsa ruwa",ya fada tare da mikewa tsaye.
"Okh son sai ka fito"....................................
COMMENT
AND
SHARE
BY GIMBIYA AYSHU馃挒馃挒馃挒.