Free chapter · Read without an account

page 18

by Gimbiya Ayshu · 💞💞💞LAILAH💞💞💞

💞💞💞LAILAH💞💞💞

STORY AND WRITTEN BY

AISHA MA'ARUF (GIMBIYA AYSHU)

ELEGANT ONLINE WRITERS

🔥FITACCE🔥 FITACCE🔥

IDAN KAJI SAREWA🎺🎺🎺🎺 NA TASHI TO TABBAS AKWAI SARAKAI A WAJAN, SARAUTA HAYAƘI KIKE BA KYA ƁOYA, FARAR ANIYYA MAI FARAR ZUCIYA, KADA NA CIKAKU DA SURUTU, DAGA FARKON MGN TA KUN SAN INDA NA DUSA, FITACCIYAR MARUBUCIYAR NAN WACCE TAYI FICE A RUBUTUN LITTAFAN HAUSA, A CIKIN JERIN MARUBUTAN ONLINE WTITERS, TANA FARIN CIKIN SANAR DAKU SABON LITTAFIN TA MAI SUNA 🌈ABU_MALEEK🌈

🌈ABU_MALEEK🌈 LITTAFI NE NA TSANTSAR SARAUTA DA KUMA ZAZZAFAR SOYAYYA MAI NARKAR DA ZCYR MASOYA, ZA KUJI YADDA FOOTBALLER⚽ KUMA DA GA SARKIN YARUBA (OBA OF YARUBA) WATO YAREEMA YAKE ƁUGEWA DA SOYAYYA DA MAKAUNIYA KUMA ALMAJIRAR KAN TITI, WACCE TA KASANCE ABAR ƘYAMA GA KOWA😭.

ABU_MALEEK YA TUƁE YA SHIGA JERIN MA NEMA AURAN MAKAUNIYA KUMA ALMAJIRAR KAN TITI INDA YA SHIGA JERIN MUTANAN DA ZA'AIWA SHAƊI 🤺, ANA DARA GA DARE YAYI A YAYINDA YAKE NEMAWA MAI MARTABA MAGANI A WATAN ƘASAR YAY KATARI DA ARNAN DAJI KAFIN WANI ABU SUN CIZAR MASA ƳAR MAKAUNIYAR SA, NAN TAKE TA KAMO DA LALURAR MAITAR SHAN JINI🙆🏾‍♀️ A DUK SANDA ABUN YA TASHI JININ JIKINSA SHIKE MAYE MATA GURBIN ABINCI.

MAZA KU HANZARTA NEMAN NAKU, MARUBUCIYAR TA SHIRYA TSAF DOMIN BAKU FARIN CIKI, ILIMANTARWA, NISHAƊANTARWA, SOYAYYA ZANBO CIKIN AMINCI.

ZATA FARA POSTING BAYAN AN KAMMALA BIYAN KUƊIN WANNAN LITTAFIN, WANDA YA KASANCE BOOK 1 2 3, ZA'A KAMMALA PAYMENT ZUWA END OF NOVEMBER BA ZATA FARA POSTING SAI TA KAMMALA BOOK 1✍🏾🔥, MASOYA NA'IMA SULAIMAN NIMCYLUV KU SHIRYA DOMIN DA SOYAYYAR KU TAKE TAƘAMA A KODA YAUSHE.

BOOK 1 2 3

AMOUNT: #500

ACCT NO: 0116886423

ACCT NAME: SULAIMAN NA'IMA S

BANK NAME: UNION BANK

EVEDANCE OF PAYMENT

***, GA ƳAN NIGER KUMA SUYI MGN TA NAN 84506476

MARUBUCIYAR SIRRIN MU🔥 UNCLE NE🔥MOON🔥AURAN FANSA🔥 THE NEW EMIR🔥JUYAYI, JIDDA, LAMRAT DA DAI SAURAN SU.

DAN ALLAH DAN ANNABI SHARE FISABILILLAHI🤲🏼🤲🏼🤲🏼

Gimbiya Ayshu's Data service

Ku siya data a garabasa

MTN

500MB-180

1GB -280

2GB - 550

3GB - 750

5GB - 1250

10GB -2500

AIRTEL

300MB - 170

500MB - 200

1GB - 300

2GB - 550

5GB - 1350

10GB - 2600

GLO

200MB - 120

500MB - 180

1GB - 300

2GB - 550

3GB - 850

5GB - 1350

10GB - 2600

9MOBILE

500 - 180

1GB -280

2GB - 550

5GB - 1300

10GB - 2500

Account number:8036434941

Account name: Maryam Maaruf Muhammad

Bank name:Opay

Contact me on this number:***

PAGE 35-36

________________________ Ajiyar zuciya mai karfi Sa'ad ya sauke ya ce"friend the only solution is"wait first mai ka yanke kai kafin na daura nawa".

Ni dai ban yanke komi ba, ita ce dai kawai ta ce mu gudu na tsawon watanni ko shekara, na dai ce ta bari idan nayi shawara zan sanar da ita, shine na kira ka, kallon shi Sa'ad ya yi a kaikaice ya ce"guduwa fah kace?, tabdi amman ba tada hankali, tana ya mace zata yi tunanin guduwa, bata tsoron tashin hankalin da iyayen ta zasu shiga, bata tunanin abinda mutane zazuce idan ta tafi, bata tunanin halin da zata shiga inta tafi, bata tunanin wata rana zaka iya juya mata baya!?, duk bata yi wannan tunanin ba, hmmmmm toh bari kaji, ko da wasa kayi gigin guduwa da yar mutane toh wallahi daga ranar ba ni ba kai ko a mafarki".

Ajiyar zuciya Hydar ya sauke ya ce"hakan ma bazai faru ba, yanzu dai mai abun yi".

Jingina da kujera Sa'ad ya yi sannan ya ce"the only solution now is ku rabu kawai tunda haka abun ya kasance, ka kirata kace ta yiwa iyayenta biyayya, Allah ne kawai yasan abunda ya gani daya raba ku, so ka gode mai, ba rabonka bace, wani hani ga Allah baiwa ce, Allah ya zaba maka wata mafi Alkairi, bawai Ina kushe ta bane ko kuma wani abu makamancin haka, nasan ilham nada hankali da natsuwa ba laifi, amman hakuri duk zaku yi, ka kwantar mata da hankali pls tayi musu biyayya, na san ka san yanda zaka yi pls friend".

Ajiyar zuciya Hydar ya sauke ya ce"insha Allah I will try my possible best Akhi".

Rungume shi Sa'ad ya yi yana murmushi, kiran sallar da  suka ji ne yasa su zare ido a tare, duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun shi Hydar ya yi yaga da gaske lokaci ya yi, tab Akhi wallahi lokaci ya tafi bari na yi sallah na wuce gida, a tare suka shiga bathroom dan yin alwala, bayan sun fito Hydar ya dau wayoyin shi da car key suka fice, bayan sun dawo masallaci suka nufi part din Mummy, suna shiga taga son din nata ya saki jiki, Hydar ya mai magana kenan, ta rasa dalilin da yasa yaki gaya mata, amman ba komi tunda hankalin shi ya dan kwanta, da Hydar zai tafi Mummy ta bashi wani laida ya kaiwa Hajiyar shi, godiya Hydar ya yi mata, Mummy bata rabuwa da kyauta, kullun yazo sai ta hada shi da kyauta, nashi ko na Ammin shi, tare suka fice da Sa'ad ya raka shi har bakin motar shi ya shiga suka yi sallama ya fice daga gidan.

Dakin shi ya nufa ya dau jakar laptop din shi ya nufi bayan gida ya zauna kan daya daga cikin kujerun da aka tanadar, ba tare da bata lokaci ba ya fara aikin da ya zaunar da shi, hirar da suka yi da Hydar ne ya fado mai a rai, tunanin yanda zai yi ta shiga motar shi yake, ya Allah kasa abin yazo min da sauki, idan na gaya mata zata yarda kuwa?, ya zata dauke ni?, ni kam soyayyah ta chuchan, haka ya dinga saka da  warwara har lokaci ya tafi, tashi ya yi ya dau jakar laptop din shi ya shige part din shi, a parlor ya ajiye jakan sabida idan ya dawo zai cigaba, bedroom ya shiga ya dau towel ya rage kayan jikin shi ya  shiga bayi ya yi wanka tare da alwala, bayan ya fito ya shafa lotion ya fesa turare, drawer ya bude ya dau bakin jeans da white T-shirt sai singlet da boxers, bayan ya gama shiri ya kara fesa turare, kamshi kawai ke tashi a dakin kaman an yi barin turare, wayar shi ya dauka ya fice daga part din, bai zarce ko ina ba sai masallacin dake kusa da gidan, bayan an idar ya dawo gida ya cigaba da akin shi, yana cikin aiki ya ji ana knocking, izini kawai ya bada ba tare daya mike ba, salame ce ta shigo dauke da tray a hannun ta, gaida shi ta yi tana ajiye tiran a center table dan dama dining zata ajiye yasa ta maido shi center table, bayan ya gama akin shi ya wuce masallaci, bayan ya dawo ya kunna Tv ya maida shi tashar news, janyo center table din ya yi ya bude coolers din daya bayan daya, na farko daya bude yaga shikafa ce sai miya a wani cooler da coslow a wani dan bowl an kulle sai tuwo da miyan egusi a dayan coolers din sai pepper meat, tuwo kadan ya saka sannan ya dibi pepper meat shima kadan, bayan ya kammala ya mai da coolers din,a parlor ya tadda Mummy, zama ya yi kusa da Mummy baya ya kai kwanonin, hira suka dan taba, goma na yi ya sallame Mummy, yana shiga ya kulle kofar parlor ya kashe kayan electronics din sannan ya wuce bedroom, kayan shi ya cire ya shiga wanka bayan ya fito ya shafa lotion ya fesa turare sannan ya shirya cikin pj max kalan sky blue mai rasin baki, kashe wutar dakin ya yi bayan ya gama shiri ya saura dim light, kwantawa ya yi ya ja bargo, nan ya fara tunanin sahibar shi, sai wani murmushi da juyi yake kaman an mishi albishir da gidan aljanna, da dai naga abin ya fi karfi na sai na sallame shi na yi gaba.

Kwanaki sun shude, zaune suke a parlor suna hira Daddy ya ce"gobe zaku dawo makaranta ko Lailah, girgiza kai Lailah ta yi ta ce"ehhh Daddy hutun ya kare".

"400 level zaku shiga yanzu kohhh!?".

"Insha Allahu Daddy".

"Ubangiji Allah ya taimaka mamana, ya tsare ki ya baki sa'a Ameeen".

"Ameen Ameen Daddy nagode".

Juyo da kallan shi kan Husna ya yi ya ce"Autana ku fahhh?".

"Saura mana sati daya mu dawo Daddy", toh shikenan Allah ta kaimu rai da lafiya Ameeen, hira suka cigaba da yi har karfe uku da minti arba'in da biyar, mikewa Daddy ya yi ya ce"su je su yi sallah shima za shi masallaci", ya fada tare da ficewa, bayan sun idar da sallah suka dawo parlor suka cigaba da hira, mikewa Lailah ta yi ta nufi kitchen ganin biyar ta yi.

Juyowan da  Mama za zata yi sai taga Husna a zune ta kafe TV da ido, dama Husna ba dai kallo ba, ban ce duk sanda Lailah zata shiga kitchen ki bita ba ko so kike ranki ya baci, maza tashi ki barnan"tashi Husna tayi tana turo baki gaba", girgiza kai Mama ta yi ta ce"bakin bai yi tsawo ba tun da banga ya kai gate ba.

Dariya duk suka yi harda Lailah dake aiki a kitchen, tunda ta shigo kitchen ta lura da yawan murmushin da Auntyn ta take, ganin abun ba na karewa bane yasa ta fadin Anty..........................................

COMMENT

VOTE

AND

SHARE

FISABILILAH

BY GIMBIYA AYSHU💞💞💞.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.