Free chapter 路 Read without an account
page 20
馃挒馃挒馃挒LAILAH馃挒馃挒馃挒
STORY AND WRITTEN BY
AISHA MA'ARUF (GIMBIYA AUSHU)
ELEGANT ONLINE WRITERS
SHARE FISABILILAH.
Gimbiya Ayshu's Data service
Ku siya data a garabasa
MTN
500MB-180
1GB -280
2GB - 550
3GB - 750
5GB - 1250
10GB -2500
AIRTEL
300MB - 170
500MB - 200
1GB - 300
2GB - 550
5GB - 1350
10GB - 2600
GLO
200MB - 120
500MB - 180
1GB - 300
2GB - 550
3GB - 850
5GB - 1350
10GB - 2600
9MOBILE
500 - 180
1GB -280
2GB - 550
5GB - 1300
10GB - 2500
Account number:***
Account name: Maryam Maaruf Muhammad
Bank name:Opay
Contact me on this number:***
PAGE 37-38
_____________________Sai wani murmushi kike kaman an miki albishir da Aljannah, murmushi kawai Lailah tayi, "hmmmm baza ki gane ba", ta fada chan kasan makoshi, bayan sun gama girkin suka jerashi a dining Husna ta wanke kwanonin da aka bata ta gyra kitchen din, bayan sun yi sallah suka danyi hira a parlor kaman yanda suka saba.
Gyaran murya Daddy ya yi ya ce"mamana".
Saurin dagowa ta yi ta ce"na'am Daddy".
"Gobe zaku koma school kohhh".
"Eh Daddy, hutu ya kare".
"Wa zai kai ki yanzu, driver ya yi tafiya ina jin cikin satin nan zai dawo ko next week".
Murmushi ta yi ta ce"Daddy i na iya driving zan iya zuwa da kaina".
Zare glass din dake idan shi ya yi ya ce"wallahi ko da wasa kika kuskura kika dau mota da sunan za kiyi driving da kanki zaki ga abinda zan miki, da baki kwaren bane zaki hau babban titi, ko da wasa karki kuskura mamana".
"Toh Daddy, insha Allah bazan yi ba".
"Idan zan shiga daki ki bi ni ki amshi transport din gobe, zan miki transfer sauran kudin a account zuwa gobe insha Allah".
"Nagode Daddy Allah ya kara budi ya kare ka daga sharrin makiya da mahassada ya kara maka tsawon rai hada baki duk suka yi wurin amsawa da Ameen.
Washe gari da wuri Lailah ta tashi, daka kalle ta zaka san tana cikin farin ciki mara misaltuwa sai murmushi kawai take akai-akai, bayan tayi sallah bata koma barci ba ta shiga kitchen ta hada mutsu breakfast, 6:20 ta gama ta gyra kitchen din ta wanke kwanonin da ta bata, a takaice dai 6:30 ta bar kitchen din, dakinta ta shiga ta yaye bedsheet din ta shinfida wani sannan ta saka wannan a basket din kayan datti, ta share dakin tayi mopping sannan ta kunna burner na turaren wuta ta fesa room fresher sai kamshi ke tashi, bayan ta gama ta shiga toilet, sai data wanke bayin sannan ta yi wanka, ko da ta fito bakwai ta yi, mai ta dauka ta zauna gefen gado, bayan ta gama shafa mai ta bi jikin ta da tularan humra, tsayawa ta yi gaban dressing mirror ta shafa powder kadan ta gyara giran ta sannan ta saka lips gloss, tadan shafa powder kadan tayi brushing eye brown dinta tasa lip gloss, kallan kanta take a madubi tana murmushi, sai data bata kusan minti biyar wurin murmushi da madubi dan bazan ce da mutun ba tunda babu kowa wurin, da tsauri ta nufi wurin kayanta ta bude drawer ta dauko inner wears first sannan ta dauko wani paper less kalan baby pink an mai kwalliya da stones riga da skirt ne sai ta dauko hijabi shima kalan kayan ta kulle drawern inners din ta fara sawa sannan tasa skirt, skirt din ya yi mata das a jiki kaman a jikinta aka yi kayan, rigan ta saka sannan tayi daurin turban sannan ta dauko hijabi tasaka ta dauko jaka da takalmi duk kalan kayan, turare mai dan saukin karfi ta dauka ta feshe jikin ta da shi, kallan kanta ta yi ta cikin madubi, ta san tabbas ta yi kyau sosai, ko makiyin ta bazai kushe ta ba, ficewa ta yi daga dakin ta nufi dakin Mama bakin ta dauke da sallama, bayan sun gaisa ta ce"Mama na gama shiri", kin cin abinci ne?.
Girgiza kai ta yi ta ce"a'a yanzu zan sauka down stairs na yi, kudi Mama ta dauko a pose ta bata tana mata addu'ar dawowa lafiya, a dining ta tadda Husna tana cin abinci, toh acici daga tashin ki har kin nemi abinci,
Murmushi Husna ta yi ta ce"ina kwana Anty Lailah".
"Lfy lau acici kin tashi lfy".
Turo baki ta yi ta ce"lfy ayyyaahhh Aunty acici fahhhh!", kujera Lailah taja ta zauna ta ce"bayan toh ba haka bane, breakfast ta yi a gurguje ta tashi ta yiwa Husna sallama ta fice tana fadin"ki gyra parlorn nan da dakin Mama kafin na dawo, saura karki yi na san halinki da shegen kiwiya".
Dariya Husna tayi tace zan mayi Anty kisha kurumin ki, wankannan ya yi cizo fahhh, Allah yasa dai kar ki sa wani lectural tuntube ta karasa da dariya, auna mata harara Lailah ta yi sannan ta ce"keko na lura kwanan nan kinfara rashinji zan yi maganin kine yarinya", Mama dake tsaukowa ta ce"har yanzu baki tafi bako kin san abin hawa zakibi ko, karki wuce ki tsaya biyema shirman Husna, sai na dawo kawai ta ce musu, Mama ta bita da Allah ya tsare sannan ta ce"kiyi addu'a kafin ki fita".
"Da insha Allah ta amsa ta fice daga parlor".
Tana fita ta sami napep ta ta gaya mai inda zata, takwas da minti sha biyar ta isa kofarakaranta ta sauka ta ba shi kudin shi sannan ta nufi cikin makarantar.
Sanye yaka da farin bathrope da wani towel a hannu, bakin gashi ne kwance a girjin shi sun kwanta luf-luf, sai sauri yake kaman zai tashi sama, yana cikin shafa mai wayar shi ta dauki ruri, janyo wayar ya yi ya ga malan Muhammad ke kira, ba bata lokaci ya daga da sallama a bakin shi, bayan sun gama gaisawar ne Malan Muhammad ya ce"ka manta yau kana da lecture kohhh?".
"Wallahi na dan makara ne amman insha Allahu ina tafe".
"Toh shikenan Allah ya kawo ka lafiya".
"Ameen ya Rabbi, ko zaka shiga kafin nazo?".
"A'a sai dai ka zon dai".
"Toh shikenan nagode", da haka suka yi sallama, duba agogon wayar shi ya yi yaga takwas har da minti sha bakwai, da sauri ya karasa shafa man ya saka kaya ya feshe jikin shi da tulare, wayoyin shi ya kwashe ya kashe Ac da wutan dakin sannan ya fita a parlor, part din Mummy ya nufa, ya shiga da sallama, salame dake kitchen ne ta leko ta gaishe shi, amsawa ya yi yana hawa upstairs, knocking ya yi a kofar dakinta ta bashi izinin shiga, gaisawa suka yi a gurguje ta tanbaye shi ya yi breakfast?, girgiza mata kai ya yi yana kokarin mikewa, ka tsaya ka yi breakfast mana, "wallahi na makara Mummy, zan naimi abu a chan na ci".
"Toh shikenan son Allah ya kiyaye hanyya, a kula banda tukin banza".
"Toh shikenan first luv insha Allahu zan kula", tun daga kofar parlor ya danna lock din motar, yana shiga ya bata wuta tare da dannan horn mai gadi ya fito da sauri ya bude mai yana Allah ya kiyaye, ba shi ya isa ba sai takwas da minti hamsin, jakar shi ya dauka da wayoyin shi ya nufi office a gurguje, bayan ya bude office din ya shiga ya ijiye jakar laptop din shi ya dau materials din da zai shiga aji da shi ya fita a office din ya kulle, office din Mln Muhammad ya nufa ya yi sallama bakin kofar ya ba shi izinin shiga, shiga ya yi suka gaisa sannan ya wuce ajin da zai yi lectures.
Karfe uku da arba'in suka gama lectures ta fito a hall direct masallaci ta nufa dan ta fisan ta yi sallah kafin taje gida tinda lokaci ya yi kuma ba driver zata biba balle ta ce zai tsaya jiran ta, bayan ta yi sallah ta nufi hanyyar fita daga makarantar.
Karfe uku da arba'in da biyar ya fito daga office, bayan ya fito ya hadu da Mln Muhammad a corridor, gaisawa suka yi sannan suka jera tare har suka fito, yana fitowa idan shi ya fada kan Lailah, da sauri ya dauke kan shi dan kar Malan Muhammad ya lura da inda yake kallo, sallama suka yi ya yi mishi sai gobe har Mln Muhammad ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya ce"kar dai ka makara irin na yau", dariya kawai Sa'ad ya yi ya nufi parking space, back seat ya bude bayan ya dannan lock din motar, ajiye jakar shi ya yi sannan ya shiga driver seat ya yiwa motar key, reverse ya yi sannan ya bar wurin tafiya yake a hankali dan akwai dan tazara a tsakanin ta da gate, kara gudun motar shi ya yi ya fita daga makarantar, parking ya yi a gaba da makarantar, ya san baza ta sami abin hawa ba saita kai bakin titi, relaxing ya yi a jikin kujera yana danna waya amman duk hankalin shi nakan kofar makarantar, ya yi kusan minti bakwai kafin yaga ta fito, kallon yanda take taku yake har takusa karasowa, saukar da glass din motar ya yi kafin ta karaso, tana kaiwa dai-dai gun kofar ya ce"ta shigo", yi ta yi kaman bata ji ba ta wuce, horn ya danna mata, juyowa ta yi fuskar ta a hade babu ko alaman murmushi balle dariya.
Leko da ka shi ya yi ta window ya ce"ki zo ki shiga muje".
Dan sakin fuska ta yi ta ce"nagode yanzu zan samu abin hawa insha Allahu".
Hade rai ya yi ya ce"bana san musu".
Turo baki ta yi ta fara takowa a hankali har ta zagayo bangaran mai zaman banza, tsayawa ta yi taki bude kofar, kallon ta yake ta cikin motar ya ce"tabdi akwai aiki a gabana, hannu yasa ya bude kofar ta ciki", sai da ta gama shan kamshi sannan ta shiga", ko kala bai ce mata ba, ajiyar zuciya ya sauke a boye sabida wani irin daddadan kamshin daya ratsa shi har bargon shi, kamshin tularen ta ya tafi da shi sosai, tayar da motar ya yi suka tafi.................................................
COMMENT
VOTE
AND
SHARE
FISABILILLAH
BY GIMBIYA AYSHU馃挒馃挒馃挒.