Free chapter 路 Read without an account
page 36
馃挒馃挒馃挒LAILAH馃挒馃挒馃挒
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU 馃挒馃挒馃挒
ELEGANT ONLINE WRITER'S 馃摎
HAPPY RAMADAN MUBARAK TO ALL MUSLIM UMMAH. ALLAH YA SA MUNA CIKIN ENTATTUN BAYI,ALLAH YA SADA MU DA ALKAIRIN DAKE CIKIN WANNAN WATAN MAI ALBARKA.AMEEEEEEEN 馃げ馃げ馃げ.
Patronize my product
BY GIMBIYA AYSHU 馃挒馃挒馃挒
***
KU tayani sharing wannan link din dake sama Kuma Dan Allah kuyi viewing.
PAGE 69-70
________________________Knocking Mai gadi yayi a kofan parlor,bayan kaman minti 1 Mai aikin su ta bude,gaisawa sukayi sannan yayi Mata bayanin abin da k tafe da shi,da toh ta amsa sannan ta kulle kofan ta nufi ciki, upstairs ta hau ta nufi dakin hajiya,sallama tayi hajiya ta Bata izinin shiga,shiga tayi da sallama ta suka har kasa ta gaida Hajiya,Amsawa Hajiya tayi da murmushi sannan tace da matsala ne,a'a Hajiya dama Alhaji ne yayi bako,yanzu Mai gadi ya gayamin shine nace Bari inzo in sanar Miki,Dan shiru Hajiya tayi dan,tasan Alhaji Baisan da zuwan wani baki ba,Ina bakon yake,amsawa tayi da inaga Yana waje,ahhhh! Ki kai shi parlorn saukar da Baki na Alhaji,Kuma ki kaimai abinsha da abinci.da toh ta amsa sannan ta mike ta fita,tana fita Hajiya ta mike ta fita daga dakin ta ta nufi na Alhaji,shiga tayi da sallama,samun shi tayi ya kishingida da gado yana zaune akan sallaya,amsa Mata sallan yayi sannan yace lafiya dai kohhhh! Hajiya, murmushi Hajiya tayi tace lafiya Kuma ba lafiya ba,gyara Zama Alhaji yayi da tsauri yace Mai ya faru, murmushi Hajiya tayi tace ka kwantar da hankalin ka ba wani abun bane Dana bako kayi, girgiza Kai Alhaji yayi yace wlh harkin tayar min da hankali, dariya Hajiya tayi tace srry Alhajina,a min afuwa, ta fada tana Kama kunnen ta, murmushi daya fitar da wushiryar shi da ainahin Kamala da mutuncin shi yayi,Yana Mai Jan kumatun Hajiya,dariya duk sukayi suka dunguma zuwa waje,daki Hajiya ta koma while Alhaji ya wuce parlor baki.......
Sallama Alhaji yayi a kofan parlor,kan shi tsaye ya kalli ko waye bakon,hada Ido sukayi da Sa'ad,suna hada Ido Sa'ad ya tsaukar da nashi sannan ya duka harkasa ya gaishe da Alhaji,Amsawa Alhaji yayi Yana Mai Zama akan kujera sannan ya bama Sa'ad izinin Zama,kin Zama akan kushin Sa'ad yayi ya gyara zaman shi akasa Yana Mai tankwashe kafa kaman zaici abinci,tsayawa Alhaji yayi Yana kallan shi Dan Bai Gane fuskan shi ba,Amman yanayin yanda yaga yaron sai ya ji ya birge shi Dan da Alama akwai tarbiya tattare da shi.
Gaishe da shi Sa'ad yayi sannan yayi shiru kan shi a kasa,Amsa mishi Alhaji yayi da kukawa,Bayan Kama minti 5 shiru ya ratsa parlor,Alhaji ne ya katse shirun da Dan tsaurayi Mai k tafe da Kai,Dan shiru Sa'ad yayi ya sunnan da Kai kasa, murmushi Alhaji yayi,kayi magana,karkaji komai kaji."Gyara Zama Sa'ad yayi sannan ya Fara Koro bayanin abin da k tafe da shi,tun da ya Fara magana Alhaji yayi shiru Yana kallan shi har ya Kai Aya,A karshen ko yace Allah yasa ba'ayi Mata Miji ba",shiru Alhaji yayi Yana nazartan yaron da kamalan shi da koman shi,Dan jimmmmmm Alhaji yayi sannan yace a gaskiya dai banyi ma Aisha miji ba,Kuma Ni diyata karatu take a halin Yanzu,bansan na Mata aure har sai ta gama karatun ta,Amman yanayin yanda kazomin da Kuma kwarjinin ka da sharadin da kabi( wato yanda Addini ya yarda a naimi Aure),zan baka izinin naiman Auren ta Amman da sharadiiii............,ya karasa maganar Yana daga yatsar shi daya,Sa'ad najin haka gaban shi ya Fadi,"Sharadin shi ne "zata cigaba da karatun ta",Aiki ne dai ban tilas ta ba,wannan duk yanda kayi dai-dai me tun da Kaine mijin ta Im Allah yaso,"yanda Sa'ad yaji baban na magana ya tabbatar mishi da yasamu karbuwa........"duk a zuciya yake wannan batun,"Dan murmushi Sa'ad yayi sannan yace insha Allah baba zata cigaba,bazan baka kunyya ba", da toh shikenan Alhaji ya amsa sannan yace An baka izinin zuwa naiman ta,Amman indai diyata tace Bata son ka toh tabbas bazan Mata dole ba,Allah yayi Mana jakora, da Ameeen Sa'ad ya amsa,Alhaji ne yace baka Sha komai ba, murmushin da yasa wushiryar shi fitowa yayi sannan yace,na koshi Alhaji,kallan shi Alhaji yayi yace I baka Isa ba sai kasha in ba haka ba baka tafiya,"yanda dattijon k Mai magana Yana birge shi sossai hakan yada hankalin shi ya Kara kwanciya da yarinyar,yasan ko ba komai yayi Aure a gidan mutunci.........Daukan drink daya yayi ya tsiyaya a cup sannan ya shanye.bayan ya shanye Alhaji yace ko Kai fahhh! Yanzu zaka iya tafiya, murmushi Sa'ad yayi Yana Sosa kan shi sannan yace zan tafi Alhaji,wani laida ya dauko ya ajiye a gaban Alhaji yace a kaima hajiya,ahhhh!Mai haka zo ka dauka Dan Allah an gode, girgiza Kai Sa'ad yayi yace ayi hakuri a amsa Abba Dan Allah ba Dan Ni ba,shiru Alhaji yayi yakasa cewa komai sai kallon Sa'ad da yake,Sa'ad ko Jin yayi shiru yasa shi sannin bazai miyar ba,San tafi Alhaji a gaida gida,tashi Abbab yayi yace toh Allah ya kiyaye ka gaishe da baban ka,da toh!Sa'ad ya amsa Yana Mai fita daga parlor,wurin motan shi ya nufa ya shiga yayi Mai key,horn yayi a bakin gate Mai gadi ya bude mai,hannu yasa ya a Aljihun ya dauko kudin da Baisan adadin su ba ya Mika mai,amsa Mai gadi yayi Yana godiya sossai,fita yayi daga gidan Bai zarce ko Ina ba sai gida,ko daya Kai gida 9:30,main parlor ya shiga ya ci abinci, sannan ya Dan taba Hira da mummy har karfe 10:30...........ko daya koma dakin shi wanka ya shiga bayan ya fito ya feshe jikin shi da Tulare sannan ya zura jallabiya ba tare da ya tsaya shafa Mai ba,darduma ya shinfida sannan ya haukai yayi shafa'i da wutri,Bayan ya idar ya Dan Yi wasu Addu'oi,bashi ya kammala ba sai karfe 11.......ko daya tashi linke darduman yayi sannan ya zare jallabiyan ya tsaura daga shi sai gajeran wando,ajiye su yayi sannan ya bi lafiyan gado,wayan shi ya dauka ya danna ma layin ta Kira,sai da Kiran ta kusa katsewa kafin ta daga.
Sallama tayi Mai cikin sanyin muryar ta Mai dadin ji da gardi,amsa Mata yayi da natsuwa,Yana tanbayan ta mutanen gida,daganan daki Hira ta barke a tsakanin su inda duk Suka tsaki jiki suna waya,ba su Suka kammala ba sai karfe 12: 26,Shima Dan suna da wurin zuwa be yasa ya katse hiran.bayan duk sun ajiye wayan Sa'ad ya gyara kwanciyan shi Yana ta tunanin irin karancin da baban Aisha ya Mai, yasan tabbatas in ya aure ta ya auri Yar gidan mutunci da dattako,haka dai yayi ta tunani har barci ya dauke shi..............
A bangaren Aisha ko farin ciki kaman ya kashe ta Dan dazu da Abba k bama Ammin ta labari tana wurin Amman duk busu sani ba.haka dai tayi ta murnar ta da farincikin har tayi barci.
A bangaren Lailah "Mrs Abba",yanzu dai jituwa ta samu bakaman da ba,sai dai har yanzu Taki Bari komai ya shiga tsakanin su inda Shima Bai taba nuna mata komai ba.yanzu har abinci suke ci a kwano daya suyi Wasa,su kwana tare.amman har yanzu takasa sake Mai jiki,inda abin k damun Abba Amman Bai nuna mata ba,itako duk a shirman ta gani take hakan data keyi ne zai sa yaji ya tsane ta ko Kuma bai iya Zama da ita ya sallame ta ta auri "BURIN RANTA"batasan ko duk abin da takeyi a shirman ta bane,Dan shi ya dau ma kan shi alkawarin ba tsaki a tsakanin su mutu ka raba takalmin kaza.haka dai rayuwan ta cigaba da tafiya a gidan wainnan ma'auratan biyun.
A bangaren Sa'ad ko ya Kai kudi nagani inaso da duk abin da ake bukata, inda magabatan shi sukace basusan lokaci sossai, Nan dai aka tattauna inda a ka dayar da bikin Nan da wata daya,i.e sati hudu kachal.
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya inda a yanzu tsaura sati daya da kwana biyu a daura ma Aisha da Sa'ad Aure,sai soyayya su suke Sha ba Kama hannun yaro,sun saki jiki sossai kowa nasan nuna ma Dan uwan shi kulawa,inda ba maisan bacin Ran Dan uwan shi.gyran jiki ake Mata na mutsanman,dama abinka da kudi ansaki kudi sossai wurin gyara Amarya,kawayen ta da Suka shigo ne Suka katse Mata hiran da take da habibin ta,Hira Suka farayi akan yanda event din bikin zai kasan ce,inda Aisha tace it's walima kawai takeso Dan duk tsauran bidi'an ba damun ta yayi ba,wata ce a cikin su tace matsalana da k kenan malanta,ko kinki ko kin so sai munyi event biyu da walima uku kenan ta karasa tana tanbayan tsauran kawayen nasu,da shewa Suka amsa suba fadin haka abin yake,inda suka tsara komai yanda zai tafi Dan ba isasshen lokaci,sun barshi akan za'ayi reception bayan an daura Aure da Rana sai Kuma dinner da daddare,sai washe gari ayi walima,Aisha najin su komi batace ba Banda murmushin da tayi mutsu.
Yau ta kama Friday/26/03/2022 inda aka shaida Auren Aisha Muhammad sani da Sa'ad Muhammad Aliyu akan sadaki dubu dari biyu da hamsin lakadan ba ajalan ba,Wanda dubban mutane Suka samu halartan daurin Auran ciki ko harda sarakuna,governs,mayya mayyan en ka suwa ciki da wajen kasar,da dai mayyan mutanen kasa,wato kusoshin kasa,abin ka da daurin Auren mayya,Ana daura Auran aka Fara guda a cikin gida,ana ta kirari na ban girma Dan ko a cikin gidan akwai matan sarakuna.da musalin karfe 2 aka Fara diban mutane zuwa hall din da za'ayi reception,a karshe a ka dauko Amarya da Angon ta inda motocin Abokan Amarya Dana Ango k zagaye da su,ana kaiwa bakin hall din Abokan Amarya Dana Ango Suka fito inda aka bude ma Amarya da Ango kofa,suna fitowa wurin ya dau wani kyalli na musamman,sun sanyya Kaya Mai kalan golding while Abokan Amarya Dana Ango Sukasa fari,jerawa sukayi inda a kasa Amarya da Ango a tsakiya,kida Mai kwantar da hankali da sa natsuwa aka saki,inda Suka Fara shigowa suna Dan taka rawa Amman Banda Amarya da Ango,har suka Kai wurin zaman su,Bayan sun zazzauna aka Fara event inda aka Kira babban Abokin Ango Hydar ne ya fito inda ya bada takaitaccen labarin Ango Bayan ya Gama aka tafa Mai,haka ma Abokiyar Amarya ta fito ta bada labarin Amarya to kuga yanda ake ihu ana tafi,daganan aka gayyaci Abokan Amarya suzo su taka,aka tsakin musu gida,bayan sun Gama aka Kira Abokan Ango sukayi nasu,sannan en uwan Amarya,Bayan sun Gama aka Kira en uwan Ango,daganan aka Kira jigajigan wato Amarya da Ango,inda Suka fito Suka shiga filin rawan suna Dan takawa ahankali Kai da ganin su kasan ba en chasu bane,Dan Basu iya rawan ba,Sa'ad me ya rike hannun ta Yana juyata yana murmushi,to kuga yanda ake shewa sai wheesul da tafi ake,sai daukan su video da hotuna ake inda anan take wasu Suka watsa shi internet,Nan dai Amarya da Angon ta Suka koma wurin zaman su inda Aka bukacu sukara fitowa Dan su Yanka cake,Sa'ad me ya yanko ya saka Mata a Baki tana kallon shi Yana kallon ta,Kuma duk suna murmushi aka dauki hoton tare da Dan shirt video Mai kyaun gaske,itama tayi kokarin bashi Amman da yake ya fita tsawo takasa kaiwa sai tayi kokarin daga kafa Amman duk da haka,shiko Yana sane ya ki dukawa,tafi kowa ya Fara Yi a wurin akace Ango kayi wani Abu Mana,kafin su Ida rufe bakin su yayi sama da ita,haba zo kuji yanda ake tafi da ihu da shewa,mutane sai tururuwan video da hoto sukeyi Dan ba karamin kyau sukayi ba,saka mishi cake din tayi a Baki inda ya ciza kadan sai ya Bata tsauran taci.bayan angama Yanka cake aka Fara cin abinci inda ake serve your self,wurin karfe biyar aka tashi a wurin inda kowa ya watse.
Da mitsalin karfe shida aka so aka Fara diban jama'a zuwa wani hall din inda za'ayi dinner,sai wuraren 7 Ango da Amarya Suka iso inda suke tsanye da Kaya kalan blue,kawayen Ango da Amarya ko Suka saka sliver,tsaurin yayi kyau sossai,jerawa sukayi Suka shiga cikin hall din har wurin zaman su,MC ne ya Fara gabatar da abinda zaiti kafin aka Fara gudanar da taro da Addu'a,sannan aka bukacu labaran Amarya da Ango,sai aka Fara rawa daganan aka ci abinci,ba su Suka tashi ba sai karfe 10:00 ko da Suka Isa gida 10:26,a gajiye duk suke,Aisha ko tafi kowa gajiya Dan ki take kaman ana karya kasusuwan ta,wanka kawai tayi tayi sallama isha'i da shafa'i da wutri dama Already tayi magrib kafin su tafi.tana idar da sallah tabi lafiyan gado sai barci,wata ce ta shigo dakin tana naiman Aisha Kai da ganin ta kasan jini ya hada ba, wata bace face Nooratu yayar Aisha,amsa Mata akayi da tayi barci,rike haba Nooratu wacce ake Kira da Noor tayi tace dama nasani i,na Gaya ma mum tayi barci,Yarinyar ga da batasan wahala,ta karasa tana tabe Baki sannan ya kulle kofan ta wuce.
Washe garj wurin karfe 2 aka Fara walima,indashi wannan a cikin gida za'ayi na en uwan Amarya me kawai sai abokan Arziki.Sai wurin karfe 4 aka kammala taron inda bayan Amarya tayi sallah aka Fara shirya ta Dan da anyi sallah isha'i za'a kaita gidan ta,ruwan wanka aka hada Mata yakai kala biyar duk na gyaran jiki ne da na Tulare,bayn tagama wankan ta shafa Mai sannan ta zauna aka rangada Mata kwalliya Mai daukan hankali da Ido,bayan angama aka dauko Mata kayanta tasa,tana sawa ta nufi drawer ta dau hijabin ta da darduma ta shinfida tayi sallah dama da Alwala ta,bayan ta idar aka Fara daukan totuna har zuwa karfe 7:45,sallan isha'i tayi,bayan ta idar aka ska Mata Alkebba dayayi matching da kayan ta,sannan aka fito da ita zuwa dakin maman ta,wa'azi Mai rasa jiki akayi Mata,inda mum ce last din yi Mata wa'azi Dan sai da kowa ya Gama,magana mum take Amman muryan ta na cracking Kai daga hi kasan kuka ke cinta,tana kaiwa karshen maganan kuka ya kupce Mata, rungume Aisha tayi tana kuka,Aisha ma kuka take,wasu daga cikin kawayen ta da en dakin ma duk kuka suke,sun Basu tausayi sossai,da kyar aka cire Aisha a jikin mum,yayar mum ce ta rike ta tana lallashin ta,haka aka janyye Aisha tana kuka aka nufi parlor da daddy yake,wa'azi akayi Mata sossai,bayan an Gama aka miyar da ita gun mum Dan suti bankwana kafin mota ya karaso,baifi minti 10 ba mota yazo,mum na kuka Aisha nayi,da kyar aka rabasu,kowa abin tausayi ya basu,haka aka janyye Aisha aka sata a mota inda wasu daga cikin mayya Suka rakata da kawayen ta da en uwan ta har gidan miji,bayan sun kaita aka Bata umurnin ta ahiga da kafan dama inda akayi Mata Addu'oi sossai kafin ta ahiga,har dakin ta aka kaita,Zama tayi a gefen gado inda en uwanta Suka sauka Dan ganin gida,Basu fi minti 20 ba Suka juya inda aka bar Abokan ta kawai,baifi minti 10 da tafiyan su ba Ango da tawagan shi suka zo,Nan dai Abokan Amarya Suka Yi ciniki da Abokan Ango aka biya kudin siyan baki,kimanin 1.5 million,Bayan angama komai Abokan Ango Suka kwashi kawayen Amarya Suka wuce inda ya tsaura daga Ango sai Amaryar shi,bayan ya raka Abokan shi ya dawo ya kulle ko Ina a gidan,ya kashe wutan parlor,dakin ta ya koma,wurin ta ya matso,hannu yasa ya daga hulan Alkebban ta,fuskan ta na kasa,hannu yasa ya daga kanta,yaga fuskan ta yayi jajawur,sunan ta ya Kira sannan yace ta kalle shi,yagi idanuwan ta da sukayi jajawur tayi ta zuba su a kan shi,sai da idanuwan ta Suka bashi tsoro saboda yanda sukayi ja,Mai ya faru,tanbayanta tafara a rude, girgiza mishi Kai tayi kawai hawaye na tsauka a idan ta,Zama yayi kusa da ita ya rungume ta Yana shafa Bayan ta sannan yace ki gayamin Maine be Mana,Jan hanci tayi sannan tace mummy naaaaa...........Dan murmushi yayi yagane missing din mummy ta ta Fara tun yanzu,hakuri ya Bata sannan yace karta damu duk sanda takesan ganin mummy ta gaya Mai zai kaita, murmushin daya da wushiryar ta fitowa tayi Dan komai na daddy ta dauko,kallan shi take Ido cikin Ido sannan tace are u serious, daga Mata Kai yayi alaman his serious,dariya tayi sossai ta rungume shi tana murna, murmushi yayi sossai yq rungume ta Shima tare da Mata peck a goshin ta, bayan kaman minti 10 ya cire ta a jikin shi tare da Bata umurnin take tayi Alwala,tashi tayi da tsauri tare da cewa toh,Alkabban ta ta cire,tare da tatare Gowan din jikin ta ta nufi kofan data gani a dakin,dai-dai zata shiga yace Baki day towel ba ko bazakiyi wanka ba,juyowa tayi tasa yatsa daya ta dungure kanta ta gefe sannan tace zanyi fahhh,wurin drawer ya nufa ya dau Mata wani towel Mai kalan sky blue ya Mika mata,amsa tayi tayi Masa godiya,juyawa tayi ta shige bayi,tana shiga Shima ya juya ya wuce dakin shi,wanka ya shiga ya hada da Alwala Bai fi minti 20 ba ya fito,Yana fita ya share jikin shi da towel sannan ya sa hand Drayer ya busar da kanshi ya share ruwan jikin shi sannan ya feshe jikin shi da Tulare bayan ya kammala ya dau wayoyin shi ya nufi dakin ta da shi,Yana bude kofa dai-dai Nan itama ta shigo dakin,kwata kwata Bata ji shigowar shi ba da yake taga baya inda ta barshi,kanshin Tulare ta Fara ji,Nan take ta Fara juye juye,a tsaye ta ganshi a bakin kofa haba da tsauri ta suka Dan Babu komi a jikin ta daga ita sai towel, murmushi yayi ya shigo cikin dakin,inda take ya nufa,ganin ta yayi ta duunkuna kanta,ki tashi Mana mutu sallah girgiza Kai tayi alamun a'a sannan tace Dan Allah ka ban hijabi na pls,kallan ta kwai yayi yayi murmushi sannan ya bude drawer ya dauko Mata wani hijabi har kasa,amsa tayi ta saka daga duken da take,tanasawa ki ta mike,wurin dressing mirror ta nufa ta shafa man da ta gani akai sannan ta shafa tularen data gani akai bayan ta Gama ta bude drawer wurin kayan barci,duk Wanda ta dauko sai taga abin Babu tsauki,Dan duk kayan Basu da kai,wani Mai Dan dama dama ta dauko wani gown Wanda iya karshi gwiwa,Mai hannun vest,Kuma shara shara me Amman ba sossai ba,kalan shi dark pink Mai rasin yellow da fari a jiki,yayi kyau sossai,daukan kayan tayi tana tura Baki sannan ta nufi bayi,shiko Sa'ad tagumi ya buga Yana ta kallon duk abin da take,bayi ta shiga tasa kayan sannan ta fito,ta dungure a gefe tace nagama,tashi yayi sannan ya jasu sallah bayan sun idar ya Yi mata Addu'a sossai sannan yayi Mata tanbaya game da Addinin ta Kuma duk ta bashi amsa bayan ya gama Mata tan bayan ya je ya dauko abubuwan daya siya,ko daya dawo dakin samun ta yayi a inda ya barta ta jingina da bango tana barci,Ajiye laidan yayi sannan ya fice a dakin,cup da spoon da fork da knife da plate da ruwa ya dauko ya nufi dakin da shi, Yana ajiye kayayyakin ya tashe ta,bude idan ta tayi kadan wanna ta mike zata wuce kan gado,hannu yasa ya riko hannun ta sannan ya jata ta zauna a gefen shi kwantar da kanta yayi akan kafadan shi,Kazan yasa a kan plate sannan ya zuba ruwa a cofi daya da holandiya Kuma a wani Kofi,feeding dinta ya farayi tanaci tana barci har ta girgiza mishi Kai alaman ta koshi,Shima ci yayi bayan ya gama ya Dan kwantar da ita a kasa wurin, kwashe kwanonin yayi zuwa kitchen sannan ya dau tsauran Kazan yasa a fridge.bayan ya dawo,ya dagata ya zare Mata hijab din dai-dai yazo Ida cirewa ta ankare sakamakon iskan daya bige ta,tsaurin rike hijabin tayi,gwada mats karfi yayi ya pincike hijabin.daukan ta yayi ya nufi bayi da ita,zaunar da ita yayi a gefen bathtub myclean yasa Mata ya Mika Mata,rikewa tayi takiyi sai duddunkulewa take,innarigaki gamawa kohhhh! Hmmmm! Zaki sani,tsaurin tashi tayi tayi brush ta wanke fuskan ta sannan ta fice a bayin da tsauri,dariya mara tsauti Sa'ad yayi,Yana girgiza kai,bin bayan ta yayi,samun ta tayi akan gado ta rufe har kanta,kashe wutan dakin yayi sannan ya Dan Kara AC kafin ya kwanta Shima,mirgino ta yayi ta kwanta a jikin shi,gaban ta ki sai bada Karan dum...dum....dum...yake,har Yana jiyo bugun a jikin shi, rungume ta yayi yace kiyi barcin ki.Asuba ta gariii....................
COMMENT AND SHARE
BY GIMBIYA AYSHU 馃挒馃挒馃挒.