Free chapter 路 Read without an account
page 19
by Gimbiya Ayshu 路 馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰(GIDAN AURENA) BOOK 1.
馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU馃挒馃挒馃挒
ELEGANT ONLINE WRITER'S馃摎
Ina mika gaisuwa ga dukkan masoya na,ina muku fatan alkairi.
Pls follow me on Arewabooks:gimbiyaayshu2503
Whattpad:Aishamaaruf1
BOOK 1:CHAPTER 37&38
_________________________Ko da Hauwa ta fito parlor bata iske kowa ba,tsaki taja tace"gantalallu kawai,daga matar har mijin duk fitinannu ne halin su daya,duk sai nayi maganin ku,en jakan uba,dani kuke zanchan".
Dining ta karasa ta ajiye coolers din,bayan ta gyara kitchen ta kaiwa su Baba nasu.
Bayan an gama break Jameela data hakimce a kan kujerar dining tace"kehhh!" ta fada tana kallon inda Hauwa take.
Ko da wasa Hauwa bata kalli inda take ba balle tayi tunanin zata bata amsa.
"Keh ba dake nake ba?",ta fada da alamun mamaki.
Mami dake cin abinci ta dakatar da cin abincin tana kallon ikon Allah.
Hauwa batako dago ba tace"malama ki daina damun mu da wani keh,daga ni har Mami babu keh a cikin mu haka zalika bamu san keh ba,dan Allah in kin ganta kice ina naiman ta".ta fadi ba tare da wata shakkah ko dar ba.
Murmushin jin dadi Mami tayi zuciyar ta wasai,sai wani cin abinci take tana kas-kas da chokali tana murmushi akai-akai.
"Kallan mamaki Jameela ta bita da shi tana mamakin karfin halin ta,ita ba yar kowa ba amman sai shegen jin kai da aji,ka kyau kamar ita tayi kanta,Allah ma ya sani babu abinda ke sata bakin ciki da takaici kamar kyan da take da shi,tsoron ta daya kar Jalal ya fara son ta".
Tsaurin kawar da zanchan tayi tana istigfari kamar wacce tayi sabo.
Daga Mami har Hauwa kallan mamaki suka bita da shi dan a fili tayi shi.
Ganin irin kallan da suke mata yasa ta saurin dakewa tace"keh yar aiki dake nake magana".
"Ko gezau Hauwa bata yiba balle tayi tunanin samun amsa".
Wani matsiyacin kallo Mami tayi mata tace"sunan tane baki sani ba ko meh?,idan ma sunan ne baki sani ba toh ki kira ta da Autar Mami,ina fatar kin fahimta".
Hura hanci tayi tace"yar tsintuwar Mami idan kin gama kije ki gyara mana daki,dama aikin ki ne,taimaka miki kawai nake kwana biyu".
Kallan Mamaki Mami ta bita da shi,murmushin takaici Mami tayi ta girgiza kai tace"daga yau na sauke aikin gyaran dakin da nace tana yi,idan ke baza kiyi ba toh ki bar dakin kacha-kacha".
Sossai ran Mami ya baci da abinda Jameela tayi,a zuciyar ta tace"wannan wace irin yarinya Jalal yaje ya Auro,yarinya ba kunya ba sanin darajar na gaba da ita,har ita da take sirikar ta bata raga mata ba,wannan wace irin masifa ce".
Ya Allah ka shirya mana zuri'ar mu Ameeeeen.
Mami ce ta fara barin dining ta nufi upstairs rai bace.
Sossai ran Hauwa ya baci da yanayin da taga Mami,ranta a bace ta dubi Jameela tace"wlh kinyi asara,mara kunya kawai,sirikar ki kikewa rashin kunya sabida tsabar rashin tarbiya irin naki,wlh Allah kyauta miki,ina rokon Allah kar ya bawa Mami jikar da zai biyo halinki,inko aka samu ya Allah ina rokon ka kasa cikin ya bare kafin yazo duniya".
Wani irin ihu da kururuwa Jameela tayi tace"na shiga uku na lalace,na bani,ashe dama kece yar bakin cikin da tayi sanadiyyar zubewar ciki na,wayyyyooooo Allah naaaa!,na bani",tayi wani uban ihun da yafi nada kara.
Da sauri Mami ta fito daga daki a rikice kanta ko dankwali babu, zip din rigar ta a bude zani a hannu tana fadin"lafiyaaa!?,mai ya faru?,mai yasa kike ihu haka?.
Da saukowar ta da tanbayar da tayi duk a cikin minti biyu tayi shi,kai da ganin ta kasan a rude take.
Da sauri Hauwa ta karasa kusa da Mami ta riko ta tace"ki kwantar da hankalin ki Mamina ba wani abu ya faru ba,kawai dai ce mata nayi...nan Hauwa ta sanarwa Mami abinda ya faru".
Wani irin dogon tsaki Mami taja tace"amman Allah ya saka min,da badan kina matsayin matar dana kuma diyar dana isa na haifa ba da wlh na miki Allah ya isa,kin cuce ni wlh",ta karasa maganar tana jan tsaki ta bar wurin tana gyara daurin zanin ta ta haura stairs tana masifa.
Wani matsiyacin kallo Hauwa ta aika mata dashi tace"amman kinyi asara wlh,mijin ki ya auro kaddara,ni ban masan abinda ya gani a tattare dake ba da har yace yana son ki,ke ba kyau ba,ke ba fasali ba,ke bah iya magana ba,keh ba keh ba keh ba!!!.....kai abin naki yayi yawa,kai ni ina mamakin yanda akayi wannan kaddararran mijin naki ya auro ki".ta karasa maganar ta tana dalla mata harara.
Ihu Jameela tayi ta nufi kan Hauwa suka fara kokuwa,dai-dai nan Jalal ya shigo yayi arba da abinda ke faruwa.
A dari da saba'in ya nufi inda suke ya fincike Jameela daga jikin Hauwa ya boye Hauwa a bayan shi yace"wannan wani irin rashin hankali ne,wai bakisan kece babba ki kama girman ki ba,mai ke damun ki ne?".
Fashewa tayi da kuka ta nufe shi zata rungume shi yaja baya da sauri yace"meh haka?,ni abinda ya faru zaki gaya min ba runguma na ba",ya fada ran shi a hade.
Kara fashewa da kuka tayi tace"itace fah tayi sanadiyyar zubewar ciki na kuma tace.....nan ta labarta mai duk abinda ya faru tsakanin su".
Tsaki Jalal yaja yace"ina jin ko da cikin nan ya bare baki santa ba bata sanki ba haka zalika nima ban santa ba,toh taya zata zubar miki da ciki,wai kodai kin fara shaye-shaye ne Jameela ban sani ba,wannan wani irin rashin hankali ne,ke ba kida tawakkali ne".
Hauwa data boye a bayan Jalal sai zare idanu take ta rike shi gam,Allah ya sani ta sorata sossai sabida yanda ta hau kanta a haukace gashi tana da uban kunba a farcen hannu kamar mayyah.
Kara karfin kukan ta tayi tace"wallahi tallahi bazan yarda ba sai naci uban ta yau a gidan nan,dama kwana biyu da taga ina kyale ta ba tsoron ta na keji ba,barin ta kwai nayi naga iya gudun ruwan ta".
Ta karasa maganar ta ta nufi kan Jalal a haukace da niyyar fincike Hauwa dake boye a bayan shi.
Hauwa dake ta leken ta ta gefen shi tana ganin ta nufo su a haukace i bata san lokaci data sa hannu biyu ta rungume Jalal ba jikin ta na rawa,yau taga haukar da yafi nata tsamari.
Wani irin shock ne ya kama Jalal jin ta rungume shi,amman hakan baiyi tasiri ba sabida masifar da ake ciki.
Da sauri Jalal ya bude hannayen shi yana yin baya yace"zanyi miki rashin mutunci Jameela,wlh ki kiyaye ni,zan miki abinda bakiyi tsanmani ba,Jameela ki bari,Jameela ki bari,Jameela ki bari".sai daya maimaita sau uku amman sabida tsabar rashinji irin nata taki ji ta nufe shi da gudu tasa hannu za taja Hauwa.
"Rike ta Jalal yayi da hannu daya ta baya dayan kuma ya rike Jameela amman ina ya gagara,sakin Hauwa yayi ya rike Jameela amman sam taki natsuwa",ji kake tassssssss! shiru parlor ya dauka na tsawon minti biyu.
"Runtse ido Hauwa tayi sabida sossai ta firgita da karan marin",i da ita aka mawa da sai dai wata ba ita ba.
Dafe kuncin ta Jameela tayi jinta da ganin ta duk sun dauke mata tsawon second biyar.
Sulalewa tayi kasa ta fashe da matsanancin kuka tace"shikenan ta raba ni da mijina ta raba ni da Mami,na shiga uku na lalace wlh bazan yarda ba sai na rama,wlh i won't take defeat",ta karasa maganar ta tana sakin wani irin gunjin kuka.
Wani dogon tsaki Jalal yaja ya riko hannun Hauwa ya nufi upstairs da ita.
Dakin ta ya kaita ya zaunar da ita a gefen gado,hankin shi dake cikin aljihu ya ciro ya share mata jinin dake gefen bakin ta yace"ki cigaba da biye mata,sai ta miki shegen dukan da zaki kasa tashi randa babu wanda zai cece ki",dai-dai nan wayar shi ya dau ringing,da sauri ya ciro wayar,ya san daga aiki ake kiran shi,shaf ya manta cewa sauri yake.
Barin dakin yayi da hanzari ya nufi nasu,daukan abinda ya dawo da shi yayi ya fice daga gidan.
Tafiyar da za'ayi cikin minti ashirin da uku aka yi shi cikin minti sha biyar.
************SATURDAY************
Kamar yanda su kayi haka abin ya kasance.
Bayan sallah isha'i gayan nan mai suna Sani yazo ya aiki wani yaro daya kira Hauwa.
Bayan yaran ya dawo yace"ance ka shigo daga ciki".
kiran kawu Lado Mama tayi tace"ya iso kawu".
"Toh shikenan gani nan karasowa dama ina cikin layin".
"Shikenan kawu nagode Allah ya taimaka ya tsare"............................
By Gimbiya Ayshu馃挒馃挒馃挒