Free chapter · Read without an account

2

by Amina Abubakar Yandoma · BAYAN AURENA

Yandoma

DAGA AURENA

 

©️MEENAT A 'YANDOMA

 

DEDICATED TO

ASMA'U ABUBAKAR MUSA (JASMINE)

 

GARGAƊI

HARAMUN NE A SARRAFA MIN LITTAFI TA KO WACE HANYA, BA TARE DA IZININA  BA. 'YAN YOUTUBE KU KIYAYE.

 

 

MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M.W.A)

Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu masu nazari da aiki da ilimi burin kungiyar a koda Yaushe shine ta faɗakar ta kuma wa'azantar ta nishaɗantar da masoyanta

____________________

PAID BOOK, FREE PAGE

 

ZAKU TURO 300 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 2294023532 UBA BANK AMINA ABUBAKAR, KU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER *** WANDA BASU DA ACCOUNT SU TURO HOTON KATIN 300 TA WANNAN NUMBER ***

 

 

PAGE 02

...A hankali na fara buɗe idona da ya min nauyi, da sauri na mayar da shi na rufe sakamakon hasken da na gani. "Alhamdulillah! Umma ta farka" na tsinkayo Muryar da bani tantama ta Zainura ce. Shigowar mahaifiyata ta sakani mikewa zaune tare da dafe goshina da nake jin yana barazanar faɗowa. "Sannu Huda, ba shakka kin auna arziki wannan ai kashemin ke suka so yi. To jira Alhaji ya zo dole a fasa auren nan." A gigice na kalli Ummana. "Umma don girman Allah kiyi hakuri wallahi ba laifin Bilal ba ne laifin danginsa ne" "Ke ar! Mara zuciya tsaya kiji in fada miki dama can ba son ki da Yaron nan nake ba. Yaro ga shi nan ɗan mace tun kafin kije gidan har Uwarshi ta fara gallaza miki to ba gajiya nayi da ke ba" Wallahi ina son Bilal in kika rabamu mutuwa zanyi Umma "Yau ni Jikar mutum hudu na shiga uku! Yanzu Huda akan namiji wanda danginshi basu kaunarki ki ke fadar za ki mutu, to kuwa sai dai ki mutu kowa ya huta kibar ganin ke daya muka haifa tsaf zan sallama ki, ke kin dade ba ki mutu ba." Cewar Umma da ke ta faman sababi "Ba za ki mutu ba Uwata aurenki da Bilal kamar an gama ne in sha Allah nan da kwana biyu kin zama matar Bilal" Alhaji da shigowar shi kenan shi da abokinshi ya fada. "Amma Alhaji ya zaka ce haka, bayan ganin idonka suna kokarin kashe mini 'ya ɗaya tilo da na mallaka" "Shi tunanin mace gajere ne, ni nasan hada laifin su Huda a wannan fadan da ya faru" Ya ƙarasa maganar tare da Kallon Huda da Zainura dake sosa ƙeya. "Alhaji Hadi ba sai ka ce komi ba tunda na kalli Zainura na fuskanci bata da gaskiya ni nasan halinta, za ki fadamin abinda ya faru ko sai jikinki ya yi tsami a wurin nan." Ya ƙarasa maganar tare da nufin fizgo Zainura. "A'a Alhaji ya za a dake su kuma a hana su kuka, gaskiya ba zaka dake ta ba." Ta ƙarara maganar tare da Boyeta a bayanta. Ƙutasa Mahaifin Zainura yayi tare jan hannu Mahaifin Huda suka bar ɗakin. "Ni wallahi Umma bazan koma gida ba har a gama bikin nan, don nasan dady zai iya bin dare ya zane ni. Kuma ma Umma in na tafi Huda ba zata iya rama faɗa yadda ya kamata ba ga dangin mijinta fitinannune ƙara in tsaya kusa." "Sha kuruminki zanyi magana da Ummanki ba inda za ki je muna tare"

 

___________________

"Yanzu Zainurar ce ta yima Hawwa haka"? "Wallahi Hajiya kada kiso ki ga abinda ya faru a wurin nan sam ba ɗiyar arziƙi ba ce Yaya Bilal zai aura, kinga irin zagin da dangin ta suka mana to Hajiya har ke sai da suka zaga" Jidda ta ƙarasa maganar tare da share tawayen munafurci. "Ni! Suka zaga"? Ta ƙarasa maganar a fusace. "To har Alhaji da ya ke kwance a ƙasa sai da suka ta fi tare da ɗuɗɗura mai ashar" Murja ta karasa maganar tare da taimakama Hawwa da ke kwance ta tashi zaune. Shigowar Bilil ce ta saka su yin tsit suna jiran abinda Hajiyar zata faɗa. "Dama jiranka nake, daga fita siyo maganin shi ne sai yanzu ka ga damar dawowa, hala kana wurin 'yar gwal." "Wallahi Hajiya banje ba layi na iske wurin Siyan maganin, rabona da Huda tun lokacin da kika hanani zuwa wurin Kamu na je na ce mata an yi min kiran gaggawa wurin aiki. Amma yanzu ina neman izininki in je in duba ta." "Laaah! Hajiya mutanen nan sun shanye Yaya na fada miki baya cikin hayyacinshi" "Yi min shuru Algunguma, munafuka figai-figai da ke tamkar an daurawa muciya zani amma kin iya hada tuggu" "Ungo nan Bilal, yanzu da rayuwata kake yi ma danginka haka saboda mace, yau ni Juma ina cikin tashin hankali." Ta karasa maganar tare da fashewa da kuka. "Hajiya don girman Allah ki rufa mana asiri a cikin asibiti muke ki taimaka ki yi shuru kada mutane su taru" "In rufa maka asiri ni ka tonamin nawa, wane irin fama ne banyi da kai ba akan ka auri Hawwa yar uwarka ta jini ubanta shi ya tsotsa ya saki naka Uban ya kama, amma fur ka ƙiya to bari ka ji na soke aure ka da Huda." "Abinda bazai taba yiwuwa ba kenan, ba zaku mayar dani karamin mutum ba in sha Allah nan da kwana biyu in dai ina raye kaine wanda zaka auri Huda. Ke kuma Hawwa ki tattare kayanki daga asibitin nan gida muka nufa don nasan ke ce Ummul ana isin faruwar komi tunda kin kasa ɗaukar ƙaddara akan Bilal." Yayan Mahaifin Bilal ya ƙarasa maganar a fusace. "Na yarda na amince zai aureta, amma rantsuwa nayi dole ne ya auri Hawwa. Tun bayan mutuwar mijina ban taba rokonka alfarma ba to yanzu ga alfarmata a gare ka nasan ba zaka watsamin kasa a ido ba." Shuru ya yi domin ta daure mai jijiyoyin jiki ya ma rasa mi zai ce mata. Shigowar Mahaifin Huda ita ta kauda maganar nan suka gaisa da Hajiya da ke daman cin magani tamkar wadda aka aikinsa da sakon mutuwarta ta kusa. Waje suka fita shi da Mahifin Huda, simi-simi Bilal ya bi bayansu. Bai zarce ko ina ba sai dakin da Huda ta ke, tun daga bakin ƙofa Umma ta fara aika ma shi da mugun kallon, amma hakan bai hana shi gaidata ba Da ƙyar ta amsa tare da barin wurin. "Nasan bakina ya yi kadan wurin baki hakuri, domin ni mai laifine a wurin ki. Huda kiji tausayi na ki taimaki rayuwata kada ki ce kin fasa aurena in ki ka barni tabbas rayuwata ta na cikin garari" Bilal ka zamo wani tsagi na rayuwata, rabamu tamkar datse numfashi na ne. Na ƙarasa maganar tare da jin hawaye su na bin kumcina. "Yawwa Bilal dama jiranka nake, ba fa zata yiwuba tun yanzu danginka su rika mana cin kashi ba ya kamata ka dauki mataki ko kuma gaskiya ƙawata ba zata zauna da kai ba." Cewar Zainura cike da fitina. "Kuyi hakuri in sha Allah haka ba zata sake faruwa ba zanyi ma tufkar hanci" "da dai ya fi" Zainura ta faɗa.

 

Washe gari aka sallamemu wato ranar jajibirin daren  bikin, dirowarmu gida nan dangin Umma suka hau masifa ce wa basu taɓa ganin irin wannan masifa ba anya kuwa auren nan zai kasance. Haka za ayi bikin amarya da bandeji a goshi. Nan fa Umma ta sake kunnuwa ranta ya yi mummunan ɓaci bada son ranta za ayi auren nan ba amma ya ta iya Abba ya fi ƙarfi ta. Sulalewa na yi daga wurin tare da shigewa ɗaki na fada saman gadona tare da sauke ajiyar zuciya. Toilet na fada na sakarwa kaina ruwa, motsin da naji a bayana ne ya sakani buɗe ido a matukar tsorace. Zallar mamaki da zullumi kwance a fuskanta nake kallon ƙatuwar Baƙar mage da na rasa shin ta ina ta shigo, don nasan kaf gidanmu kai harma da makwafta ba mu da mage, alamun na gani magen zata yo tsalle ta fadamin a gigice na fizgi Towel da bani da tabbacin ta yadda na daura shi na fito a guje. "Jama'a ku tare get Amarya zata fita tsirara, yau Ni Kubra muna ganin bankaɗa." Ƙanwar Mahaifiyar Huda ta faɗa tare da miƙewa ita da wasu mata suka yi kan Huda. Sai dai kafin su ƙarara sai gani sukayi ta yanke jiki ta faɗi babu alamun numfashi a tattare da ita, yan biki ne suka fara girgizata masu kuka na yi masu ihu na yi...

 

 

 

Meenat A Yandoma

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.