Free chapter · Read without an account
7
Meenat A Yandoma
DAGA AURENA
©️MEENAT A 'YANDOMA
DEDICATED TO
ASMA'U ABUBAKAR MUSA (JASMINE)
GARGAƊI
HARAMUN NE A SARRAFA MIN LITTAFI TA KO WACE HANYA, BA TARE DA IZININA BA. 'YAN YOUTUBE KU KIYAYE.
MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION (M.W.A)
Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu masu nazari da aiki da ilimi burin kungiyar a koda Yaushe shine ta faɗakar ta kuma wa'azantar ta nishaɗantar da masoyanta
____________________
PAID BOOK, FREE PAGE
ZAKU TURO 500 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN 2294023532 UBA BANK AMINA ABUBAKAR, KU TURO SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER *** WANDA BASU DA ACCOUNT SU TURO HOTON KATIN 500 TA WANNAN NUMBER ***
PAGE 07
...Ƙarar wayar ta ne ya fito da ita daga ɗaki sabuwar number ce, ɗauka ta yi tare da kanga ta a kunne. Amsawa ta yi da eh ni ce "Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Bilal ɗin ne a asibiti" kashe wayar ta yi tare da kallon su Hawwa da suka shigo tamkar an karbo su a kibiya. "Lafiya daga ina ku ke"? "Hajiya Huda zata kashe mu, da aljanu ta haɗamu aka yi ta shirgarmu da ƙyar muka kufce mata" "yanzu ita Hudar tana ina" Hajiya ta faɗa "Ta na can ta suma don ita ma hada ita aka hada, amma nasan karya ta ke ta yi haka ne don a ce ba hannunta a ciki" Jidda ta ƙarasa maganar ta na share wahayen karya. "Ku yi maza ku shirya mu je asibiti Bilal ne ya yi hatsari" "Hajiya hatsari kuma? Mun shiga uku" Hawwa ta faɗa tare da ɗora hannu a ka. "Ba mu lokaci kuyi sauri ku fito mu je" Tun bayan isar su asibiti ganin an naɗe ma Bilal kai da bandeji bai san wanda ke kan shi ba, nan fa ta hau rizgar kuka. "Ku kiramin Murja ta zo ta ga ɗan uwanta kafin ya amsa kira, wannan yarinya Allah ya tsine mata albarka sanadin ta ga shi ina shirin rasa ɗana. Ya je ya kwaso mana mai farar ƙafa ga shi nan ya na neman rasa rayuwar shi." Likita ne ya shigo dakin ya fiddo su tare da tabbatar ma Hajiya ya na samun sauki kan shi ne ya ɗan bugu.
_________________
A hankali ta fara buɗe idanun ta da suka yi mata nauyi, sauke su ta yi akan hannunta da ya gaji da ɗigar jini har ya bushe, saurin miƙewa ta yi tare da tuno abinda ya faru daki-daki. To ina su Hawwa suke? Na tambayi kaina, ganin ba mai bani amsa miƙewa na yi na nufi wurin mai gadi nan ya ke sanar da ni yadda ya ga sun fita. A guje na fada daki ina rike da hannuna da ya ke min raɗaɗi, waya ta na dauka nan na samu misscall goma da sabuwar Number. Fara kiran Number na yi bugu daya aka dauka, abinda aka fadamin shi ya yi sanadin daukewar numfashina na wucin gadi. Sakin wayata na yi tare da faɗuwa ƙasa daɓas, kai ƙarya ne ba Mijina bane ya yi hatsari. Hannuna na daure da bandeji tare da ɗaukar wayata na nufi asibitin. Tafiya mu ke ina kuka tamkar raina zai fita, muna isowa ban tsaya amsar canji ba na faɗa asibitin. Tsattsaye na iske su bakin kofar da kukana na tunkari dakin da ya ke ina tambayar ko dai ya mutu. Gani da jina ne suka ɗauke na wucin gadi sakamakon marin da Murja ta dauke Ni da shi. Ban ɓata lokaci ba na dauke ta da mari "Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun! Wannan wace irin musiba ce da bala'i Bilal ya kwaso mana, a gabana ki ɗaya hannu ki dauke min diya da mari. Kinci arzikin Bilal da ke kwance ba lafiya yau da sai kin gane matsayina a wurin Bilal" Ji na yi kukan da nake ya tsaya zuciyata ta fara bushewa game da lamarin su. "Hajiya da kin gyaleta na koya mata hankali, har ni zata daga hannu ta mara" "Ta marekin, kiyi abinda za kiyi ko ita an fada maku bata da galihu ne" cewar Anti Kubra tare da Zainura da isowarsu kenan. Da gudu na rungume Anti Kubra ina kuka "To karamar mara kunya wa ya gayyato ku a wurin nan, ko dama kunzo me don kuyi mana rashin kunya wa ya gayyato ku a wurin nan" ce War Hajiyar Bilal "Ba bu batun rashin kunya a wurin nan, ya zata daga hannu ta mareta ko tausayin ta bata ji ba ganin halin da mijinta ya ke ciki. Maganar gayya kuma gidan Huda na je mai gadi ke sanar da ni halin da ake ciki, ko da ya ke ko banyi dogon bayani ba tunda aka auri irin danginmu yanzu aka fara ganinmu." "Ke ki kula kada ki ce za ki gaya ma Hajiya magana don in sumar da ke a wurin nan karamin aikina ne" Murja ta karasa maganar tare da ƙutawa. "A hayye nanaye! Yanzu ke Murja ko a mafarki aka ce za ki iya sumar da ni ai sai ki yarda? ko da ya ke ai zaren ba kalar yadin ba ne ki kwatanta tazarar da ke tsakanina da ke ta kai tarazar da ke tsakanin sama da ƙasa." "Ya isheku na ce" Likita da hayaniyarsu ce ta fiddo shi ya fada. "Ya na cikin wannan halin ba ku yi mai addu'a ba amma Ku zo kuna kokarin dambatawa" "Doctor su zaka yi ma gana domin su ne suka fa ra janmu" Zainura ta ƙarasa maganar tare da daka tsoki. "Ba neman ba a si nake ba kuyi hakuri, in kuma ba ku iya shuru ku fita daga waje don Allah." Tsit! Wurin ya yi kowa da abinda ya ke sakawa, motsin Bilal da muka ji ne ya saka mu shiga dakin da gudu. Hawwa kuwa rugawa ta yi ta kira likita, sannu muke jero ma shi ya na amsawa tare da dafe kanshi. "Hajiya ku kiramin Huda" Bilal ya fada tare da kallon sama. "Yau ni na shiga uku! An a siremin ɗa, daga tashinka matarka ka ke tambaya ba ni mahaifiyarka ko danginka ba" Da sauri na matsa kusa da shi ina ma shi sannu. Nan fa hannunsa ya sauka akan hannuna da ke dauri "mi ya sake ki" "yanke wa na yi" na ba shi amsa a takaice. Mun jima a dakin Hajiya ta kora kowa ta ce ita daya zata kwana wurinshi. Ba don raina ya so ba na bi su muka nufi gida, Anti Kubra kin shiga ta yi ni da Zainura muka shiga. Nan fa Abba ya ce bazan kwana gida ba maza in tafi gidan mijina, ba yadda Hajiya ta iya hakuri ta bani ta ce gobe zamu hade a sibitin. Sai da Zainura ta kai Ni har daki muka yi bankwana ta tafi, gabana faduwa ya fara da na tuna abinda ya faru ɗazu. Anya zan iya kwana ni daya tunawa da nayi da maganar Abba dole na hakura tare da tashi na yi alwalla, bayan na gama sallah abincin da aka zubama Bilal na dauko ina fara ci na ji na koshi. Bin abincin da kallo na yi sakamakon wasu bakaken abubuwa masu kama da kura in ta faɗa ga abu amma sunfi kura girma. Jikina bai bani wani abu ba na dawo daki na kwanta zuciyata fal da tunane-tunane barcin da ya fara fizgata kashe wuta na yi na koma na kwanta. Cikin barci na riƙa yijo kukan jarirai a firgice na mike tare da bude kofa, falo na nufa cikin sanɗa ina lalube na kunna haske. Mutuwar tsaye na yi ganin jarirai birjik sai tsala kuka suke, juyawa nayi sai dai jin kafata na yi kamar an hada ta da magana ɗiso ta manne da kasa ko da kuma ta rufe kanta. Fankoki ƙara gudu suka yi har labulen ya rika ta shi sama, ɗif wutar dakin ta dauke ji nayi ilahirin jikina ya daddaure kamar an sakamin sarki. Bakina kuwa ya datse ta yadda bani iya furta ko kalma daya. Wani abu na ji saman wuyana wanda ya ke tabbatar min da jariran ne suka fara hawana, dariya falon ya dauka tamkar zai kice "ki goya muu" hargitsattsiyar murya ta faɗa. Daga nan ban sake sanin mike faruwa ba sai bude ido na yi na ganin tsakar falo har safiya ta yi. Fashewa na yi da kuka ina mai hada kaina da gwuiwa, wannan wace irin baƙar ƙaddara ce ke bibiyata na rasa wa zan fadama damuwa ta ko da na yi niyyar fada sai in ji na kasa. Ganin kuka bazai fissheni ba Toilet na fada nayi wanka nayi sallar asuba, kitchen na shiga na hadama Bilal kalaci a gaggauce na shirya na fito. Napep na tsaida muka fara tafiya zuciyata maƙil da tunani, burkin da na yi ya taka shi ya dawo da ni cikin hayyacina "Hajiya mai na ya kare, sai dai ki shiga wata a karasa da ke" kudin shi na ba shi na yi tsaye bakin titi. Karaf ido na ya sauka akan fuskar da na jima ban gani ba fuskar da ita ce mafarin matsalolina, da gudu-gudu na bar wurin ina addu'ar kada Allah ya ƙara haɗani da fuskar nan. Cikin ikon Allah na samu wani abin hawa amma akwai mace sanye da daƙaƙen kaya tare da niƙaf, ban damu ba na fada ina mai jaddada masa in da zai sauke ni. Karaf na ji matar na ta riƙe min hannu dagowar da zanyi na yi tozali da abinda ya sakani daskarewa....