Free chapter 路 Read without an account
Page 48
by Gimbiya Ayshu 路 馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰(GIDAN AURENA) BOOK 1.
馃尰馃尰 MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU馃挒馃挒馃挒
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION馃摎
BOOK 1:CHAPTER 95&96
___________________________Bayan sati daya kayan da Sani yayi order suka iso,kaya ne mai uban yawa,haka aka jera su a shagon gwanin ban sha'awa,masha Allah shago ya hadu domin ko ina Kaya ne,sai wuraran la'asar aka gama jera kayan ya kulle shagon ya nufi masallaci,daga masallacin bai zarce ko ina ba sai gida.
Zama yayi a kan kujera yana sauke ajiyar zuciya.
Hauwa da fitowar ta daga daki Kenan tace"ahhh! har ka dawo?".
Wlh kuwa,nazo tafiya dake ne dan kiga aikin ki.
Dariya Hauwa tayi tace"Kai kohhh!ba'a raba ka da kayan magana,bari na watsa ruwa sai na fito muje".
Bayan tayi wanka tayiwa Ameen ta shirya shi suka fito.
Amsar Ameen yayi daga hannun ta ya ajiye shi kan kafafun shi,da yake yana tafiya.
Wani farin hanki ya ciro daga aljihun shi ya daura mata a ido.
Murmushi Hauwa tayi ba tare da ta furta komi ba.
Kwance mata hankin yayi bayan sun shigo shagon.
Baki bude Hauwa ke kallan shagon, sossai shagon ya tafi da ita,komai na shagon ya tsaru yanda ya kamata.
Fuskar shi dauke da murmushi yace"your highness rate your hand work".
Dariya Hauwa tayi ta bigi kafadar shi sannan ta kwantar da kanta a kan kafadar shi,Allah ne kawai ya san irin farin cikin da ta ke ciki,tana san mijin ta sossai,sam ba tasan abinda zai raba su.
Har gida Ammi ta zo tayiwa Hauwa godiya idan ta na tsiyayar da ruwan hawaye.
Rungume ta tayi tana share mata hawayen tace"babu komai Ammi i an zama daya".
Da za ta tafi Hauwa ta bata abubuwa dayawa,kin amsa Ammi tayi,sai da Hauwa ta nuna bacin rai kafin Ammi ta amsa ta rage wasu abubuwa tace"wannan ma ya isa yar nan,nagode sossai,ko iya abinda kika yiwa dana ma ya ishe ni duniya da lahira,hakika bazan daina gode miki da yi miki addu'a ba,tabbas kin cika mutun kuma mata ta gari".
Har bakin titi Hauwa ta raka Ammi,bayan an sami abin hawa ta gaya mishi inda zai kaita sannan tace"nawa drop".
Bayan ya gaya mata kudin ta biya shi sannan ta ajiyewa Ammi kudi akan cinya bayan keken ya fara tafiya.
A hanyar su ta tafiya Ammi tace"baza ka dauki passenger bane dan nan?".
Dariya yayi yace"Baba i kudin drop ta biya".
Da mamaki take kallan shi tace"Meh hakan ke nufi dan nan".
Dariya yaran yayi yace"duka keken ta siye Baba,ke kadai zan dauka,sai na sauke ki kafin zan iya daukan wasu".
Tagumi Ammi tayi,ta rasa ma mai za ta ce.
Da yamma Hauwa ta kira Ammi dan taji yanda ta isa gida.
Ruwan Addu'a kawai Ammi ke suburbudowa,bayan ta gama Addu'ar tace"hakika ke haske ce a cikin rayuwar dana,kin mai abubuwan da ko dan uwan shi na jini ba lallai yayi mai ba,har na gushe bazan taba manta alkairin ki a"..................
Dan Allah Ammi kiyi shiru ya isa haka,ki daina gode min dan Allah, hakika ke mahaifiya ce a gare ni kin wuce godiya a guna,komai nayi chanchanta ce.
Bayan sati daya aka saka Ameen a makaranta mai kyau da tsada dai-dai karfin su,tare suke fita da Abban shi,idan ya ajiye shi makaranta sai ya nufi shago,da zaran lokacin tashi ya kawo kai zai je ya dauko shi ya maida shi gida sannan yaci abinci kafin ya koma.
Alhamdulillah Jalal ya samu sauki ta dalilin Addu'a,Azumi da sallan dare.
******BAYAN WATA BIYAR*******
Zaune Sani yake a shago da waya Kare a kunnan shi,kai da ganin yanda yake zaro kalamai ba sai an gaya maka dawa yake waya ba.
Ganin wata ta shigo shagon ne yasa shi fadin"zan kira ki".
Hade rai yayi sossai Kaman ba shi ba,murya a hassale yace"mai na gaya miki game da zuwa inda nake,keh ni bari kiji,babu abin da zan yi dake,ke ko ba ke ba ni ban da ra'ayin san wata bayan matata,ina fatan kinji ni,matata itace ni,itace farin ciki na,itace walwala ta,itace komai nawa,my wife is my life,my wife is my breath,my wife is my joy and happiness,ina fatan kin gane,wlh idan na kara ganin ki a shagon nan police zan kira nace kin min sata,ina fatan kin gamsu",ya karasa maganar a tsawacen da sai daya firgita yar budurwar dake tsaye a gaban shi.
Ranta a bace tace"zaka gani wlh,dani kake zance,karya ne nace ina san abu ban same shi ba,ko ta halin kaka ne sai na same shi,na bika ta lalama kaki,wata dai-dai har uku nayi ina binka da zance guda daya amman kaki,miye aibu na,miye laifi naaaaaa"....................
Tabe baki Sani yayi ya toshe kunnan shi da earpiece ya kishingida idan shi a lumshe.
Sai data karaci haukar ta kafin ta fice mai daga shago.
Jin shiru yayi yawa yasa shi bude ido daya,zare earpiece din dake kunnan shi yayi ya gyara zama yace"wata kuchakar banza dake,mai zan yi dake Allah na tuba,ina da matata yar Indian da ita".
Duk rigimar nan da ake Hauwa bata sani ba,ya san idan ya gaya mata za ta tashi hankalin ta.
Bayan sati biyu da faruwar haka waccan yarinyar mai suna Lubna ta dawo,a wannan karon da hannu biyu Sani ya tarbe ta................................
Ana dara ga dare yayi,toh masu karatu mu hadu daku a next page.
By Gimbiya Ayshu馃挒馃挒馃挒.