Free chapter 路 Read without an account

Page 59

by Gimbiya Ayshu 路 馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰(GIDAN AURENA) BOOK 1.

馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰

               (GIDAN AURENA)

STORY AND WRITTEN BY

GIMBIYA AYSHU 馃挒馃挒馃挒

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION馃摎

BOOK 2 IS LOADING...............

BONUS 300

LATE PAYMENT 500

COMPLETE 1000.

BOOK 1:CHAPTER 117-118

____________________________Ba Hauwa ta farka ba sai gabda la'asar,kokarin mikewa take aka turo kofar,mayar da kallan ta ga bakin kofar ta yi dan ganin mai shigowa,ajiyar zuciya ta mai karfi ta sauke duk a tunanin ta Lubna ce,har ta fara tunanin yanda za ta ci duka a hannun ta yau,dan ko dan yatsar ta baza ta iya dagawa ba balle ta kwaci kanta.

Karasowa Maman Fauzan tayi da sauri tace"mai yasa kike kokarin ji ma kanki,kin san jikin ki ba kwari kuma kina kokarin tashi,so kike jiri ya kwashe ki mu shiga uku".murmushin karfin hali ta yi tana lumshe idan ta,taimaka mata ta yi ta jingina sannan ta shige bayi ta hada mata ruwan wanka mai zafi sossai ta kai mata kujera,bayan ta kammala ta taimaka mata har cikin bayin,kayan da zata sa ta naiman mata a gurguje sannan ta fara gyara dakin,tana shara Hauwa ta fito,ajiye tsintsiyar hannun ta tayi ta nufe ta,daga mata hannu Hauwa tayi tace"na ji karfi Anty ba sai kin kama ni ba,nagode sossai da kulawar ki a gare ni".

Dan dakatawa tayi da tafiyar da take tace"kin tabbata?".

Girgiza kai Hauwa ta yi tana tafiya tace"gashi kinga ina tafiya ni kadai ba tare dana dafa bango ba,kuma ko jirin da nake fama da shi ya ragu sossai".

Kin tafiya Maman Fauzan tayi har sai da ta tabbatar Hauwa ta zauna a gaban dressing mirror.

Bayan ta kammala ta taimaka mata tasa kaya sannan ta bata abinci,da farko kin amsa ta yi,sai da taga ran ta ya baci sannan ta yarda ta bata abincin,bayan ta gama ta bata magani ta sha sannan ta kara mata pillow a bayan ta yanda zata ji dadi sossai,dauke kwanonin tayi ta ajiye sauran abincin tace"bari naje,zan fita,idan na dawo zanzo,na sa driver ya dauko Ameen idan sun tashi daga makaranta".

Godiya sossai Hauwa tayi mata harda zubar da Hawaye.

Share mata hawayen tayi tace"shiiiii!,kukan kuma na meh?,ki share su dan Allah bana san ganin su".

Share su Hauwa tayi suka yi sallama ta tafi.

Washe gari Hauwa ta ji karfin jikin ta dan har aikin gida ta yi.

Bayan kwana biyu.

Zaune Hauwa take a parlor ta kishingida da jikin kujera hannun ta rike da remote,idan ka mata kallo daya za ka zata kallo take,amman idan ka kure kallon zaka tabbatar da gabadaya hankalin ta baya ga kallon ta lula chan duniyar tunanin halin da take ciki,tana  cikin wannan tunanin Ummi ta shigo har fallo ta dungure mata goshi,a kufule ta juyo bangaren da take da zumar masifa sai kuma tayi tsit fuskar ta kunshe da mamakin,washe baki tayi tace"Anty Ummi oyoyo",ta fada tare da mikewa tasaye ta rungume ta tana murna.

Cire ta Ummi ta yi daga jikin ta tace"ni dai kyale ni fushi nake da ke,sai kinga mutun ki dinga wani murnar munafurci amman ba ki iya zuwa duba ta,gashi wuri ba wani nisa ba,Mama kullun da tunanin ki take kwana take tashi kuma take wuni,kira ma ba ki yi,ko da yake da sauki kina kiran Mama amman ni yaushe rabon da ki kira ni?".

Shiru Hauwa tayi idan ta na zubar da hawaye tace"ba haka bane Anty Ummi".

A fusace Ummi tace"toh ya abin yake tunda kin ce ba haka bane"

Share hawayen dake gangaro mata ta yi tace"banda lafiya ne Anty shiyasa,kuma wani lokacin idan na kira bana samu,dan Allah ki yi hakuri ki yafe min,bana san kina fushi da niiiii!",ta karasa maganar ta tana kuka.

Rungume ta Ummi tayi tana bubbuga bayan ta tace"ya isa ban san ganin kukan ki,maza share shi,ko so kike kishiyar ki ta gani ta ce ke ragguwa ce",ta fada fuskar ta dauke sa murmushi tana jan kumatun ta.

Murmushi Hauwa tayi idanuwan ta na kan zubar da hawayen tausayin kanta,tana san gaya musu halin da take ciki amman tana tsoro,ta san idan ta fada sai Ummi ta san yanda ta yi ta raba auren,dama chan ba wani son auren take ba.

"Wai baza ki bar kukan bane?,ko so kike nima na yi kuka".

Saurin share hawayen idan ta tayi tace"na bari wlh,kar ki yi kuka kinji".

Dariya duk su ka yi gaba daya.

Ina baby na yake?,naga banji duriyar shi ba tunda na shigo.

Ya je islamiya,sun kusa tashi ma i,ta fada tana kokarin duba agogon dake manne a bangon parlor tace"ashe da sauran lokaci,yanzu ma biyar ta yi.

I ko bazan iya jira ba dan daga nan akwai inda na nufa ban san dare ya min,kin san yau na dawo makaranta,ban gama siyayya ba.

kya tafi biki sha ko ruwa ba.

Kyabe baki Ummi tayi tace"sai ki gayawa bako ba dai ni ba".

Ke dai bari na tafi kar dare ya min,zan kuma dawowa insha Allahu kar ki damu,ita kuma kishiyar taki fah?.

Bata nan ta fita,ni kadai ce a gidan.

Toh shikenan Allah ya baku zaman lafiya mai dorewa.

Da Ameen Ameeen Hauwa ta amsa jikin ta a sanyaye.

Har bakin titi ta raka ta kafin ta juyo ta dawo gida,a bakin kofa ta sami lubna ta cika ta yi fam sai hura haci take.

Ko takan ta Hauwa bata bi ba shige daki.......................

Ku yi hakuri da wannan pls

Comment

Vote

Share

By Gimbiya Ayshu馃挒馃挒馃挒.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.