Free chapter · Read without an account

5

by Surayya Ibrahim · DINGISHIN KWADO

5

*Gunis hijab ba na biyunta wajen kawo hijaban da suke da kyau da nagartar.*

*Gunis hijab ado cikin wayewar addini da rayuwa*

*****

Gidanmu na cikin unguwar low-cost wacce shiyace ta tsofaffin y'an boko, kuma masu kumbar susa..

Katafaren gida ne da ya amsa sunan mahdi ka ture sabida k'arfin ginin. Hakanan gida ne iya ganinka domin kafin ka kai k'arshen katangar da ta kewaye gidan ma aiki ne babba.

Gidan na dauke da sassa daban daban har guda biyar.

Sai dai tsakanin ko wanne sashe tafiya ce mikakkiya. Ma'ana akwai tazara mai yawa ta yadda ba za'a iya yin komai tare ba. Shashen farko na Alhaji Musa ne wanda kowa a zuriarmu ke kiransa da Baba babba. Sai shashen tsakiya na mahaifiyarsu ne kafin ta rasu. Daga baya sai ya koma wajen ajiye amfanin gona domin iyayenmu manoma ne na fad'a a jarida.

Sai sashen Alha Isa wanda muke kiransa da Baba k'arami. Shine kuma mahaifina.

Akwai sashin ma'aikatan gidan da kuma sashe guda na baki da samarin gidan.

Su biyu kacal mahaifiyarsu ta haifa. Mahaifinsu Malam Muhammadu babban mutum ne a Funtua asali yana da alak'a da gidan sarautar garin, suna da zuria mai yawa. Y'aaya'nsa shida ne, sai dai kakarmu ce kawai ta haifi maza, sauran Duk Mata ne wanda amuwargidansa ta haifa masa, sai dai shi ya rasu tun suna k'ananu ainun, don haka ba wani zumunci suke yi sosai ba a dalilin kishi ya rufe idonsu, sannan mijin ya rasu kowa saita ja gefe da ya'yanta.

Mahaifiyarsu kakarmu kenan. Malama Batulu amma da Ladi aka fi saninta ta sadaukar da kuruciyarta wajen ganin ta INGANTA rayuwar yaranta biyu.

Dan haka bata yi aure ba sai da suka girma suka zama samari duk da akwai tazarar shekaru biyar tsakanin Baba babba da Baba k'arami. A lokacin da suka girma kuma ta yi aure ta wuce shekarun haihuwa.

Sun taso cikin wata irin soyayya da ririta junanmu don kuwa mahaifiyarsu ta yi matukar cusa soyayya da tausayi a tsakaninsu. Bayan haka kuma sun samu Ilimin addini da na boko.

Baba Babba tsohon ma'aikacin gwamnati ne, haka tsohon d'an majalisar dokokin jihar Katsina ne tun a jamhuriya ta biyu. Sannan mashahurin manomi ne dan kuwa sai an sako shi a cikin sahun manoma a k'asa gabad'aya ba wai jihar Katsina kawai ba.

Baba Babba gabjejen attajiri ne da Ubangiji kad'ai yasan yawan arzikin da ya bashi. Dan na yi imani shi da kansa bai san adadin dukiyarsa ba. Ni bansan hekta nawa yake nomawa a shekara ba balle na hakaito.

Idan na ce manomi ina nufin kololuwar manomi ne da yake noman da gaske. Dan kuwa makudan milyoyin kudi yake narkawa a gonaki. Idan kaka'a ta yi kuwa shima ba k'aramin dukiya yake cika dakuna da manyan shaguna ba.

Baba k'arami kuwa likitan dabbobi ne. Shima da nasa arzikin tunda yana kasuwancin siyar da lafiyayyun dabbobi, tunda ga kan awakai, tumakai, dokuna, shanaye da rakuma.

Shiyasa gidan gonar Baba Babba cike take da lafiyayyun dokuna, rakuma da kuma raguna harma da shanaye da tsuntsaye daban daban. Danginsu dawisu da tatalo, jimina, geese, agwagi, da sauransu. Gidan gonar duk fad'in Funtua da kewaye babu ta biyunta. Domin cike take ainun da dukiyar dabbobi, hatta kaji ana zuba sama da dubu ashirin na k'wai da na ci, kajin Hausa ma birjik ne iya ganinka. Tattabarun da suke ciki kuwa baza su kayyadu ba. Gidan gonar Ladi farms ta yi bunkasar da har Madara ake sarrafawa a cikinta domin shanayen waje masu bada Madara zallah ma yawansu ya kai kurewa. Kifaye kuwa ba'a magana. Baba k'arami ke kula da ita a dalilin shi din kwararren likitan dabbobi ne. Samun kulawa da kiwo na mussaman da suke samu ya sanya dabbobin suke ta bunkasa suna haihuwa akai akai. Idan ana lissafin manyan gidajen gona a Nigeria ba wai a Funtua ko arewacin Nigeria ba sai an sako gonar Ladi farms ta Baba babba.

Gidanmu da muke ciki na Funtua tare suka yi ta siyan filayen suka kuma gina abunsu. Kowa zuba kudi yake yi, dan haka mallakinsu ne su biyu.

Bayan haka suna da kadarori daban daban da suka yi tarayya a kai. Misali gadonsu basu raba ba. Sannan akwai wasu kadarori da suke siya tare.

Amma a zahirin gaskiya Baba babba ya fi mahaifinmu dukiya nesa ba kusa ba. Duk da namu mahaifin ma attajiri ne na gaske.

Ina wannan bayanin ne dan ku fahimci labarin da kyau. Iyayenmu biyu hamshakan alhazai ne, sai dai dole wani ya fi wani.

Dukkan iyayenmu maza matayensu guda daya ne.

Haka kuma Ubangiji ya azurtasu da haihuwa sosai.

Ya'yan Baba babba guda shida ne. Wacce matarsa Hajiya Saratu ta haifa masa, muna kiranta da Momi.

Ukun farko maza ne Yaya Abubakar, amma Asad ake kiransa, Yaya Umar Faruku, Yaya Usman. Sai Yaya Salaha wacce tazara ce sosai kafin a haifi Yaya Munira. Sai Abida da take auta, kuma ita kad'ai na girma duk da dai ba wani fiko ne mai yawa ba, tare aka yi goyonmu.

Sunan mahaifiyata Haj Habiba, muna kiranta da Mami. Mu bakwai ta haifemu. Yaya Sulaiman, Yaya Hamida, sai ni Bilkisu, Ansari, Anisa, sai autarmu Saddiqa.

Idan aka had'amu da y'aya'n Baba babba mun zama sha uku ke nan.

Amma kuma Ya Munira tafi shakuwa da baba karami, matuk'ar yana gari to Duk inda zaka ganshi tare da Munira a gaban matarsa ta shiga ransa ainun fiye da mu ya'yan cikinsa.

Gabad'aya mun taso ne bisa jagorancin Baba babba. Domin baba k'arami idan ya tafi Katsina ranar litinin sai alhamis da yamma yake dawowa. Idan ya dawo din ma mafi yawa yafi zama a Ladi farms sai dare ake samunsa.

Gabad'aya mun fi shakuwa da Baba babba, akan mahaifinmu tunda yafi shi haba haba da yara, sannan shi muke ga ni kullum yaumin.

Iyayenmu mata suna zaune lafiya duk da babu abin da suka had'a. Misali ko wacce bangarenta daban sannan akwai tazara mai yawa.

Sai dai dukkan ahalin gidan k'wai da kwarkwata da hadiman gidan ana cin abinci ne daga tukunya guda. Domin akwia sashe guda da na y'an aiki maza masu kula da gyara harabr gidan da shuke shuken gidan, da mata masu girki da gyara cikin gidajen.

Kawai umarni ake basu.

Mu kuwa yaran gidan kowa na da yancin ya zauna a sashin da yake so ko dai na Baba babba ko sashen Baba k'arami.

Idan an fahimce ni bamu taso mun ga banbanci ko wani rikici a tsakanin iyayenmu maza ko mata ba. Shiyasa soyayya ce mai yawa a tsakaninmu gabadaya.

Bamu zama yan mata ba aka yi auren Yaya Salaha da Yaya Zainab da Kuma Yaya Hamida fiko mai yawa suka yi mana, amma da yake sai da suka yi digiri a fannoni daban daban mun data kafin a aurar da su. Amma dai ko sakandire bamu shiga ba, kawai muna ita tuna sadda aka yi auren ne.

Mun taso mu uku Yaya munira da ni da kuma Abida.

Ni da Yaya Munira mun taso cikin wata irin soyayya da shakuwa. Da wahalar gaske mu yi fad'a sabanin da babu jituwa ko kad'an tsakanin ta da Abida.

Koda yake ita Abida da ta kasance k'aramarmu tana da wani irin hali murdadde, bata kaunar ka tab'a mata abinta ko kad'an, hakanan ta yi matukar kyamar ka kwanta mata a gadonta. Duk da dama gado uku ne a cikin dakunanmu na kowanne sashe.

Bayan haka kuma tana cikin mata masu high taste bata amfani da kowanne irin garabitin abu, sai zababbe. Y'ar kwalliya ce ta sosai tun tana k'arama. A zahiri mun fita kyau, amma da yake tafi mu gayu sai ta fimu daukar ido. Kusan kullum sai ta sani kuka domin ni tun tasowa ta haka nake sanyi kalau mai matukar raunin zuciya. Yaya Munira ke k'watata a hannunta sanadin da ya ta'azzara rashin shirinsu kenan. Amma kuma bata yarda a ci zalina a makaranta. Nan da nan Abida zata yi makarbiya ta mayar da fad'an kanta ko da kuwa bata yi mini magana.

Kazalika basa shiri da Yaya Sulaiman kwata kwata basa jituwa, a cewarta shi din mai nuna son kai ne da takama, a gabanta yake nunawa nice kanwarsa alhalin Yana ganin yadda Yaya Farouk yake mini alkunya fiye da ita. Shi Kuma ya ce ra'ayin lta da iyayyinta ne Basu masa ba, yarinya ta yi ta juya mutane, matukar yana gidan to kuwa sai an musu Shari'a don sai ya yi Mata abin da zata harxuka sai da Baba karami ya yi masa wuta wuta sannan ya daina fitinarta, don kuwa gaban Baba karami ta kai maganar tana rusa ihun ya mata iyaka da shi ko ta kira masa yan civil defence. Ba karamin dariya Baban ya yi ba, karshe ya wanke Sulaiman ya ce "ka fitinar mini Abida fa Sulaiman. Maimakon ka jata jikin ka, har ku kulla alheri sai ka dinga yi mata sheganta to ina ruwanka da bak'inta? Ina ce dakin Allah ma bak'ine ashe kuwa bak'i ba muni ba ne ba kuma tawaya ba ce!

Ya ce "Na daina Baba amma lallai ka ja kunne ta akan gatsinen da take mini tare da harara ko da ban mata magana ba, sannan duk ranar da ta sake kwashe mini takalma idan na ajiye a bakin kofa, komai na yi mata ita ta ja".

Baba ya gintse dariyarsa ya ce "Kin ji ko Abida ki daina, shima ba zai kara bata mini ba".

Ta ce "Shikenan yanzu dai ka sake jaddada masa ka yi mana iyaka babu ni, babu shi har gaban abada".

Baba ya kwashe da dariya ya ce "A a ba haka za'a yi ba, ba Shi ba tsokanar Ki bare ya saka Ki kuka, kema ba ke ba masa rashin kunya, wannan Kam na sha muku layi, Duk wanda ya tsokani wani kuwa to la shakka da ni take fadan!

Daga haka ya sallame su. Shikenan aka samu saukin rikicinsu, Ni mamakin Yaya Sulaiman nake yi Idan ya sako Abida a gaba da wulakanci don magana ma da kyar yake yin ta baya son hayaniya ko kadan, yayin da Abida take yar kwarfniya ta gaske watakila wannan banbancin ya sake habaka yar tsamarsu.

Muna kammala firamare aka kaimu Makarantar gwamnatin tarayya ta Bakori(F G.C Bakori).

A lokacin Yaya Munira na aji uku(J.S.3) na k'aramar sakandire a Makarantar.

Tare ake yi mana komai. Kayanmu a hade suke, amma Abida bata yarda muci abinci tare.

Sai dai kwanonta daban.

A shekarar kuma babban wanmu Yaya Asad ya yi aure, ya wuce da amaryarsa Asaba da yake d'an sanda ne mai mukamin ASP a lokacin.

Sannu a hankali rayuwa take shudewar har muka sami shiga aji uku. Yaya munira tana aji biyar. Ta fara zama budurwa sosai.

Tsayinmu d'aya da ita saboda ni din doguwa ce sosai. Amma siririya sai da ina da kugu sosai. Haka nan farare ne mu tamkar tsada sabanin Abida da take bak'a. Gayunta da farar fatarmu basu rudeta ta yi sha'awar sauya launin fatarta ba. Ko mai zata siya sai ta duba ingredient matukar ta ga sinadarin hydroquinone to kuwa zata ajiye shi.

Tsayina da sanyin halina ya sanya dalibai suka lankaya mini Bilki sola.

Matukar ka ce Bilki sola a lokacin da muke FGC Bakori kowa ya san ni.

Ba ni da k'awaye, daga ta botsara Abida sai kuwa Basma Bello Maska.

Kawai Ubangiji ne ya k'ulla abotarmu, don tafi dacewa da Abida, masifaffiya ce ta gaske itama. Kawarmu ce gabad'aya tunda ajinmu d'aya haka dakin kwananmu guda. Amma kawancen yafi k'arfi da ni.

Da wahala mu yi fad'a sabanin ita da Abida kullum sai sun yi, wani zubin sai su yi sati basu yi magana ba domin dukkansu masu ra'ayin rukau ne, masu ji da kansu ne.

Sannu a hankali Yaya Munira ta kammala ta barmu, ta yi sa'a a shekarar ta samu gurbin karatu a jami'ar Ahamadu Bello ta Zaria.

Kafin mu gama FGC mun zama cikakkun yan mata. Da Basma da Abida matsakaicin tsayi ne da su. Sabanin ni da nake doguwa sosai. Na keresu, a wanccan lokacin har kunyar tsayina nake ji, domin bana jin za'a samu wacce ta fini tsayi a makarantar sai dai mu yi taya. Daga sama ba ni da kiba ko kad'an, amma ina da fad'i ta kasana. Gabad'aya kirar jikina ya fi dacewa da kwalbar coca cola.

Doguwar fuska gareni mai dauke da siririn dogon hanci tamkar biro. Haka nan bakina d'an tsut mai dauke da jajayen lebuna, da k'ananun hak'ora jerarru farare kal tamkar kankara.

Gashin kaina baki mai sulbi har gaban goshina.

Sannan a cike take ga kuma tsayi. Kallo d'aya tak zaka fahimci ni din kyakkwar mace ce lamba d'aya sabanin Basma da Abida da suke da boyayyen kyau, irin sai an kallesu da kyau kafin a fahimci kyaunsu. Har ila yau ni yar kwalliya ce, ina son gayu ina son kamshi, ko nawa zan samu zan iya karar da shi a turare.

Mun dawo hutun zango na biyu muka yi sa'a Baba babba ya sahale mana muka tafi katsina hutu gidan Yaya Salaha wacce ma'aikaciya ce a ma'aikatar ruwa ta jihar Katsina.

Bana manta ranar da muka fara haduwa.

Yammacin wata juma'a bayan Yaya Salaha ta dawo daga aiki, ta aike mu, mu karbo mata sak'o a gidan iyayen mijinta a k'ofar bai.

Direban mijinta ya kaimu. A k'ofar muka tarar da samari guda biyu. Tun daga nesa muke hangensu da yake fuskar gidan muke nufa. Su kuma a zaune suke kan tebirin da yake girke a k'ofar gidan.

Mun fito zamu shiga gidan, idona ya fad'a cikin na dogon saurayi fari tas. Sumarsa ta tabbatar mini yana da alak'a da mutanan Habasha ko Bafulatanin Usul.

Faduwar da gabana ya yi, a kallon farko ya sanya ni cikin rud'u.

K'afafuwana suka hau sark'ewa, da k'yar na daure na bi Abida a baya muka wuce. Zuciyata na cigaba da dokawa da tsananin gaske.

Bamu wani jima ba muka fito.

Muka sake tarar da su , mun gota su kad'an, kafin mu shiga mota, suka taso da azama. Wanda yafi tsayin ne ma'ana wanda na kadu da kallonsa ya yi jarumtar ce wa "Sannunku y'an mata".

Zuciyata ta sake tsinkewa domin sai na ji tamkar wanda hausar tasa ma ta dabance.

Ya zuba mini ido, yana son mini kallon tsanaki, gangar jikina ta taya zuciyata rawa.

Na kasa amsa masa sannun da ya yi mana.

Abida cikin ko d'ar ta ce "Sannunku dai Rijalu!

Dariya ta k'wacewa d'ayan mai duhun fata da kuma matsakaicin tsayi.

Cikin dariya ya ce "Bari na matso kusa da ke da alamu ke na dad'e ina jira".

Ta rausayar da kai ta ce "A a kada ka matso, domin kuwa shekaruna sha shida, karatu zan yi, kuma na likitanci ka ga ina buk'atar nutsuwa mai yawa akan karatuna".

Ya sake fadada murmushi ya ce "Nima dalibin ilimi ne, hutu na zo, ina karatun Islamic law a k'asar Sudan. Sunana Lawal ".

Ta ya mutsa fuska ta ce "Idan daga Allah ne zai sake had'amu kamar yadda muka had'u yanzu babu tsammani."

*MalaysianFabrics*

*Materials masu aji, masu class, na manasana sirrin gayu irinsu jacquard, luxe, viscose, dobby, embroidered jacquard da dai sauransu.*

*Materials masu quality masu dadin sakawa a jiki basu da zafi ba su da nauyi.*

*7020695644.*

✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.