Free chapter · Read without an account

1

by Kansa'u Bello · MATAR MANYA

💓 MATAR MANYA 💓

By

OUM FATIMA

GAJEREN LABARI

PAGE 1

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

Ko wane bawa da kagani a rayuwa da iya arziƙinsa a duniya, duk abinda kaga ka samu a rayuwa yana daga cikin ƙaddarka kuma rabonka ne. Duk abinda kuma kaga baka samu ba to ba rabonka bane, duk kuma irin cida zucin da zaka nuna akan ganin ka cimma wani buri naka ba zaka je ko ina ba matuƙar ba rabonka bane kuma baya cikin kundin ƙaddararka. Irin hakan ne ya faru a cikin rayuwata nima.

Sunana *Salamatu* Shehu amma ana kirana da Salma kasancewar bana son ana kirana da salamatu don a ganina sunan tsofaffi ne. Mahaifina Malam Shehu talaka ne mai neman abinda zai rufawa kansa asiri, tsohon Malamin Makarantar primary ne da yayi retired don haka É—an abinda ake biyansa na fensho ba abinda yake tare masa. Ga tarin Æ´a'Æ´a da Allah ya bashi.

Matansa biyu na aure da yara goma sha biyar, uwar gidansa da muke kira da Baba Mari ita ke da yara goma sai Mahaifiyarmu Hadiza da muke kira Mama ita keda biyar huɗun duka Maza ne ni kaɗai ce Mace kuma nice Babba. Na kasance kyakykyawar gaske mai dirin halittar jiki, babu ta inda Allah ya rageni a fannin kyau da dirin jiki. Hakan ne yasa nake da matuƙar jin kai da jin nafi kowa a gidanmu dama unguwarmu.

Zuzuta kyawuna da ake yake ƙara min girman kai nake jin na isa na kai in taka kowa, gaba ɗaya mu goma sha biyar ɗin da Mahaifinmu ya haifa kowa rayuwar da yaga dama yake yi sabo da Babanmu bashi da isasshen abinda zai riƙe mu. Ɗan abinda ya samu ya lalubo ya kawo bai wuce ayi tuwon dare ba wanda ake karkasa shi a hannu a hannu, maganar abin kari kuwa ko abincin rana sai dai kowa ta cida ƴa'ƴanta.

Baba Mari dake da ƴammata biyar duk ba wacce bata yiwa sana'ar abincin sayarwa da shi suke rufawa kansu asiri. Mahaifiyata kuwa da ni kaɗai ce Mace a wurinta ƙannena duka Maza ne ni kuma na dire nace nafi ƙarfin talla ba zan yi ba, bata matsa min ba saboda itama bata son ɗorawa ƴa Mace tallah don haka take ƙulle-ƙullen kayan miya a cikin gida.

Rayuwar da ake kira nafsi-nafsi ita ce ke gudana a gidanmu domin kuwa kowa ta kansa yake ba mai taimakon wani, rashin haɗin kan da muke dashi yana matuƙar damun Babanmu amma babu yanda ya iya don yana magana Baba Mari zatace "Sai ka bari idan ka nemo ka kawo sai kasaka dokar amma ba akan abinda na nema da gumina ba."

Kar in kaiku da nisa, duk irin wannan rayuwar dake gudana a gidanmu idan ka ganni a waje bazaka taɓa cewa nice ƴar Malam Shehu mai neman abinda zai rufawa kansa asiri ba.

Tsaf zaka ganni cikin sutura ta kece raini tamkar ƴar wani hamshaƙin mai kuɗin, na amince in hana cikina abinci in ɗinka sutura ta kece raini don kare mituncina.

Ko ƙawaye bana kula ƴa'ƴan talakawa Irina sai ƴa'ƴan masu kuɗi da nake cusa kaina garesu su kuma kyawuna yasa suke mua'amala dani basa wulaƙanta ni.

MATAR MANYA shine sunan da kusan kowa ya sanni da shi wanda ya samo asali tun ina aji uku a Makarantar sakandire lokacin dana fara tasawa Mazan ajinmu suka fara rubibina irin soyayyar Class mate da ake yi. Ni kuma nayi tsalle na dire nace nafi ƙarfin yara ni ɗin zubin MATAR MANYA ce. Sabo da hakan da ake yawan faɗa min idan aka kalli zubin halittar da Allah yayi min, tun daga wannan lokacin nasa hakan a raina nake kuma burin auren hamshaƙin mai kuɗin da zan fantama inyi rayuwa dai-dai da ra'ayina.

Suhail shine saurayi na farko dana fara yi bayan tasawata, Suhail kyakykyawan saurayi mai tsananin kyau da zubin hallita mai birgewa. Makarantarmu É—aya da shi yana aji shida ina aji uku a lokacin. Kyawunsa da yanda Æ´ammatan ajinsu su ke haukan sonsa yasa na amince muka fara soyayya duk da cewar talaka ne dan talaka amma kyansa da gayunsa yaja hankalina muke soyayya har ya gama Makaranta bai daina zuwa ba sabo da ni da yanda kowa ke sona a Makarantar.

Har zuciyata nake son Suhail sai dai bana jin zan iya aurensa sabo da baya da kyawun aljihu ni kuma shi nafi so. Sosai Suhail yake tsananin so da kishina shi yasa kullum muke rikici da shi akan samarin dake sona, ni kuma idon cin Naira ne dani don duk wanda ya buɗe min bakin aljihu yasa nake son raina domin da hakan nake samun na sayen kayan ƙarya don kare mituncina.

Kullum Mama cikin yi min faɗa take da nasiha akan irin rayuwar da na ɗaukarwa kaina wacce ni kaina nasan tafi ƙarfina, duk sanda nayi wannan tunanin sai kuma in dubi kaina inga irin surar da Allah ya bani, hakan ke sawa in ji ai nama wuce inda nake a yanzu don haka kullum burina ƙara zurfafa yakeyi da nisan tazarar da takai har bana jin kira bare in wai-wayi bayana...

Oum Fatima

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.