Free chapter 路 Read without an account
7
by Kansa'u Bello 路 MATAR MANYA
馃挀MATAR MANYA馃挀
By
OUM FATIMA
GAJEREN LABARI
PAGE 7
BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM
Sallama Baba ya fara da ita ya bu蓷e da addu'a kafin ya shiga yi mana nasiha gaba 蓷ayanmu. "Alhamdulillah ina godiya ga Allah daya nuna min wannan ranar da na sauke nauyin da Allah ya 蓷ora min naku, Alhamdulillah nayi bakin 茩o茩arina wurin ganin na sauke nauyinku dake kaina iya yanda zan iya abinda nayi kuskure ina ro茩on Allah ya yafe min. Yanzu lokaci ne da zan mi茩a ko waccenku 蓷akin Mijinta wanda a yanzu yafi kowa iko daku, Sabo da haka kuyiwa Mazanenku biyayya domin samun aljannarku." Dakatawa yayi ya sauke numfashi yana jin wata irin kewar yaran na kama shi.
Gyaran murya yayi yaci gaba da cewa "Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa aljanar Mace tana 茩ar茩ashin kafar mijinta ne, saboda haka ku dage ku samu aljanarku. Sai abu na gaba da zan ja hankalinku akai shine ha茩uri, dole a zamantakewa sai anyi ha茩uri musamman zamantakewar aure, ku zamo masu ha茩uri da 蓳oye sirrin Mazanenku."
Juyowa yayi kaina ya kira sunana "Salamatu ina so ki manta da duk wani abu daya faru a baya ki zauna da Mijinki lafiya, kiyi masa biyayya in sha Allah zakici riba. Ki sa a ranki cewar ibada zakiyi ki nemi aljannarki, ina son tunatar dake cewa ba komai ne mutum keso yake zama alkairi a gare shi ba, shi yasa ako da yaushe ake so ka nemi za蓳in Allah akan dukkanin lamuranka ba za蓳in zuciyarka ba."
Saurarawa yayi yana binmu da kallo gaba 蓷ayanmu kafin yace "Allah yasa albarka a cikin aurenku ya baku zaman lafiya da zuri'a 蓷ayyiba, ku tashi ku tafi a kaiku gidajen ku."
Tunda Baba ya fara magana dukkanin mu kuka muke musamman ma ni da jikina ya gama yin sanyi akan abinda na aikata da kuma fargabar abinda zai faru idan Suhail ya kasa rufa min asiri akan abinda zai tarar, duk da cewar dama shirina shine ya sake ni in auri Alhaji, amma bana so asirina ya tonu ko dan mutuncin Iyayena.
Tausayin Iyayena naji ya kamani sai dai wata zuciyar na fa蓷a min cewar koma me na aikata sune sila tunda na fa蓷a musu cewar bana son sa amma suka dage. Cikin kukan da nake wanda a zahiri za'a 蓷auke shi a matsayin normal kuka da kowacce amarya keyi yayin da za'a kaita gidan Mijinta, amma a zahiri ba hakan bane kuka ne na ba茩in cikin inda za'a kaini in yi zaman aure bayan na gama saka rai da inda ya lun-lunka shi sau ba adadi.
"Dan Allah Baba ka yafe min dukkan laifukana wanda ka sani da wanda baka sani ba." Na fa蓷a cikin kuka. 茒an dakatawa yayi yana nazarinta kafin ya sauke ajiyar zuciya yace "Na yafe muku gaba 蓷ayanku Allah yayi muku albarka."
Baba Haja da Baba Auwa ne 拼an'uwan Babanmu suka shigo suka fita damu. Karima aka fara kaiwa saboda ita ce babba har mu aka mata rakiya gidanta yayi kyau dai-dai gwargwado, sannan aka kai Sajida itama dai a cikin gari ne kuma ba laifi Mijinta yayi 茩o茩ari.
Nice 茩arshen kaiwa gidan Suhail da yayi Namijin 茩o茩ari ya gina gidansa na kansa kuma mai kyau dai-dai na masu rufin Asiri, ciki da parlo da ban 蓷aki a ciki yayi sai kuma safaya 蓷aki, kiching da store da toilet na waje sai rijiya da aka rufeta. Ko ina kuma tiles ya saka sannan hada 茩aramin gate ya saka a 茩ofar gida.
Gida yayi kyau masha Allah dai-dai zaman talaka mai rufin asiri dangi nata yabawa, sai dai ni ko ka蓷an bai burgeni ba sabo da gidan da Alhaji yace zai sakani tamkar aljanna yake a kan wannan, yayin da nake ganin wannan tamkar kejin ajiyar kaji.
瞥an kawo amarya na gama tafiya na cire lullu蓳in da aka min na gyara kwanciyata saman gadona wanda Babanmu yayi matu茩ar 茩o茩arin saya mana tare da taimakon 拼an'uwa da abokan arzi茩i, wayata na ciro na shiga dannawa ina duba abubuwa. Data na bu蓷e inda sa茩onni suka ri茩a shigowa tamkar zasu fasa wayar, kwananta biyu a kashe sabo da damun da 茩awayenmu suka rin茩a yi min akan wai da gaske Suhail zan aura.
Haushi yasa na kashe wayar saboda na san izgiline kawai yasa suke tambayata akan cika bakin da nake musu na cewar nafi 茩arfin 茩ananan mutane sai Manya. Sa茩onnin Whatsapp na fara dubawa 蓷aya bayan 蓷aya ina replying wanda ya dace in barin na shirme.
In shiga group 蓷inmu na 拼an Makarantarmu naci karo da wani posting daya harzu茩ani ya 茩ara taso min da tsanar uren.
"Yau dai 茩arya ta 茩are wai ruwa ya 茩arewa 蓷an Kada, yau ne aka 蓷aura auren Salma Shehu (Matar manya) da Suhail, abin tambayar anan shine shin ina manyan Alhazan ne ko sun茩u zuwa an gaji da jira aka bawa talaka?."
Wannan shine abinda naga an rubuta an saka emojis na dariya daga 茩asa. Raina naji yayi mummunan 蓳aci ina jin da zanga Yusura yanzu a gabana ba abinda zai hana ni sha茩eta in mata dukan tsiya akan wannan posting 蓷in da tayi sabo da nasan don aci min mutunci ne yasa tayi hakan.
Class mate 蓷inmu ce tana 蓷aya daga cikin 拼ammatan dake masifar son Suhail tun muna Makaranta, na san yanzu ma kishi ne yasata yin hakan don a titseni akan cika baki na in kunyata.
茒aya bayan 蓷aya na fara bin comments 蓷in da mutane keyi akan maganar da tayi, wanda sa茩onnin sun kusa 蓷ari biyar don masifa kamar jira ake daman kowa da abinda yake tofawa, masu Allah ya 茩ara In banda rashin godiyar Allah me nake nema da Suhail bashi da akwai.
Magan-ganu dai barkatai na sha茩iyanci da masu fa蓷a min ba茩ar magana, Kairiyya ce ka蓷ai ke 茩o茩arin kare ni wacce itama aka yi ca!!! A kanta ana cewa bata son gaskiya don 茩awata ce.
苼acin rai yasa na manta da cewar amaryace ni yau aka kawoni gidan miji kamata yayi in zauna cikin lullu蓳i har sai ango yazo, ina tuni na watsar da lullu蓳in wurinsa da ban na shiga maida martani inda rigima ta kaure sosai a group 蓷in har sai da admins suka kulle gidan sannan aka saurara. A haka Suhail yazo ya same ni sai tsaki nake ina masifa ni ka蓷ai, da yake yasan halin abarsa bai yarda wasu sun rako shi ba duk nacin da suka yi kuwa.
Zama yayi dab dani yana mai-maita sallamarsa a karo na biyu wanda sai lokacin na lura da shigowarsa, da 茩yar na 蓷aga baki na amsa masa ina matsawa daga kusa da shi. "Barka da dare." Ya fa蓷a yana kallon yanda na ha蓷e rai sosai fuskata ba alamar fara'a dama ga 蓳acin ran abinda na gama gani a group 蓷inmu.
Sai da na 茩ara ha蓷e raina sannan nace masa "Barka da dare." Murmushi ne ya 茩wace masa a saman kyakykyawar fuskarsa, shifa a hakanma ya ri茩a kallonta a matsayin mallakinsa ba 茩aramin farin ciki yake jiba, duk wani borenta ya bashi lokaci ne domin ya shirya tsaf don lugui-guita zuciyarta da tsaftatacciyar soyayyarsa irin wacce bata isa ta kauce mata ba.
"Ba za'a kalleni ba." Ya fa蓷a cikin 茩aryar da murya yana jifanta da sassanyan kallonsa, 蓷agowa nayi na watsa masa harara ina 蓷auke idanuna wanda hakan ya kusa wucewa da numfashin Suhail, idansa ya lumshe ya fuzgo numfashinsa da 茩yar ya bu蓷e baki yace "A dai tausayawa bawan Allah kar a sumar da shi."
Wato Suhail 茩arshene a wurin iya soyayya da tattalin wanda yake so, ni kaina na shaida hakan don munyi soyayya a baya wacce na bashi ha蓷in kai ya nuna min gata da kulawa irin wacce sai an tona ake samun Namiji mai irin wannan kulawar. A yanzu haka wancen tsohon tsumin ne ke motsa kansa a cikin zuciyata amma sai dai taurin kaina da son cikar burina ya hana ni bayyana hakan.
Duk abinda take yi yana ankare da ita yana kuma karantar duk wani motsi nata yana fassara shi saboda ya da蓷e da sanin wacece ita tun tana 茩wailarta yake sonta ya san ko wane motsi nata. Tashi yayi ya fita yaje ya shigo da laidojin daya bari a parlo ya aje a gabanta ya koma kiching ya 蓷auko duk wani abinda za'a bu茩ata wurin cin abincin ya aje kafin ya zauna a gabanta ya fitar da komai.
A natse ya fitar da dan茩waleliyar kazar dake ta nason mai tana fitar da dadda蓷an 茩amshi wanda ya fisgi hankalina ba shiri na kai kallona wurin ina jin yawun bakina na tsinkewa, ta 茩asan ido yake kallonta murmushi na shirin su蓳uce masa sabo yanda yaga tana satar kallon naman tana tura baki gaba. Tsokar duka ya salu蓳e ya fitar da 茩ashin ya yankata yanda zata yi da蓷in ci sannan ya tura mata shi gabanta yana fa蓷in Bismillah.
Mantawa nayi da wani rashin so da nake masa na gyara zama na shiga zirawa cikina naman ina korawa da holandiya sai da naji na 茩oshi sannan na ture kwanon ina 蓷agowa muka ha蓷a ido ya tsareni da wa蓷annan idanun nasa masu hana ni yi masa rashin mutunci lokuta da dama.
Harara na watsa masa na 蓷auke idanuna na mi茩e na shige toilet don yin wanka in kwanta saboda a gajiye nake ga bacci na fizgar idanuna. Ajiyar zuciya ya sauke bayan shihewarta ya maido da kallonsa saman plate 蓷in naman data rage yayi bismillah ya fara ci cike da natsuwarsa.
Ruwa na 蓷iba a cikin babban bokitin da aka cika min da ruwa a ban蓷akin ciki ga electric kettle na jona ruwan zafi da yake akwai wuta nayi wankana na gasa jikina sosai ina jin gajiyar dana kwasa tana sakewa a hankali.
Alwala nayi na fito na samu baya 蓷akin don haka na shirya cikin gaggawa nabi lafiyar gado nayi kwanciya ta, ina jinsa ya dawo ya gama kwashe komai ya kai shi inda ya dace kafin ya shiga wanka wanda tun ina jin motsinsa har bacci yayi gaba dani ban san fitowarsa ba har ya kwanta kusa dani sai da asuba dana tashi na ganshi kwance kusa dani yana baccinsa cikin nutsuwa. Kyakykyawar innocent face 蓷insa na zubawa ido ina jin wani abu a game da shi amma zuciyata na kwa蓳ata akan ban dace da shiba.
"Ya ishe ki haka ko na bari ki 茩ara more wa." Na tsinci muryarsa yana fa蓷a cikin alamun wanda ya tashi daga bacci, wata irin kunya ta kamani don ban san idonsa biyu ba da ban zuba masa ido haka ina kallonsa ba gashi ya kamani dumu-dumu ina kallonsa bayan kullum ina cika bakin cewa bana sonsa.
Mazewa nayi na mi茩e ina 蓳ata rai nace "Meye abin kallon?."
"Kin ganshi tunda kika 蓳ata lokaci kina kallon kyakykyawan Mijinki mana." Ya fa蓷a yana bu蓷e idonsa gaba 蓷aya ya tashi zaune ya zuba mata ido. 苼ata rai nayi na nufi bayi ina gun-guni a raina fa蓷i nake 'yanzu da ina can na kwana a saman bene na shiga bathroom na sakarwa kaina shower in fito in sauko daga saman bene in bada umarnin abinda za'a dafa min, amma Baba ya hana ruwa gudu yanzu ga inda na kwana a matsayin gidana wanda ban ta蓳a hasaso shi haka ba.'
Tsaki nayi a fili dana duba ba wuta bare in jona kettle in dafa ruwan wanka, ina tsaye ina taraddadin abin yi wanka da ruwan sanyi ko bari naji knowking 蓷insa a bakin 茩ofa. Banza nayi masa tamkar ban jiba sai da yace Salma ki bu蓷e ruwan zafi ne na kawo maki."
Sai da ya fa蓷i haka sannan na bu蓷e na na kar蓳i planks 蓷in ruwan zafin na maida na rufe ba tare dana tanka masa ba, murmushi kawai yayi ya juya ya zauna bakin gado yana jiran fitowar ta. Shifa hakanma ya masa don bai ta蓳a tunanin iya haka rikicin nata zai tsaya ba, yayi tunanin ranar da aka kawota bazata bari suyi bacci ba musamman ganin yanda ta nuna bore sosai akan 茩in auren.
Yana nan zaune har na fito nayi tsaye ina jiran ya shige in shirya amma ya茩i tashi sai kallon daya bini da shi wanda yake ratsani ba ka蓷an ba. Ganin ta茩i zuwa ta shirya gashi ana 茩o茩arin shiga sallah yasa shi tashi ya shige toilet 蓷in bayan yace mata ta jira shi suyi jam'i.
Yana gama shigewa nayi sauri na bu蓷e akwatina na jawo doguwar riga na zira na saka hijab na fesa turare na kabbara sallah, raka'atanin fajri na fara gabatarwa na zauna lazumi bayan na gama nayi addu'a sosai na ro茩i Allah ya yafemin akan kuskuren dana aikata. Ina nan zaune ya fito ya zira jallabiya ta maza ya saka turare ya matso ya jamu jam'i.
Muna gama sallah na tashi zan haye gado saboda baccin dake idona na tsinci muryarsa yana cewa "Barka da safiya Salma." Kunya naji ta 蓷an kamani saboda nice ya kamata in gaishe shi amma na kasa har sai daya fara gaishe ni, mazewa nayi nace masa "Ina kwana." Ba tare dana juyo ba.
Cike da kulawa ya amsa min yana tambaya ya ba茩unta na masa shiru na haye gado naja bargo nan da nan bacci ya kama ni.
Bai koma bacci ba yayi zaman karatun Alkur'ani sai da ya kammala sannan ya fita waje ya fara tsaftace gidan, sai daya gyara ko ina ya saka turare kafin ya shiga kiching ya ha蓷a musu breakfast kafin ya shiga wanka...
Akwai complete document a Naira 300
***