Free chapter 路 Read without an account

9

by Kansa'u Bello 路 MATAR MANYA

馃挀MATAR MANYA馃挀

OUM FATIMA

GAJEREN LABARI

PAGE 9

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

Na gama she茩a amai kenan ina birgima a tsakar 蓷aki naji sallamar Mama wacce tasa na 蓷ago kai don ganin ta inda zata shigo. "Subhanallah Salamatu jikin yayi tsanani ne har haka ?." Mama ta fa蓷a cikin damuwa tana kamani na tashi zaune da 茩yar ina sauke numfashi.

"Sannu Salma, Allah ya baki lafiya." Suhail ya fa蓷a tamkar zai saka kuka, tashi Mama tayi ta fita waje tana 茩o茩arin 蓷aura ruwan zafi don ta taimaka min in yi wanka kafin mu wuce Asibitin. Fitowa yayi yana cewa "Mama akwai ruwan zafi a plaks ba sai kin 蓷aura wani ba." Ya fa蓷a yana shiga kiching ya 蓷auko babban tea plaks 蓷in ya bawa Mama.

Ruwan ta ha蓷a ta kai toilet kafin ta koma ta kamo Salma dake ta lan茩washewa ta kaita ta taimaka mata tayi wanka da ruwa mai zafi sosai kafin suka fito ta taimaka mata ta saka kaya ta 茩arasa shiryawa, zuwa lokacin Suhail yaje ya taro adai-daita sahu ya 蓷aukesu zuwa Asibiti don a dubata a san meke damunta duk da Mama dai ta fahimci ciwon nata amma dai tayi shiru suka nufi Asibitin ko don jikinta da yayi laushi.

Suna zuwa Asibiti ba wani dogon jira aka amsheta aka yi mata duk wasu gwaje-gwajen da suka dace kafin result ya fito likita ya bu茩aci ganin wa蓷anda suka kawo ta. "Masha Allah tana 蓷auke da juna biyu yanzu za ayi mata scanning don sanin kwanakin cikin." Likita ya fa蓷a yana murmushi.

Murmushi Mama tayi tana fa蓷in "Masha Allah." Yayinda shi kuma Suhail wani mugun shock ya kamashi har bai san lokacin da yace "Ciki kuma Doctor? Juna biyu dai na haihuwa!?." A firgice ba.

"Kwarai kuwa zan iya mata scanning don ka tabbatar da hakan."

Shiru yayi ya kasa cewa komai yayinda Mama ta zuba masa ido tana nazarin sa. "Koda wata matsala ne Suhailu?." Mama ta fa蓷a tana kallon sa.

"A'a babu wata matsala kawai abin ne yazo min ba zata, farin ciki ne ya sani ka蓷uwa abinda ban tsammata ba ne." Ido Mama ta zuba masa tana tantamar abinda ya fa蓷a 蓷in. Ya茩en dole yaci gaba dayi don kar ta gano wani abun amma a cikin zuciyarsa tsananin tsoro, firgici da mamakin al'amarin yake yi. 'idan har Salma na 蓷auke da ciki bayan wata mua'amalar aure bata ta蓳a ha蓷a suba to kenan cikin waye? Yaushe kuma hakan ta faru?, innalillahi wa inna ilaihirraju'un!." Wannan shine abinda ke yawo a zuciyarsa.

"Zamu iya zuwa don yin scanning 蓷in." Doctor ya fa蓷a, Suhail da yayi nisa a tunani bai jiba har sai da ya mai-maita kafin yace "Ok ok ba matsala." Ita dai Mama ido take bin sa da shi zuciyarta na sa茩a mata cewar duk yanda aka yi akwai abinda ke tafiya ba dai-dai ba amma zata binciki Salmar.

Ina kwance a 蓷akin da aka saka min 茩arin ruwa suka shigo gaba 蓷ayansu har Doctor, Suhail na kalla wanda yayi matu茩ar 茩o茩arin 蓳oye yanayin da zuciyarsa take ciki amma kana kallonsa zaka san baya da cikakkiyar natsuwa. Sai kuma Mama data zuba min ido tana kallo na.

茦arin ruwan da dama ya kusa 茩arewa kuma shine na 茩arshe da za'a saka min aka cire Mama ta taimaka min na tashi, kama ni tayi muka tafi 蓷akin scanning yayinda zuciyata ta shiga dokawa da 茩arfi ganin an sakani na kwanta a gadon Doctor ya matso da table 蓷in da computer ke kai ya shiga saita wa. Rigata yasa na 蓷age sama ya shafa min wani abu mai sanyi ya goge kafin ya shiga yawo da na'urar saman shafaffen cikina wanda gaba 蓷aya muka 茩urawa na'urar ido, bamu ga komai ba sai wani ba茩in 蓷igo kwance a mahaifata wanda yasa naji zuciyata ta shiga dokawa da mugun 茩arfi.

Sai da ya gama tsaf ya rubuta komai kafin ya kalli Suhail yace "Cikin yana da sati shida har da kwana uku." Wani dim!!! Naji a kaina wanda yasa na 蓷ago da sauri na kalli Doctor nace "Ciki? Ni kuma!." Na furta a ki蓷ime.

"Ke ban son sha-shanci." Mama ta fa蓷a tana kallona kafin Doctor yace "Itama tayi mamaki ne kamar mai gidan." Takarda ya 蓷auka yayi rubutu ya mi茩owa Suhail yace "Ga wa蓷annan magun-gunan tayi amfani dasu, Allah ya bata lafiya."

"Ameen doctor mun gode." Ya fa蓷a a sanyaye yana amsar takardar.

Tunda na sadda kaina ban 蓷ago ba sai da Mama ta kamani tana fa蓷in "Muje ko." Cikin mutuwar jiki na rashin lafiya da kuma fargabar abinda zai faru na tashi muka fito, abin hawa ya taro mana muka nufin gida kowa da abinda yake sa茩awa a cikin zuciyarsa.

Koda muka isa shimfi蓷a Mama ta min a Palo na kwanta ta zauna ta tsare ni na sha duka magungunan da aka sayo, sallama Suhail ya mata akan zai je ya dawo tace masa babu komai don itama so take ya fita ta samu tayi magana da Salamatun.

Yana fita Mama tace tashi ki zauna muyi magana Salamatu." Ba alamar wasa tayi maganar don haka na tashi da 茩yar ina jingina da filon data saka min a bayana na sadda kai 茩asa na茩i kallonta don gani nake kamar zata gane gaskiyar abinda ke faruwa a idona.

"Akwai abinda ke faruwa ne kike 蓳oyewa?." Mama ta tambaya ba alamar wasa. Shiru nayi na茩i kallonta na茩i kuma magana wanda hakan ne ya hasalata ta daka min wata muguwar tsawa tana ce "Salamatu dake nake magana, nace akwai abinda kike 蓳oyewa ne? Me yasa kika firgita da jin cewar kina da ciki? Me yasa shima Mijinki ya nuna razana? Akwai abinda kika aikata ne!." Ta fa蓷a a tsawace.

Wasu irin hawaye ne suka shiga sintiri a saman fuskata da 茩yar na bu蓷e baki nace "Ba abinda nake 蓳oyewa Mama." Na za蓳i na 蓳oye mata gaskiya tunda har shi Suhail 蓷in ya rufa min asiri bai fa蓷a mata komai ba mai zai sa ni in tonawa kaina da kaina.

"茦arya kike Salamatu baki da gaskiya, ki fa蓷a min in akwai abinda ba dai-dai ba tun wuri a 蓷auki mataki kafin abin yayi munin da ba zai gyaru ba."

"Allah Mama ba komai kawai ban shirya haihuwar yanzu bane." Na mata 茩arya don 蓷auke hankalinta daga waccen maganar. Ai kuwa fusata tayi ta wanka min mari ta shiga fa蓷a ta inda take shiga ba ta nan take fita ba.

"Don Ubanki baki shirya haihuwa yanzu ba sabo da bakya son sa ko? Wato dama akwai abinda kika shirya ko? Tun farko dama ni ban yarda da saukowarki lokaci 蓷aya ba sabo da na san taurin kanki, baki shirya haihuwa ba sabo da ba zama kika zo yi ba to ai gashinan Allah ya nuna maki ikonsa kuma ko da wasa naji wata magana ta fito daga wurinki wallahi sai ranki yayi mummunan 蓳aci!."

Ni dai tunda ta fara fa蓷an nake kuka da tunanin ranar da zata gane gaskiya wane irin hali zata shiga, fa蓷a tayi sosai don har Suhail ya dawo bata yi shiru ba. Ha茩uri ya shiga bata tace "Ka bar ni da wannan mara hankalin Suhailu, in banda tsabar rashin hankali dama sai mutum ya shirya haihuwa Allah ke bashi ita." Kallonta yayi yana ayyana cewar haka na fa蓷a wa Mama kenan.

Shi dai ha茩uri yaci gaba da badawa ya aje laidar kayan fruit daya shigo da su ya shige ciki, anan Mama ya yini sai yamma ya mayar da ita gida shima ita ta dage zata tafi kafin ya kaita. Tana zuwa gida ta samu Baba ya dawo daga tafiyar da yayi. "Har kin dawo? yaya kika baro mai jikin?." Baba ya tambaya da kulawa.

"Da sau茩i Malam ka san halin Salamatu idan bata jin da蓷i dama ya aka 茩are bare yanzu da yake laulayin ciki mai wahala." Mama ta fa蓷a lokacin data jawo kujerar tayani gulma irin ta tsakar gida ta zauna, Baba Mari ta 蓷ago da sauri daga inda take iza wutar abincin dare na sayarwarta tace. "Salamatun har ciki ta samu daga yin aure ko wata biyu ba'a cika ba?."

Duka ido suka zuba mata suna kallon tsabar hassada a idonta na jin da tayi ance Salma ta samu rabo, Baba ne yace "Kaji wani shirme fa don Allah, to idan rabon a kusa yake mai zai hana." Ta蓳e baki tayi taci gaba da aikinta ba tare da ko Allah ya raba lafiya ta fa蓷a ba.

"Yaya jikin nata da sau茩i dai ko? Kuma ita ka蓷ai kika baro?." Baba ya tambayi Mama cike da farin cikin biyayyar da Salamatun tayi masa na kwantar da hankalinta har gashi an samu rabo.

"Eh ai da yake Mijinta na tare da ita, dama cewa nayi da zai yiwu sai a tura mata Zainab tunda laulayin nata mai zafi ne ba abinda take iya yi sai ta 蓷an ri茩a taya ta wasu ayyukan kafin ta 蓷an samu 茩warin jiki tun da kaga su Sagir ba zai yi suje ba sabo da Maza ne su." Mama ta fa蓷a tana kallon Baba Mari.

Ai kuwa cikin sauri har tana sakin ludayin da take juya abinci da shi tace "Wannan fa 蓷aya babu inda 拼ata zata je tayi bauta wallahi ta bar min tallar abincin da da shi nake rufawa kaina asiri ki ma sake tunani."

Shiru sukayi duk suka zuba mata ido saboda yanda ta ha茩i茩ance tana masifa, sai da tayi shiru sannan Baba yace "Nine Uban Zainab kuma nike iko dake da ita gaba 蓷aya don haka gobe Zainab ta shirya zata je gidan 拼ar'uwarta ta zauna har taji sau茩i, na gama magana." Masifa Baba Mari taci gaba dayi tana fa蓷in "Yo ikonka na banza da wofi har ni zaka nunawa iko, sai ka bari sai ka fara sauke nauye-nauyenmu da suke kanka sannan sai kayi ikon damu amma ba dai yanzu da nake cida kaina da 拼a'拼ana ba."

Ba wanda ya 茩ara kulata har tayi ta gaji tayi shiru yace dai ya gama magana kuma dole ayi yanda yake so.

Suhail kuwa bayan ya aje Mama kasa komawa yayi gidan sabodakomai zai iya faruwa idan ya koma a wannan lokacin yanda zuciyarsa take masa wani irin zafi da ra蓷a蓷i, mutum ne shi mai tsananin kame kansa daga abinda Allah ya haramta masa da gujewa duk wani abin da ba nasa ba, shi yasa yake da tsananin kishi akan abinda ya zama mallakinsa.

Duk sanda ya tuna cewar wani ne da ban ya riga shi shiga yayi shuka a gonarsa da yake tsananin so fiye da komai a zuciyarsa bayan Iyaye sai yaji zuciyarsa tamkar zata fashe. Gidansu Abokinsa Usman ya nufa duk da sun yi waya baya gida.

Makullin 蓷akin Usman 蓷in aka bashi ya shiga ya kwanta ya lumshe idonsa ya shiga tunanin mafita game da lamarin nan, a gaskiya yaji matu茩ar tsoro da tashin hankali saboda bai ta蓳a sanin cewa abin na Salma har ya kai haka ba don shi shaida ne akan cewar tana matu茩ar tsare mutunci da 茩imarta duk tsananin son duniyarta kuwa. To amma garin ya haka ta faru? Yaushe? Kuma a ina? Wa蓷annan sune tambayoyin da dole sai ta amsa masa su.

Bai koma gidan ba sai da dare yayi sosai don kusan goma da rabi 10:39pm shima sai da Usman ya matsa masa da tambayar ko lafiya mai ya same shi kafin ya masa sallama ya hau lifan 蓷insa ya tafi gidan zuciyarsa a 茩untace.

******* Tunda suka fita shida Mama nake sauke ajiyar zuciya yayinda fargaba da tashin hankali da tunanin makomar cikin dake jina da yake amsa sunan mara Uba suka ha蓷u suka yiwa zuciyata nauyi wanda hakan ya haifar da 茩ara rikicewar jikina zazza蓳i ya dawo min sabo ga rashin abincin kirki a cikina don ma kafin Mama ta tafi ta matsa min na sha fruit kuma cikin ikon Allah ban amayar dasu ba.

Zuciyata ta shiga raya min ba tan-tama wannan cikin na Alhaji Murtala dala ne domin abinda ya faru a tsakaninmu saura kwana hu蓷u bikina ya dawo min a raina. 'Yanzu miye abin yi? Kiran Alhaji zan yi na sanar dashi ko kuwa, a'a a'a bai kamata na kira shi na fa蓷a masa ba domin in nayi haka tamkar na da蓳awa kaina wu茩a ne domin abinda nake 蓳oyewar sai ya fito kowa ya sani. To amma idan Suhail fa ya kasa rufa min asiri? To ko dai zuwa zanyi a zubar da cikin kowa ma ya huta?, amma ha蓷arin dake tattare da zubar da ciki kuma fa?.'

Wa蓷annan magan-ganu da tarin tambayoyin ne suka yi ta yawo a zuciyata wa蓷anda na rasa amsoshinsu sai kawai na fashe da kukan rashin samun mafita zuciyata na yimin nauyi a 茩irjina ina jin ba zan iya dakon wannan abin ni ka蓷ai ba, gashi kuma ko Kairiyya ba zan iya sanar da ita ba duk kusancinmu da ita kuwa.

Kuka na 茩ara fashewa da shi ina sabbatu cewa nake "Wannan wace iriyar lukutar masifa ce ta same ni ni Salamatu? Koma miye ya faru Baba ne da Suhail suka ja min, da an barni na auri wanda nake so da duk da ba'a zo wannan matakin ba. Amma saboda kafiyar Baba da azabar nacin Suhail ga abinda ya haifar, ni ban auri mai ku蓷in ba gani 蓷auke da cikinsa a gidan wani." Kuka naci gaba dayi wanda ya matu茩ar galabaitar dani lokaci 蓷aya na fita a hayyacina, gashi ni ka蓷ai a gida sai birgima nake ina kuka ina sabbatu a haka yazo ya same ni....

Oum Fatima

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.