Free chapter · Read without an account

Page 14

by Zainab iliyas · NI DA GIDANA BOOK 1

NI DA GIDANA

Zainab ilyas mazawaje

Best brilliant intelligent writer...✍️

Page 14

Hajiya Mariya tayi 'yar dariya tace.

"Shak'iyyar wofi. Kwana biyu dai munji kunne, da kika yi gaba, yanzu kyayiwa mijinki kuma."

Baba Talatu, tace"Sa'a ma kika yi muka zo yau. Dama idan dad'i yayi wa Mutum yawa, Sai yace Allah kasheni na huta. Da Kawunki Sulaiman cewa yayi, kar muzo, a bari an d'ebi lokaci tukun. Kakan kine, ma yace sai munzo mun duba masa ke lallai, duk da dai bake kad'ai bace ma a gidan, ko menene ai da wasu, amma shine za kiyi mana godiyar mayu ko?".

Naji nauyi, na saddakai k'as nace kuma.

"Yaya Kawuna yake?".

Baba talatu, tace.

"Dama nasan shine a layin farko. To Lfy Lau yace a gaisheki da kyau."

Na yi murmushi kuma nace.

"Allah sarki tsoho mai ran k'arfe, yaya yake, kina kulamin da shi kuwa? (kakana). Tace

"Tace.Ko ke albarka.Lfy Lau yake, yace na gaisheki."

Hira sosai muka yi, daga bisani, na kaisu

wurin Momi. Momi ta karb'esu da daraja kam, suka yi tama hira, har Hajiya Mariya tace da Momi. Ina Angon yayi, bamu ganshi ba?".

Momi, tace. "Sun tafi ziyarce ziyarce, shida Khalifa, d'azu. Tace"Ai nayi zaton jin za muzo ne, ya waske, gudun kar muzo muyi masa d'iban Karan mahaukaciya,saboda ya Samu, Sabuwa, ya ya damu gefe."

A kasa dariya, a tare.momi tace cikin dariya. "Ina zai ya daku, ai da tsohuwar zuma ake magani, kuma da sabon gini gwara yabe".

Hirar barkwanci tsoffin nan sun Shashi da Momi. Hakan yay min dad'i kam, sosai. Nuriyya tazo a ranar, kuma da ita muka yi ta tarben bak'i har girke girke, duk da momi ta aiko da nata daron tace a bawa bak'i.

A Sati na na d'aya a gidan, Ina zaune gaban mudubi Ina taje kaina, Wanda yasha washing da retourching, yana ta shining ya kwanta lamb'am. Ba kuma wani tsawo ne da shi ba can, iya saman kafad'ata yake tsayawa. Ina kuma alfahari da a bina a hakan.

Half vase ce a jikina, da under wear na siket iya gwiwa, domin kwalliya na gama nasa turarurruka na jiki, zan saka kaya na kenan, naji an banko k'ofa da sauri, an shigo. razana nayi, bawai ga yanayin under wear kawai

dake jikina ba ma, saboda nasan babu mai iya shigomin d'aki kai tsaye haka ba, domin ko Ancle Fa'iz mijina iya kacin'sa falo, bai tab'a Shiga cikin d'akina ba.

Wanda na yanke tsammanin zai shigo, shid'in ne ya shigo.

Ancle. Sau d'aya ya dubeni, sai naga ya yi saurin juyar da kai, ta yiyu yanayin da ya ganni ne bayaso idanunsa su sake sauka a kai. Da ya shigo ya wuceni ya isa kan gado, ya zauna.

Na Samu sauk'in razana, ganin shine. Naja dogon Hijab na sallata nasa da sauri domin bansan me yake faruwa ba, na sake kai duba gareshi, cike da Mamaki. Da ganin'sa kasan daga wanka ya fito. Silk d'in sumarsa da bata taru da yawa ba, jik'e take da ruwa. Zulaika ce gajera a jikin'sa, da towel fari, sol, da ya sak'ala a kafad'a.

Nace. "Lafiya kuwa, Ancle?" .

Kafin yace komai, k'ofar d'akin da take a bud'e ya tashi ya jawo ya rufe. Sannan

Yace.

"Mutum, domin ya shigo d'akin matar'sa laifine?".

Na girgiza kai.

"Ko kusa, my Ancle. Gani nayi baka tab'a shigowar bane"

Yace. "To, yau na shigo, then so what?".

Nayi shiru, Ina kallon'sa.

Ya sake zama kan gadona, ya cire towel d'in da ya sagala a kafad'a ya ajiye gefe.

"Sumayya, wani a bune ya faru, nake so, Kije falo ki zauna, ko da Momi ta aiko kirana, kice bananan".

Toh! wata Sabuwa Inji 'yan caca. Kallon da nayi masa galala, yasan tambayace zan masa na dalili, ya katseni.

"Karki tambayeni dalili. Just ki aiwatar, kyaji komai daga baya. Yanzu babu lokaci, kiyi sauri Kije" .

Na ja zani zan d'aura, kasan Hijab yace. "Kisa kayanki mana, tun da kin d'ebo. Kiyi sauri amma".

Bani da zab'i face bin umarnin'sa da nasan zai iya jefani a matsala babba, idan a kasamu kuskure a ka gane gaskiya. Amma k'arya kuma ba'halin Ancle Fa'iz bace, ko mai amfani ce. Tun da yau yayi kuwa, nasan da akwai babban dalili, ba kuma k'arami ba.

Na Shiga kici kicin cire Hijab domin saka Kayan da sauri, duk da nauyin'sa da yake zaune a d'akin yasa nake komai a sanyaye

kuma.Ko Fahimtar hakan da yayi Sai naga ma juyar da kan'sa gefe ya jawo wani littafi irin na ma'aurata zalla da Nuriyya ta sayomin yana dubawa, kamar na warce littafin, don bazan so ya karanta ba, amma bazan iya ba, sai na rabu da shi na mai da kai ga abin da ya kawo min farmaki yanzu, da ana samun a kasi tawa ta sameni.

Ban gama d'aura d'an kwali bama na fito, na jawo k'ofar d'akin na barshi a ciki.

Na fara da kunna kallo, domin Samun Nutsuwar yin basaja.Amma, zuciya ta cike da tararrabi take, na me yake faruwa. Fatana dai ko maye, kar ya ritsa da ni, wurin yiwa Ancle Fa!iz Mijina biyayya. Ko minti biyar kuwa, ban cika da zama ba, Sai ga Muhibbat ta d'aga labulen k'ofata tana daga tsaye k'erere, da jin isar nan da fad"in rai tace. "Yayan yana nan?".

Nace.

"A'a bai shigo ba ai ."

Ta tsuke fuska.

"To, Ina zai Shiga Kenan?".

Nayi tsai, Ina kallon'ta Sai kuma nace.

"Kin duba, d'akinsa baya nan?".

Bata amsamin ba, illa tsaki da taja, ta saki labulena ta tafi.

Na d'an ji ciwon hakan. A binda na kasa tantancewa, ni take yiwa tsakin, ko kuwa rashin ganin yayan nata.

Bayan mintuna da fitarta na Shiga d'akin na sameshi, a kwance ma yake a binsa. Ya ajiye littafina can gefe, da alamu ba karantawa yayi ba, ya dan dudduba ne sama sama kawai.

Nace".Muhibbat tazo nace mata baka nan, wai don Allah me ya faru ne?".

Yace.

"Zan fad'a Miki, Jeki d'akina ki d'auko min Kaya marasa nauyi, shirt da jins, ko T. Shirt da troser da takalmi, da under's, a Kwai sababbi da ban bud'e ba under's, su za'ki d'ebo."

Nace" Tom."

Da na fito a d'arare, nayi sa'a duk suna saman Momi, Ina jiyo hayaniya kuma. Na Shiga d'akin Ancle, a karo na farko. Gado ne Kawai da kwabar zuba Kaya,set, da kujerar zama guda daya. Na bud'e kwabar, duk na d'auko Kayan da ya sa na d'ebo. Wasu Kayan duk a hargitse, bayan da gogaggu a ciki. Nafi zaton wurin neman wani abu ya hargitsa.

Da na kawo masa, na d'ebo mayuka da turarurruka na jiki da na Kaya, da comb nawa. Domin ban d'auko nasa ba.

Yace"Sumayya kwashe turaren nan, banasa turare mai k'arfi, Sai mai sent, cool, irin nawa.

Nace. "To" .

na kwashe.

Na fito na barshi yana shiryawa. Da na fuskanci ya gama na kai masa Karin kumallo d'akin. Tea da soyayyan plantain ne da k'wai da Khairat ta kawomin.

Ya juyo yana mai gyara botton d'in riga yace.

"Ke me zaki ci, da kika kwaso Break fast d'inki kika kawomin?".

Nace. "Ancle, ai yayi min yawa dama, na Mutum biyu Khairat ta kawo."

Yace "Duk da haka, Kije ki karya, idan yayi Miki yawa kikai kichean a ba mabuk'aci. Ni a waje zan karya ma."

Ba haka na so ba, na maze amma, saboda na soma karantarsa, idan yace Bazai yi a buba, to fa a rabu da shi kawai. Na kwashe kayan da ya cire da nufin wankewa ko ba a lokacin ba. Na zauna a falo. Ya fito yace. "Zan fita, ki rufemin d'akina an jima, mukullan suna kan tebur d'in ward robe."

"Nace"To, Ancle".

Sai da ya lek'a tsakar gidan, yaga babu kowa Sannan yay wuf ya arce.

Nayi masa a dawo Lfy, Bayan ya Fice, bai amsa ba, shi yasa nasan bai ji bane.

Bansan me yake faruwa ba, amma Ina ta jiyo hayaniya a Saman Momi, da a lamu bak'ine.

K'arfe takwas na dare, Ancle Fa'iz ya dawo. Dama yakan lek'oni, kafin ya wuce wurin Momi, idan ya dawo.

Karfe takwas na dare Ancle , ya shigo falona da sallama na amsa, nayi masa sannu da zuwa.

Yace. "Bari naje wurin Momi naga yarda za mu kwashe da ita

Sai nazo na fad'a Miki kome ya faru, nasan kin zak'u. "

Yafi a wa d'ya, kafin ya dawo. Na d'ebo turare cikin show glass ya shigo. Kan kujera two seater ya zauna. Nima Sai nazo kusa da shi dab, na zauna.

Nace. "Nayi zaton kamanta fa"

Yace.

"Yaya zan manta, bayan ninace zan fad'a Miki. Ya kwantar da kan'sa jikin tudun kujera ta baya, cikin galabaitacciyar murya yace. "Don Allah Sumayya ki daina saka wannan turaren d'akin mai k'arfi. Wanda kike sawa ma na jiki sent d'insa is high. Turare mai k'arfi har kaina yake hawa."

Na danne, ba dad'in da naji nace.

"To my Ancle, zan daina sawa na samu air freshner Kawai mai sanyin k'amshi na d'aki. Na jiki kuma zan saka iya body spray mai sanyi, sansanya".

Yace. "Koma wani iri kiyi amfani da shi, amma d'an kad'an zaki sa. Yayi a jiyar zuciya ya zarce.

Dazun Salima ce tazo gidan nan. Ina wanka naji sallamarta. Shi yasa Ina jin ta hau benen Momi, ni kuma da na fito daga wanka shine nayi sauri na shigo d'akinki. Saboda nasan Momi zata tilastani da cewa,na bita Muje

wurin mamanta, saboda ta turo kirana har sau uku nak'i zuwa. Tayi laushi tayi nadama sosai, ni take ta zabarin nema nazo ta bani hakuri na auri 'yarta, batasan ta makaro ba. In dai nine to Wallahi ba ta ma soma nadama ba.

Sai jiyan Salima da yamma ta samu labarin aure na dake, domin mamanta b'oye mata tayi a she a son samunta Sai an nemoni an dai daita komai, Sai Salima ta Sani, saboda tasan taga katin auren ma ba k'aramin hauka zata yi musu ba. To jiya ta samu labari, ta tashi hankalin su. Ta nemeni a waya na fad'a mata a binda mamanta tayi min. Kuka ta rink'ayi min sosai, Wai banyi mata a dalci ba da tun farko na rufeta. Wai ai babanta yana raye ai shi Sai ya d'aura mana aure.

Amma Yaya zanyi aure? Ina nake ta tsoma rayuwarta. Ko ina zaton zata iya rayuwa babu ni. Ke surutai kala kala. Jiya ma cikin dare ta kirani a waya tana kuka da surutai. Gaba d'aya daren jiya ban samu bacci ba fa. Kiran waya, babu hutu. Lallashin duniya nayi domin ta fahimci bawai na barta Kenan ba, Ina sonta, kuma Ina da burin auren ta, amma da sauran lokaci. Kuma auren da nayi duk Saboda ita ne, domin idan ban tauna tsakuwa a ya taji tsoro ba, al'amari Bazai gyaru ba.

Amma Salima fafur ta kasa fahimtata. Da na gaji na kashe waya ta, naki kunnata kuma har yau. Shine fa kika ga tazo da safen nan, Wai mamanta tace tazo ta tafi dani, saboda ta gigita nutsuwar su."

Duk da fargaba ta rufeni da jin a binda ya faru, da nima zance ya shafeni dole. Cikin taushin murya nace.

"Ancle, Kayi hakuri mana kai ma. Tayi nadama fa maman nata. Kuma naga burinka kenan."

Ai gani nayi, ya mik'e zaune sosai ya dubeni.

"What? Nayi me? Wai nayu hakuri yanzu? Lallai yarinya baki sanni ba, labarina kike ji."

A raina nace. Ban dai gama sanin ka ba.

"Wa'adin da na yankar mata wallahi Sai ya cika. Ina son Salima. Ina son 'yarta fiye da zaton su. Amma wallahi ban shirya auren'ta yanzu ba, ko da kuwa za'a tattaromin kud'in masu arzik'in k'asan nan a bani a matsayin gudun mawar aurenta. Wallahi bazan aure ta ba sai wa'adin da na d'ibar musu ya cika".

Nan nasan lallai Ancle Fa'iz ya wuce sanina da karatuna. Zuciyar da Kawu Sulaiman yace yana da ita, ta wuce zatona. Amma a hakan kullum zuciyta k'ara zarmewa take a son sa, duk da zahirin halayan'sa masu wuyar Sha'ani da juriya, suna dad'a tallata kan su da kan su. Wannan bai hana Soyayyarsa k'araci gaba da hab'aka a raina ba. Wuyarta mu kwana Mu tashi, nayi ido hud'u da shi, naji muryarsa kuma.

Zan iya cewa, tun da daga ranar nan, gaba d'aya naga gidan sun sauyamin fuska, idan a ka cire Khairat, da Ancle Fa'iz. Amma Khairat ta d'an ja baya dani kad'an a kan da. Ta yiyu kashedi a kayi mata, saboda ko magana zata yi min zan ga bata da nutsuwa. A kan matsalar Ancle fa da Salima na zurma wannan rigima. Saboda Momi tayi iya yinta Ancle yak'i saukowa a yi sulhu shida maman Salima. Domin burinta Kawai yazo ta bashi hak'uri ya auri Salima. Shi kuma yace ba yanzu ba, bashi da ra'ayi Sai lokacin da yayi ra'ayi. Momi da kan'ta tasan halin d'an ta, idan ya kafe a hak'ura, idan ba haka ba, to lamari b'aci zai yi. K'arshe ma a yi uwar watsi, yace auren ma baza'ayi ba ya hak'ura da ita.

Da wannan dalili Momi ta danne zuciya tasa masa na mujiya. Wato ido.

Amma a damuwa take game da lamarin, saboda a wurinta a ke kamun k'afa, ita kuma ta kasa yin yadda suke so ga Ancle. Shi yasa Sai a Kayi haushin kaza huce kan dami, ni fushin a ka juyeshi a kaina, saboda su so suka yi ya sakeni ya auri Salima a lokacin, tun da sun zo neman sulhu. Shi kuma Ancle sun ga bashi da niyyar, hakan. Sun fahimci baya nunamin wata kulawa,ko ta aure. Domin kowa ya Sani, baya zaman minti biyar a d'akina, ballanta na wai ya kwana ciki, bayacin a binci na ko da wasa.

Amma kuma babu wani fitintunu na rikici tsakani na da shi, duk da borar da na zama. Ina girmamashi, da yi masa biyayya dai dai gwargwado. K'alau muke zaune ba'ajin ko tari na na wai muna ko da da musu. Wannan shi ya zamo k'arin umda da ya had'u da na bijurewar sa ga auran sa da a ke so yanzu da Salima, a kace Ina wuta a jefani.

Alhakin komai kamar gani suke a wuya na yake, nice sila.

A tunani na inda a dalci basa yi min haka ba. Matsalar Auren Salima da Ancle tun kafin a San Ancle zai aure nine. Ya kuma fad'i hujjar bijirewar sa ga Momi. To don me zan zama a bar juyewa haushi? nima a barni naji da kashe wutar gabana Mana, da suma sun San da ruruwar ta. Zaman aure na da Ancle ko a suna ma bashi da takwara, ko mahad'i.

Ban ware girki na ba, har lokacin tare muke yi da Khairat na gidan duka. Wani zubun ni keyi, amma Ancle bayaci momi ke yi masa nasa shi kad'ai kullum.

Momi ta kirani har saman ta, naje na gurfana cikin sababben ladabi da nake mata, ko uwata albarka, domin jiki na har rawa yake, saboda tsabar biyayyar da nakewa Momi idan ta Sani a bu. Idan nasan tana son a bu ma, bana jira, Sai ta sani, yi nake.

Cikin d'aure fuska Momi ta dubeni."Sumayya daga yau, bana son ki sake saka hannunki cikin girkin gidan nan, ki rink'ayin naki.Dama Fa'iz nike yi masa, Kinga iya cikinki zaki dafa. Na fad'awa Fa'iz ma zaki soma girkin ki."

Nace"To, Momi".

Naci gaba da tsuguno, koda sauran umarni, da naga tayi banza dani, na mik'e na janyo sanyayyun k'afafuna nayi waje.

Ancle bai min zancen girki ba, momin ce ta sake kirana tace"Nayi magana da Fa'iz ya

ce. Ko me kike so, ki tambaye ni, na baki, kudin girkin cefane da abin da kike so ki dafa".

Abinda na fahimta, so a ke a kara nisantani da shi, yarda komai babu ruwansa dani, sai dai na tambayi momi, kuma dama ce da za a rinka samu da za a rinka gasa mini magana, son rai.

Tun yanzu kenan na soma haduwa da matsaloli, kafin ma na soma samun kofar da zan dana tarko na ga Ancle Fa'iz yarda zan soma janyo raayin sa gareni ya ma soma saurarata ko a hira ne, wanda wannan aiki ne na sani ja mai zaman kansa, to ban kzi ga wannan ba ma ga wata gwaramar ta tunkaro ni, ta mutan gidan, idan a ka cire khairat kowa ma ba kauna ta da son zama na yake a gidan ba, musamman khalifa da kallon kiyayyarsa gareni yafi na kowa, to ta ina zan fara, abinda yawa wai kura ta shiga kasuwa, kwace goriba kuma hannun kuturu ai bazai yi wuya ba. Abin nufi banje koina a zuciyar Ancle ba, ballantana a sha wuya wurin rabani da shi.

Taku

Zainab ilyas mazawaje

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.