Free chapter 路 Read without an account
CHAPTER 6
Game bukatar document din sa ko kuma PDF sai ya siya 500 ne ga lambar account dina sai ya turamin da receipt din ta Whatsapp ***
Number account dina
9115902627
Abubakar Ishaku
Opay Bank
Thanks 馃憤 馃槉
CHAPTER 6
Bayan kamar watanni uku da faruwar Al'amarin sai Maryam ta dada fadawa kogin tunani na rashin haihuwa, nan take kuwa ta soma ramewa matuka, har ta dan soma rashin lafiya shi kuwa Bukar hankalin sa ne ya yi matukar tashi, domin kuwa ya rasa me zai yi mata wanda zaisa ta manta da batun haihuwa, amma kuma abu ya ci tura kullum abu sai gaba-gaba yake yi babu alamar sauki, nan take kuwa suka ziyarci likita akan ya duba musu matsalar da ta hana su haihuwa, amma kuma bayan wadansu 'yan gwaje-gwaje da likita yayi sai ya kira Bukar ya sanar masa cewar matar sa Maryam baza ta taba haihuwa ba har abada.
Domin kuwa mahaifar ta a matse take, ciki bazai iya shiga ba koda kuwa anyi mata aiki ma to fa mahaifar tata baza ta dauki ciki ba, saboda mahaifar tata bata da kwarin da za ta dauki cikin, da wannan kalamin ne likita ya sallame su suka dawo gida, amma kuma Bukar bai bari Maryam din ta ji abunda ya same ta ba, nan take ya nuna mata cewar lafiyar ta kalau kawai dai Allah ne bai nufe su da samun da ba, shi yasa bata haihu ba har yanzu, sai a sannan Maryam hankalin ta ya dan kwanta don ta ji cewar lafiyar ta kalau kuma shima lafiyar sa kalau.
Tun daga wannan lokacin ne Maryam ta dan soma samun sukuni a zuciyar ta sannan kuma ta fara saka tsammanin zata haihu amma shiru ko kadan bata ji sauyi a tattare da ita ba, nan take kuwa sai ta koma gidan jiya ma'ana ta koma duniyar tunanin samun haihuwa, nan take ta kuma fadawa rashin lafiya, amma na wannan karon ya ninka na baya ma domin a halin yanzu magana ma da kyar take iya yi, koda ganin hakan sai hankalin Bukar ya dugunzuma matuka nan take shima ya yanke shawara akan cewa zai sadaukar da rayuwar sa muddin matar sa zata samu ciki, badon komai ba sai don rashin lafiyar da take yi ya bar ta, da wannan shawarar yayi amfani.
Lokacin da dare ya raba sosai sai Bukar ya mike daga kan gadon su, ya fice gaba ki daya daga cikin gidan ya nufi inda ya saba haduwa da wadannan 'yan matan, amma kuma a wannan karon sai da ya dan jira kamar mintuna talatin sannan 'yan matan suka baiyana a wajen, koda baiyanar tasu sai Bukar ya dube su sannan ya ce musu. "Barkan ku da zuwa 'yan mata na kai tsawon lokaci ina jiran baiyanar ku anan." Koda jin hakan sai daya daga cikin 'yan matan ta yi murmushi a gare shi sannan ta ce masa. "Ai lokacin baiyanar tamu ce bai yi ba shiyasa baka gan mu ba, amma kuma yanzu da lokacin baiyanar tamu tayi ba gashi ka gan mu ba?"
Bukar yace "Hakane kam." Budurwar tace masa. "To yanzu me ka yanke akan abunda muka baka zabi akai?" Bukar yace mata. "Nayanke hukunci akan cewar nizan bada rayuwata muddin matata zatayi farinciki, to ashirye nake da hakan." Kodajin hakan sai budurwar tayi murmushi sannan tace masa. "Tabbas kayi matukar burgeni daka kasance jarumi mai dakakkiyar zuciya, jarumtarka ta burgeni, sannan kuma soyayyarka da kake nunawa matarka ma tayi matukar burgeni, banso ba ace jarumi kamar ya mutu amma kuma babu yadda za'ayi domin bakin alkalami ya rigada ya bushe dolene ka tafi kabar matar ka."
Yayin da budurwar ta zodai-dai nan azancenta, saita ciro wata 'yar karamar kwalba mai dauke da wani koren ruwan tsafi acikinsa, sannan ta mika masa tace masa. "Karbi wannan ruwan, kasani cewar anyi wannan ruwan don mutum biyune kacal, idan mutum na farko yasha ruwan dake cikinsa, to shine wanda zai mutu, idan kuma na biyu yasha to shine zai rayu, kuma asannanne burinsu zai cika, kowanne irin burine aduniya indai ka sakashi acikin zuciyarka yayin da kake shan ruwan dake cikin kwalbar, tofa burinnaka zai cika kowanne irine burin kuwa, kuma ko guda nawane burin sai sun cika, sunan wannan ruwan sunansa "Mutuwa da Rayuwa."
Saboda haka kaine wanda zai fara shan ruwan dake cikinsa, kafin itama Maryam din tasha nata, kada ku rage ko kadanne ku tabbatar da cewar kun shanyeshi baki daya, batare da kun rage koda digo dayaba don kada wani ma yasha, inkuwa kukayi sake wani ma yasha to dukkaninku ku biyunne zaku mutu, wanda yasha daga karshen kuma zai rayu. Sannan kuma kasani cewar inhar mutane biyun sukayi amfani da ruwan, tofa dayan bazai mutuba har sai burinnasu ya gama cika tukuna sannan zai mutu, hakan ya nuna cewar har sai matarka ta haihu tukuna zaka mutu.
Daga karshe inamai sanar dakai cewa bazaka sake ganinmu ba arayuwarka har abada, domin aka'idarmu idan muka baiyana na tsawon shekara guda to baza asake ganinmuba har sai bayan shekaru ashirin da biyar, sannan zamu sake wanzuwa, kuma yau shine karshen shekarar mu inda ace kayi jinkiri na tsawon kwana daya rak, daka rasamu kenan na tsawon shekaru ashirin da biyar, tabbas kai mai sa'ane." Nantake kuwa Bukar ya karbi karamar kwalbar daga hannun budurwar.
Har ya bude baki da nufin yace mata wani abu, amma kuma sai ya nemesu sama da kasa ya rasasu, domin sun bace bat! Tamkar basu taba wanzuwa ba awajen, faruwar hakan keda wuya kuwa, sai Bukar ya juya da baya ya nufi gida cikin tashin hankali, nantake zuciyarsa ta soma danasani akan hukuncin da ya yanke batare da ya shawarci matarsa Maryamba. Bai gushe ba yana wannan zancen zucin nasa har ya iso gidan sa, ya wuce kai tsaye izuwa dakin matar sa Maryam, da zuwan sa sai ya kwanta akan gadon kusa da Maryam din, ita kuwa Maryam din har a sannan bata farka ba daga baccin da take tayi, shi shi kuwa Bukar har gari ya waye ba tare da ya sake rintsawa ba, sai tunani kawai ya ke tayi marar amfani.
Washe gari kuwa lokacin da Maryam ta farka daga baccin ta asannan ne kuma Bukar har ya gama shirin sa tsaf na fita shago, nan take kuwa Maryam ta girka musu abincin karin kumallo suka zauna suna ci cikin shauki, duk kuwa da cewa kowannan su hankalin sa a tashe yake sakamakon rashin cikar burin su, shi Bukar hankalin sa ya tashi ne saboda sadaukar da rayuwar sa da yayi saboda farincikin matar sa, ita kuwa Maryam hankalin ta ya tashi ne saboda rashin haihuwa, amma kuma kowanne daga cikin su ya na kokarin ya kawar da alamun damuwa daga kan fuskar sa, don kada dayan ya fuskanci halin da dan uwansa yake ciki.
Lokacin da Maryam da Bukar suka gama cin abinci, sai Bukar ya ciro wannan 'yar karamar kwalbar daga aljihun sa sannan ya bude ta ya shanye rabin ruwan dake cikin ta, sannan ya mikawa Maryam yace mata. "Ungo wannan kwalbar ki shanye maganin dake cikin ta, da yaddan Allah burin mu zai cika na samun Da, amma kafin ki sha ruwan dake cikin kwalbar ki aiyana acikin zuciyar ki cewa kina bukatar haihuwa da kuma rufin asirin da zaki kula da kanki da abunda zaki haifa ba tare da kun tozarta ba, bayan kin gama aiyana hakan acikin zuciyar ki sai ki kwankwade ruwan dake cikin kwalbar, kada ki rage koda kadan ne aciki, ki tabbatar kin shanye duka."
Game bukatar document din sa ko kuma PDF sai ya siya 500 ne ga lambar account dina sai ya turamin da receipt din ta Whatsapp ***
Number account dina
9115902627
Abubakar Ishaku
Opay Bank
Thanks 馃憤 馃槉