Free chapter · Read without an account

10

by JamilaUmarJanafty · SAIFUDEEN

SAIFUDDEEN

(Ba mutum ba ne)

Wattpad:JamilaUmar315

Mallakar:Janafty♥️

Amnaf_sudanese _collection

Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401

🅿️10

A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah,haka rayuwar ta cigaba da gangara da dad'i babu dad'i bawa ya amsheta yadda Ubangiji mai sama ya tsaramai.

Ta bangaran Muhibba ta cigaba da zuwa aikinta gefe daya kuma suna ta shirye shiryen Speech and price givingday din da zasu yi a makarantar tasu karo farko tun bayan fara kafuwar makaranta shekaru shida da suka gabata in akace Speech and price giving day ana nufin Rana mai muhimmanci domin Dalibai,Ma"ana yaye su da za"ayi da sauran shagulgulan da makaranta ta tsara musu a karo na farko zasu fara sallaman Yan SS3 da kuma Primary 6 dalilin haka yasa suka shirya hakan Saboda karrama Daliban da kuma Taya makaranta murnan Shekara shida da kafuwarta sannan da Jadawalin Cigaban da suka samu a cikin wad'anan shekarun

Gabadaya suna ta shiri ne ba Daga primary section ba daga secondary Section ba,Saboda taro ne da basu taba yiba sai wannan karon suna bukatar Tsari mai kyau yadda akaron Farko abunda zai kayatar fiye da Tunanin wanda ya samu Hallatar Taron.

Daliban yan SS3 tuni sun fara zana jarabawar ta WAEC,Sannan kuma wasu Daliban ba"a makaranta iyayansu suka biya musu ba sai dai an biya da yawa tunda Sabuwar Center ce sune First bach din da suka fara zana Jarabawar Secondary acikin makarantar shiyasa sai aka shirya a bari sai sun gama Neco gabadaya suma yan primary6 din sun yi Common Interest din sai ayi Bikin Gaddamarwa din kamar yadda aka Tsara komai..

Dalilin haka ne ma Director Musa ya Kira Meeting na malamai gabadaya Ranar Alhamis bayan an tashi Makaranta gabadaya su muhibba sai da suka jira sai uku aka fara Taron a Babban Hall din na cikin makarantar suka zauna Director musa da kansa ya fara Jawabi tunda shi ke da alhakin kula da makarantar gabadaya a Hannunsa malaman duka suna zaune saman kujeru suna Fuskarsa shi da Head Teacher da Sakariyarsa,Sai wani Uncle Abdulwasi bayarbene shi ke kamar mataimakin Director musa,Ammh shi Musa Bahaushe ne Tsantsan Cikakken bazazzagi ne.

Ya fara da jawabin yanayin Tsare tsaren da suke dashi kan abunda kowa ya sani zasu gudanar sannan yace yana Bukatar kowa ya kawo nashi Shawara kan abunda yaga ya dace a kara kan abubuwan da aka Tsara za"a gudanar aranar.

Acikin Malamai akwai Wadanda ba musulmai ba su hudu mace Daya sai maza Uku,sauran duka mata da mazan musulmai ne Muhibba na kusa da Anty Jidda Malamar Jss2 Teacher din Su khalipa sosai suke mutumci da Muhibba tana rike da karamar yarinyarta fatima suna kiranta Batula tana Sanye da bakar abaya mai Ratsin Blue ajikinta sai tayi amfani da Blue din mayafi tayi Rolling dinsa sai glass data sanya saboda yanayin iskar garin Dayake ba amabociya kwalliya bace tana nan yadda take sai liptick data Sanya a bakinta saboda kada ya Bushe mata.

sakatariya ce ta tashi ta Rabama kowa Wata Takarda mai Dauke da Jadawalin tsare tsare da shirye shiryen da zai gudana aranar saboda kowa ya gani kuma ya karanta Muhibba ta karbi nata kuma ta Duba bayan Tsawon mintina goma d aka basu sugama Dubawa sannan Head teacher ta mike tace kowa zai iya mgana in yana da abun cewa Uncle Hafiz ne ya fara Daga hannu aka bashi Dama ya mike yayi gaisawa ga Hukumaer makaranta kafin yace"Sir na duba duba Tsare tsaren kuma komai yayi sai dai ina da wata yar shawara."

Nan da nan Director Musa yace ya fadi shawarar sa daman ai abunda yasa suka tara meeting din kenan saboda ataru abama juna shawarar da ta dace Cikin Girmamawa Uncle Hafiz yace"Sir me zai hana ayi katin gayyata na waya da printing one saboda gayyata da zamu yi zuwa ga iyayen yara da sauran manyan baki da muke ganin in suka Hallaci wannan taron zasu yabama wannan makaranta da Tsarinta gabadaya"

Yafada cikin yanayin mganarsa cikin Harshen Turanci kamar yadda kowa ya sani Director Musa ya jinjina kai yana cema Sakatariyarsa ta Rubuta abunda Hafiz yace sannan ya juyo garesa yana mai jinjina Uncle Hafiz yayi mirmishi kafin yace"Sir sai na gaba shine me zai hana shima shugabar wannan makaranta mu gayyatosa ya zama shine babban bakom mu..?

Na tabbata Dalibai ma da iyayan yara zasu ji Dadin in har shugaban wannan makaranta yazo kuma ya kalli duka shirye shiryen da zasu gudanar"

Director Musa yayi shuru sai chan yayi mgana cikin Turanci mai kyau da Tsari yace"Tanque for u Advice Uncle Hafiz.!"

Hafiz ya gyada kai kafin ya zauna D.Musa ya gyada kai kafin ya gyara zaman gilashin dake idonsa yace"Nima zan so hakan sai dai nayi mgana dashi har yanzu bai ce min komai ba,ammh zan cigaba da mai mgana nagani ko zai amsa zai samu zuwa..Mutum ne mai sabogigi da yawa ba Lalle ranar mu same ba, sai in bashi da wani Uzuri ammh kamar yadda kace zan Turamai katin gayyata da korafinku Insha Allahu zai ki amsa gayyatar ba.!"

Kowa ya gamsu da jawabinsa Domin gabadaya kowa ya dauka mai makarantar,yan"uwana juna suke da D.Musa Tunda ganin shi ke rike da makaratar Bisa gaskiya da Amana,Abunda basu sani ba shi kanshi D.Musa bai hada komai dashi ba kawai Jajircewansa da iliminsa yasa ya Daukosa ya damka masa Amana shi kuma yayi alkwarin rike masa makarantarsa Bisa Amana duba da Tarin Alherinsa garesa.

Daya bayan malaman ke mikewa suna bada nasu advise din kuma D.Musa baya watsa musu kasa a ido Sakatariyarsa na rubuta jawabin kowa Cikin Mutuntawa Muhibba kamar bazatayi mgana ba ganin ba wanda yayi mganar da ke ranta yasa ta Daga hannu aka bata izinin mgana Tunda ta mike Anty khadija da suke Zaune waje daya da Anty Usaina suka Bita da kallo tana jin Khadija na Fadin"Uwar iyayi."

Ita dai ki ta kansu bata bi tana Rike da Batula har Lokacin mgana ta fara Bayan tayi sallama ta fadi sunanta da ajin datake koyarwa duk da ba kowa ya Damu daya gabatar da kansa ba.

Su Anty Usaina sai tabe baki suke yi suna mgana kasa kasa ita bata ma san sunayi ba ta fara jawabinta mgana tayi kan me zai hana tunda an shirya Dalibai zasu yi Quiz da Games,to me zai hana su yi Debete da Drama shima Sosai yana taimaka ma yara sannan ta tabbata abun zai kayatar.

D.Musa yayi mirmishi sosai yake yaba Natsuwar Muhibba ga Hankali ga Hazaka Cikin jinjina mata ya karbi Mganarta sannan yace ya dorata kan Abunda ya Shafi Debete din da yaran zasu yi shi kuma Uncle Hafiz da wani Uncle James su duba bangaran Drama din,Sai aka fara tafi ana mganganu irin su Anty Usaina yan bakinciki kamar su fashe Uncle James ne ya mike yana fadin shi da ba bahaushe ba ta ina zai shirya drama..?

Uncle Hafiz ya bashi amsa da ai Drama din guda biyu ne In Hausa and In English,Dariya akayi gabadaya kafin acigaba da Tattaunawa sai karfe Hudu saura aka tashi Meeting din Kowa ya Dauki Maltina dinsa da aka raba awajen muhibba ajaka ta saka nata saboda bata cika cin wani abu ba indai ta baro gida ba.

Bata tafi ba saboda Uncle Hafiz yace ta jirasa sai da sukayi mgana Da D.Musa sannan ya fito suka fito alokacin duk malaman sun watse har su Anty Khadija.

Tare suka fito har bakin Titi Tare suka Hau Kekenapep saboda Uncle Hafiz shima yau Dogawara zai je gidan yayar mahaifiyarsa da bataji Dadi zai Dubata,gidanta na farkon Layi ne ita kuma nasu Muhibba sai an shiga Ciki shi aka fara saukewa suka rabu yana jadaddamata ta samo Topic gobe zai tayata Tsara komai kada taji komai,tayi mirmishi ta Dagamai hannu da Fatan ya gaida mai jiki.

Hudu da Rabi ta shigo gida a gajiye Inna ta samu a tsakar gida tana Shanya wake,Dakyar muhibba tama Inna Sannu da gida ta shige Daki...

Inna ta bita da kallo tana Fadin"Auta yau ina kika tsaya ne..? Lokacin dawowarki ya wuce baki dawo ba nayi ta kiran wayarki baki dauka ba na kira Habiba tace min baki biyo su Siyama ba."

Muhibba Daga cikin Daki tana Kokarin Cire Rigar Jikinta Tace"Inna muna makaranta fa..Meeting mukayi.

Inna tace"Meti kuma..?

Muhibba tace"Taro inna mukayi Akan Taron da makaranta zata gudanar.

Inna tace"Ni dai nace to Allah ya taimaka."

Muhibba data fito ta amsa da Ameen,Inna ta Dago tana kallonta Karamin zani ne ta Daura kafafunta duk a waje buta ta sura tayi makewayi Inna ta bita da kallo tana Fadin"Auta ban hanaki daura wannan Falen zanin ba..?Na fada miki yayi miki karami ki rika Daura wanda na baki din nan shine babba da zai rufe miki har kafunfunki.

Daidai sanda Muhibba ta fito bakin makwarara ta  tsugguna tana fadin"Inna to waye zai shigo...?

Inna tace"Ba domin haka ba sai ka kauce ma idon shedanu ke da yaushe ma kika Rabu da mai bibiyar naki..? Ammh Taurin kai zai sa ki kara jajibo mana wani bala"in.."

Muhibba data fara alwala tace"Allah ya tsaremu Inna..

Inna ta amsa tana fadin"Ameen ammh ki rika kiyayewa Auta.

Muhibba tace"To Inna Insha Allahu.

Sai da ta idar da alwalan sannan ta mike tana kallon Inna Dake ta Faman kara baza wake fari a kan Shararren Simitin dake shashen nasu.

Kallon waken tayi kafin tace"Inna An fara ciro amfanin gona ne..?

Inna tace"Eh mana ai kwanakin nan chan Yayanki ke tafiya kwana uku suna aikin wannan ma bai gama Bushewa bane ya kawo Zeenatu ta bazamai,batanan taje gidansu sai ni na karba na baza.

Muhibba tace"Inna ammh gonar Gabari bata gaya ba ko..?

Inna tace"Na gaya ai aikinta ya bada kila sai an gama duka mota zata kwasomai hatsin.

Muhibba ta jinjina kai kafin tace"Allah ya taimaka..Inna bari nayi sallah..

Inna ta amsa mata daganan ta koma Dakinta ta sauya zani ta saka Hijabi ta tada sallah sai da tayi Nafila sannan tayi sallar La"asar tana idarwa Inna ta shigo mata da abinci Taliya Jalop mai kifi Zeenatu ta Dafa kafin ta fita,taci kadan ta Kora da maltinan da ta zo da ita daga makaranta ta sauya kaya zuwa wata Doguwar rigar wani jan yadi Dakin Inna ta koma tana bata Labarin abunda ya wakana a makaranta ta karishe da Fadin"Inna Director musa ni fa ya wakilta wai na bada topic din gasan da yaran zasu yi,ni yaushe zan wani iya..?

Inna na ballan goronta tace'Kul kar na sake jin kince ina zaki iya in bazaki iya ba ai bazai zabeki ba ko ba sauran malaman ne..?.

Muhibba ta daga kai tace"Akwai Inna sannan Uncle Hafiz yace zai tayani.

Inna tace"kin ma ji..Hafizu ai dan albarka ne Dalilin aikin ku tare a makaranta sau nawa in ya shigo anguwannan yake zuwa gaisheni kuma bai zuwa hannu Rabbana ni da Farko ma har nayi Tunanin Sonki yake yi."

Muhibba ta tura baki kafin tace"So kuma Inna..?Tab ni wlh ba sona yake yi ba koma yana sona ni bai min ba.

Inna ta harereta kafin tace"Ai shikenan kin ma kanki ke ai banga wanda zai miki ba kowa kika gani kice baki so.

Muhibba ta mike tana kokarin fita Daga Inna tace"In ma wannan Aljanin kike jira Allah ya rabaku kenan har Abada,Sakarya kawai ina kika taba jin wani soyayya tsakanin mutum da Aljan ban da wannan Saifudden ban taba ganin kince wani ya burgeki ba..

Ita dai har ta fice bata ce komai tasan Halin Inna in ta fara Fadanta bata gajiya.

Dakinta ta shigo alwalan mangariba ce kadai ta fito da ita nan sai ga Anty Zeenatu ta shigo suka gaisa,Sannan ta shigo Dakinta tayi sallar mangariba ta zauna tana azkar bayan ta gama Ta Dauki wayarta ta Bude data ta hau WhaApps sakonnin suna ta shigowa Sakon Sani ne ya bata mamaki yaushe Rabon da yayi mata mgana tana Budewa data ga abunda ya rubuta sai da ta kusa dukawa saboda Dariya ga Abunda yace.

"Lalle ma yarinyar nan..Wai nan gaba kike dani...?

To ni dai ko a musulunci na fita Hakkin ki Assalamu alaikum."

Sai da ta gama Dariyanta sannan ta fita Daga sakon tasan abun sai yafi kudar da shi yaga tagani batayi mgana ba Sauran sakonnin ta dan Duba ta bada amsa sai dai abunda ya bata mamaki tun ranar da Abun nan ya Faru tsakaninta Sani Abbati bai kara kiranta ba,sannan bai kara mata mgana achart ba,baki ta tabe aranta Tana Fatan Allah yasa ya Hakura ne.

Sai da ta yi sallar isha"i ta koma Dakin Inna Lokacin ta wuce ta sameta tana waya da yan Gaya Goggo Naja tana Fadamata an saka Lokacin Bikin Autar ta Inna Firdausi,Ita dai muhibba ficewa tayi ta koma Shashen Anty Zeenatu ta isketa tana Firan doya ta karba tana Tayata tare sukayi girkin Souces din Doya ne za"a ci da Buredi ta Kira Ya Habibu zai zo dashi to bai ma kai ga shigowa ba ya aiko dashi Muhibba tare sukaci da Zeenatu da yara ta zauna suna kallon Gidan badamasi a tashar arewa sai goma ta baro Dakin ta koma Dakin Inna tana shiga Inna na zaune na shafa man Zafi ta Toshe Hanci Tana fadin"Kai Inna basai ki rika shafawa da rana ba kinsan na tsani warin man nan naki.".

Inna ta dago tana fadin"Ga Hanya ficemin daga daki ai ban kiraki ba.!

Muhibba na Dariya tace"Inna nice Auta..Autar taki kike kora ai sai yan Bakin ciki irin su Sani in sunji su rikamana Dariya."

Inna ta tabe baki kafin tace"Ayi mana ina ruwana.

Jin yadda ta amsa ne yasa Muhibba tasan Inna acike take,gadon ta karisa tana Fadin"Allah ya huci zuciyarki Innata...

kai tsaye Inna tace"Ameen.

A kufule ne sai Muhibba ta koma tana Toshe baki ta haye gadon Inna tana sosa bayan ta kafin ta mike ta cire rigar jikinta zani taso Daurawa ta kwanta ganin Inna na Hararanta yasa ta dauki Rigar Barcinta saman Sif din Inna ta zura doguwa mai taushi ta kama kanta ta saka cikin hula domin Inna fada take mata in ta kwanta ba Dankwali..

Zuwa washegari Inna ta Huce Tare ma suka fita Inna ta wuce gidan su Zeenatu zata  biyama Hajiya karima zasu Dubiyar wata makociyarsu ne aka kwantar a asibiti.

A ranar Uncle Hafiz ya Tayata suka Samo Topic between water da Fire wanne ne yafi amfani Support d motion za"ayi kowani bangare zai Dauki nashi,Duk aranar kuma suka Fitar da sunanayen Daliban da zasu yi Debete din,har da khalipa ta zaba sanin shima yana da kokari yan Jss zasu buga da SS Ne sannan sun fitar da na primary section mai Take Between A doctor and a Teacher wanne yafi muhimmanci Primary 4_5 Zasu kara da yan primary 6 masu Fita Sun zabi jajirttatun da suka san zasu yi abunda sukace Ranar Monday da suka zo makaranta suka kira duka Daliban da suka zaba suka basu Topic sannan kowani bangare ya Dauki Nashi Uncle Hafiz kuma yace duka bangororin zai rubutu musu Motion dinsa nasu kawai su haddace sannan su iya yanayin Debete din.

Sai taji Dadi sosai itama batayi kasa a gwiwa ba ta fara taimakamai wajen Drama dinsa tare suka rubuta Drama din kan muhimmanci karatu ga ya"ya mata,shima an zabi daliban da zasu iya Drama din an basu a rubuce suje gida su karanta kafin afara nuna musu shi pratical yadda zasu fi ganewa Daga baya suma zasu yi nasu Rizahal din agani kafin Ranar.

Yadda Muhibba da Uncle Hafiz ke koma tare yafi kona ma Anty Khadija rai daman ya lafiyan kura..!ta tsani Muhibba kuma bazata taba kaunarta ba Sannan ai ita kanta Muhibban ta san Khadijan na son Hafiz tunda Har Sakon data turamai ta chart ya nuna mata itace dai bata bashi daman ya rika kawo mata mganar Khadijan ba ba ruwanta,Tasan tana jin haushin ganinsu tare bata da yarda zatayi ne,Sannan ita kanta Muhibba tasan koda Hafiz bai furta mata aikinsa da iyayin sa sun Nuna sonta yake ammh kuma ya kasa Fadamata ita kuma sai ta nuna mai bata gane ba tana dai ganin girmansa saboda Uncle Hafiz nada mutumci Saboda chan wata banza bazata Datse zumuncin dake Tsakaninsu ba in suka gansu tare su dinga Haibaici kenan har Hafiz din sai ya koma yana bata Hakuri yana fadin"Kiyi hakuri Muhibba..Kada ki tankasu..Khadija mahaukaciya ce ita kuma Anty Usaina bansan meke damunta ba ta girma tana Abun yara."

Muhibba bata mgana sai dai tayi Dariya Wai wanda kake so yana ce maka Mahaukaciya ina kima..?sau tari wasu matan basu ganewa wajen kokarin nuna a soki sai ki zubar da darajanki ta ya mace kamar yadda Khadija ta watsar da nata a wajen Hafiz.

******

Kaduna..

Yau yana gida bai je ko Office ba, da yammah ne dai ya shiga Ministry of Education,bai koma gida ba ahanya mangariba ta sameshi ya Umarci su Bama su tsaya yayi sallah tukunnah A wani masallaci dake anguwan Dosa sai da akayi isha"i dashi sannan ya fito suka tafi suna Hanya ya samu kiran Mujaheed kan in yana gida zai shigo suyi mganar daya fadamai yace yana Kan Hanya yanzu zai karisa Mujaheed yace to shikenan shima yanzu zai fito daga gida.

Kusan kamar tare suka iso domin atare suka shiga ,sukayi parking waje Daya Tim ne ya Budema ogansa Murfin Mota ya fito yana sanye cikin Manyan kaya yadi mai ruwan kasa shara shara domin har Farar vest dinsa ana gani kafarsa sanye Cikin Bakin Takalmi mai Rufi kansa ba hula Wayoyinsa Tim ya kwasomai yana tsaye a gefensa yana Jiran Mujaheed ya kariso wanda ke Dauke da wani katon Abu anyi Raffing dinsa sai kwando cike da Kololin abinci Tun kafin ya kariso Saifuddeen ke kallonsa yana mirmishi Cikin wani yanayi yace"Samun Adda as my Sister is a blessing a big blessing Allah nagode maka da kayi ni dan gata Addata.."

Mujaheed ya zabga masa harara yana Fadin"Kace is a blessing mana kasa matata tun safe bata zauna ba duk wannan uban aikin data sha ba Lada zata samu ba."

Saifudeen na karban kwadon Hannunsa yace"Karya kake yi..Ladan da zata samu sai yafi wanda zata samu in kai tayi mawa."

Sun jera suna tafiya zuwa Cikin gidan Tim na bin bayansu Dauke da wayoyin Saifudeeen,Mujaheed yace"Kace Allah na tuba domin kayi babban Zunubi.

Saifuddeen yayi mirmishi bai ce komai har suka shiga Falon gidan Kan karamin Center table din dake falon suka sauke kayan hannunsu Sannan suka samu kujera mai zaman mutum Biyu suka zauna Sai alokacin Saifudeen ya yi ma Tim mgana da Hannu ya iso gefensa ya sauke masa wayoyinsa saman Karamar kujeran dake gefensu,sannan ya juya ya fice.

Saifudden bai ko Jira Mujaheed ba ya fara Bude Cooler din Farko Ferfesun Nama ne yaji kamshin sai da ya Lumshe ido kafin yace"Allah ya baki Aljannah Addata.

Mujaheed ya amsa mai da Ameen sauran Cooler din kuma Tuwon shinkafa ne da miyar Gyada taji Kifi da Naman rago sai kanshin manshanu miyar ta alaiyahu ne,Saifuddeen yace"Addata tafi kowa sanin zabina bayan Uwata.."

Mujaheed yace"kuma bai hana in rashin mutimcinka ya tashi baka Ciresu aciki ba"

Yana jinsa bai basa amsa ba ya fara kokarin Bude wanda mujaheed ya Dauko yana fadin"Miye wannan kuma..?

Mujaheed yace"To ka bude mana bakauyen Lere.

Hararansa yayi kafin ya Yaye foul paper sai ga Cake da Donut da Cokiess mai yawa aciki da wata karamar Takarda ya Dauko ya duba Rubutun  Sadiya ne layi daya.

"Hamma na saboda na sanka da shan Tea.."

Haka kawai ta Rubuta farinciki ya kamasa ya murmusa fararan Hakoransa suka bayyana awaje a Fili ya Furta"Gaskiya da yanzu ne Man bazan baka auran Addata wai ai matar manya ce in ba gwamna ba ai sai sanata."

Mujaheed na Duba wayarsa yayi karamin Tsaki kafin yace"Yanzu ma baka makara ba sai ka raba auran ka aura mata gwamna tunda kune gwamnatin.

Saifuddeen ya fashe da Dariya Saboda ya kular da Mujaheed aiko ya kuli bai ma samu zarafin mgana ba Saifudeen yace"Kasan kuwa tsab in nace mishi ga Addata bazai ki karba ba Gwamna na Respecting di..!

Bai gama mgana ba Mujaheed ya sakarmai naushi a gadon baya Saifudden yayi kasake yana jin zafin Naushi mujaheed ya kallesa yana Huci kafin yace"Wlh in kara Danganta matata da wani kato sai na maka naushin da sai hakoranka na gaba sun watse..!

Saifudeen ya ware ido yana kallonsa ganin yadda yake Huci yasan ya harzuka kishi ya motsa kafadansa ya Dafa kafin yace"Cool down Man..!

Sauke Hannunsa yayi kamar ya doramai kashi yace"An ki ayi cool down din..!

Saifuddeen bai kara mgana ba ya kyalesa,ya tashi Dauke da Cake dinsa ya shige kitchen dinsa ya saka cikin karamin Fridge din dake kitchen din sannan ya Dawo kasa ya zauna ya Jawo kwando abincinsa ya Fara zubawa ko kara kallon mujaheed bai yi ba shima bai ta kansa ba sai faman sakin Huci yake yi,Wayarsa ce tayi kara Shi mujaheed din har ta katse bai Dauka ba sai da aka kara kira sannan ya Daga a fusace yana fadin"Menene wai..?

Sadiya Dagachan bangaran cikin mamaki tace"Sweety me ya faru..?

Baka samun Hamman bane..?

Cikin Tsawa yace"Bansani kada ki kara kirana.."

Daga haka ya katse wayar yana Huci,Saifudeen na jinsa bai Tanka ba mujaheed da kishi,shi nan kishi ne kan Sadiya kamar dariya zata tsinke masa,sai dai baiyi dariyan ba, ya kanne ya fara cin abincinsa hankalinsa kwance yaci da yawa saboda daman cikinsa akwai yunwa.

Yana gamawa ya kwashe Filet din yakai Kitchen da sauran abinci ya sanya afridge saboda kada ya Lalace..

Ya wanke hannunsa sannan ya Dawo Falon wannan karon sai ya sauya wajen zama ya samu kujera mai zaman mutum daya ya zauna ya Dauki Romot din dake wajen ya kunna Tv din yayi kamar bai san da zaman mujaheed a wajen ba yana jiran ya huce tukunnah

Shudewar mintina Ashirin Sannan Mujaheed ya saki karamin Tsaki kafin yace"Ammh kasan mgana nazo muyi ko..?

Saifudeeen yace"Eh ai ina ta jiranka tun dazu ka gama cikar da batsewar taka. Sai muyi mganar"

Mujaheeed yace"Zaka sani ne ka guji Ranar da zamu hada kashi dakai."

Saifuddeen yace"Bakomai ko ka dakeni bazan rama ba Naci girman kasan ba Kima aciki suruki ya daki surikinsa."

Mujaheed yace"Suruki nabi surukin da gudu namai sintir ba wando.

Saifudeeen ya zaro ido kafin yace"Ni kake nufin kayi ma sintir din.."

Mujaheed yace"Tabbas..!

Saifudeen yace"Allah ya shiryaka Mujaheed"

Ya amsa mai da Ameen Sannan sukayi Shuru na wani Lokaci kafin Mujaheed ya gyara zama yana Fadin"Daman nace mu zo nan ne saboda mganar tana da muhimmanci.."

Saifudeen dai bai ce komai ba Mujaheed ya cigaba da Fadin"Akan matsalan ka ne Saifudeeen tun ranar da kayi mganar su iya da Hashashensu akanka na fara Hango hakan anya kana ganin mganarsu ba kamshin gaskiya..?

Saifudeen bai kallesa ba hankalinsa na wajen Tv yana kallon Mbc3 suna Cartoon kamar wani yaro Mujaheed ya gaji da jiran mganarsa sai ya kara Bude murya yace"Ai kana jina ko..?

Saifuddeen ya kallesa kafin yace"Najika ina auna mganganunka ne da kuma amsan da zan baka.

Mujaheed ya tamke fuska kafin yace"Ok.!

Saifudeen ya dora kafa daya kan Daya kafin yace"Kana nufin kaima ka yarda da mganar cewa Aljana ta aure ni..?

Mujaheed yace"Ye of course in ba Aljanna ba ta yaya ka isa aure ga kudi ga kyau ga gwamnati ga asali ga Nasaba..Ko dai Aljana din ko kuma baka da lafiya wannan kuma bazan ce ba tunda ai banace mata basa burgeka ba ballatana na dora zargina anan.."

Saifudeen yayi shuru bai ce komai ba Mujaheed ya cigaba da fadin"Ka fadamin mtsalanka ni dan"uwanka ne kuma Amininka da baka da kamarsa ka sanar dani in kana da wani Laluran ne..?meke damunka..? Kana Mafarki ne ko jin wasu abubuwan da ba halinka bane..?

Saifudeeen yayi kamar bai ji ba gabansa na fadi na irin yadda Mujaheed ke neman gano abunda ya Dade da boyewa,wannan sirrinsa ne baya fatan wani yaji koda Ummi ce kuwa.

Sannan mganar Aljanah ta auresa bai yarda ba,Saboda shi baya yarda da wannan Chanfe chanfen sam,Koda Iya ta saka Baffa Hashimu ya kirssa tana kiramai jawabin abunda malamin da sukaje wajensa yace wai Aljana ce hatsabibiyace ta auresa in ba"a Dage ba shi da aure har Abada shi dai bai ce komai ba Sannan Iya ta matsamai sai da ya aika Bama ya karbo Mganguna suna bayan Booth tun sanda aka karbo masa ko kalan su bai gani ba,Sannan bayan haka akwai wani abu Dangane da mganar Mujaheed akan bai taba jin chanji Daga yanayinsa ba..?

Tabbas ya taba ji shekaru Takwas da suka gabata sanda yaje Standford University,akwai wata class mate dinsa Janet baturiya ce suna mutumci da ita har suka zama abokai watarana suna Dakin karatu ta kama bakinsa ta faramai kiss wani abu ne daya faru kamar kiftawan ido Ya mike jikinsa na rawa kansa ya juye ya shake janet Dakyar Dalibai suka ceceta sai da ta kwana asibitin makaranta shi kuma Ya kwashi Littafansa ya koma Inda yake zama Ranar har washegari kansa kamar ba nasa ba sannan lamarin da ya faru ba nasa bane wani Sabon Hali ne da bai sanshi ba yasan bai da Saurin hannu kuma domin Janet tamai kiss ai bai kai ya yi mata abunda yayi mata.

Washegari da yaje dubata tuni akace ta bar asibitin yaje gidan data ke zaune ya iske ta kwashe kayanta ta bar gidan sai daga baya ya samu Labarin ta tsorata da abunda yayi mata ta bar makaranta ta koma garinsu Daga wannan ranar ya rike abun a ransa duk da hakan bai kara Faruwa dashi koda yake daga wannan bai kara rike koda hannun wata macen da ba Muharraminsa ba.

Mujaheeed nata mgana bai ma jisa ba sai da ya taso gabansa ya Dafasa sannan ya dawo Hayyacinsa.

Ya kalli mujaheed da idonsa ya fara Kadawa jikinsa a sanyaye Mujaheed yace"Akwai damuwa ko..?fadamin naji Allah yasa,muna da hanyar warwareta."

Saifudeen yayi saurin kauda kai kafin yace"Mujaheed ka bar wannan mganar ni lafiyata Kalau..Mganar wannan wata aljana chanfi ne ni bazan hanaku yin tunaninku ba,Ammh ka sani ni am fine ba abunda ke Damuna.

Mujaheed na Nazarinsa yace"Kuma ka saki mata har biyu da aka Daura maka..?

Saifudeen ya mike yana Fadin"Bana son su ne kafini sanin bani nace ai ina so ba..Bazan iya zama dasu Allah ya kamani da laifin danne musu hakki ba."

Daga haka kawai ya shige bedroom dinshi ya bar Mujaheed sake da baki Yasan da wani abu domin bai yarda da Saifudeen ba daga mganarsa ya Fahimci akwai wani abu yasan sa da Zurfin ciki,bazai gayamai cikin Sauki ba.,bai matsa ma kansa ba ya juya ya Fice,ya hau motarsa ya fice Daga gidan,koda ya koma gida ya iske Sadiya Cikin Damuwa,bai wani Tsaya maata wata mgana ba ya dai lallasheta da tsawan da yayi mata ammh ita kanta ta tsorata da yanayin Damuwar da muhajeed ya kwana aciki Ta fara tunanin kodai Hamma ne wani abu ya sameshi..?

Sai dai da Safen bayan Mujaheed ya tafi wajen aiki Saifudeeen din ya kirata yana mata godiya sai hankalinta ya kwanta kad'an.

Na fada muku Salo biyu ne acikin wannan Labarin in salon waje ya fito in da sunan Muhibba ya fito ni zan jagoranci Labarin in kuma Salon ciki ya fito Muhibba zata karbi Ragamar labarin nata ne,Tafiya in tayi tafiya ita zata ja zaren ta har zuwa karshen Labarinta

Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar *** ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye *** mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke

Janafty

SAIFUDDEEN

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.