Free chapter · Read without an account
023
*KIRAN RABO.*
#Fitattubiyar2025
©️ *Nana Haleema.*
Wattpad@Nanahaleema
Arewabooks@nanahaleema11.
*Book 1*
*P 23.*
Jin dogon salatin da Nayla tayi Didi ta kalle ta da mamaki, Nayla tayi saurin cewa, "Kuma itama tana sonsa? Taɓ bata san waye shi bane." Jin abinda ta ce sai Didi tayi dariya ta ce, "wallahi tana son Omar matuƙa Nayla, har nan tazo ta zube min akan na saka baki Omar ya saurareta. Amma tsabar wulaƙanci irin nasa a gaban idanunta yake cewa in ma yaudarar sa tazo yi yafi ƙarfinta. Shi da ita ya ce mata shi bazai yi soyayya da ita ba kar ta sake gangancin furtawa, kuma fa ƴar manya mutane ce wallahi, mahaifinta shine Senator Kano central a yanzu. Omar yana yiwa mahaifinta aikin siyasa, kin san ƴan siyasa suna son irin su Omar a tafiyar su. To shine fa da zata zo Kano ya ce Omar ne zai dinga kaita duk inda zata je saboda ya yaba dashi, daga nan dai sai ta fara sonsa."
Nayla tana ji amma bata fahimtar me take cewa, tayi tsitt zuciyarta na bugawa a guje, sai goge ido take yi bata so hawayen da ya taru a ciki ya zubo. Didi ta cigaba da faɗin, "A hankali dai shima ya fara sonta, sonta ya fara dai ko ba so bane shi ya sani. Ban da hauka irin na Omar ina shi ina wannan yarinyar? To baya jin magana, ya ce min tunda ya ɗauki hanya bazai karkace ba, ni wallahi tsoro nake ji kar a cutar dashi.."
Nayla bata iya magana ba tayi shiru zuciyarta na bugawa sosai har zazzaɓi take ji yana neman rufe ta. Jin tayi shiru sai Didi ta ce, "ki daina tsoron sa don Allah, abinda ya yi miki da yanzu bazai miki ba."
Nayla tayi murmushin yaƙe ta ce, "ba tsoron sa nake ji ba Didi, kawai na tafi tunani da mamakin sa ne. Daman zai iya son wata mace? Lallai tayi sa'a ko wacece."
"Mtsww! Meye abin sa'a dan Omar yana son wata? Rashin sa a ne ma ai wata ta fara sonsa ni a wajena. Meye abin so a Omar don Allah?. Farar fata ko kyaun fuska? Allah dai ya shirya kawai."
Nayla tayi murmushi bata ce komai ba dan kanta ya yi mata nauyi sosai kwanciya take da buƙatar yi. Miƙewa tsaye tayi ta ce, "Didi bara na koma wajan Hajja." Did ta ce, "To Nayla. Na gode Allah ya bar zumunci. Zan aiko miki da mutuminki shinkafa da wake shi nake dafawa." Nayla tayi murmushi ta ce, "to Didi" ta faɗa tana fita kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki.
Tana fitowa tsakar gidan taji muryarsa ya yi ƙaramin tsaki ya ce, "to ni ƙaramin yaro ne da wani abun zai same ni a hanya? Lafiya naje gida." Nayla tana takowa inda yake tana jin zuciyarta na cigaba da bugawa dan ta san da budurwarsa yake waya. Tana zuwa kusa dashi ta ji ya ce, "kar ki dame ni" Sai ya yanke wayar amma kuma murmurshi yake yi.
Ya ɗago ido suka haɗa ido daidai lokacin da hawaye ya sakko daga idanun ta. Kallon ta yake yi da mamakin abinda ya saka ta kuka tunda yaga tana hawaye a wajan Didi. Da sauri tazo zata wuce doguwar rigar jikinta harɗe ta zata faɗi tayi saurin dafa bango bata faɗi ba, yana tsaye shi dai yana kallon ikon Allah dan kallon ta yake yi. Da sauri ta fice shi kuma ya yi tsaki ya ce, "tunda ba a nutse ki ke ba ai dole ki nemi faɗuwa, yarinyar ta cika rawar kai" ya faɗa yana shiga ɗaki.
Nayla a guje ta shiga falon Hajja ko kula Hajja da Salma bata yi ba ta wuce ɗaki a guje ta faɗa akan gado tana sakin kuka mai sauti. Hajja da Salma suna jiyo sautin kukan nata Hajja ta kalli Salma ta ce, "Salma wai me yake damun ƙawar ki ne?." Salma ta ce, "Wallahi Hajja ban sani ba, amma tun waccan tafiyar ta na lura tana cikin damuwa, dana tambaya sai ta ce babu komai."
Hajja ta ce, "ki duba har rama tayi fa, gaskiya tana cikin damuwa ya kamata ki tambayeta ki ji abinda yake damunta. Ko ki yiwa takwararta magana tunda ku biyu ne ƙawayen ta." Salma cikin damuwa ta ce, "to Hajja. Amma tabbas tana da damuwa, ki duba da farin ciki ta fita amma ta dawo a wannan yanayi. Gaskiya akwai abinda yake damunta sosai." Hajja ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba amma tana tunanin abinda ya damun jikar ta ta.
Nayla kuwa kuka take yi kamar ranta zai fita, in ta tuna Omar yana son wata mace sai taji sabon kuka da hawaye yana ambaliya daga idonta. Zuciyarta fara harbawa take yi kanta na juyawa, kanta ya yi nauyi haka ƙirjinta ma ya yi mata nauyi sosai.
Shikenan ita a haka zata gama rayuwa da dakon sonsa, tunda gashi yana da wacce yake so kuma har yana cewa zai je ya samu mahaifinta. Shikenan ta ta ta ƙare, sai dai ta mutu da sonsa ba tare da ya sani ba. Kalaman Didi take tunowa ta fara girgiza kai ta ce, "Ko da zan mutu ni bazan ce ina sonsa ba, bazan faɗawa Didi Ina sonsa ba, bazan faɗa ba" ta faɗa tana kuka sosai tana kwanciya a kan gadon jiki na rawa.
Sai da tayi kuka mai isarta sannan ta iya yin shiru ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan ta zauna tayi shiru tana salati. Wayarta ta ɗauko ta kira Baba Salisu da ya kawo ta ta shaida masa gobe yazo ya ɗauke ta fasa kaiwa ranar Sunday.
Salma ce ta shigo bayan ta gama wayar ta zauna kusa da ita ta ce, "Nayla a duniya a baki da ƙawaye masu baki shawara kamar ni da Twiny, ana kallon ki an san kina cikin damuwa, ki faɗa min abinda yake damunki."
Kallon Salma tayi jin ta ce Twiny sai ta ce, "Sayyadi...Driver Hajja, yana nan ya kai ku gidan Twiny?." Salma ta ce,"yana nan." Nayla ta miƙe ta yafa mayafin doguwar rigar ta ce, "na fasa kaiwa jibi a garin nan gobe zan koma Kaduna, muje ya kaimu ko zuwa anjima ne ma dawo." Tare suka fito suka faɗawa Hajja inda zasu je tayi musu a dawo lafoya suka fita.
Jidda tayi murnar ganin Nayla a gidan ta suka baje a falo dan sun saba da Salma sosai. Salma ta kalli Jidda ta ce, "Jidda wani abun da yana damun Twiny ki wallahi, nayi-nayi ta faɗa min taƙi faɗa. Tsabar damuwa wai Nayla ce take cewa ta fasa yin kwana biyu a Kano gobe zata koma Kaduna. Kowa ya ji wannan magana sai ya yi mamaki sai kuma ya tambaya meyasa." Twiny ta kalli Salma ta ce, "tun a Saudia muka yi maganar nan da ita, amma abin yawa yake sake yi yana bani mamaki" ta kalli Nayla ta ce, "Nayla don ki faɗa min waye wannan da ki ke so."
Salma ta ce, "wai zaman akan soyayya ne? Da yake bata faɗa min ba ta ce kawai mu zo nan." Jidda ta kalle ta ta ce, "akan soyayya ne Salma, wani take so shi bai ma san tana sonsa ba."
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Lallai Nayla tana cikin azaba mai tsanani." Jidda ta ce, "tayi addu'a a Saudia amma ta ce soyayyar bata raguwa sai ma sake sonsa da take yi, nace ta nemi zaɓin Allah in shine alkhairi Allah ya kawo silar da zai fara sonta shima. Amma sai tayi murmushi ta ce ko da yana sonta auren sa da ita da wahala ya yu."
Suka kalli Nayla a tare da take hawaye Salma a raunane ta ce, "Nayla waye wannan?." Nayla ta goge ido ta ce, "Sanin waye bashi da amfani, ku taya ni addu'a kawai Allah ya kawo min mafita. Twiny bani paracetamol kaina ciwo yake yi."
Ba musu ta tashi ta kawo mata haɗi da ruwa ta sha kafin Jidda ta ce, "amma faɗa mana zai iya sakawa ki ji sauƙi a zuciyarki, kin san babu wanda zai ji labarin daga bakin mu." Nayla tayi murmushi ta ce, "qaunar da zaku nuna min shine ku yi min addu'a."
Ganin ta dage taƙi faɗar waye sai suka ƙyaleta suna ta hira har ita, dan ta ɗan sake amma da ta tuna sai hawaye. Sai tara na dare suka baro gidan Twiny zuwa gidan Hajja. A nan Hajja take faɗa mata ga abinci Didi ta kawo mata kaɗam ta iya ci ta ajjiye ta kalli Hajja ta ce, "Hajja gobe zan koma Kano, na kira driver Abiy zai mayar dani gida."
Hajja ta kalle ta tace, "Hauwa'u an fasa kaiwa jibin?." Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Na fasa Hajja. Na tuna akwai abinda zan yi a gidan, kuma ranar ranar litinin Ina da aiki." Hajja ta ce, "To Hauwa'u Allah ya kiyaye hanya ya nuna mana goben, Allah ya yi miki maganin damuwarki." Ta amsa da amin daga nan bata sake cewa komai ba, Salma tana kallon Labarina ita kuma ta miƙe ta shiga cikin ɗaki.
Kamar yadda ta fada washe gari da ƙarfe goma na safe driver ya zo daga Kaduna, sai da ta bari ya huta ya ci abinci a wajan Hajja bayan sallar azahar suka ɗauki hanyar Kaduna.
Ko a can kasancewar babu wanda ya san da dawowata, da yake ta asabar ce Abiy yana gida shi da Yaya Ahmad tayi sallama a falon ta shiga. Yaya ya ce, "A'a, mutanen Kano." Murmushi tayi ta ƙaraso ta zube akan carpet ta ce, "Abiy ina yini."
"Lafiya lau Mamana, ya kika baro Hajja?."
"Lafiya lau, tana gaishe ka. Ga saƙo ta ce a baka." Ya karɓa yana cewa, "Hajja bata gajiya da hidima in dai aka je sai ta bayar? Na kuwa gobe sosai. Zan yi mata waya na yi godiya."
Da Yaya suka gaisa kafin ya ce, "mutanen kano, ba sai gobe zaki dawo ba daman?." Ta yatsine fuska ta ce, "Gajiya nayi kawai na kira Baba Salisu na ce ya zo ya taho dani yau." Ya yi dariya ya ce, "ikon Allah, zaman Kanon ne kuma ya ishe ki?." Tayi dariya kaɗan Abiy ya ce, "nima nayi mamaki, bata faɗa min ma zata taho ba, sai Salisu ne yake cemin ita zai ɗauko tayi amsa waya jiya, na ce to sai ka dawo. Gaskiya zan faɗawa Hajja taci tarar ki kin gudo kin barta."
Nayla tayi dariya ta miƙe ta shiga wajan Mama. Itama tayi mamakin ganin ta suka gaisa daga nan ta koma ɗakinta tana sauke ajiyar zuciya. Zaman Kano ai ba nata bane, indai tana son kanta da zaman lafiya dole ta bar shi.
Da daddare Mama ta shiga wajan Nayla ta same ta ta yi shiru ita kaɗai. Zama tayi kusa da ita ta ce, "Nayla." Nayla ta kalle ta ta ce, "Na'am Mama."
"Tunanin me ki ke yi haka?."
"Babu komai Mama."
"Haba Nayla, kowa ya ganki ya san kina cikin damuwa mai yawa. Meyasa baza ki faɗa min ba? Ko dan bani na haife ki ba?."
Nayla ta girgiza kai ta ce, "A'a Mama ba haka bane, babu damuwar ne shiyasa." Mama ta zo kusa da ita ta riƙe hannunta ta ce, "uwa nake a wajanki, na haife ki na yi jika dake Nayla. In baza ki iya faɗa min damuwar kiba wa zaki faɗawa? In baki furta min abinda yake damunki ba wa zaki fadawa?. Uwa ce fa ni, ko bani da maganin damuwarki in nayi miki addu'a Allah zai amsa." Nayla kalaman Mama suka karya mata zuciya ta fara share hawaye. Mama ta sake nutsuwa ta ce, "faɗa min Ina jinki."
Nayla ta ce, "Mama babu komai, in akwai zan fada miki bazan ɓoye ba." Mama tayi murmushi ta ce, "shikenan Nayla. Allah ya yi albarka, ki fito ki ci abinci" daga haka ta tashi ta fita tana tabbatarwa da kanta ƙarya Nayla tayi mata, amma zata tambayi Jidda dan ta san ita ta san dalilin damuwar Nayla.
••••••••
Washe gari Didi ta shiga gaishe da Hajja ta kuma yiwa Nayla sallama dan fita zata yi kar ta shiga bata nan tarar da Nayla ta tafi, tayi mamaki sosai Hajja ta bata labarin a yadda ta shigo gidan da yadda ta ce ita ta fasa zama. Didi ta ce, "Allah ya sa ba Omar ne ya tsorata ta ba, dan ke baki ji ajiyar zuciyar da tayi da ta ganshi ba. Ni wallahi tsoron nasa da take ji ya fara bani tsoro." Hajja ta dinga dariya tana faɗin ba wani tsoro kawai akwai abinda yake damunta ne.
*Abuja*
Kamar ko yaushe suna zaune gabaɗaya suna hira Narma ta kalli Dad ta ce, "Dad." Ya kalle ta ya ce, "Narma." Narma ta ce, "mun gama magana da Faruk ya ce zai zo ku gaisa." Sai kuwa Najwa ta ce, "Awwnn! Ki ce shima dai yanzu da gaske yana yi ko Sis?."
Aka yi dariya Dad da fara'a ya ce, "da gaske ki ke?." Ta ɗaga kai alamun da gaske kafin ta ce, "yana so ka bashi date da time ɗin da zai zo." Dad ya ce, "wow! wannan abin farin ciki ne sosai. Inda zai iya zuwa ranar Monday zan so hakan, zan kira minister mu zauna tare domin mu tarbe shi" sai kuma ya kalle ta ya ce, "Ko kuma ranar Monday da aiki?."
Narma ta ce, "Dad ko yaushe ne zai zo indai a kaina ne. Zan faɗa masa in ya amince ranar monday ɗin zai zo." Mum da take dariya ta ce, "oh my god! Narma....." Narma tayi dariya ta ce, "Mum I love him so much, my feelings for him are impossible to hide" ta faɗa tana murmushin sannan ta ce, "then he loves me too." Nabil yayan ta ya ce, "Ma sha Allah, muna taya ki murnar samun wanda ki ke so." Tayi murmushi ta ce, "thank you bro, let me go and call him" ta faɗa tana tashi ta shiga ciki a guje. Dad yayi dariya suna tattauna yadda za'a tarbi siriki in yazo.
Narma na shiga ɗaki Omar ta kira bai ɗauka ba, ta sake kira bai ɗauka ba sai ta ƙyale shi dan baya son tana tara masa kira. Wajan mintina kaɗan da kiran ya kira ta ta ɗauka da sauri ta saka a kunne sai ta ce, "kashe na kira ka."
Daga can ɓangaren Omar ya ji abinda ta ce ya maimaita a zuciyarsa, me take nufi kenan? bashi da kuɗin da zai iya kiran ta kenan sai dai ita ta kira shi?. Kafin tayi magana ya yanke wayar, Narma ta kira sau adadi yaƙi ɗauka.
Narma ta tayar da hankalinta ganin yaƙi ɗauka, ta je WhatsApp ta tara masa message tayi masa text message shima ba reply. Tun tana kiran sa har ta gaji ta kuma kasa gane laifin da tayi wanda ya saka ya yanke mata waya ya kuma ƙi ɗauka.
Shi kuwa Omar yayi haka ne dan ya koya mata hankali nan gaba bazata sake cewa ya kashe ta kira shi ba. Yana ganin message ɗinta da kiran yayi banza ko kallo bai yi ba dan ya yi alqawari bazai ɗauka ba, kuma bazai kira ta ba, zata san waye Tiger.
Sunday ta wuce, Monday ta wuce Omar baya ɗaukar wayarta kuma baya kiran ta. Narma hankalin ta ya tashi sosai sai ƙarya ta yiwa Dad ta ce ya ce ranar Monday baya nan. Sai ranar talata da yamma ya ga kiran na zuwa bai ɗauka ba sai da ta katse sai ya kira ta da hanzari ta ɗauka, tana sakawa a kunne ta ce, "laifin me nayi maka haka? Me nayi ka ke hukunta ni da wannan hukuncin Faruk?."
"Gobe in na kira ki sai ki sake cewa na kashe ki kira ni. Banda kin raina ni saboda kinga ina surarenki har ke zaki ce min wai na kashe ki kira ni? Nuna min ki ke yi bani da kuɗin da zan kira ki?." Jin yadda yake maganar da tsawa sai Narma ta ce, "I'm sorry...." Cikin tsawa ya katse ta ya ce, "kin manta gargaɗin da nayi miki ko?." Narma ta ce, "yi haƙuri, na saba da yin English ne ko yaushe shiyasa, Amma zan dinga kiyayewa. Kayi haƙuri don Allah."
"Mtsw! Faɗi matsalarki" ya faɗa kai tsaye yana sauraren ta.
"Ka yi haƙuri, nayi kewarka, kuma Ina sonka, Ina ƙaunarka." Sai ya ɗan sassauta murya ya ce, "Ina jin ki."
"Daman tun ranar asabar na faɗawa Dad maganar zuwan ka ya ce in kana dama kazo Monday...au litinin, shine na kira na sanar dakai a lokacin."
"Yanzu sai me?."
"In zaka iya zuwa gobe yana jiran zuwan ka."
Omar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "bazan zo gobe ba, amma zan zo ranar alhamis hakan ya yi?." Narma tayi murmushi ta ce, "Ya yi Faruk ɗina, na gode Allah ya barmu tare na haifa maka yara masu kama da kai." Samun kansa ya yi da murmushi mai sauti har taji murmushin nasa. Omar ya ce, "na faɗa miki ban shirya aure ba ko? Ban ma san yaushe zan yi ba."
Narma ta ce, "ai fata nayi mana ko?" Ta faɗa cikin shagwaɓa tana narkar da murya. Shagwaɓar da take yi yana ƙara masa karkasashi da yanayin da ya saba ji in suna waya. Jin ya yi shiru sai Narma ta ce, "baka ce amin ba, baka so na haifa maka yaran ne?." Murmushi ya sake yi har Narma tayi mamakinsa, dan ta san sai a gama waya dashi bai yi maganar kirki ba balle murmushi. Ya ce, "Ki jira lokaci."
"Alhamdu lillah! Faruk yana son ya auri Narma har ya haɗa jini da ita. Wannan abin farin ciki ne." Nan ma murmushi ya sake yi amma bai ce mata komai ba, tana ta yi masa zance shi kam baya tanka mata sai ya ga dama, sai da ya gaji ya ce, "Zamu yi magana anjima" daga haka ya yanke wayar yana shafa gajin fuskarsa yana murmushi. Ajiyar zuciya ya yi ya miƙe ya shiga wajan Didi da niyar faɗa mata zai je gidan sirikai.