Free chapter · Read without an account

15

by Kansa'u Bello · MATAR MANYA

💓MATAR MANYA💓

By

OUM FATIMA

GAJEREN LABARI

PAGE 15

BISMILLAHIRRAHAMANURRAHIM

Shiru nayi ina tunanin yanda zan yi rayuwa a ƙaton gidan da nake mafarkin samu tun yarinta, gashi dai yau Allah ya cika min burina amma na kasa jin abin irin yanda nake tunani. Tunda su Kairiyya suka wuce nake zaune a bakin gadon da aka aje ni ban motsa ba, tunani ne barkatai ke zuwa min babu kalar wanda ban yi ba ciki har da tunanin inda Suhail yake da halin da yake ciki.

Ko ya manta dani yana rayuwarsa ko kuwa har yanzu ina ransa oho, "Astagafurullah." Na furta a bayyane tanawar da nayi cewa ni matar wani ce a halin yanzu bai kamata in rinƙa tunanin wani da ban ba.

Ƙofar da aka murɗa aka buɗe ta ne yasa na ɗago na kai kallona don ganin mai shigowa duk da na san mai gidan kaɗai keda ikon shigowa a dai-dai wannan lokacin. Ai kuwa shi ɗinne ya shigo da sallama hannunsa riƙe da manyan laidoji bakin nan tamkar gonar auduga tsabar fara'a.

"Amarya ba kya laifi ko kin kashe ɗan masu gida." Ya faɗa lokacin da ya ƙaraso ya zauna kusa da ni yana buɗe mayafin dana rufe fuskata da shi.

"Sannu da zuwa." Na furta a hankali ba tare dana kalle shi ba.

"A kalle ni mana, ni wai kunyata kuma ake ji yau ɗin?." Ya faɗa cike da son yaga ta sake fuskar. Murmushi nayi na ɗago na kalle shi yace "Yauya to ko ke fa, yanzu dai na san kina jin yunwa don baki ci komai ba a wurin dinner, ga abinci na kawo maki sauko muje da kaina zan baki sai kin ƙoshi.

Duk da cewa kulawa ce ya nuna min amma dai naji abin bai wani ɗaɗa ni da ƙasa ba kamar yanda kulawar Suhail take yin matuƙar tasiri a gareni nake yin abinda yake so koda ban shiryawa hakan ba a ɗan zaman da muka yi da shi.

Saukowa nayi saboda alƙawarin da nayiwa kaina na yi masa biyayya tsakani da Allah domin samun aljannata da kuma gyara kuskurena na baya, daƙwalen kaji ne ya fitar a ɗaya daga cikin laidojin sai kuma ɗayar mai ɗauke da kayan fruit sai mai ɗauke da lemuka. Tashi nayi nace "Bari na ɗauko kayan amfanin, ina kiching ɗin yake?." Na faɗa ina kallonsa da jiran ya faɗa min.

Faɗa min inda yake yayi naje na ɗauko duk wani abinda za'a buƙata bayan na ƙara ɗauraye su.

Naman kajin ya riƙa yanka a plate ya miƙo min sannan ya zuba mana drink a cup, ni kuma na shiga yanka fruit ɗin dana wanko a kiching. Kun san mutuniyarku dai bata ganin kaza ta kauda ido, ban cuci kaina ba na ware naci kazar nan na ƙoshi kafin na ɗora da apple sai water melon kaɗan na sha drink saboda yunwa nake ji da gaske dan rabona da abinci tun wanda Aunty Zali ta bani da safe.

Fita Alhaji yayi zuwa É—akinsa don yin shirin bacci, ni kuma tashi nayi na tattare komai na gyara wurin kafin na shiga toilet don watsa ruwa, dama can ina da san wanka tamkar agwagwa, musamman yanzu da shower kawai zan sakarwa kaina ko in tara ruwa a bath tub in shige abina sak irin rayuwar da nake so duk da cewa burin nawa ya ragu yanzu da nayi hankali.

Wankana nayi bayan na gama taɓe-taɓen abubuwan amfanin da aka ƙawata toilet ɗin da su na ɗaura alwala na fito na shirya cikin doguwar rigar bacci nayi amfani da khumrata mai ƙanshi kafin na tada sallar isha'i da ban samu yiba nayi shafa'i da wuri kafin na haye gado na kwanta zuciyata cike da tunanin sabuwar rayuwar dana shigo yau. Ban jima da kwanciya ba Alhaji ya shigo ya kwanta a bayana, a dabarance na matsa ya sake bina yana faɗin "Meye haka sai kace wata ɓakuwar abin, haba ki saki jikinki." Ya faɗa yana ƙara matsata.

Cikin wani irin yanayi da nake ji na ɓacin rai tamkar kuma mai jin tsoro na buɗe baki da ƙyar nace "Alhaji bamu yi sallar godiya ga Allah ba wacce Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar damu."

Cikin zaƙuwar da yayi yace "Kina jiko, ki bari mun yi daga baya amma dai yanzu ki barni na samu natsuwa, kin san yanda nake ji a kanki kuwa tun wancan lokacin da muka haɗu?."

Bai ƙara bani damar magana ba ya shiga biyan buƙatarsa cikin zaƙuwa da rashin natsuwa.

Ba ƙaramar jigatuwa nayi ba a hannun Alhaji saboda bai tausaya min ba ko kaɗan, sannan daya gama ba wata kulawa dana samu daga gare shi ya tafiyarsa ɗakinsa ya kama bacci ya barni da tsamin jiki da gajiyar daya tara min ga ɓacin ran da nake ji haka kawai tamkar wacce ta aikata wani laifi.

Kuka nayi sosai na tausayin kaina don na lura cewa dalilin Alhaji na aurena kenan biyan buƙatarsa kawai bayan shi ba wata soyayyar gaskiya da zata sa ya tsaya ya bani kulawar data dace, da ƙyar na lallɓa na gyara kaina kafin na samu bacci ya ɗauke ni.

★ Washe gari da ƙyar na iya tashi na gasa jikina nayi wanka na fito, lallaɓawa nayi na gyara saman kafin na nufi ɗakin Alhaji na samu yayi ficewarsa ba tare daya duba halin da nake ciki ba. Ko break fast ba wanda ya kawo min tun ina zuba ido har naji yunwa zata kar ni na shiga kiching na dafa tea na ɗauki indomee na dafa na karya sannan na samu natsuwar tunanin wacce irin amaryace ni? Ina Alhaji ya tafi a washe garin kawo masa amarya? Anya kuwa akwai soyayya a wannan tsarin? Ko su manya haka suke rayuwa da iyalansu dama???.

Yinin ranar haka nayi shi ni kaɗai tamkar mayya ba Alhaji ba wani daga cikin danginsa, ƴan gidanmu ma ba wanda ya leƙoni sai dai in danna waya in na gaji in kwanta bacci. Da rana ma ni na shiga kiching na samawa kaina abinci haka ma da dare, da abin ya ishe ni kuka na saka nayi mai isata na haƙura ina tunawa da irin tattali da kulawar dana samu a wurin Suhail a ɗan zaman da nayi da shi duk da rashin kyautawar da nake masa, dama hausawa sunce baka taɓa sanin girman ni'imar da Allah yayi maka sai lokacin da ya jarabceka da rasata sannan, ita kuma dama in ka sake ta kuɓuce maka tana da wahalar sake dawo maka mai tsananin rabo ne yake sake samu a karo na biyu bayan yasha wuya.

Alhaji bai tashi dawowa gidan ba sai da dare har na kwanta bacci ya shigo, ina fara masa ƙorafin inda ya shiga ya dakatar dani. "Amma dai kin san yanayin harkokina ba zai yiwu inzo inyi ta zama a gida ba ko?."

"Amma dai ko ba komai zaka ɗan huta ko na kwana biyu ne ko tunda sabon aure kayi." Na faɗa ina ƙoƙarin danne ɗacin dake yunƙuro min.

"Kinga ya isa mu bar wannan maganar, yanzu dai kawo min abinci."

Har zan buÉ—e baki ince masa ba'a kawo min ba nima sai na fasa na tashi na shiga kiching É—in, jalop É—in spaghetti nayi da daren nayi amfani da saura naman kazar jiya. Sauran dana saka a plaks na É—auko na kawo masa da ruwa da lemo.

Zama ya gyara yaci abincin sosai yana tambayata "Haka kika iya girki ashe?." Murmushi kawai nayi masa bance komai ba.

Yauma Alhaji bai ɗaga min ƙafa ba haka ya moreni son ransa duk da irin roƙon dana masa akan warkewar da ban gama yi ba.

★ Washe gari ma haka ya shirya yayi tafiyarsa sai bayan ya fita ne direbansa ya kawo kayan miya da su nama da sauran kayan buƙata da zan nema aka zuba a kiching, lallaɓawa nayi na tashi naje na gyara kayan na adana komai a inda ya dace.

Ƙasa na sauka inga ko zan iya gyarawa don tunda nazo yau kwana biyu ban sauko ba sai yanzu, ina gama sauka ana ƙwan-ƙwasa ƙofar shigowa Palon don haka da sauri har ina tuntuɓe da kujera na nufi ƙofar na buɗe ba tare dana tsaya tambayar waye ba. Kairiyya na gani sai Zaituna da Raliya da Zeezah ƙawayena da muke unguwa ɗaya dasu, da farin ciki sosai muka rungume juna nida Kairiyya ina jin daɗin ganinta.

"Kunga kuzo mu koma mu tunda ba'a ganmu ba." Zaituna ta faɗa tana ƙoƙarin juyawa, da sauri na saki Bestie na riƙota ina faɗin "Haba dai ya zaki ce haka kin san in Bestie na wuri ita nake fara gani kafin kowa, maraba ku shigo." Na faɗa ina matsa musu duka shigo suna tsokanata irin na ƙawaye.

Ko zama ban yi ba aka ƙara buga ƙofar na juya da sauri na buɗe, Aunty Zali ce dasu Sagir suka kawo min kayan gara su dubulan da cin-cin da alkaki wanda Aunty ta ɗauki nauyin yinsu. Da gudu na rungume su suma ina murnar ganinsu daɗi kamar zai kashe ni yau ba zan yi yinin kaɗaici ba.

Haka muka yini cikin farin ciki ina ta jin daɗi, nida su Bestie muka shiga kiching muka dafa abinci mai rai da motsi muka haɗa drinks. Bayan munci mun ƙoshi suka taimaka min muka gyara gidan ko ina ya ɗau ƙamshi, Aunty daman bata zauna ba tana gama abinda ya kawota ta tafi bayan ta tambaye ni in babu wata matsala na tabbatar mata babu.

"Wai Bestie ina Mijinki? Tunda muka zo bai shigo ya duba ki ba, kuma banga ya kira ki a waya ba."

"Yana wurin aiki bai dawo bane shi yasa, waya kuma a airplane mode na sakata."

"Kin tabbata dai babu wata matsala ko?."

"Babu komai Bestie ki kwantar da hankalinki." Daga haka muka bar maganar saboda Zaituna data shigo É—akin tana cewa. "Kairiyya ya kamata muyi niyar wucewa tunda angon bai zo mun gaisa ba har magriba ta kusa."

"Haka kam ya kamata mu wuce." Kairiyya ta faɗa tana miƙewa.

"Haba dan Allah tun yanzu zaku tafi, ku bari kuyi sallar magriba mana." Na faÉ—a ina jin har na fara kewar su.

"A'a Bestie gara mu wuce sai wani lokacin kuma."

Kayan kwalliya na haÉ—a a cikin lefena na bawa su Zaituna banda Bestie da nata da banne zan kai mata, su dubulan na É—iba da yawa na haÉ—a musu da shi na basu na musu rakiya har bakin gate suka tafi suna ta godiya.

Haka na cinye satin amarcina cikin kaɗaici da rashin samun lokacin Alhaji da in na ganshi a gidan to dare ne yayi gari na wayewa zai kaɗa kai yayi tafiyarsa, har lokacin na kasa sabawa da zaman kaɗaici a ƙaton gidan daga ni sai mai gadi. Sai dai in kwanta in yi bacci in na gaji in sauko ƙasa in kunna kallo, in na girka abinci zan fita in miƙawa mai gadi da mai kula da farfajiyar gidan in bai tafi ba.

A sati ɗayan har wata ramar rashi kwanciyar hankali nayi, ga takurawar da Alhaji ke min kullum ba ɗaga ƙafa na rasa dawa zan tattauna abin. Bana so ace daga yin auren na fara ƙorafi don na san ba mai goya min baya hasali ma masu min Allah ya ƙara sun fi yawa kada ma Baba Mari ta samu labari don kullum jiran jin matsala ta ɓullo daga gare ni take.

Sai dai duk da haka zaman wuri ɗaya da sauyin abinci yasa fatata ta ƙara murjewa tayi kyau na ƙara haske, sai dai ƴar ramar da nayi. Muna waya da Mama da Aunty Zali har da Kairiyya da a kullum take ƙara min ƙwarin gwiwa da kwantar min da hankali na.

Ranar dana cika kwana bakwai zan fita girki kenan ina zaune a parlon ƙasa na gama abinda nake ina duba wayata ina kurɓar orange juice Dana ɗauko a cikin fridge aka ƙwan-ƙwasa ƙofa, mamaki ya ɗan kamani ganin tunda aka kawo ni bayan zuwan dasu Kairiyya suka yi da Aunty ba wanda ya ƙara zuwa. Alhaji baya dawowa da rana sai dare shi yasa na ɗan ji mamaki.

Tashi nayi naje na buɗe ƙofar na leƙa don ganin waye aka tureni da ƙarfi aka buɗe ƙofar, babbar Mace ce ƴar gayu da kana ganinta kasan tana hutawa don jikinta ya nuna hutu sosai. Sai ƴammata guda biyu a dama da hagunta da suke bina da wani wulaƙantaccen kallo tamkar sunga kashi.

"Wannan karon kuma wacce ƴar matsiyatan ce Abba ya kwaso mana?." Babbar yarinyar dake gefen damar matar wacce nake kyautata zaton Mahaifiyarsu ce ta faɗa tana wani yatsina fuska da bina da kallon raini. Wani ɓacin rai ne yazo min wuya jin abinda ta faɗa, kiran Alhaji da Abba da tayi ne ya tabbatar min cewa Matarsa da yaransa ne suka zo.

Ƙoƙarin buɗe baki nake in yi magana Uwar tace "Da alama dai wannan ƴar cikinsa ce ya ɗauko mana tsabar zubar da girma."

"Kema Umma asiri suke masa fa, kin san talakawan nan da shegen kwaɗayin tsiya, a haifesu a gidan jar ƙasa su gama girmansu a ciki suna cin miyar kuka, amma gidan Miji sai suce sai mai bene inda zasu ci jar miya su jira da lemu, basu damu ba su auri sa'an Babansu akan kwaɗayin abin duniya."

Gaba ɗaya magan-ganunta sun yi dai-dai da rayuwata don tamkar wacce ta san asalina haka ta zayyanosu, dalilin da yasa jikina yayi sanyi bakina yayi nauyi na kasa furta maganar da nayi niya da farko har suka ƙare rashin mutuncinsu suka tafi suka barni da sakakken baki. Har sunje bakin ƙofa uwar ta dawo tace "Kuma kar kiyi tunanin cewa zaki miƙe ƙafa ki rashe a gidan nan, tun wuri ki fara haɗa kayanki don auren biyan buƙata aka yi dake, da zarar amfaninki ya ƙare zaki ƙara gaba saboda babu ƴa Macen data isa ta haihu da Mijina, gadon da kukewa kwaɗayi yafi ƙarfin ko wace zalamammiyar, cin gadon Alhaji daga ni sai ƴa'ƴana."

Tana gama faÉ—ar haka ta wuce ta barni ina juya magan-ganunta a cikin raina da son war-ware ma'anarsu....

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.