Free chapter 路 Read without an account
Chapter 41-42
by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...
馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮
_WRITING BY AMANAR COOL_鉁嶏笍
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*
Page 41&42
___________Mama kuwa kuka take yi sosai, irin kukan nan mai ta蓳a zuciya, tunda Gwaggo ta ja Afnan ta fita da ita, gaba 蓷aya ta rasa me yake yi mata da蓷i. Baba ne ya shigo ya tarar da ita cikin wannan ya na yin.
Zama ya yi, ya rasa me zai ce mata, domin shima abin na damunsa a zuciyarsa.
Kallon Mama ya yi da ta ke kuka ba tare da ta kula shi ba, tabbas tunda har Amina ta kasa danne kukanta ya san wannan al'amarin ba 茩ara min ta蓳ata ya yi ba. Duk ha茩urin ta amma yau ita ce ke wannan kukan.
Ya na so ya bata ha茩uri amma ya kasa, gashi dai kukan na ta ba 茩aramin 蓳ata masa rai yake yi ba. Ganin ba daina kukan za ta yi ba, shi kuma ya na son bata ha茩uri amma kamar an 蓷aure masa baki ya kasa magana
Ya sa ya mi茩e ya bar mata 蓷akin.
茦ara fashewa tayi da kuka, ta ce "Ya Allah ka dube ni, Ubangiji ka shiga lamurrana da na 拼a,拼ana. Ya Allah ka kula mini da 拼ata. Allah kashiga lamarin ta, ka kare ta daga dukkan sharri na mutum da aljan".
Ta 茩are addu'ar ta na kuka ba na wasa ba.
Ikon Allah ne ya kai Haidar gida, da 茩yar ya fito da ga cikin napep 蓷in ya shiga gida, babu kowa a tsakar gidan Umma na 蓷aki, kai tsaye 蓷akinsa ya bu蓷e ya shiga kwanciyar rub da ciki ya yi, ba abin da ke yi masa yawo a idanuwansa sai fitowar da ya ga an yi da Afnan ta na kuka an sakata a mota, kenan da gaske an yi mata aure? Ji ya yi gaba 蓷aya dubiyar na juya masa, ya rasa inda zai saka ransa, ya ji sau茩i da ra蓷a蓷in da yake ji, 茩irjinsa zafi yake yi masa ba na wasa ba, zuciyasa na bugawa da 茩arfi, wata irin fitinaniyar soyayyar Afnan yake jin ta na barazanar tafiya da numfashinsa.
Umma jin motsi ya sa ta fitowa
茒akin Haidar ta gani a bu蓷e, da mamaki ta ke bin 蓷akin da kallo, ta na tunanin me ya dawo da shi gida a irin wannan lokacin, kuma bai nemeta ba.
茒akin ta nufa da sallama ta shiga, a kwance ta ganshi, ta da蓷e tsaye ta na 茩are masa kallo, da ta ga alamar bai ji shigowar ta ba, dan ko sallamar da ta yi bai amsa ba, ya ta ce
"Haidar"
Shiru bai amsa, kuma bai motsa ba.
Ta kuma ce wa
"Haidar" nan ma Shiru
茦arasawa tayi ta bubbugi 茩afan shi, ta ce
"Haidar" da 蓷an 茩arfi, sai a lokacin ya motsa da 茩yar.
A hankali ya juyo, tare da bu蓷e idon shi ya sauke su akan Umma da ta tsare shi da ido, ta na nazarinsa.
"Haidar lafiya ka ke kuwa? Me yake damunka na ga ka dawo gida yanzu? Bayan ba lokacin dawowarka ba ne".
Haidar ya furzar da iska mai zafi sannan ya ce "Umma ba na jin da蓷i ne"
"Ashsha subhanallah, me yake damunka? Kuma shi ne zaka shigo baka neme ni ba?"
"Ki yi ha茩uri Umma ba na son 蓷aga miki hankali ne".
"To kasha magani ne?"
"Eh nasha shi ya sa na dawo gida na 蓷an kwanta ko zan samu yin bacci". Da ido kawai Umma ke binsa. Ta mugun tausayin 蓷an na ta, ta na son yin magana da shi amma ganin ba shi da lafiya yasa ta 茩yale shi. Ta ce "To Allah ya baka lafiya, ka samu ka yi bacci 蓷in, in sha Allah ciwon kan zai ragu". Tashi tayi ta fita, ta na fita Haidar ya sauke a jiyar zuciya. "Ya Allah kai ka saka mini son wannan yarinyar a zuciyata, Ubangiji ka kawo mini sau茩i da salama, Allah ka kawo mini mafita.
Sai bayan la'asar motar su Afnan ta isa, a 茩ofar gidan mai gari ta tsaya. Har lokacin Afnan ba ta daina zubar da hawaye ba.
Kawu Sanusi ya fara fitowa, ya na gaisawa da mutanen da ke gurin.
Sauran matan fitowa suka yi, Aunty Murja ta ja hannun suka nufi cikin gidan, da murna aka tarbesu, kai tsaye 蓷akin Asabe uwar gidan mai gari aka wuce da Afnan. Saura matan kuwa shimfi蓷a a ka yi musu, sannan aka a jiye musu abinci shinkafa da wake, aka ha蓷o musu da fura tasha nono.
Aka zubawa direba shima aka kai masa
Afnan ma an kai mata na ta, sai dai ko kallon shi ba ta yi ba, daga 茩arshe ma tura fuskarta tayi cikin hijabi ta ci gaba da kuka.
Kawu Sanusi ko fada ya wuce ya gaisheda mai gari, suka gaisa da sauran jama'ar wurin
Mai gari ya ce "Sanusi ya hanya? Sannuku da 茩o茩ari kun sha tafiya, ita amaryar tawa an shiga da ita cikin gida? Ko da yake mijinta ya yi mini 茩wace" ya yi maganar ya na murmushi
Kawu ya yi dariya ya ce "Eh an shiga da ita ciki"
Mai gari ya ce "To ma sha Allah, Allah ya sanya alkhairi a cikin wannan auren, ya kauda fita, sarkin fada ga amana nan an kawo muku Allah ya taya ku ri茩o, za ta zauna a gidana zuwa jibi in kun kammala gyaran sai ta tare a 蓷akin ta".
Da Amin aka amsa, sarkin fada ya 茩ara yi wa kawu godiya
Sannan mai gari ya tashi domin shiga cikin gida su gaisa da mutanen. Shiga ya yi suka gaisa cikin girmamawa.
Ya ce "Ina amaryar tawa ne?"
Asabe ta ce "Ta na 蓷akina".
Ya ce "To shikenan bari na 茩yaleta yanzu zuwa anjima ma gaisa".
Kawu Sanusi ya ce idan sun kammala su tashi kar dare ya yi musu a hanya.
Aunty Murja da Bilki suka shiga 蓷akin da Afnan take, nan suka tarar da Maryam da ita suna kuka, zama suka yi suna rarrashinta tare da ba ta ha茩uri, Aunty Murja ta ce "Afnan ki yi ha茩uri, ki ci gaba da addu'a in sha Allah za ki ji da蓷in ha茩urin da ki ka yi, ki rungume mijinki, ki yi masa biyayya, domin aljannarki ta na 茩ar茩ashin 茩afarsa, ina son ki rungume 茩addararki Afnan, haka Allah ya 茩addara auren ki zai kasance, dan Allah ka da ki saka damuwa a ranki, gudun jawowa kanki wata matsalar, ki zauna da kowa lafiya, ki yi wa iyayen mijinki biyayya, sannan ka da ki wala茩anta danginki na nan".
Kuka sosai Afnan ke yi kamar ranta zai fita, ha茩uri ina Bilki ta cigaba da bata, sannan suka ce Maryam ta tashi su wuce ana jiransu, jin hakan ya 茩ara 蓷aga hankalin Afnan ta rirri茩e Maryam ta na kuka
Asabe ta shigo 蓷akin ta ce "Wai ku fito ana jiranku, sauran matan har sun fita waje"
Aunty Murja ta ce "To shikenan mun tsaya bata ha茩uri ne, gata nan sai ku cigaba da bata ha茩uri da rarrashinta, sannan idan aka ji tayi ba dai-dai ba dan Allah ku tsawatar mata".
Asabe ta ce "In sha Allah zamu yi iya 茩o茩arin mu".
Mi茩ewa suka za su fita Afnan ta mi茩e ita ma
Kallonta suka yi Bilki ta ce "Ina kuma za ki je Afnan?"
Cikin kuka ta ce "Biyar ku zan yi Inna, dan Allah ku koma da ni". Tayi maganar ta na ci gaba da kuka.
"Haba Afnan ina kuma aka ta蓳a yin haka? Ki dai yi ha茩uri, in sha Allah nan da kwana biyu zamu dawo".
茦ememe Afnan ta ce ba za zauna ba, sai da aka kira kawu Sanusi ya ce su wuce, dan ubanta ko 茩ofar 蓷akin nan ta 茩araso sai ya sa蓳a mata.
Ri茩e Maryam tayi ta na kuka sosai ta ce "Dan Allah Maryam ke kar ki ta fi ki bar ni".
Maryam ma ri茩e ta tayi ta ce ba inda za ta je ta bar ta, takaici ne yasa kawu ya ce "Ku zo mutafi idan ta iya ita ma ta tabbata a nan 蓷in".
Ba yadda ba a yi da Maryam amma ta ce ba za bisu ba, mai gari ya ce "Su yi tafiyar su zuwa gobe ko jibi dai-dai sun samu nutsuwa sai ta koma, haka aka yi su kawu suka kama hanyar komawa gida.
Afnan ganin Maryam a kusa da ita ya 蓷an kwantar mata da hankali, ta 蓷an saki jiki har suka samu cin abinci.
*********
Gaba 蓷aya Mudan ya rasa suku ni a zuciyarsa, soyayyar Hasina ce tayi masa babakere a zuciya, baya ganin kowace mace face ita, komai yake yi tunanin ta ne a zuciyarsa, ge 蓷aya ga fitanar Huda kullun da sabuwar fitana da tijarar da take zo masa da ita, ya rasa yadda zai da ita, gashi ya na kokwanto akan cikin da take i茩irarin ta na da shi, shi fa baya jin idan ma gaskiya ne ta na 蓷auke da cikin ya kasance nasa ne. Dan baya jin iya shi ka蓷ai take bi.
Tashi ya yi ya shiga toilet wanka ya yi a gurguje, ya shirya, makullin motar shi ya 蓷auka ya fito, in da motar shi take ya nufa, ya ja ya bar gidan. Kai tsaye gidan Turai ya nufa.
Turai na zaune a falo, ita da wata dillaliya, sai Hasina dake saman kujera ta 蓷ora 茩afa 蓷aya kan 蓷aya ta na taunar cingam.
Mudan ya yi sallama ya tare da afkowa cikin falon kamar wanda aka je ho.
Turai ta ce "A'a Mudan yau kaine a gidan namu babu sanarwa?"
"Eh Momy ni ne, fatan na same ku lafiya?".
Ya yi maganar ya na 茩uwara Hasina ido, da tayi kamar ba ta ganshi ba. Alhalin hankalinta na kansa kawai mazewa ne tayi.
"To ma sha Allah, ka ce yau zumuncin ne ya motsa? To ya ka baro mini Mamin taku da Huda fatan su na lafiya?"
"Lafiya 茩alau suke, sunce ma a gaisheki".
Murmushi Turai tayi jin abin da Mudan ya ce, ta sallami dillaliya sannan ta dubi Hasina ta ce
"Ke Hasina baki ga yayankin ba ne? Na ga ba ki gaishe shi ba".
Sai a lokacin ta 蓷ago ta dube ta ce
"Barka da wannan lokacin Ya Mudan"
"Yawwa 茩anwata barka ya ki ke?"
"Alhamdulillah" ta bashi amsa .
Turai ta kuma cewa "To ki kawowa Yayan na ki ruwa mana"
Mi茩ewa tayi ta je ta 蓷akko masa ruwa da kofi sannan ta zuba mishi ta mi茩a masa.
Kar蓳a ya yi ya sha ruwan ka蓷an
Turai "Mudan jira ni zan 蓷an shiga ciki".
"To Momy ba damuwa, sai kin fito". Tashi tayi ta bar falon ta shige bedroom 蓷in ta. Ya maida dubansa ga Hasina ya ce "茦anwata hutawa 蓷ai ake yi?".
"Eh" ta bashi amsa ta na 蓷an basarwa
茦are mata kallo ya yi ya ce "茦anwata wai ko na yi miki wani laifi ne? Ina magana ana amsa mini sama sama". "A'a, ni kuwa me za ka yi mini kai da ba guri 蓷aya muke ba". "To ai na ga ina magana ne ana basarwa".
"No ba komai kar ka damu, ya Huda?"
"Ta na nan 茩alau".
"Ok"
Mudan ya yi gyaran murya ya ce "Hasina wurinki fa na zo"
"Wurina kuma? To Allah yasa ba wani laifin na yi ba?"
"Ina ai ke ba kya laifi, komai ki ka yi dai-dai ne, Hasina magana nake so muyi mai muhimmanci, wato a gaskiya ba zan tsaya yi miki 蓳oyon komai ba, sonki nake yi, kuma so na aure".
Da sauri ta kalle shi ta ce "So kuma ni 蓷in?"
"Eh mana ko akwai haramcin auren mu ne?"
"A'a ko 蓷aya kawai dai ina mamaki ne"
"Me yasa za ki yi mamaki dan na ce ina sonki da aure?".
"No ba komai". "To shikenan Hasina ba na son 蓳ata lokaci ko jan aji irin wanda ku ke yi idan an ce ana sonku, amsa nake bu茩ata, shin ki na ga za ki iya aurena?"
"To ka bani nan da kwana biyu zan yi shawara". Mudan na son musa mata amma ya kasa yi mata musun, ya ce "To shikenan, ina jiranki" suka yi musayar lambar, har zai wuce ta ce ya bari ta kira masa Momy suyi sallama. Kafin ya tafi, ya amsa mata da "To".
Ta mi茩e ta kira masa Turai suka yi sallama sannan ya bar gidan.
*********
Sai bayan isha su Bilki suka isa gida kowa a gajiye yake, Gwaggo da ta samu labarin Maryam na can ba ta dawa ba, masifa ta shiga yi, ta in da ta shi ba ta nan take fita ba, ta ce dan kawai dare ya yi da sai ta je ta dawo da ita. Mama kuwa da ta samu labarin Maryam na can kasa magana tayi sannan kuma ta 蓷an ji da蓷in zaman Maryam 蓷in ko ba komai Afnan za ta ji sanyi idan ta ga 拼ar uwarta a kusa da ita.
Da dare mai gari ya shigo gidan ya na fa蓷in "Ina amaryar take ne, ta so ga angonki nan ya zo zai duba ki"
Gaban Afnan ya buga da 茩arfi jin an ambaci angonta, ka sa tashi tayi, sai da mai gari ya sake magana sannan ta mi茩e a hankali tayi waje.
_A yi ha茩uri da in da aka ga typing errors_
Amanar cool ce 鉁嶏笍
***