Free chapter 路 Read without an account

Chapter 53-54

by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...

馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮



_WRITING BY AMANAR COOL_鉁嶏笍



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



Page 53&54



__________"A'isha ke da ki ka ce mini sai gobe za ki zo, sai kuma na ganki yanzu? me ya sa za ki yi tafiyar dare? Bayan kin san hanyar tamu wani lokacin ba ta cika lafiya ba".

"Ka yi ha茩uri Yaya ba na son kowa ya san na shigo garin nan, shi ya sa ban sanar da kai cewar yau zan zo ba".

"Kamar ya ba kya son kowa ya san kin shigo? A'isha gidan ne ba za ki je ba? Ke yanzu za ki iya shigowa garin nan ba ke je gida kun gaisa da sauran 拼an uwa ba? Wai ke me yasa abu baya wuce wa ne a gurinki?".

Shiru ta yi ta kasa magana, ba ta son tuna abin da ya faru ko ka 蓷an, haka kuma ba ta jin za ta iya zuwa gidan nasu.

Atika ta shinfi蓷a mata tabarma ta ce "Zo ki zauna kin yi tsaye, sai ka ce ba茩uwa".

Zama ta yi Atika ta kawo mata abinci, sai da ta fara yin sallolin da ake binta kafin ta ci abinci. Bayan ta kammala ne Atika ta ce "Sai mu je ki ga surukar tamu, yau ma ba ta jin da蓷i".

Umma ta ce "Ashsha Allah ya ba ta lafiya" 

Tashi suka yi Atika ta yi wa Umma jagora da sallama suka shiga 茩ofar, Afnan na 蓷aki a zaune ta takure guri 蓷aya, ta ji muryar Atika na sallama, fitowa ta yi tana amsa sallamar ganinta tare da ba茩uwa ya sa Afnan ta du茩a har 茩asa ta gaishesu. Duk da ya na dare na, amma hakan bai hana Umma hango natsuwar da ke tattare da yarinyar ba, nan take ta ji tana mugun son yarinyar, kuma ta yi farin cikin kasancewarta suruka a gareta.

Amsa mata gaisuwar suka yi, sannan ta mi茩e ta 蓷auko tabarma ta shinfi蓷a musu a barandar gurin, zama suka yi. Atika ta ce wa Afnan "A'isha ga surukarki nan ta zo duba ki, mahaifiyar mijinki, ba a nan garin take ba".

Afnan ta yi 茩uri da ido tana kallon Umma duk da ba ta ganin fuskarta sosai, tunani take dama ita wannan matar ba ita ce ta haife shi ba? Ikon Allah, to ita wannan daga ina ta zo kuma?.

"A'isha ya na ji kin yi shiru?" Atika ta yi maganar. 

"Babu komai Inna".

Sannan ta mai da dubanta ga Umma ta ce "Barka da zuwa Umma ya hanya?". Haka kawai Afnan ta ji bakin ta ya kama sunan Umma, shi ne ta kira ta da shi.


Umma ta ce "Lafiya 茩alau Alhamdulillah, fatan mun same ku lafiya? Ya ki ke? ya ba茩unta?".

Afnan ta ce "Alhamdulillah". 

Atika ta kuma cewa "A'isha dama ta zo duba ki ne, kuma tana son idan za ta koma ku wuce tare can in da take, saboda an 蓷an samu matsala ne, rashin isowar mijin na ki, ashe juyawa ya yi ya koma can gida, shi ya sa bai 茩araso ba, kuma yanzu bashi da lafiya, to kin ga bai da ce ki ci gaba da zama a nan ke ka 蓷ai ba, gara ki na kusa da shi".


Afnan ta ce "To shikenan Inna, Allah ya bashi lafiya".

Da amin Atika ta amsa

Umma ta ce "Ashe dai takwara ta ce? To ni da wane suna zan kira ki?" Ta yi maganar ta na murshishi. 


Sunkuyar da kai ta yi, ta ce "A gida Afnan a ke kirana da shi".

Umma ta ce "To shikenan ni ma Afnan 蓷in zance. Yawwa sannan ki shirya saboda gobe nake so mu yi sammakon tafiya".

Afnan ta amsa da "To".


Atika ta ce "Gobe kuma A'isha? Nazata sai jibi". 

Umma ta ce "A'a goben dai zan wuce".


Tashi suka yi tare da yi mata sallama. Afnan ji ta yi kamar ta ce wa Umma ta zauna su kwana tare.

Ba yadda sarkin fada bai yi da ita ba a kan ta bari har jibi ta koma, amma ta 茩i, kuma ta 茩i yarda da batun zuwa gidansu ta gaishesu, dole ya ha茩ura ya 茩yaleta, 蓷akin da ke kusa da na Atika Umma ta kwanta. Bacci ya kasa 蓷aukarta, tunanin rayuwarta ta baya take yi, da irin abubuwan da suka faru da ita a wannan garin. A hankali ta ji 茩walla na zubuwa da ga idonta, ta sa hannu ta goge. Duk yadda Umma ta so ta rintsa amma bacci ya gagareta, kiran sallan farko a kan kunnenta. 

Tana idar da sallan asuba ta fito a lokacin Yayanta bai dawo da ga masallaci ba, ta yi wa Atika ina kwana tare da tambayarta ko Yaya ya dawo masallaci? 

Atika ta ce "A'a bai dawo ba, amma A'isha tun yanzu za ki tafi sai ka ce wadda a ke kora? Ai ya kamata ki bari ku karya mana".

Dan babu yadda za ta yi ne ya sa ta tsayawa ta karya, Atika ganin tana son wucewarta ne ya sa ta 蓷ora abin karin, ko da gari ya yi haske sun karya har Afnan 蓷in. Umma ta ce ba sai Afnan ta 蓷auki komai na kayanta ba, iya kayan sakawanta za ta 蓷auka. Sarkin fada ya so Umma su biya ta gidan mai gari Afnan ta yi musu sallama amma Umma ta 茩i wai ita ba ta son kowa ya ganta ne. Haka suka yi musu sallama suka ta fi.

Afnan sai tunanin take ina kuma za ta koma da zama? Yanzu idan Maryam ta zo ba ta ganta ba fa? Shiru ta yi tana nazarin rayuwa.


Bayan gari ya 茩arayin haske, mai gari ya kira Sanusi gaisawa suka yi, sannan ya nemi da ya kaiwa Gwaggo wayar, tana zaune Sanusi ya kawo mata wayar, ta amsa tana fa蓷in "Ummaru ne ko? Ai wallahi saina shiga 茩afar wando 蓷aya da kai...." Ba ta 茩arasa maganar ba ta ji mai gari ya ce "To uwar fitana bashi ba ne, wai ke Halima a rayuwa idan ba fitana ki ka yi ba kya jin da蓷i? Kuma ki rasa wa拼anda za ki uzzurawa sai 拼a,拼anki? Wannan wace irin rayuwace? Ai koma dai masifar za ki yi masa kya bari ku gaisa". 

Gwaggo ta ce "Ka bari kawai Yaya yaran ne da abin haushi, ina kwana dai, ya mutan gida?".

Bai amsa gaisuwarta ba, ya ce "Ba wani abin haushi, yara na yi miki biyayya amma ba kya gani, wannan dai ba hali ba ne ki canza". Nan ya shiga yi mata fa蓷a ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, sai da ya yi mai isarsa sannan ya 茩yaleta.

Gwaggo ta ce "Allah ya ba ka ha茩uri, in sha Allah za a gyara".

Ya ce "Da dai ya fi miki, dama ina son fa蓷a miki cewar A'isha surukarta ta zo ta tafi da ita can in da take da zama a yau 蓷in nan, saboda mijin na ta a can yake zama kuma baya jin da蓷i ne".

Gwaggo ba ta tsaya jin ba'a sin komai ba, ko tambayar wane gari ne uwar tashi take ba? ta ce "To Allah ya basu zaman lafiya. Duk in da za su je da ita, su je, ai yanzu nauyinta a kansu yake".


Shi ma bai tsaya yi mata bayanin komai ba suka yi sallama. Mi茩awa Sanusi wayar ta yi, tare da fa蓷a mishi abin da mai gari ya ce. Sannan ta mi茩e ta nufin 蓳angarensu Mama, dama tana da haushin Maryam ta dawo jiya ba wanda ya bi ta kanta, kuma ta san dole ne sai ta zo da tsaraba, amma a ka hana ta.


Maryam na zaune kusa da Mama suna karyawa, Baba na 蓷aki, Gwaggo ta shigo musu kamar an hanka蓷ota, gaisheta Mama ta yi. Maryam ko ta yi kamar ba ta ganta ba.

Wani banzan kallo Gwaggo ta yi wa Mama sannan ta ce "Ki ri茩e gaisuwarki ba na bu茩ata, ai ni ban kai matsayin da za ki gaisheni ba, kuma ba ni da darajar da za ku zo har 茩ofata ku gaishe ni ke da waccan 蓷ayar marar kunya, wallahi duk Hajara ta fi ku hali. Sanusi ya yi sa'ar mace ta gari. 茒an ladi da Ummaru kam ina ro茩on Allah ka da ya 蓷auki raina ba tare da na ga sun a jiye mata na gari ba. Yanzu saboda an 蓷auke ne banza, an mai da ni ba kowa ba, har wannan marar kunyar ta dawo ban sani ba? Kuma na san ba za ta zo haka hannu rabbana ba, dole za ta zo da wani abin, amma da yake ke ce uwarta ke ki ka haifeta, ke ka 蓷ai ki ka 茩wamushe kayanki ba bu wanda ki ka ba wa a gidan nan. To ki ci, idan ma kin ci iya wannan ne, dan wadda za a ri茩a fakewa dominta a ce za a je 茩auyen ita ma yanzu ba a nan za ta zauna ba, uwar mijinta ta zo ta tafi da ita can garin da suke da zama, in ya so yanzu sai muga ta tsiya".

Tunda Gwaggo ta fara magana babu wanda ya kulata sai yanzu da ta ce Afnan ba ta nan. Suka 蓷ago da sauri suna kallonta.

Maryam ta ce "Aunty Afnan 蓷in ce ba ta nan? Jiya na baro mata a gidanta yanzu ki ce ba ta nan, hmmmm".


Gwaggo ta ce "Rufe mini baki mara kunyar banza, ko uwarki gata nan zaune na fi 茩arfin na yi mata 茩arya balle ke, shashasha". 

Murgu蓷a mata baki Maryam ta yi tana hautsinarta, nan fa Gwaggo ta ce ina wuta ta saka Maryam a ciki, ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, sai da ta yi musu tatasss sannan ta bar gurin.

Abin da ya sa Maryam ta yi wa Gwaggo shiru sannin cewar Baba na 蓷aki kwance, da wallahi sai ta yi mata rashin kunya da ma kwana biyu tana 蓷aga mata 茩afa. Baba kuwa na jinsu amma ya yi shiru kamar baya nan.

Mama ba 茩aramin tashi hankalinta ya yi ba, ta san tunda Gwaggo ta fa蓷a to tabbas haka ne, yanzu shikenan ba ta san wace uwa duniyar 拼arta take ba. Duban Maryam ta yi ta ce "Maryam da gaske Afnan ba ta nan? Yanzu ba mu san in da take ba kenan?".

"Mama kar ki damu, in sha Allah duk in da ta je za ta nememu". Maryam ta yi maganar.


Shiru Mama ta yi, ta kasa magana, ita ka蓷ai ta san me take ji a zuciyarta.

Kawu Sanusi ko ya na zuwa ya gaya wa Hajara abin da ke faruwa, wani irin da蓷i ta ji, ta san ko iya haka Amina za ta yi ba茩in ciki na rashin sanin in da 拼arta za ta zauna, nan take ta ji Allah ya kawo mata sau茩i, ba ma sai ta yi wahalar kashe kudinta ba, wurin koma wa wajan Malam ba. 


********

Turai kuwa iya 茩uluwa ta 茩ulu da abin da Mami ta yi mata, sannan ta 蓷auke alwashin sai Mami ta yi nadamar da ba ta ta蓳a yi ba a rayuwarta. 

Ta sake kiran Malamin ta ce "Ya 茩ara uzzurawa zuciyar Mudan da soyayyar Hasina, a rufe masa idanuwansa da ga ganin kowa sai ita, hatta Mahaifiyarsa, kar ya saurara". Mugunta kala kala ta shiryawa Mami.

Mami kuwa hankalinta ya fara tashi da rashin lafiyar da Huda ke yi, gashi 茩ememe ta ce ba za a kaita asibiti ba, kuma ba ta so a kira likita ya zo ya duba ta, ta rame sosai ta yi haske, ga ba茩in cikin abin da Mudan ya yi mata na damunta ga wannan ciwon da Huda ke yi.

Sannan a gefe 蓷aya tana cikin farin ciki na jin cewar Hajiya Maimunata na nan tafe, ta san ko ba komai Zainab za ta sha hantara da wula茩anci.

******

Misalin sha 蓷aya da rabi, Haidar na zaune ya gama cin abinci Faruk ya shigo 蓷akin ya ce "Abokina har yanzu fa 茩ofar gidan nan a rufe take, an ya duk in da Umma ta je tafiyar ba ta da ala茩a da wannan 蓷an uwan nata da ka ce? Tunda a yadda na yi maka misalin kamanninsa ka ce shi ne wanda ya ha蓷a auren nan".

Haidar ya ce "Ni ma na fara tunanin hakan, amma dai ya na da matu茩ar wahala a ce Umma za ta bisa zuwa 茩yauyen nan, sai dai ko wani abin da ban, Faruk hankalina ya tashi fa, ashe kamar na san wani abu zai faru jiya na ce ka je, ka yi baddasau ka duba halin da take ciki".

Faruk ya ce "Ni ma dai hankalina ya tashi, dan jiya a fusace na ga ya shiga gidan, amma ko da ya fito kuma sai na ga fuskarsa a sake, sai dai abin tambayar ba lokaci 蓷aya suka fito ba, da na tambayi mai shagon nan dake kusa da 茩ofar gidan ya tabbatar mini da yamma Umma ta fita, da ga gidan".

Haidar ya ce "To ina Umma ta je? Ka ga Faruk saka lambarta a wayarka sai ka kirata, mu ji".

Kar蓳ar lambar Umma ya yi ya saka a wayarsa, ya kira bugu biyu Umma ta 蓷auka ganin ba茩uwar lamba ce, tana 蓷auka ta ji muryar Faruk ya na fa蓷in "Umma ina kwana".

Dakewa Umma ta yi ta ce "Lafiya 茩alau Alhamdulillah Faruk ya a ka yi na jiku shiru kwana biyu kun 蓷aga mini hankali? Ya mai jikin? Da sau茩i". 


Faruk ya ce "Umma ki yi ha茩uri don Allah garin ne babu newtork, ko da muka je sai Malamin ya ce sai mun 蓷an zauna zuwa nan da kwana hu蓷u daidai ya ha蓷a maganin sai mu tafi da shi, da yake garin da nisa, mu ma duk hankalinmu a tashe yake, sai yanzu muka 蓷an samu newtork 蓷in ya dawo, shi ne na ce bari na kira ki dan hankalinki ya kwanta".

Umma ta ce "Allah sarki to Allah ya bashi lafiya, kar ka damu ka yi masa sannu, sai kun dawo".

Faruk ya ce "To Umma ai bacci yake da na baku kun gaisa".

"A'a kar ka tasheshi ina yi masa sannu idan ya farka, Allah ya yi muku albarka, sai anjima". Faruk zai yi magana Umma ta kashe wayar tana mamakin iskanci irin na yaran, amma ba komai zai gane ba shi da wayo. Afnan kallon Umma take tana kallon garin da suka zo, idan ba gizau idonta ke yi ba, garinsu take ganin an dawo da ita cikisa, kenan dama mijin na ta a nan garin yake zama shi da maihaifiyarsa? Ta yi wa kanta tambayar da ba ta da mai ba ta amsa, shiru ta yi ta zubawa sarautar Allah ido.

Faruk ya ce "Haidar Umma fa lafiyanta 茩alau ai ka ji duk yadda muka yi da ita, wato na so na tambayeta ina ta je, to ina gudun kar ta ce ina muka ji ba ta nan".

Haidar ya ce "Haka ne, ka san wani abu Faruk akwai abin da na manta a gidan, mai muhimmanci, ina son yanzu zan je da sauri na 蓷auko, tunda ina da makullin 茩ofar gidan a hannuna dama rabasu muka yi ni da ita kowa ya ri茩e a hannunsa".

Faruk ya ce "Haidar karfa ka je tsautsayi ya sa Umma ta cimmaka a gidan".

"A'a in sha Allah ba za ta cimmi ni ba, bari na tashi na je".

Haidar bai tsaya komai ba, ya bar 蓷akin Faruk ya ce bacci yake ji da ya raka shi.

Babu 蓳ata lokaci Haidar ya 茩aroso gidan ya bu蓷e ya shiga, baifi minti biyu da shigarsa ba mai napep ya sauke su Umma a 茩ofar gidan.


Amanar cool ce 鉁嶏笍 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.