Free chapter · Read without an account
SIRAƊIN UƘUBA 6
🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥
__Free_book_
✍️Nusy bee
Page 6
Abba yace"Weldone DR KHAIRI!in Sha Allah Zaki zama likita,ki rinƙa allura kina yanka cikin mutane ko?"abin ya bata dariya,ta rufe fuskar ta da tafukan hannayen tatana murmushi
Kallon shi ya mayar ga inna sabuwa,cikin girmamawa yace"inna da ni da barrister mun yanke shawara game da Rayuwar khairi,zata koma gidan shi da zama,zai mayar da ita makaranta,idan ta kai munzalin aure kuma zan aurar da ita ga mutumin da ya dace,tare da wannan zata yi karatun ta in Sha Allah,har sai tace ta gaji"inna sabuwa ta taɓe baki bata ce uffan ba,don dai wannan yarinya babu ruwan ta da ta mutu ko ta rayu tunda mahaifiyar ta ta ɓata kanta a wajen su shikenan gaba ɗaya abinda ya shafe ta ya fice mata a rai
Barrister ne ya kalli mahaifiyar tasu da girmamawa yace"inna ya kamata a saka mana albarka,don zumunci muke da niyyar yi,kuma baki ce komai ba"inna ta ɗauke kai tana faɗin"Allah sa albarka"
Hajiya salma kallon su takeyi cike da takaici,ganin bazata iya jurewa ba ta daure tace"inna me zai hana a bar ta a inda yafi wayo?idan aka kai ta cikin mutanen da bata saba dasu ba bakya ganin zata takura?idan yaso sai a nema mata makarantar da ƴan uwan ta na nan suke zuwa ko?"
Da yawan ƴan matan da suke zaune waɗanda suka ji ciwon abinda akace za'ayi wa Ummiyo sunji sanyi, musamman ruƙayya da ta ga tafi Ummiyo kyau,gata da ilmi,ita ya kamata tayi rayuwar birni ba Ummiyo ba,amma yanzu wai ace ba da ita za'a je birnin ba?
Kafin kowa ya sake Magana Sulaiman yace"mum there is nothing wrong idan ta zauna a can tare damu,mu zamu ja ta a jiki,mu koya mata yadda zatayi rayuwar ta tare damu,idan ma kina magana akan rashin wayon ta ne I'm telling you mum tana shiga makaranta komai zai zama tarihi"
"Da kasan haka meyasa baka bawa mahaifin ka shawara ya ɗauke ta ba?"ta bashi amsa a zafafe,daga yadda tayi maganar kawai ya bayyana tsananin ɓacin rai da take ciki
Hankalin mutanen ɗakin ya koma kanta,feena kamar ta nutse don kunya, Azad ma bai ji daɗin wannan maganar ba,Hajiya Raheena ma dai bata ji daɗin yadda kowanne lokaci Hajiya Salma bakin ta baya iya shiru ba,da ƙarin bakin ta ya saka ta ƙara baƙin jini a wajen surukar tasu
Barrister Umar ne ya kalli hajiya salma fuska a haɗe yace"khairi zata zauna damu,a gidan mu,tayi karatu,Wanda yaga bazei iya zama ba yana iya bata waje"Beely da Azad kallon baban nasu sukeyi kawai,don shi Azad babu abinda ya tsana kamar yaga ran mum ɗin shi a ɓace ko da ace da laifin ta kuwa,Beely kuwa a ranta ita tasan me take shiryawa wannan matsiyaciyar yarinyar don ta rabu dasu salin alin,a cewar ta idan sukayi sake zata raba su da dad ɗin su,to gashi tun daga yanzu ma yana faɗawa mum ɗin su magana ina ga tafiya tayi nisa kuma?
Duk abinda akeyi kan Ummiyo yana ƙasa, fuskar ta babu alamun damuwa ko walwala,su kam Barrister da lieutenant general tashi sukayi suka fice daga ɗakin, Azad da haidar da Ma'aruf suka bi bayan su,itama Beely ta miƙe, mahaifiyar ta da Amra suka miƙe,duka su ukun suka fice daga ɗakin kusan a tare, Sulaiman da Hajiya Raheena dai sai kallon su sukeyi,feena kam takaici ma bai bar ta ta kalle su ba saboda haushin halayen maman nasu
Inna sabuwa ta taɓe baki tana faɗin"shi dai Umaru baiyi dacen mata ba ta ko'ina wallahi,kwata kwata babu tarbiyya babu ɗa'a a al'amuran ta, shiyasa ga yaran nashi nan duk idanun su a fetsare,daga waɗanda suka gandame suka ƙi aure sai masu shigar fitsara,sai masu gaida manya gandaidai,gashi abin baƙin ciki an tara yara amma taron tsintsiya babu shara, Allah wadaran naka ya lalace dai!gaskiya dai gidan Umaru idan ya cigaba da tafiya a haka dole ya nemo wadda zata tarbiyantar masa da yara,idan yayi min musu irin na wannan yaron Allah yaji ƙan shi,ko da ban sallama wancan yaron ba shi zan iya sallama shi"
A razane Hajiya Raheena ta kalli inna sabuwa,a duniyar ta babu abinda ta tsana irin kishiya,sai taji abin ma kamar saukar aradu,don sai taji kamar ita inna tace ayiwa, addu'a ta shiga yi a ranta Allah kar ya bawa inna ikon saka lieutenant general yayi mata kishiya,don tana jin ranar mutuwa kawai zatayi
Cikin sanyin jiki ta rissina tana faɗin"to inna zan ɗan shiga ciki na huta,don har yanzu ƙafa ta ciwo take saboda zaman mota,mu wuni lafiya inna"
"A fito lafiya!"shine abinda innar ta iya faɗa batare da ta kalle su ba,Hajiya Raheena ta miƙe cikin sanyin jiki ta fice daga ɗakin
A can masaukin Hajiya salma kam Beely ce ta zauna kusa da ita fuskar ta babu walwala tana faɗin"mum!you have to be careful of what you are saying in front of this old woman,Kar taje tayi miki abinda zai dame ki,kinga ko me tayi miki wallahi ta gama dake don ba iya ramawa zakiyi ba"
Wani mugun kallo mum ta jefawa Beely tana faɗin"ba dai taƙamar ta ɗan ta ba?nasan ƙarshen abinda zata ce kenan ko?to sai me?tayi duk abinda zatayi,ta raba mu,duk bala'in ta dai na haihu da ɗan nata, dole a kira yaran ƴaƴan shi,kuma ace ƴaƴa na,ni bazan iya jurar ta rinƙa taka ni tana wulaƙanta ni yadda take so ba,haba!shekaru da talatin da kusan biyar da aure ana abu ɗaya?bata bar ni na huta a ɗakin aure na ba?ita haka akayi mata lokacin da take da nata mijin?waye ya matsa mata da take son matsawa rayuwa ta?bana manta zuwan ta na ƙarshe babu irin gori da cin mutunci da batayi min ba wai na kasa ɗabbaƙa sunnah na bar ki kin ganɗame ba aure, Azad da haidar kuma wai basu da tarbiyyar gaida na gaba,ita kenan kullum cikin aibata min yara,to na gaji,zan fara saka wa idanu na kwallin rashin mutunci na wanke ta ciki da bai,sai ta faɗi duk abinda zata faɗa da hujja"ta ja tsaki,ita dai Beely bata sake magana ba, tanadin ta akan Ummiyo ne kawai,wadda duk silar za'a ɗauke ta ake ta wannan ɓaɓatun
Bayan Isha'i kamar yadda aka saba mutanen gidan suka taru gaba ɗaya a ƙaton tsakar gidan,ciki har da Hajiya Raheena da yaran ta,sai dai babu Hajiya salma ita da Beely,amma sauran yaran duk sun hallara. Bayan an gama cin abinci Sulaiman yayi ta ba da labarun abin dariya ana dariya, Azad Kam ba karamin ƙular dashi Sulaiman ɗin yakeyi ba,don shi a nashi ganin bai ga abin ɓata lokaci a wajen waɗannan ƙazaman ƙauyawan ba,haka kawai su raina mutane?"
Ummiyo kam tana daga gefe kanta a ƙasa kamar koyaushe,feena na gefen ta,Amra kam ƙare mata kallo take tun daga sama har ƙasa a fakaice
Shigowar Barrister Umar da lieutenant general Usman,sai ƙannen su,baban Jamila da baban Bello ne ya katse surutun Sulaiman,gaba ɗaya aka ɗaga kai ana kallon su, ƴaƴan su da matan su sai sannu da zuwa sukeyi musu
Kai tsaye wajen inna sabuwa suka nufa,cikin girmamawa suka gaishe ta,ta goge hawayen ta tana faɗin"na gode wa da ya sake nuna min yara na a haɗe,ko a yanzu na mutu buri na ya cika,nayi farin ciki"da sauri Usman ya rike mata hannu yana faɗin"in Sha Allahu zakiyi ta ganin hakan inna,mu ƴaƴan ki ne,ko cewa kikayi mu dawo kusa da juna mu zauna hakan zamuyi"da yawan ƴaƴan nasu a firgice suka kalle shi idanu a waje,ciki har da Hajiya Raheena ma, Inna sabuwa tace"a hakan ma alhamdulillahi, Allah ya albarkace ku duka"
Umar yana murmushi ya amsa da "ameen innar mu maganin kukan mu"
Sun ɗan taɓa hira da mahaifiyar tasu,daga baya Barrister Umar ya kula babu matar shi Hajiya salma a wajen,ga matar yayan shi Hajiya Raheena,ga matan ƙannen shi da yaran su duka,hatta da baban Nadiya da baya nan akwai matar shi da yaran shi a wajen,don haka ya zare jiki a sace ya nufi ɗakin da aka sauke ta
A zaune ya ganta akan gado tana shan fruit a wani ɗan ƙaramin bowl da yake da tabbacin da abin ta tazo,daga ƙasa kuma Beely ce ta shimfiɗa darduma tana danna waya
Daga yadda yayi sallama Beely a razane ta ɗago ta kalle shi,ya kalle ta fuska babu rahama yace"ke!get out of this room! idiot!!"a gudu gudu sauri sauri ta fice,ya mayar da hankali ga mum ɗin tata da ta cigaba da shan fruits ɗin ta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,ko kallon shi batayi ba ballantana ta damu da irin mugun kallon da yake jefa mata
"Salma wai menene matsalar ki ne?"
Ɗago kai tayi tana jifan shi da kallon rainin wayo tana faɗin"me kuma nayi?"
"Au baki san me kikayi ba ko? Salma Wai so kike saboda ke mahaifiya ta ta tsine min kafin na bar garin nan?ke kullum ƙoƙarin takalar mahaifiya ta kikeyi kamar wata sa'ar ki?baki da aiki sai tsiwa da rashin kunya kuma don rashin mutunci ki rasa wadda zakiyiwa sai mahaifiya ta?"
Wani kallon banza take watsa masa har ya gama ɓaɓatun kafin ta kyaɓe baki tana faɗin"idan Ni ban yi faɗa da mahaifiyar ka ba ko ɓata maka suna kai naga alamun so kakeyi ka zubar min da ƙima a idanun waɗannan ƴan uwan naka,me nayi maka da zaka zo ka rufe ni da masifa kamar wata ƴar ka?"
"Me kika ɗauki kanki?ko kina ganin akwai bambanci tsakanin ki da Mutanen da kika ƙi shiga cikin su?kowa na waje sai kece zaki zo don munafurci ki wani shigo ɗaki kina kitsawa ƴar cikin ki sharri?"
"Au!Wai don banyi wancan zaman majalisar bane kazo kana ta tada jijiyar wuya dama?ni na ɗauka wani abin ma akace nayi,to Allah ya bada haƙuri,na ɗauka zaman ra'ayi ne shiyasa ban fita ba,kasan ni bana son hayaniya da saka idanu ne"
Kallon ta yakeyi yana jinjina halayyar ta,sam bata jin kunya ko shakkar gatsa masa magana kowacce iriya ce, daurewa yayi yace"to ba ra'ayi bane wajibi ne,don haka tashi ki fita"
Muskutawa tayi tana yatsina fuska tace"gaskiya bazan iya ba,don ba wani daɗi nakeji ba"
Shiru yayi na ƴan sakwanni yana kallon ta,ita kam tana gama shan fruits ɗin ta ta ajiye bowl ɗin ta kama danna waya, Barrister Umar ya gyaɗa kai yana faɗin"Salma do whatever you like,lokacin ki ne, watarana da kuɗi akace kiyi bazakiyi ba"ya juya ya fice ya bar ɗakin
Gaskiya dai Hajiya Salma, with all due respect baki da mutunci 🥺
#likecommentshare
#Nusy_bee