Free chapter 路 Read without an account

Chapter 65-66

by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...

馃挮 *RAMIN 茦ARYA....*馃挮



_WRITING BY AMANAR COOL_鉁嶏笍



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*

 
_A yi ha茩uri da in da a ka ga typing errors_



Page 65&66



Assalama alaikum taku hafsat collection take muku sallama ina yan gayu suke uwar gida da amarya harma da yan mata yan kwalisa馃コ馃コ hafsat collection ta shirya tsab wajan zakulo ma bambanta hadaddun kaya nagayu tundaga kan kayan kawata gida kitchen nasakawa 馃拑馃拑 ado da kwalliya shine cikar macen datasan kanta bata wasa da kayan gayu馃グ馃グ musamman da suka kasance na hafsat collection gasaukin farashi ga inganci babu inda bama tura kaya cikin aminci da yardar Allah馃憦馃グ kudai kukasance da hafsat collection ga kadan daga cikin abinda take kawomuku lace,zip gwns ,jaka,takalmi,mayafi yan yayi ,kayan kitchen masu kyau sauki inganci kai tsaye ku tuntubi ta ta wannan number kamar haka *** ko kuyi join group kai tsaye dan ganin kayan datake kawowa mungode sai munjiku mutanan arziki馃コ馃コ馃コ馃グ馃グ馃憦馃憦



____________Afnan tana jin salatin da Umma ke yi, 茩afafuwanta ne suka yi mata nauyi, tana so ta tsaya sai dai idan ta tuna warning 蓷in da Haidar ya yi mata, sai ta ji gara ta daure 蓷in ta kai masa. Duk abin da Umma za ta ce, na ta mai sau茩i ne a kan abin da ya ce zai aikata mata.

Da sallama ta shiga 蓷akin, ya na kashingi蓷e saman katifarsa ya na dariya, saboda ya na jin salatin da Umma ke yi, kuma ya ga Afnan 蓷in ba ta fasa kawo masa abincin ba.

Tashi ya yi zaune ya na kallon ta cikin dariya ya ce "Sannu da 茩o茩ari amaryar Haidar, ko ke fa yanzu ba gashi kin samu lada ba, Allah ka蓷ai ya san adadin ladan da ki ka samu".

Ita dai shiru ta yi ba ta ce masa komai ba.

Umma kuwa ba 茩ara min takaici ne ya kamata ba, wannan yarinyar an yi mara wayo. Duk yadda take 茩o茩arin hukunta Haidar da alama ba za ta ba ta ha蓷in kai ba, amma ta san wannan shirin na Haidar ne, dama ta lura da yanayin ta gaba 蓷aya a tsorace ta wuni yau, ta san duk yadda a ka yi zuwan da Haidar ya yi 蓷azu gidan nan ya hure mata kunne, ko kuma ya tsorata ta, tashi ta yi ta shigewarta 蓷aki dan ba 茩ara min haushi ta ji ba, gaba 蓷aya yanayin fuskarta ya sauya.

Afnan kuwa bayan ta a jiye masa abincin ta mi茩e za ta fita sa cewa ya yi "To ina ruwa? Ko a haka zanci abinci ba ruwa kusa? Sannan kuma ki zuba mini ruwan wanka".

Afnan kamar za ta yi kuka, fuskarta babu walwala ta fita a 蓷akin, ganin Umma ba ta wajan ya sa ta 蓷an ji sau茩in kunyar fitowarta a 蓷akin da take ji, kasa shiga 蓷akin ta yi ta 蓷akko kofin da za ta 蓷ibar masa ruwa, dan haka ta ja burki ta tsaya nan wajan. 

Haidar ya na jiran dawowar ta, ta kawo masa ruwa shiru ba ta dawo ba, bai damu ba, dama ya san ba lallai ne ta dawo 蓷in ba, ko iya haka dai da ta yi ya ji da蓷i, kuma ya san dole Umma za ta ha茩ura ta 茩yale mishi matarsa, matu茩ar ta ga Afnan 蓷in na yi masa haka. Bayan ya kammala cin abinci ya fito, a zaune ya ganta ta yi tagumi.

Ya yi 茩asa da murya ya ce "Shi ne ki ka 茩i kawo mini ruwan ko? Wato har kin fara sa蓳a shara蓷in nawa, shikenan babu komai hakan da ki ka shi ya tabbatar mini da kin shirya kar蓳ar ta, dan haka a kowa ne lokaci zan iya...." Bai 茩arasa ba ya yi shiru ganin Umma tsaye tana kallon sa, shafa sajensa ya yi, ya na mazurai da ido, kamar wani tsoho munafuki.

Ya 蓷auki buta ya yi alwala da yake an fara kiran magariba, ya fita Masallaci.

Umma ma alwalar ta yi, ta koma 蓷aki

Ita ma Afnan ta yi alwalar ta shiga 蓷akin.

Bayan sun gama sallah ne Umma ta dubi Afnan ta ce "Afnan" sai da gaban Afnan ya fa蓷i, ta 蓷ago cikin yanayi na fargabar jin me Umma za ta ce mata, ta ce "Na'am Umma"

"Afnan me yasa ba ki da wayo ne? Duk 茩o茩arin da na ke yi na ga na karkaro miki mutuncinki a gurin mijinki shi ne ki ke 茩o茩arin watsa mini 茩asa a ido? Afnan da ke san dalilin da ya sa nake yi wa Haidar haka a kanki da ba ki biye masa ba, na san wannan abin da ki ka yi shi ne ya saka ki yin hakan, ke kuma ki ka biye masa, Afnan Haidar wayo ne yake yi miki, kuma ina tunanin duk yadda a ka yi ya fuskanci ki na jin tsoron sa ne, shi ya sa zai yi amfani da wannan damar ya sa ka ki yin abin da ya san zai tun zura ni, amma shikenan babu komai tunda har kin nuna mini umarnin mijinki za ki bi, ga ki nan gashi, sai ki tattara kayan ki ki koma can 蓷akin nasa da zama".

Afnan kasa magana ta yi, wata matsananciyar kunyar Umma ce ta kamata, ta kasa bu蓷a baki ta yi magana ko 茩o茩arin kare kanta, sai dai har cikin zuciyarta ba ta ji da蓷in abin da Haidar ya sa ta yi ba, amma ba yadda ta iya ne.

Umma tana jiran ta ji me Afnan za ta ce mata amma shiru, nan ta 茩ara jinjinawa rashin wayon Afnan.

Ko da Haidar ya dawo gidan dare ya yi, ya shigo har 蓷akin Umma ya yi mata sai da safe, Afnan na kwance tana jinsa, amma ta yi kamar bacci take yi, fita ya yi a 蓷akin Umma ta bi bayansa.

"Haidar" ya ji Umma ta kira sa

Tsayawa ya yi ya ce "Na'am"

"Haidar wato saboda ka nuna mini iyakata shi ya sa ka yi mini haka ko?".

Ya ce "Umma me na yi miki?"

"Rufe mini baki ai duk abin da nake magana a kai ka sani, saboda ka lura da yarinyar na da tsoro da kuma rashin wayo da ke 蓷awainiyya da ita shi ne za ka yi amfani da ita wurin nuna mini ka isa? Mara kunyar banza, wai kai ga mai mata, wallahi Haidar ka fito idona na rufe".


Haidar ya ce "Don Allah Umma me ye laifina? Ni fa babu abin da na ce mata, ko ita ta ce miki ni na saka ta yin wani abin? Yarinyar da ko magana kin hana ta yi mini, kuma Umma na baki ha茩uri, ko Allah da ya halicce muna yi masa laifi, kuma muro 茩e sa ya yafe mana, don Allah Ummata ki yi ha茩uri, wallahi natuba, ki ba ni matata haka nan".

 
"Haidar na baka matarka ka ce? Kar ka mata fa baka da lafiya, to yaushe har ka samu lafiyar da za ka ce a baka matar ka?".

Ya ce "Umma don girman Allah ki yi ha茩uri, ki dai na wannan maganar, komai ya wuce, ni dai ina 茩ara ba ki ha茩uri ne".

"Au kenan rashin lafiyar ma ta 茩arya ce? Ai shikenan ka je kan ka ka yi wa". Da ga haka ta komawar ta 蓷aki ta bar Haidar nan tsaye.

Gajiya ya yi da tsayuwa ya wuce 蓷akin sa. Ko yau dai kamar kullum ce da 茩yar Haidar ya ga wayewar gari.

*******

Mami da ta dubi Abba bayan ta yi masa barka da asuba, ta ce "Alhaji magana nake so mu yi da kai mai muhimmanci".

Abba ya ce "To ina jinki".

Ta ce "Dama akan zancen Mudan".

Ya ce "To ina fatan kin ha茩ura ne ya auri wadda yake so 蓷in?".

"Alhaji ba wannan zance ba ne, yanzu magana ce nake son yi a kan ha蓷a shi aure da Huda da nake son a yi".

Da sauri Abba ya dubi ta fuskar shi 蓷auke da mamaki, ya ce "Saratu kin san me ki ke fa蓷a kuwa Mudan 蓷in ne za a ha蓷a shi aure da Huda?".

"Eh mana Alhaji, ai na ga akwai aure tsakaninsu".

"To su suka ce miki suna son junan su ne ko kuma wannan tsarinki ne dan kar ya auri wadda yake so?".

"A'a wallahi dama ashe suna son junansu da da蓷ewa, fa蓷a ne basu yi ba sai yanzu". 

Abba ya ce "Suna son junansu ne Mudan 蓷in zai zo mini da maganar wata? Saratu ba na son irin wannan abin da ki ke yi, me ye laifi dan Mudan ya ce ya na son 拼ar aminiyarki? Ai naga farin ciki ya kamata ki yi, domin zumuncinku ne zai 茩ara 茩arfi".

Cikin damuwa Mami ta ce "Alhaji ni fa ban yarda da son da Mudan ke yi wa Hasina ba, wannan soyayyar ba ta domin Allah ba ce, ina zargin kamar wani abin a ka yi masa, sannan Huda na son Mudan shi ma ya na sonta, yanzu da ga bisa ya juya mata baya, sakamakon hakan ne ya sa take wannan rashin lafiyar, shin Alhaji ta yaya ka ke tunanin zan bari ya aure wata bayan ga Huda na son shi, kuma wai ashe har al茩awarin aure ya yi mata".

Abba ya ce "Ke ya aka yi ki ka san ba don Allah ne ya ke son yarinyar ba? Wai me yasa ku mata komai naku sai kun danganta shi da wani abin daban? Ba na son irin wannan zanttutukan, sannan zan bincike yaran da kai na na ji". 

Shiru Mama ta yi ba ta kuma magana ba, lamarin Alhaji sai shi, ita ta rasa wannan dalilin sai ta ga kamar asrin da ta yi masa ya na son tasiri a jikinsa sai kuma abu ya lalace.

Can ta ji ya kuma ce mata "Yau da yamma jirginsu Hajiya zai sauka".

Cikin murna Mami ta ce "Ma sha Allah, Allah ya sauke su lafiya". Ya amsa da Amin

*******

Misalin goma da rabi Maryam ta gama shirinta, Mama ta ha蓷a tsarabar da za a kai wa Afnan, dama ta kira Haidar babu 蓳ata lokaci ya zo suka tafi, a hanya Maryam ke tambayar sa, ya aka yi ya san gidan da Afnan take ko dai 拼an uwansa? Haidar ya yi murmushi ya ce "Maryam manya eh 拼an uwana ne, idan ki ka je Afnan za ta sanar dake ala茩armu da su". Maryam ta ce "To shikenan" suka ci gaba da hira har suka iso 茩ofar gidan .

Afnan na 蓷akin Umma kamar daga sama ta ji sallamar Maryam, da sauri ta fito aikuwa ita 蓷in ta gani, cikin farin ciki suka rungume juna, Umma ta fito daga ban蓷aki ta ce "A'a ba茩uwa muka yi ne?"

Afnan ta ce "Umma 茩anwata ce".

Umma ta ce "Ma sha Allah, to ku shiga ciki mana".

茒akin suka shiga Afnan bakinta ya kasa rufuwa.

Afnan ta ce "Maryam ina Mama da Baba lafiya suke?".

Maryam ta ce "Suna nan 茩alau, suna gaisheki Aunty kin ji da蓷in da muka ji kuwa? A lokacin da Gwaggo ta zo muna da zancen cewar surukar ki ta tafi dake, wallahi mun shiga damuwar rashin sanin inda ki ke, sai gashi Allah ya dawo mana dake kusa da mu, ma茩iya da munafukai Allah ya 茩i ta tasu".

Afnan ta ce "Hmmm ki bari kawai ni ma haka naga abin kamar a mafarki".

"Yawwa Aunty me ye ala茩ar mutanen gidan nan da ya Haidar ya ce mini suna da ala茩a?".

Afnan ta ce "Gidansu ne ai"

"Laaaa kenan 蓷an uwan mijinki ne ko?"

Dariya Afnan ta yi, Maryam ta ce "Dan Allah Aunty fa蓷a mini mana"

"Maryam shi ne fa"

"Shi ne me?" Ta yi tambayar 

"Shi ne wanda aka aura mini"

Zaro idon Maryam ta yi cikin mamaki ta ce "Kamar ya bangane ba".

Nan Afnan ta gaya mata komai

Maryam ta ce "Ikon Allah, lallai Allah Allah ne, Allah mai juya al'amurransa yadda ya so, yanzu Yaya Haidar ne mijinki? Kai Alhamdulillah Allah mun gode ma".

Suna nan zaune Umma ta shigo suka 茩ara gaisawa da Umma, Umma ta tambaye ta mutan gidan. 

Suna nan zaune Haidar ya shigo da sallama ya siyo wa Maryam lemu da ruwa.

Maryam sai kallon sa take yi ta ce "Sannu Yaya Haidar ashe ma kai ne angon bamu sani ba? Kuma ba ka gaya mini a hany ba". Ta yi maganar tana dariya

Haidar ma dariyar ya yi ya ce "To ba gashi nan ta gaya miki".

Dariya suka yi gaba 蓷aya Umma ta tashi za ta 蓷ora girki Afnan ta ce ta bari su yi, haka suka yi aikin tare da Maryam, Afnan ta ji da蓷in zuwan Maryam sosai.

******

Abba ya shigo sashen Ammi domin ya duba ta da yanayin jikin nata, kwana biyu nan laulayi ya sako ta a gaba, nan ya ke sanar da ita maganar da Mami ta zo masa da ita.

Ammi ta ce "Ba abin mamaki ne ba dan hakan ta kasance, ni na da蓷e da fuskantar akwai wata ala茩a tsakaninsu, idan ba ka manta ba, a kwai lokacin da Huda ta ta蓳a fasa wayarta a falon nan, kuma ba komai ya janyo haka ba jin ka ce za a ha蓷a Sharifa da Mudan aure ne" nan Ammi ta shiga zayyano masa abubuwan da ta fahimta, sai dai ba ta gaya masa cewar ta ga Huda na zuwa sahensa ba.

Abba ya ce "To yanzu ya ki ke ganin za a yi ne?"

Ta ce "Ka 茩ara ba da lokaci ko nan da sati 蓷aya ne, kar ka sake yin maganar mu ga abin da hali zai yi, idan Mudan 蓷in na nan a kan bakarsa ta sai a san abin da ya kamata a yi". Ya amsa mata da Madam ya na shafar gefen fuskarta. 

Ammi ta ce "Ya batun tafiyar su Hajiya yau 蓷in za su iso ne?".

Ya ce "A'a yanzu nan ba da da蓷ewa ba ta ki shaida mini cewar an samu matsala ba za su samu taho a wannan satin ba, kuma fa har komai na tafiyar su ya kammala".

"Allah Sarki ka san tafiya ta Allah ce"

"Haka ne Madam 蓷ita". Sallama ya yi mata ya fita dan ya na sauri zai fita ne.

******

Sai Bayan la'asar sannan Maryam ta yi shirin komawa gida, Afnan ji ta yi kamar kar su rabu, Maryam ta ce mata kar ta damu za ta dawo ba da jima wa ba. Haidar ne ya mayar da ita gida. 

Mama ta yi farin cikin jin cewar Afnan na cikin kwanciyar hankali, nan ta 茩ara yi wa Allah godiya.

Wasa wasa yau kusan kwana biyar da zuwan Maryam gurin Afnan, kuma har yanzu Umma ta hana Haidar ya ke 蓳e da Afnan, sannan ta kasa ta tsare ta hana ta yi masa komai, yau Haidar abin ya kai shi bango, kuma ya ji yau ba zai iya ha茩ura ba. 

Haidar bai shigo gida da wuri ba, sai kusan sha 蓷aya ya shigo da ledarsa a hannu, motsin ruwa ya ji a ban蓷aki alamar wanka a ke yi, ya shiga 蓷akin Umma ya ga tana bacci, kuma da alama baccin nata ya yi nisa, nan ya san cewar Afnan ce ke wanka.

Fitowa ya yi ya ja burki ya tsaya a waje, Afnan kuwa bayan ta gama wanka hijabi ne kawai a jikinta sai zane da ta 蓷aura ta shiga da shi, tana fitowa ta ga mutum a tsaya zabura da ta yi dan ta tsorata, tunda ba ta san da shi ba.

Za ta yi magana Haidar ya 蓷ora hannunsa a le蓳enta, ya ja hannunta zuwa 蓷akin sa, Afnan kamar wata doluwa ta bi bayan sa, tsabar tsoratar da ta yi. 

Haidar suna shiga ya maida 茩ofar 蓷akin ya rufe, ya cire mata hijabin jikinta.

Afnan gaba 蓷aya tsoro ya bayyana a fuskarta, idanuwanta suka ciko da 茩walla, cikin rawar muryar ta ce "Don Allah Ya Haidar ka yi, wallahi na tuba ba zan sake ba".

Kallon ta ya yi ya ce "Ai ba ki isa ba, dama na gaya miki ka da ki bari na kama ki, wallahi Afnan yau ko hmmm". Shiru ya yi ya janyota jikinsa za ta yi ihu ya ha蓷e bakinsu guri 蓷aya.


Amanar cool ce 鉁嶏笍 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.