Free chapter 路 Read without an account

Chapter 73-74

by Amanarcool 路 RAMIN 茦ARYA...

馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮



_WRITING BY AMANAR COOL_鉁嶏笍



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*


Not editing 


Page 73&74


__________Rufe idanuwa Umma ta yi tana ambaton Allah a zuciyarta. Duk maganar da su Alhaji Munir ke yi ta kasa bu蓷e idonta balle ta tanka musu.

Duban Haidar Abba ya yi ya ce "茒an samari barka dai" 

Sai a lokacin Haidar ya samu damar yin magana, saboda gaba 蓷aya kanshi ya 茩ulle ya kasa fahimtar komai. Ganin yadda lokaci 蓷aya Umma tana 茩o茩arin rikicewa

Ya ce "Yawwa barkan ku da yini".

Abba ya amsa da "Barka dai 蓷an samari, ya mai jikin?".

"Da sau茩i Alhamdulillah, sai dai ban waye ku ba". Cewar Haidar

Murmushi Abba ya yi ya ce "Ai ba lallai ne ka san mu ba, amma kai waye a gurin ta?".

Haidar ya ce "Ni 蓷anta ne, sai dai ina mamakin rashin sanin ku da ban yi ba, saboda gaba 蓷aya 蓷anginta ba wanda ban sabi ba". Haidar ya dubi Umma da har yanzu idanuwanta a rufe suke, kuma tana jin duk abin da ake yi, ya ce "Umma dan Allah ki bu蓷e iadonki, ko jikin ne? Tun 蓷azu kin rufe idanuwa kuma ga dukkan alamu ba bacci ki ke yi ba, sannan ga wa拼an nan bayin Allah sai magana suke yi kin yi shiru".

Tunda Haidar ya ce shi 蓷an Umma ne, Alhaji Munir yake binsa da kallo, ko 茩iftawa ba ya yi. 

Abba ma haka ya kalli Haidar ya kalli Alhaji Munir, kasa ha茩uri ya yi ya kuma cewa "Yaro da gaske kai 蓷an Amina ne?".

Haidar ya ce "Eh ni 蓷anta ne".

Abba ya ce "To kana da 茩anne ko kuma kan 蓷aya ne a gurinta?".

"Ba ni da wa ko 茩anne ni ka蓷ai ne" Haidar ya ba shi amsa.

Abba zai koma yin magana suka ji Umma ta yi magana da 茩yar ta ce "Haidar kira likita ya sallame ni daga gurin nan".

Ya ce "Umma me yasa? Ki bari ki 茩ara samun sau茩i naga jikin naki har yanzu da saura. Umma ga fa ba茩i nan sun zo gurin ki, ki kula su mana".

Umma ba ta kuma magana ba, ta yun茩ura da 茩yar ta tashi daga kan gadon, jiri na 蓷iyarta ta nufi hanyar barin 蓷akin. Da sauri Haidar ya ce "Subhanallah Umma ina za ki ne? Ki yi ha茩uri mana bari na kira likitan".

Bata ko tsaya saurararsa ba ta bu蓷e 茩ofar ta yi waje, Haidar kallon su Abba ya yi ya ce "Dan Allah ku yi ha茩uri, ina ga akwai abin da ke damunta ku jira ni ina zuwa". Daga haka ya bi bayan Umma.

Sai dai ya duba ko ina bai ganta ba, fita ya yi harabar asibitin, can ya hango ta tana 茩o茩arin tarar abin hawa, da sauri ya 茩arasa gurin, lokacin har ta shiga napep 蓷in.

Ya ce "Haba Umma ya za ki tafi gida ba a bamu sallama ba? Kuma su wa拼ancan bayin Allah da suka zo gurin fa? Ba kya gudun suga kamar kin wula茩anta su ne?".

Cikin muryar ta rashin jin da蓷in rai Umma ta ce "Haidar ba na son damuwa, idan ka tashi kawai ka shigo mu wuce gida".

Ba yadda ya iya ya san tunda har ta tari abin hawa ba za ta koma ba, shiga ya yi mai napep 蓷in ya ja suka bar gurin.

Su Abba kuwa tun suna jiran dawowar su Haidar shiru babu alamar za su dawo, Abba ya dubi Alhaji Munir da ya yi nisa a duniyar tunani, ya ce "Munir anya Amina ba guduwa ta yi ne ta yi ba?".

Da sauri ya dubi Abba ya ce "Tabbas na san ba za ta tsaya ba, yi sauri mu bi bayan ta".

Fita suka yi sai dai ko alamar su Haidar basu gani ba, da sauri suka shiga mota suka bar asibitin, sai dai sun rasa wace hanyar zasu bi. Alhaji Munir ya dafe kansa ya na fa蓷in "Wayyo Allahna, ina zan kuma ganinki Amina? Na san ba lallai ne ki koma bari mu ha蓷u ba".

Abba ya ce "Dakata ba ance da Sharifa aka kawo ta asibitin ba? Ai kaga zamu iya bincikar Sharifar mu ji ina suka ha蓷u da har ta kawota asibiti". 

Munir ya ce "Yes haka ne, mu je gidan ta yi mini baya ni". 

Ko da su Umma suka iso gida, su Afnan har sun gama girki, gudun kar Haidar ya zo ya tambaye abinci. 

Sallamar Umma suka ji, da sauri suka fito waje suna yi mata sannu da zuwa, ta amsa musu cikin yanayi na damuwa, Afnan ta shimfi蓷a mata tabarma a waje tana 茩ara yi mata ya jikin. Sai dai Umma ba ta zauna ba ta yi shigewarta 蓷aki.

Tana shiga kwanciya ta yi ta shiga tuna rayuwarta ta baya.

*茦AUYEN UNGOGGO*

A hankali yake tafiya har ya 茩arasa cikin 茩auyen, tsaye ya yi ya na duban garin, garin ya yi tsit babu yawan jama'a, ya rasa ta ina zai bi ya sada kansa da gidan mai gari, kasancewar rana ta yi sosai babu yawan maza a garin, kowa ya kama sabgar gaban sa, ya na nan tsaye sai ga wata matashiyar buduwa ta zo za ta wuce shi, har ta gota shi ya ce mata "瞥an mata ji mana" kamar ba za ta tsaya ba sai kuma ta juyo tana kallon sa.

Ya ce "Sannu boyar Allah, dan Allah in ba damuwa gidan mai gari nake son sani, ni ba茩o ne a garin nan".

Ta ce "Allah Sarki tom biyo ni muje".

Godiya ya yi mata, sannan ta yi gaba ya bi ya bi bayan ta.

Da suka zo ta nuna masa 茩ofar gidan, sannan ta yi gaba abin ta, godiya ya sake yi mata, ya na bin ta da kallo. Sai da ya ga ta sha kwana sannan ya 茩arasa 茩ofar gidan, wani mutum ya gani gaisawa suka yi, nan yake sheda masa cewar shi ba茩o ne, ya so anyi masa iso gurin mai gari, mutum ya je ya sanar da mai gari, nan ya ba da damar a shigo da shi. Da sallama ya shiga fadar, cikin girmamawa ya gaida jama'ar gurin, mai gari ya yi gyaran murya ya ce "Bawan Allah sannu da hanya, muna maka barka da zuwa wannan gari namu mai tarin albarka, muna so mu san sunan ka, kuma muji me ke tafe da kai?".

Gyara zama ya yi ya ce "Da far茩o dai sunana Munir, ni 蓷an garin Kano ne, aiki ne ya kawo ni nan garin, idan ba damuwa ina so zan yi zama na sati biyu zuwa uku ne a tare da ku, domin fahimtar halayyar mutanen karkara da yanayin rayuwarsu".

Mai gari ya ce "In dan wannan ne ba damuwa. In sha Allah za ka samu kar蓳uwa da tarba mai kyau a gurinmu, sai dai kai ma ina son ka zauna da mu tsakani da Allah".

"In sha Allah, ba zaku same ni da cin amana ba". Nan mai gari ya sa aka bashi masauki, aka kawo masa abinci da ruwa mai sanyi. Mai gari ya sanar da jama'ar gari cewar ba 茩onsa ne bai yarda ko kallon banza a yi masa ba. Da yamma munir ya fito ya na zagaya gari duk in da ya ga jama'a sai ya tsaya sun gaisa cikin girmamawa da mutunci, a hanyar sa ta kumawa gida ne, ya kuma ha蓷uwa da budurwar 蓷azu, gaba da gaba suka yi, ta ra蓳a shi za ta wuce da sauri ya kuma cewa "Barka da yamma 茩anwata". Duban sa ta yi da kyau, nan take ta gane sa, ta ce "Yawwa barka dai".

Ya ce "Baki gane ni ba ne?" .

Ta ce "Na gane ka mana, ba茩on mai gari ne" daga haka ta yi wucewar ta, da kallo ya bita, ya na murmushi.

Kwana biyu da zuwan Munir ya fara sabawa da jama'ar garin, sannan ya na yawan ha蓷uwa da yarinyar da har yanzu bai san sunan ta ba, ya na zaune a 茩ofar gidan mai gari shida Habibu, sai gata ta zo za ta shiga gidan, gaishesu ta yi ta shiga gidan, Habibu ya ce "Amina boyar Allah ba ruwan ta, wannan yarinyar akwai hankali sosai a gurin ta".

Jujjuya sunan Munir ya shiga yi.

Suna nan zaune ta fito daga gidan, Munir ya kuma binta da kallo sai da ya daina ganin ta.

Habibu ya ce "Munir lafiya dai?".

Murmushi ya yi ya na shafa gemunsa ya ce "No ba komai". Ci gaba da hirarsu suka yi.

Amina tunda ta 蓷ora idonta akan ba茩on gidan mai gari ta ji ya burge ta, kullum ba ta da buri sai na son ha蓷uwa da shi. Shi ya sa take yawan bin duk wata hanya da ta san za ta ha蓷u da shi, sai dai ta 茩i bari ya fuskanci komai a game da abin da take ji akan shi.

Bangaren Munir ma haka yake ji akan yarinyar, lokaci 蓷aya ya ji yariyar ta burge shi, kuma ya kamu da sonta, har yake tunanin da za a bashi dama zai iya auren ta. Sai dai ya rasa ta yadda zai bayyana mata manufar shi a gare ta. Duk da ya san ba abu ne mai yiyuwa ba, ko da ace iyayen ta sun yarda, ya san na shi iyayen ba zu yarda ba.

Yau da yamma kamar daga sama ya ha蓷u da ita a wani lungu, tsayar da ita ya yi ya ce "Gimbiya Amina barka da yamma".

Cikin mamakin ya aka yi ya san sunan ta ta ce "Yawwa barka dai, fatan ka yini lafiya?".

Ya ce "Lafiya 茩alau Alhamdulillah da fatan ke ma haka?".

Ta ce "Alhamdulillah".

Munir ya ce "Idan kin ba ni dama ina son yin magana dake ne".

Wani irin da蓷i ne ya mamaye zuciyarta, amma sai ta maze ta ce "To shikenan amma gaskiya ba zan tsaya da kai a hanya ba, sai dai ka zo 茩ofar gidanmu".

Ya ce "Tom ba damuwa kwatan ta mini gidan naku, anjima zan zo".

Nan ta yi masa kwatance sannan ta bar gurin, tana jin kamar an yi mata bushara.

Bayan sallar isha Munir ya isa 茩ofar gidan su Amina, da 茩yar ya gane gidan, kasancewar a lungu gidan yake, ya aika yaro ya ce ana kiran Amina, babu 蓳ata lokaci ta fito, domin ta san mai kiran nata.

Da sallama ta iso idan yake, ya amsa mata ya na murmushi mai 茩ayatarwa.

Ta ce "Barka da zuwa".

Ya ce "Barka dai Gimbiya, ya daren"

Ta ce "Alhamdulillah".

Munir ya ce "Ma sha Allah, Amina na san za ki yi mamaki da na ce ina son magana dake, tom ba abin mamaki ba ne shi lamarin Ubangiji babu yadda baya kasancewa, Amina ba zan tsaya yi miki wani 蓳oye 蓳oye ba, maganar gaskiya sonki nake yi, kuma so na aure idan kin ba ni dama". Da sauri ta dubi shi ta ce "Taya zan yarda da abin da ka fa蓷a? Bayan kana 蓷an birni wayayye, ni kuma 拼ar 茩auye ce, a hakan za ka ce kana sona?".

Munir ya ce "Amina shi so ba ruwan sa da wayewa ko rashin ta matu茩ar kana son mutum, dan haka ni duk wannan bai dame ni ba, in dai kin ba ni dama zan nimi auren ki a wajen magabatanki".

Ta ce "To na ji, kai idan ka yarda kana sona za ka aure ni, su iyayenka za su yarda ne?".

Ya ce "Wannan ba damuwa ba ne, iyayena na san zasu so duk abin da nake so, ni dai burina ki amince da ni".

Ta ce "Tom ka ba ni kwana biyu zan yi shawara".

Ya amsa da "To" sannan suka yi sallama ya bar 茩ofar gidan.

Bayan kwana biyu ya kuma tun tu蓳arta da maganar tunda daga yanayin tarbar da ta yi masa ya san cewar ya samu kar蓳uwa, nan ya shaida mata cewar zai yi wa iyayensa magana su zo nema masa aurenta, sai dai gefe 蓷aya ya na fargabar sanar da iyayensa dan ya san ba yarda zasu yi ba. 

Cikin 茩an茩anin lokaci labarin soyayyar ba茩on mai gari da Amina ya zagaye ko ina, mutane sai fa蓷in suke 茩arya ce ba sonta yake yi ba, yaudararta ne zai yi. Magana har ta je kunnen mai gari nan ya kira Munir yake tambayar sa maganar da ya ce gaskiya ce?.

Munir ya ce "Eh ranka ya da蓷e gaskiya ce"

Mai gari ya ce "Anya Munir wannan lamari zai yiyu kuwa? Taya mutum kamar kai zai ce ya na son 拼ar 茩auye kuma da aure?".

Munir ya ce "Ranka ya da蓷e Allah ne ya jarane ni da sonta, kuma ne babu cuta ko yaudara a zuciyata game da Amina".

Mai gari ya ce "Tom shikenan Allah ya shige mana gaba". Da amin ya amsa sannan ya tashi.

Amina ta tashi cikin tashin hankali saboda iyayenta sunci ko za ta mutu ba za su aura mata shi Munir ba, haka kawai daga ganin mutum ba ta san ko waye shi ba ta ce shi take so za ta aure shi, saboda ba ta da hankali, ta yi kuka kamar ranta zai fita, sannan gashi sun hana mata hita saboda kar ta ha蓷u da shi, kuma an fara ya ma蓷i蓷in cewar har 蓷akin shi take iske shi.

Shi ma Munir ya na cikin damuwa dan iyayensa sun nuna masa cewar ko da wasa kar su sake jin maganar a bakin sa, dama ya san hakan za ta faru. Gashi yau kwanan sa goma a garin kwana hu蓷u ya rage masa, ya kuma garinsu. Duk abin duniya ya dame shi, ga surutun da mutane ke yi akan sa, ga rashin ganin Amina da bayayi. Duk ya damu kansa har wata rama ya yi, ji yake idan bai aure Amina ba komai zai iya faruwa da shi, saboda ba 茩aramin so yake mata ba.

Amina ma gaba 蓷aya ta fita a hayyacinta, na rashin ganin Munir da ba ta yi, gashi ta ji ra蓷e ra蓷in cewar gobe zai bar garin, dan haka yau ta yanke hukuncin ko mai zai faru sai ta fita ta je girin sa, kuma sai ta ai watar da abin da zuciyarta ke umarta ta da ta aikata, ko da hakan ya na nufin salwantar da rayuwarta ne.


Amanar cool ce 鉁嶏笍 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.