Free chapter ยท Read without an account

5

by Aisha Abbakar ยท NAYI SAKE DA DAMA TA

_*NAYI SAKE....!*_๐Ÿ’˜

    ๐Ÿ’˜ '''DA DAMA TA'''

   FREE BOOK ONE

*E.W.F*

Mrs bb

Mom muhseen.

Watt pad name

Humaira3461

      ๐Ÿ…ฟ๏ธ.....9&10

"Sati cikin na biyu kenan da yin maganar mu akan Amnat amman bakace mun komi ba, ko kana nufin ka bar mata yar ne?"

Cewar Anty muhibba da ta kirashi yana zaune cikin office suna tare da Sagir yazo masa ziyara, lumshe idanun sa yai yana ajiyar zuciya ahankali kafin ya bata ansa cikin sanyin murya.

"Anty munyi maganar nan dake tunda har na amsa maki ai dole ne na ansota, kawai dai na bari mu samu hutu gaba d'aya ne sai na daukota"

Cikin fad'a tace, "karka nemi raina mun wayau kajiko, meya shafi aikin ka da dauko yarinya? Driver kawai idan ka aika ya wadatar ai ko?"

Dafe kai yayi don shi baya son masifa, "Anty pls nayi baki idan sun tafi zamu yi waya"

"Allah yasa jahar kano ce duka sukazo maka"

Ta yanke wayar, yaja iska ya fesar yana aje wayar gabansa ya sadda kanshi yana kallon tarin takaddun dake gabansa, tsawon lokaci baice komi ba har sagir din yagaji yai magana.

"Maman ilham ce halan?"

Jinjina masa kai kurin yayi bai magana ba, sagir d'in yayi jimm kafin ya nisa yana duban sa ya ce, "ina ganin mai zai hana ka gaya mata zaka d'an bar yarinyar zuwa wani lokaci, inyaso hidimar makarantar duk kayi mata zuwa sadda uwarta zata d'an samu lafiya saika anshetan, don gaskiya taban tausayi dana sameta cikin wani hali har asibiti fa"

D'agowa yai yana kallon sagir d'in da idanun sa da sukai jaa kad'an,cikin low voice d'insa mai cike da haiba da sanyi yace, "Sagir in kana fad'ar haka sai nake ganin kamar ka mance wacece BAH......"

shiru yayi saboda aduk sadda zai ambaci sunanta wani ciwone yake taso masa azuciyarsa, runtse ido yai yana budesu akan sagir ya cigaba da cewa, "kasanta kasan wacece ita,kasan illar da tayi mun abaya kasan irin wuya da gwagwarmayar danasha, why kake cewa tabaka tausayi? Har kana goyon bayan na bar mata y'ata"

Daga yadda yake magana kasan akwai mikin dake taso masa,sagir ya amsa shi cikin son kare kanshi, "I'm sorry Aboki,ba ina nufin duk hakan bane, duk wanda yasanka da ita abaya yasan ta saka matsala ba kadan ba, amman ba shine zai saka ka kasa jin tausayin mutum a lokacin da kaganshi cikin wani hali ba, duk wani mataki da zaka dauka akanta ka dauke shi, wannan ne kad'ai ya rage tsakanin ku,tabbas idan ka rabata da Amnat karshen hukunci da zakai mata kenan, amman fa'iz ka tuna tsakanin d'a da mahaifi kayi rayuwa da iyayenka  tsawon lokaci har sadda Allah ya anshi ransu,kasan dad'insu kasan ciwon rabuwa dasu,shin inkaine matsayin Amnat ko Bahiyya a wane hali zaka tsinci kanka?"

"Yarinyar nan da cikinta tabar gidanka, ta haifeta tazo ta cigaba da renon ta tsayin wannan shekarun suna tare, sai ace rana tsaka za'a rabasu kai kanka abun baiyi maka wani kala ba don Allah,?"

Kallonsa kurin yake da idanun sa da suka sake rinewa, sagir ya cigaba da cewa "Har gobe ina tayaka jin haushin Abunda tai maka, amman wancen daban haka wannan daban, shekara ba kwana bace balle shekara shidda cikin ta bakwai,yaci ka mance haka nan duk da bai yuwuwa gaba d'aya, kuma ko ka anshi Amnat ba rabuwa kukai da juna ba fa'iz, dole za'ace mata tsohuwar matarka haka kaima akiraka tsohon mijinta, ni zan iya baka tabbaci da cewar Bahiyyar shekarun baya ba itace a yanzu ba, amman nasan b'ata bakina kawai zanyi ba yarda zakai ba, ni dai shawarata ka kara mata lokaci"

Kamal ne ya shigo da Sallama ganin sagir d'in yasaki fara'a yana cewa, "manya-manya inji k'anana ashe ana ganin ku?"

Suka cafke hannun juna suna musabaha sagir yana dariya yace, "ina manyan anan ai kune, kuna nan cikin kud'i ganin ku sai ancike form da interview"

Suka sanya dariya Fa'iz d'in yana taya su da murmushi, kamal ya aje masa wani file yana cewa,"akwai buk'atar ka sanya hannu anan jirana ake yanzu"

Bud'ewa yai yana karantawa daki-daki sannan ya sanya hannun yamik'a masa, yana cewa "Allah yasa basu yi mana raggon ciniki ba"

Kamal yace, "mun turza dasu sosai kasan masu jajayen kunnuwan nan sunfi mun son kud'i, amman dai daga karshe mu mukai nasara"

Ya ce, "to Alhamdulillah sannu da kokari"

"Yawwa, sagir bari na wuce sai mun sake had'uwa"

"To rankayadad'e"

Sukai musabaha sannan ya fice, tashi Fa'iz yayi yana dauko ruwa a frig yasha, yana tsaye jikin frig d'in yake cewa, "bank'i shawarar ka ba sagir,hasali ma ina sane ban sake taga maganar daukotan ba amman Anty muhibba ba zata tab'a barina na huta ba muddin ban daukota ba, karshe idan na b'ata mata rai karamin aikinta ne taje gidan da kanta,wanda nasan sai tayi rashin mutunci bana son hakan koba komi Daddy kamar mahaifina na dauke,ina ganin girmansa inhar ta cigaba da damuna dole zanje na daukota"

Jinjin kai sagir din yai yace,"na fahimta duk yadda kukai ba damuwa hakan Allah keso, zan wuce na baro aiki sai mun had'u"

Sukai sallama ya fice yabarsa da tarin tunanika.

***********

    *ASALIN MU*

Kakana Alaji Halilu dan asalin garin funtua ne,yayi zamanin sa mai cike da abun alfahari da tutiya don har gobe inkaje unguwar daya zauna acikin garin futua daka ambaci sunan sa, Alaji Halilu makiyayi tabbas inhar akwai wanda sukai zamani dashi zasu bada labarinsa, mutum ne nagari mai dattako mai alheri mai mutunci, sannan alokacin yana cikin jerin masu arzikin garin, don Alaji Halilu jarumin gaskene, ba zauna haka nan ba yafara da noma tun yana da yar gonarda d'aya ta gado katuwa, acikinta ne yake noma masara,gero,dawa,wake,waken suya,gyad'a kai acikun wannan gonar saiya noma abu goma acikinta, da haka da haka Allah ya bud'e masa kofar arziki,takai ga duk kewayen su babu mai tarin gonakin sa sannan babu wanda ke noma irin nashi, don masara kad'ai idan ya noma yana cire buhu dari da wani abu, banda sauran hatsi da kananun abubuwa, har takai ga kamfani musamman suke zuwa siyen hatsi wajen kakana, karma ace masara da dawa anfi zuwa sarinsu.

Kan kace me! Sunan Alaji Halilu yayi shura acikin funtua da kewayen ta, harma da wasu kasashen, tun yana matashinsa Allah yabashi baiwar Arziki duk abunda ya kama saiya bunk'asa, cikin wannan lokacin ne aka tasoshi gaba mahassada da yan bakinciki, cewar duk tarin dukiyarsa baida iyali waya sani ma ko bokansa ne yace karyayi,wannan surutun ya sashi cikin damuwa da yake hannun kawunsa yake bai tashi da iyayensa ba,kawun nashi ne ya tirsashi yin aure alokacin saboda surutun mutane, ya nema masa auren wata bafulata diyar wata mata dake kawo musu fura da nono, cikin wata uku akai auren su to sannan ne ya samu sauk'in magauta, amman duk da haka ba akyalesa ba.

Auren su da kaltume kakata kenan,ya kara kawo masa wani irin nasibi a rayuwa, don duka basu wuce wata shidda da aure ba ya bud'e wani gidan kaji wawakeke wanda ya ware wajen kiwon awaki tumakai da kuma shanu, sannan ya sake ware wani wajen wanda tantabaru ne kurin sai d'awizu a wajen, sannan wajen kajin kanshi shima daban aka shirya wajen sosai,sannan ya zuba ma'aikata wad'anda zasu ringa taya sa kulawa dasu, ya zab'o wadanda yasa nagarine bazasu ci amanar sa ba, kan kace me wani arzikin ya sake bai baye Alaji Halilu, ta ko ina sunan sa kakeji saboda irin wannan arzikin, sannan tsaye yake wajen addua da karatun qur'ani, daman kuma kawun sa malami ne sosai don har makaranta garai ta almajirai,

Haka rayuwar ta cigaba da tafiya yauda gobe bata bar komi ba, inyau an samu riba gobe fad'uwa daman haka rayuwar take, saida kakana suka shekara goma sha biyu da kakata basu samu haihuwa ba, duk yadda suka kasance cikin damuwa da son haihuwar Allah bai kawo ta da wuri ba, nan ma aka shiga yawo dasu agari maganganu marasa dad'in ji, kakata tayi kuka har ba iyaka ta dalilin wanan kukan ta samu lalurar ciwon ido saida gilashi take gani, cikin ikon Allah da taimakon sa sai gashi sun samu rabon yan biyu haihuwar fari,kuzo kuga farin ciki wajen masoya da abokan arziki karma ace kakana, aikuwa sunga gata baba hasan da baba usaini, duniya kanta ta shaida haihuwar su kuma daga ko ina gata suke damu ainun, Allah sarki ashe bama su rayuwa bane,shekarar su d'aya ko yayesu ba'ai ba suka fara zawon hak'ora da amai daga wannan shikenan, usaini yafara rasuwa da kwana bakwai sannan hasan yabisa, anci kuka an shiga damuwa daga karshe aka hakura aka barma Allah ikonsa, ashe kaltume nada wani cikin tun kamin rasuwar su,anan aka gane kila cikine suka sha.

Watansu tara da rasuwa ta haifi wani namijin mai suna kamilu, shima shekarasa daya yace ga garinku nan, wannan jarabawa itace babbar jarabawa da Allah ke masu,nafarko ga dukiya iyakar dukiya basu nemi komi sun rasa ba,amman Allah ya hana yaransu su rayu dasu.

Dalilin kamuwar Alaji halilu kenan da hawanjini ita kuma kakata idonta ya sake lalacewa,sai tayi da gaske sannan take gane mutane, haka suka cigaba da rayuwa shekara ta sake xagayowa ta haifo babana *ABDUL-KAREEM*

Basu nuna wani farin ciki sosai ba,saboda gani suke shima yana cika shekara guda zai mutu, saidai kuma Allah bai nufi hakan ba baban saida ya shekara goma daidai sannan kakana Allah yai masa rasuwa,kuma daga kan babana basu sake samun wani cikin ba, wannan mutuwa itace tayi silar makantar kakata kaltume,don kuwa tayi kuka tayi kuka har ba iyaka mutanen gari ma sunji wannan mutuwa ainun, aka share mako guda ana zaman makoki kafin kowa ya watse akabar kakata da babana, cikin kewa da kuncin rashi.

Hakan da kawu yagani yasashi cewa su dawo kusada iyalinsa saboda d'ebe kewa, kawu ne ya cigaba da kula da dukiyar kakana sannan yana kula da babana da kakata bakin iyawarsa, ahaka rayuwar ta cigaba da dad'i ba dad'i kakata anata nema mata magani asibitoci daban daban,Amma Allah baisa an dace ba a hakan kuma manema suka yo mata caaa wai suna son aurenta, ta buga kai ga bango tace ita da aure har abadan, kuma da dama ba wai sonta suke ba dukiyar dake kewaye da ita da d'anta suke son cinyewa,kawu da matar sa sune suketa bata baki da cewar har gobe bata wuce aure ba,tana kuka take cewa kawun.

"Bazan tab'a damun kamar Halilu ba kawu, duk wanda zaice yana son aurena ayanzu to hakika bani yake so ba, dukiyar wannan marayan Allah suke ma hari,taya zan tafi inmika ragamar sa hannun wani ya cinye"

"Kiyi hkr kiyi auren nida kaina zan tsaya tsayin daka wajen zab'ar wanda ya dace dake, dazai aureki don Allah badan dukiyar ku"

Da haka kawu ya fara bincikar duk masu nemanta aboye, yana nazartar su tsawon wata guda har Allah ya tsayar da zabinsa akan shafi'u wani dan kasuwa gwanjo yake siyarwa, ba laifi kawu ya samu kyakkyawan tabbaci kansa.

Wata guda bayan nan akai bikinsu ta tare harda babana, wanda lokacin yana aji uku secondary, zama ya cigaba tsakanin kakata da kuma malam shafi'u dafari zaman gwanin dad'i yana kyatata mata ita da babana, amman da tafiya tai tafiya zaman ba dad'i ga kishiyoyi sun tasota gaba, suyi mata shima yai mata.

Dole ta ringa daukar hidimar kanta agidan, data Babana don daman tuni ya daina masu komi, abinci kanshi daker ake basu idan andafa, ana cikin haka shekaru sun fara ja kakata ta haifi Baba Badaru, daidai da lokacin da kawu ajali yai kira,wannan tashin hankali ya sake fidda kakata daga hayyacinta, damuwa da bakin ciki suka zaja mata ciwon zuciya, saukin ma kamar kawun yasan ciwon sa bana tashi bane ya tattaro dukkan wasu takaddu yaba ta na dukiyarsu, sannan akwai wani dake tayasa kula da kadarorin nasu, ya sanar da ita inda zata sameshi zai damk'a mata komi inhar tana buk'atar hakan.

Mutuwar kawu kamar salla haka ta zamo ma shafi'u don tun daga lokacin yake wanda k'a da dabbobin su da duk wasu kiwon su, dayaji baida ko asi zaije yace kaltume taturo shi,babu musu za'a barshi yashiga ya dauki abunda yakeso yaje ya saida, yauda gobe komi yafara ja baya mutumin dake gadin wajen da kula da su yazo ya sameta daidai sadda malam shafi'un baya nan,

Tasha kuka sosai ranar babana yace mashi, "Baba saminu inaganin ka sanya gidan kajin nan kasuwa, da duk dabbobin dake warin asiyar dasu kaf,zanje na bud'e asusun banki a zuba kaf kudin aciki, inaga hakan zaifi da dai abarshi yaje yanata zarar su yana shagalinsa,"

"Kin amunce kaltume?"

Tana ta kuka tace, "ayi hakan malam saminu, ayi in aka biye shafi'u kashe mu zai"

Hakan akai aka saka cigiyar wanda zai siya,mutane nata jajanta abun mutuwa kenan mai tonan asiri, tunda shafiu yaji wannan labarin ya dawo a fusace, ya hau bala'i yana cewa tunda shi takema bakin cikin cin arzikin su, to wallahi sai babana yabar masa gida, ranar farko kenan da Ta maida masa magana da cewa,

"Ba shikadai zai bar gidan ba har dani, inhar ka koresa kamar ni ka kora"

Cikin hargagi yace, "au haka kikace ko? Toshikenan kije na sakeki saki daya,biyu,uku daman kin isheni banda wahala ma irin tawa mezanyi da makauniya,"

Wannan furucin shine ya bakanta ran kakata, ciwon zuciyarta ya tashi, haka babana ya dawo ya isketa kofar gida tana ta haki, ga kayansu nan a watse ga kanen sa nata kuka, don cewa yai shima ta had'a duka baya so.

Cikin tashin hankali ya dauki kanan nashi d'an shekara hud'u, ya tafi neman abun hawa don kai mahaifiyarsa asibiti, nan suka bar kayan su mak'ota suka tai asibiti, Allah sarki ashe tun a cikin adaidaita rai yai halin sa, daman tunda suka taho take bashi wasiyya,banda kuka babu abunda yake suna zuwa aka dunata akace  ai ta rasu.

Fadar irin tashin hankalin da babana ya shiga ba'acewa komi, ya dawo baida kowa aduniya sai wannan kanen nashi.

Mom muhsennโœ๐Ÿป

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.