Free chapter · Read without an account
chapter 15
RUFAFFEN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)
Karamci Writers Association.
Wattpad:Khairi_muhd
Arewabooks:Khairatup01
15
BIRNIN GWARI.
Ƙauyen Birnin Gwari kusa da kan iyakar Kaduna ne. Iska na kaɗawa, ƙananan yara na rawa a bakin wutar da aka kunna.Ƴan mata kuma suna zaune kashi-kashi suna hirar da ta shafe su.
Kawai sai jin ƙarar babura suka yi, wanan karon ƙarar ba ta babur biyu ko uku ba ce ƙarar baburan da yawa. Ji kake vrrrrrrrrrrrrrrm suka faɗo cikin ƙauyen kamar guguwar hamada. Fuskar maharan na lulluɓe da farin ƙyalle,da bindigu a hannunsu.
Jagoransu yace "ku kwashe su gabaɗaya kada ku bar ko guda ɗaya amma ku tuna kar ku kashe kowa."
Tuni kowa y firgita aka soma gudu ana ihun neman ceto ai kuwa jagoran ya saki harbi a iska aka kuma ruɗewa. Ƴan mata suka firgita,suka fara gudu,amma ƙarar harbin saman da yayi ya sa kowa ya tsaya cak a inda yake cike da fargaba da tsoro. Haka aka dinga saka ƴan mata suna hawa babur ko wann babur mace biyu ake ɗorawa cikin kuka da rawar jiki.
Haka suka kwashe ƴan mata ba tare da sun kashe ko sun daki kowa ba suka tafi suka bar su da hayaniyar kuka kawai.
Bayan tafiyarsu ,Dukansu suka zauna a ƙasa shiru kamar za a yi musu shari'a, ɗaya daga cikin mahaifin wanda aka ɗauka ya rarrafa ya zauna,ya dafe kan sa yana kiran sunan Allah cikin kuka.
Wani matashin saurayi ta miƙe yace "Ba zamu yi shiru ba! Sai mun sanarwa ƴan sanda ,sai mun bi sawunsu ko da kuwa sahun zai kai mu dajin Falgore."
Kowa yayi na'am da zancen saurayin amma cike da tsoro fal a cikin zukatan su. A daren yau dai ƙauyen ya koma musu tamkar makabarta.
Washegari!
Ina kitcen ina haɗa shayi saboda ciwon kai da ya ishe ni. Mama ta shigo da waya ta a hannunta.
"Amshi ke an ishe ni da kiɗin waya."
Maryam ta amsa tana dariya. A kunne ta kara ganin Shehnaz ce ta ke kiran ta.
"Madam!"
"Ana nan ana jiran ki maza ki shigo zaku tafi ɗauko rahoto a Birnin Gwari an sace ƴan mata sama da ashirin a daren jiya. Ina son jaridar mu ta fara wallafa labarin."
"To Madam."
Tana ajiye waya ta koma falo cike da tunani. Bayan zuwan ta gidan yari a daren kuma sai a sace ƴan mata sama da ashirin me yasa? Da gaske suke ashe da suka ce basu ba ne mastermind ɗin na nan daban. Wai duk me yasa ake wannan hare-haren ne? Ba zata samu amsarta ba sai in taje Birnin Gwari.
A gurguje ta shirya ta ɗauki duk wani abu da take so tayi sallama da Mama tana sa mata albarka.
Daga can Global Times aka kwashe su don zuwa wurin da lamarin ya afku.
Ƙauyen ya cika da ƴan sanda sai tsirarun ƴan jarida.Tunda suka sauka Maryam ke bin ko ina da kallo musanmman ma jam'ar da aka kwashe ƴa'ƴansu mata abin tausayi. Kallo ɗaya zaka yi musu ka ga zallar tashin hankali a tare da su da kuma raɗaɗin da suke ji na rashin yaransu a gabansu.
Babu shakka Maryam na ɗaya daga cikin ƴan jarida mai kwazo da kuma ƙarfin hali ba wai aikin take yi don kuɗi ko suna ba,aikin take yi don tana son tayi kuma don tana son gaskiya tayi halinta. Wata dattijuwa ta samu a zaune ta rafka tagumi abin duniya ya ishe ta.
Maryam ta saita ƙaramar kyamarar ta a hannunta tace "Baba ko za ki gaya min abinda ya faru? Ina son na san komai kuma nayi miki alƙawarin kai koken ku inda duniya zata ji kuma a taya ku nemansu."
Dattijuwar nan kuwa rai-rai ta fara zayyana mata labarin yadda abin ya wakana tun zuwnasu har harbin fark da yadda aka kwashe ƴan matan da kuma hanyar da suka bi suka wuce ta nufi Kaduna-Birnin Gwari expressway. Maryam ta rubuta wannan bayanan kaitsaye zuwa ofishin DPO a Kaduna.
Wani abokin aikinta Aminu yace" Maryam ,wannan lamari ba ƙarami ba ne. Wannan hanyar ta Birnin Gwari ce duk wanda ya san ta ,ya san haɗarinta. Kina da tabbacin za ki iya shiga cikin wannan binciken?"
"Aminu idan bamu shiga ba ,wa zai kare waɗannan ƴan matan? Zan bi wannan al'amarin har sai na gano inda suke."
"Yanzu muje ofishin ƴan sanda mu samu DPO, dole ne mu bayyana musu abinda muka samo muka kuma gano. Hakan zai taimaka wajen bincike sosai.A hasashensu ma kamar dajin kuyello, aka kai ƴan matan kusa da iyaka da da jihar Zamfara.
Wannan ba rahato ba ne kawai, wannan babban labari ne da tonuwar shi zai girgiza ƙasa gabaɗaya.
*
Sam yau bata ji daga wurin Muhammad ba. Daman ita ke neman sa. Ta tari adaidaita sahu don komawa ofis kiran Shehnaz Ahmad ya shigo mata. Bata yi wata-wata ba ta ɗauki wayar kuwa. Tun kan tace wani abu ta soma yi mata magana cikin fushi.
"Wa ya ba ki izinin kai rahato station? Aika ki nayi ki kawo min rahoton don mu wallafa ba cewa nayi kije can ki nuna iyayin ki ba. Yaushe za ki fara yin aikin ki kamar sauran ne?"
"Ba laifi ba ne don na kai rahoto satation ba, lafiya da kuma samun waɗanan ƴan'matan da aka sace shi ne a gaba ba wai mu wallafa a jarida ko mu haska ba.Ni ƴar jarida ce na yarda amma kafin nan ni ƴar adam ce kamar ke kamar su kamar kowa."
"Za ki yi bayanin wannan abinda kika aikata ki dawo nan da mintuna ashirin in ba haka ba yau sai kin bar aiki."
Maida wayar cikin jakarta tayi. Ranta cike da tunane-tunane fal ranta tana mamakin yadda rashin gaskiya da son zuciya da yaɗa labarai ya kwashe son gaskiya a doron duniya kowa TRP yake so ba a son ainihin gaskiyar magana.
Lumshe idanuwanta tayi cike da gajiya. A hankali take mayar da numfashi.
Ita fa ta sani zuciyarta ta ƙuna, kuma ta sani ba ita kaɗai ba ce take samun matsala daga wurin ubangidanta ba, amma wannan karon, mahanar Shehnaz ta shige ta fiye da sauran lamura. Wannan fa magana ke ta yara mata da aka kwashe an rasa ina aka kai su amma ita ta rahoton kawai take. Mtsw ta saki tsaki ta sa hannu tana murza idanuwanta. Mai adaidaita sahu na sauke ta ta sallame shi ta shiga cikin farfajiyar ma'aikatar ta su.
Kallo ta ga ana bin ta da shi hakan yasa ta gane akwai matsalar da gaske dai. Ko kwankwasa ƙofar bata yi ba ta tura ta shiga dake ita ma a sama take fuskokin mutanen ƙauyen kawai take gani na mata gizo yadda suka kasance hopless and tired akan lamuran duniya gabaɗaya.
Shehnaz na zauna a kan kujera ,hannunta riƙe da biro tana sa hannu a kan takardu tamkar ba ita bace yanzu ta kirata tana mata masifa ba.
"Na dawo." Ta faɗa a hankali amma da murya mai cike da ƙwarin guiwa.
Shehnaz ta ɗago kai ta kalle ta,idanuwanta suka nuna mamakin irin sautin da tayi amfani da shi wurin yi mata magana ba shakku ba fargaba.
"Bayanan fa?" Ta tambayeta kaitsaye ita ma.
Kujera ta ja ta zauna ba tare da an bata izinin zaman ba. Haɗe hannuwanta tayi ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.
"Madam Shehnaz wannan fa ba labari ba ne da za mu buga don mu samu kuɗi ba ne. Na ga tsoro da tashin hankali a cikin idanuwan iyayen yaran nan da aka kwashe,na ga yadda iyayensu suke roƙon Allah suna kuka da hawayensu."
"Bayani nace ki bani ba wa'azin ki nake son ji ba."
"Idan na dawo ofis don na rubuta labari kamar ba komai ne ya faru ba ,to ban yi aikin da zuciyata ke so ba."
Shehnaz ta kama haɓa tana kallon ƙarfin halin Maryam. Sai da ta gama nazarin ta tsab sannan ta janye idon ta gefe sannan ta ce mata. "In na fahimta kin fi so ki rasa aikin ki saboda abubuwan da ba ruwanki da su?"
"Idan aikin jarida shi ne kawai naɗa labarai domin samun riba ba don kawo sauyi ba, to ban san me amafanin shigata wannan sana'ar ba." Ta miƙe tsaye.
Shehnaz ta yi shiru na wasu sakannni bata ce komai ba sai da ta ga da gaske zata fita daga Ofis ɗin sannan tace "Maryam"
Maryam ta tsaya a bakin ƙofa.
Shehnaz tace "kin tabbata kin yarda da kan ki muma za ki iya kare kan ki?"
"Na tabbata.Ina tare da gaskiya babu abinda zai same ni. Kuma zan ci gaba har sai na gano waɗanda ke da hannu a wannan kwashe yaran."
Ta fita daga ofishin ba tare da ta kalli ko ina ba. A zuciyarta ta riga ta yanke shwarar wannan lamarin ba labari ba ne a wurin ta kawai gwagwarmaya ce."
Kan teburin ta ,ta koma ta zauna ,wayarta tayi ƙara. Sunan ta kalla a hankali ta furta "DSP Hamza."
Ɗaukar wayar tayi tace "Yallabai."
"Muna da wata shaida na san zai taimaka miki."
"Yallabai. Me aka samu?"
"Mun kama wani yaro ana zargin da sa hannunsa da satar yaran nan a daren jiya."
"Kai Yallabai na ji daɗin wannan labarin."
"Za ki iya zuwa?"
Tuni ta suri jakarta ta miƙe a lokaci guda tace "Yallabai na taho ma."
Cikin sa'a tana fita ta samu adaidaita sahu , suna tafe zuciyarta na bugawa da sauri kamar ana kaɗa mata gangi. Wannan ba ƙaramin ci gaba ba ne a wurin ta. In har da gaske yaron da aka kama na da sa hannu a wannan harin da aka kai Birin Gwari to tabbas zasu san su waye silar hakan.
A hanyar ta na zuwa station ɗin ta ga kiran Muhammad ya shigo mata da sauri ta ɗaga.
"Miss kina ina ne?"
"Ina hanya zan je station akan wannan case ɗin."
"Kina da buƙata ta a wurin?"
"In dai baka komai zan so ka kasance a wurin."
"Zan zo na same ki a wurin nan da mintuna goma sha biyu haka. Wannan wata dama ce da ba za mu bari ta kubce mana ba."
Suka ajiye waya.
Dsp ya tarbe ta da fuska mai nuni da lamarin na da muhimmanci sosai.
Maryam muje ciki ,zo ki gan shi. Ya faɗa yana nuna mata wani matashin saurayi wanda shekarunsa basu wuce talatin ba, hannunsa ɗaure da ankwa. Idanuwansa cike ta tsoro,gumi da yake zubo masa yake kamar wanda ya yi gudun awanni.
"Ya bada wani bayani ne DSP?"
DSP ya gyaɗa mata kai. Ya nuna mata wuri ta zauna tana kallon saurayin.
"Bai faɗi komai ba amma yace da shi a cikin maharan ,sannan akwai sunayen da ya sani amma yana tsoron ya faɗa su kashe shi."
Da sauri Maryam ta ja kujerar ta gaban DSP tace "Yallabai in ku ka ba shi tsaro da kariya zai faɗa. Ina son ka bani damar yin magana da shi a ƙebance."
DSP ya tafi tunani kafin yace "Zan baki mintuna goma sha biyar kawai. Amma ki sani ,abubuwan da zai gaya miki zasu iya tada jijiyar wuya ga mutane da yawa."
Maryam ta gyaɗa masa kai da sauri tace "Na sani! Kuma na shirya."
Maryam ta shiga ɗakin binciken inda aka maida mai laifin. Zaunawa tayi tana kallonsa da kyau. Recoder ɗinta ta kunna ta ajiye a ƙasa daga gefe.
"Sunan ka?" Ta tambaye shi cike da murya mai laushi.
"Kabiru." Ya amsa kaitsaye muryarsa na rawa.
"Me yasa?"
"Ni dai ba ni da niyyar cutar da kowa.Na yi aikin ne saboda ina cikin talauci da yunwa. Ban ma san abinda zamu yi kenan ba."
"Ya akai ka shiga tawagar?"
"Wani abokina ne ya kira ni. Yace min wanda ya ɗauke mu aikin babban mutum ne."
"Yaya sunan sa?"
Shiru Kabiru yayi jikinsa na rawa cike da tsoro.
"Look! Kabiru idan ka faɗi gaskiya zaka ceci yara da yawa da aka rabasu da iyayensu. Kai kan ka na san kana da na sanin aikata wannan ɓarnar.ka sa kan ka a matsayin iyaye da yayye da ƙanne na waɗan da aka sata yaya zaka ji in kai ne?"
Kabiru ya kalle ta idanuwansa na fitar da ƙwalla. A hankali yace "Bana son na rasa raina ta wannan hanyar ban taɓa yi ba sai wannan karon ,yaran sun bani tausayi, na kasa daina ganin fuskokinsu cike da roƙo da hawaye da neman taimako. Madam,ina da yaƙinin ba wai iya satar ba ne akwai wani abu da ake shiryawa wanda hakan zai ɗauke hankulan jama'a da hukuma daga wani babban laifi da ake son kaddamarwa."
"Amma me yasa ka kawo kan ka gaban hukuma?"
"Saboda na san ko na faɗa sai sun kashe ni ko ban faɗa ba ma zasu kashe ni, don na san yanzu sun samu labarin kamanin da aka yi kuma suna shirin yadda zasu kawar dani daga doron ƙasa don kar na tona musu asiri. Madam ki kula da duk wani da kike ganin ki yarda da shi zai kyautu ki yarda da iya kan ki kawai."
"Kabiru ka yarda da Allah. In sha Allahu babu abinda zai same ka. Ƴan sanda zasu baka kariya."
Murmushin gefen baki yayi ya ɗauke kai yace "Madam, ƴan sanda,ƴan jarida,ƴan siyasa duk akwai ɓata gari a cikinsu. Ke ma don na yarda da ke ne da shi DSP ɗin ne yasa zan gaya muku kuma na san ko ba ni zaku yi ƙoƙarin banƙaɗo gaskiya."
"Na gode."
"Alhaji Tukur , da kuma Alhaji Ɗanzaki,da wasu guda biyu wanda ban riƙe sunayensu ba. Amma suna da yawa ba mutum ɗaya ko biyu ba ne, mutane ne da dama."
"Ya akai ka san sune?"
"Sune suke kawo mana kuɗi. Aikin mu kawai shi ne mu sato yaran mu kai su wani gida wanda ake kira da "Farm House".
Da sauri Maryam ta zaro wata takarda daga aljihunta zanen taswira ne. "Zaka iya nuna inda Farm House ɗin yake a nan?"
Ya kalli taswirar da kyau, ya kuma jinkirta a nutse a hankali ya nuna wata hanyar wani ƙauye mai nisa da gari sosai. Da sauri Maryam ta sa biro tayi circling ɗin wurin ta cusa a jakarta gudun kar wani ya gani.
Tana fita ta ce da DSP sun gama magana. Kuma su cika alƙawarin ba shi kariya har a yanke mai hukunci. Ya so ya ji ko ya gaya mata wani abun amma ta ƙi sanar masa da komai.
Tana fita ta ci karo da motar Muhammad daga tsallake yana jiranta. A gajiye ta isa wurin motar ta buɗe ta shiga gidan baya don ta ga kamar akwai direba yau.
"Sannu Miss."
"Yauwa."
"Akwai bayani ne?"
Ta kalli direbansa ta kalle shi. Yace "Oh! Journalist Madam na manta privacy. Za ki ci abinci?"
"Aa a maida ni Global Times."
"Aa zamu je mu ci abinci ne. Nima dawowa ta kenan."
"Ina kaje?"
"Akwai kayana da suka zo naje clearance ne."
"Oh!"
Ya gayawa Direba inda zai kai su.