Free chapter · Read without an account
Episode 5
*MUGUN ICCE*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.....*
PAGE 5
*House No 26, Gadon ƙaya, Kano State Nigeria*
Kallon ƙofar gidan Yusura tayi ganinta ita ɗaya ta shigo cikin gidan, ta kasa haƙuri ta ce.
"Umma ina Salma?"
Wata uwar hararara ta watsa mata tana cire Hijab ɗinta ta zauna a tsakar gidan tana faɗin.
"Ban sani ba, na je na sayar da ita"
"Allah ya baki hakuri Umma tabbaya ce fa nayi"
"Matsww to ban sani ba"
Ganin Aunty Murja a sama-sama take yasa Yusura ɗauke kanta daga gare ta tana maida dubanta ga wayar Salma da take ta dannawa tun ɗazu.
Kallon wayar ta sake yi ganin kira ne ya shigo yasa Yusura ɗauke kanta daga wayar tana kallon Umma data juyo tana dubanta itama, bata ce komai ba ta danna wayar tana saka ta a amsa kuwwa.
"Hello Aunty Ummi!!"
"Yusura wai har yanzu bata dawo ba Salma?"
"Eh, amma yanzu kin ganta ta dawo insha Allah"
"Matsww tana can yawon ta zubar ya za'ai ta dawo da wuri, yawo ne dai irin wadda kuka saba shine ta je"
Cewar Aunty Murja tana miƙewa gaba ɗaya kamar zata shige ɗaki sai kuma ta ja ta tsaya, jin wata magana da Ummi ɗin ta mayar mata.
"Shi dai babba ya kasance kullum yana riƙe girmansa dan Allah, saboda dai shi mutumci Madara ne idan ya zube baya kwasowa yawwa".
Cike da masifa Aunty Murja ta waigo tana duban wayar kamar Ummi ɗin ce a kusa da ita, a yadda ta waigo a zuciye tana jefama wayar wani mugun kallo.
Da sauri Yusura ta datse kiran tana kallon Aunty Murja da jikinta ke rawar masifar dake cinta.
Nuna Yusura tayi da yatsa tana cewa.
"Maza-maza ki kira min marar kunyar nan, Allah sai na ci mata mutumci, yau sai ta gaya min wadda take faɗa ma magana haka"
"Haba Umma, kefa kika ja ta faɗa miki hakan, kiyi dai haƙuri yanzu please, idan an kira ta to fa haka zakuyi ta faɗa ma juna magana, dan kin san dai Aunty Ummi bata shanye wulaƙanci kamar yadda kike ma Aunty Salma, ita Salma mai haƙuri ce da kawaici, amma Aunty Ummi bata da duk wannan"
"To ub*an waye zatai mawa?, kuma wallahi zata san waye ta faɗa ma magana haka, ni nasan mi zanyi ai"
Yusura zatai magana kenan suka ji ƙarar mota a ƙofar gidan, da sauri Yusura ta miƙe tana cewa.
"Lahh ko Baba ne ya zo yau?"
Taɓe baki Aunty Murja tayi tana daga tsaye Yusura ta zo ta wuce ta ta nufi waje.
Jim kaɗan sai ga Yusura da Salma sun dawo cikin gidan, Yusura riƙe da wata baƙar leda a hannunta tana riƙe da hannun Salma.
"To ikon Allah sai kallo, wato ke aka aje a Mota ba?, ohh'ni Murja, ke ko kunya bakya ji ma?, baki da lafiya ma amma sai kinje kin nemi Maza a waje?"
Cakkk Salma ta dakata tana kallon Aunty Murja cike da wani irin bala'in raunin zuciya, zatai magana kuma sai ta fasa tana wucewa ɗakinsu da ɗan gudu saboda kukan daya taho mata.
"Haba haba Umma, bafa wani ne ya kawo ta ba, Doctor ɗin da ya duba ta asibiti ne ya rage mata hanya ya kawo ta har nan ƙofar gidan shine ya wuce, da yake ya ce hanyarsa ce nan ɗin"
"To wannan baƙar leda ta ub*an mi ce?. Shima dai Doctor ɗin da alama irinsu ne, ko shi ne yasa ma bai faɗa min gaskiyar abunda ke damunta ba?"
Aunty Murja ta faɗa tana ɗan riƙe baki alamar ɗan mamakin data shiga.
"Wai Umma mi yasa kike haka ne dan Allah?"
"Dalla ni rufe mini baki. Miƙo ledar nan kuma"
Da mamakin halayya irinta Umman tata ta miƙa mata ledar tana ƙara bata mamaki.
Buɗe ledar tayi tana kallon abunda ke ciki tana cewa.
"Ba shakka lallai kuwa, kayan daɗi ne ma a ciki, ai dole ya siya mata kayan daɗi man tunda ya gama samun rabonsa shima"
Girgirza kai kawai Yusura tayi tana wucewa ɗakinsu.
Ita ko Aunty Murja a nan ta ƙara zama ta ɓararraje ta fiddo kayan cikin ledar ba kunya ta kama ci tana mita tana ƙarawa.
"Dan Allah Aunty Salma kiyi hakuri haka nan, ki daina wannan kukan"
Share hawayen dake zubo mata tayi ta ce.
"Babu komai Yusura na daina"
"Yawwa Aunty Salma, ya kamata dama wannan halin da Umma ya ci ace kin saba dashi ma"
"Hmmm"
Kawai Salma ta sami kanta da cewa, tana ayyana wa a ranta, ya za'ai mutum ya saba da cin mutumci da wulaƙanci a kullum fa da sabon rashin mutumci da cin zarafin da Aunty Murja ɗin ke ɓullo masu dashi, ya za'ai ta iya jurewa?.
Dafata taji Yusura tayi ne yasa ta katse tunanin data faɗa, Yusura ta ce.
"Kinga ga wayar ki Aunty Salma"
"An kira ne ko?"
"Eh an kira ki bayan kun tafi, Aunty Ummi ce sai wata number ban ɗauka ba dai, shine ma duk ya ishe ni da kira"
"Ayyah ina ga Abdul ne fa"
"Mtsww dan Allah Aunty Salma ki rabu da wannan Abdul ɗin, kwata-kwata bai dace dake bafa, kar kiyi kuskuren zaɓarsa a matsayin abokin rayuwarki please"
"Uhmm Yusura kenan, idan ban fiddo dashi ba waye zan fiddo to?, kina gani duk yawan masu suna ɗin babu wadda ke maka maganar aure, shifa shi ya nuna auren nawa zaiyi, duk da nima nasan tabbas bai cancanta ya zamo mijina ba, halayarsa ba mai kyau bace, kuɗi kawai yasa a gaba, baya bada mahimmanci sai akan sana'arsa, kullum dai jiya iyau nayi-nayi ya sauya amma ina"
"Hmmm lallai Aunty Salma wallahi ɗan ƙauye ne zam wannan Abdul ɗin naki"
Girgiza kai kawai tayi tana lalubar number ɗin Ummi ta kira.
Tana ɗauka sai Yusura ta miƙe ta shige uwar ɗakin nasu tabar Salma a parlon.
"Na kira wayar ki Yusura ke ce min wai kun tafi asibiti baki da lafiya?, mike faruwa ne?, muke damunki to?"
Daga cikin wayar Ummi ta faɗa bayan ta ɗauki kiran sun gaisa a taƙaice.
Sauke lumfashi Salma tayi tana ɗan gyara zamanta ta jingina da jikin kujerar da take zaune ta ce.
"Wallahi Aunty Ummi zazzaɓi ne na tashi dashi shine yasa muka je asibiti"
"Hmmm baza ki dai faɗa min gaskiyar abunda yasa Aunty Murja ta kai ki Asibitin ba?, dan nasan wacece ita ko mutuwa zakiyi bana jin zata iya rakaki wani asibiti"
Shiru Salma tayi na ɗan wani lokaci, jin tayi shiru yasa Ummi ƙara cewa.
"Ko dai ma miye aniyarta tabi ta wallahi. Sana Allah ya baki lafiya. Inaga nima gobe ki jibi zan taho Kano ɗin nima"
"Wai da gaske Aunty Ummi?"
"Eh amma gaskiya ba wai dan ina so zan zo ba, Mama ce ta matsa min dole sai naje gidan Aunty Binta na zauna mata koda na sati biyu ne ko wata ɗaya, kin riga kin san kuma bana ƙaunar zuwa inda Aunty Binta take"
Salma tayi shiru tana tunanin ai da zama gidan Aunty Binta gara ta zauna tare da Aunty Murja, dan ita Aunty Binta ko zama kuyi fira bata yi, kullum fuskar nan a murtuƙe take, ba sakin fuska, ga saka aiki na bala'i da gadara da take yi. Garama sunfi shiri da ita Ummi ɗin, amma ita kwata-kwata basa zama a waje ɗaya sai sunyi faɗa, duk da faɗan Ummi idan taje gidan Aunty Binta bata yi, duk wani abunda ta ce tana mata, gudun ɓacin ran Mama ne kawai yake dakatar da Ummi. Kai ko dai ina babu daɗi, tunda nan ma ɗin babu maraba da hakan.
"Gaskiya Mama mi yasa take haka?, mi yasa bazata barki a gida ba kawai?"
"Hmm tunda ta kira ta zuge ta cewar wai idan muna zaune a ƙauyen nan ya za'ai mu sami miji?, wai sai dai mu ƙare a nan miji kuma sai dai mu sami ɗan ƙauye, ita kuma wai bata so mu zauna rayuwarmu ta ƙare a ƙauye. Kinji fa Salma?, sai ka ce ban san wacece Aunty Binta ba, auren ma namu ai baƙin ciki take da mu sami mijin muyi Auren, ita ai so take kawai muyita zama a haka ta yadda za'a rinƙa turo mata mu muna mata bauta, ai duk na gano ta wallahi"
"Kai Aunty Ummi"
Salma ta faɗa tana ɗan murmushin ƙarfin hali.
"Hmm kina jin wasa ko?, ki daina ganin ko dan mun fito ciki ɗaya da ita, kin mance ne ba uba ɗaya ya kawo mu duniya bane?, nifa tunda nake ban taɓa ganin mai baƙin hali irin na Aunty Murja da Aunty Binta ba, abunda bai kai ya kawo ba suke maida shi na faɗa da abun tsegumi, amma ni kaina nasan ƴan baƙin ciki ne, basu so kowannen mu yayi gaba sai su kawai suke so suyita yin gaba kai kana bayansu, taya za'ai kuwa a ci gaba a rayuwar nan?, yama za'ai su so mu sami miji wai ma a birni?"
"To Aunty Ummi kusan hakan ne gaskiya, saboda komi zamuyi na ƙaruwa bata nuna farin ciki ko jin daɗi a fuskarta sai ta kushesa, ita Aunty Binta dama halinta ne wannan, amma wannan dama Aunty Murja ai ita idan ta nuna za'a iya cewa kishi ne take dama da iyayenmu damu kanmu, shi yasa nima na fara zargin hakan a tattare da ita, Allah dai ya kyauta kawai amma mutum mugun icce ne babu abunda bazai iya aikatawa ba hakan abunda zuciyarsa ta kitsa masa"
"Uhum Allah dai ya kyauta, amma aniyar kowa ta bisa wallahi. Nifa na fara tunanin wani abu ma Salma, amma dai sai na zo Kano ɗin zamu haɗu ne ai insha Allah, sai munyi magana yanzu dai idan na zo ɗin"
Sallama sukai ta kashe wayar tana ɗan kallon baƙin kofar fita tana zurmawa kogin tunani sosai.
Tayaya za'a ce uwa ɗaya ta kawo su duniya amma wai ace a ɗaki ɗaya a sami mai maka baƙin ciki da ci gabanka ko samunka?, anya wannan rayuwar za'a ci gaba kuwa?.
Sosai take tunanin halayyar Aunty Binta ɗin kusan duk jirgi ɗaya ya kwaso su ita da Aunty Murja, duk ta ɓangaren wani baƙin halin nasu na ɗaya yafi na ɗaya.......