Free chapter · Read without an account

Chapter 1

by Khadija Gambo Ali · RANA ZAFI

Tunda gari ya waye take jin wata irin faɗuwar gaba mara misaltuwa, ga wani uban zillo da cikinta yake yi tamkar mai shiri fitowa duniya yau, abunka da mai tsohon cikin fari dan haka sam hakan bai ɗaga mata hankali ba.

Cigaba tai da sabgoginta na yau da kullum har izuwa lokacin sallar la'asar, yayin da a gefe guda kuma bugun zuciyarta ya sake tsananta, jin abun ba na ƙare bane yasa ta nemi guri ta zauna, zancen zuci ta fara don gaba ɗaya bugun zuciyarta ya hanata sukuni, ga babyn cikinta da yake ƙara takura mata wajan shure shure tamkar zai turo fatar cikinta ya fito.

"Ikon Allah mu kuma tanan muka fara tamu naƙudar?" ta faɗa lokacin da ta haɗa kai da gwiwa.

"To amma an ce min ciwo ne zaka ji shi wanda tunda iyayenka suka haifeka baka taɓa jin irinsa ba?, to ai ni kuma ba ciwo nake ji ba, duk da ma iya wannan mutsu mutsun ma ya isa in tabbatar da naƙuda nake yi, don yau lamarin na daban ne" tayi tambayarta ta bawa kanta amsa.

Ta jima a zaune kafin ta yunƙura ta tashi tare da ɗaukar buta don yin alwalar sallar la'asar, dakyar take sunkuya wa wajan yin sujjada saboda matsin da cikin yake ta yi mata, gashi gaba ɗaya ya hanata sukuni dan haka tana samu ta idar ta samu guri ta baje ba tare da ta iya samun damar karanta koda ayatul ƙursiyyun da ta kasance tana karantawa a bayan kowacce sallah ba.

Barcine mai nauyi ya ɗauke ta, saboda yadda iskar sanyin la'asar yake ta busawa, cikin barcinta taji ƙarar mashin ta karaɗe illahirin cikin layinsu.

Har zuciyarta taji ba daɗi saboda yadda ƙarar ta cika mata dodon kunnne, wani guntun tsaki ta ja mara sauti kafin ta fara gyara kwanciyarta don gaba ɗaya wuyanta ya sage.

Sai da ta ɗan jingina da jikin gini sannan ta ɗan samu sawabar kwanciyarta ta.

A daidai lokacin kuma mai mashin ɗin da ya cika ta da ƙara ya tsaya a daidai ƙofar gidanta,

Tsaiwarsa tai dai dai da lokacin da zuciyarta tayi wani irin mumunar bugawar da tunda take bata taɓa yin irinta ba, baki ta buɗe da zummar addu'a amma me kawai taji ana buga ƙofar gidan.

Sake jan uban tsaki tayi kafin ta kama jikin banpgon tana ƙoƙarin miƙe wa saboda barci da tayi gaba ɗaya jikinta ya ƙara nauyi.

Hijabin dake jikinta ta gyara tare da sanya takalman dake kusa da ita sannan ta nufin ƙofar fita tana faɗin

"Waye?"

Shiru ba'amsa, dan haka a hasale ta sake faɗin

"Wai waye ne haka?"

"Buɗe ki gani mana!"

ya bata amsa cikin kakkausar muryar da sai da ta ɗan firgita saboda yadda muryar tasa take da kaushi.

Jitai kamar karta buɗe don sam bata da haɗi da mai makaman ciyar wannan muryar, tanan nan tsaye ƙikam aka sake buga ƙofar tare da faɗin

"Ko bazaki buɗe ba ne?, to saƙo aka bamu idan kuma mu mayar to!?" ya faɗa a hasale.

Ko amsa bata bashi ba ta kai hannunta da yake rawa tai unlocked ɗin ƙofar.

Tana buɗewa tayi arba da waɗansu mutane guda biyu waɗanda yau itace rana ta farko da ta fara arba dasu a rayuwarta, ko ƙala basu ce da ita ba saima ledar da na bayan ya miƙo mata da faɗin

"gashi? aka ce a kawo miki"

Fal zuciyarta ta cika da tarin tambayoyin wanda kallan yanayinsu da yanayin fuskarsu yasa ta kasa ce musu komai.

Hannu ta miƙa ta ƙarɓa ba tare da sanin waya aikosu?, mene ne aciki?, tana ƙarɓa su kuma suka ja mashin ɗinsu suka barta tsaye tare da tarin tambayoyi.

Zuciyartace ta shiga wani irin wasu wasi gami ga addabar jerawa kanta tarin tambayoyin da suka gaza futa daga cikin bakinta a gurin waɗanda suka dace, ganin sun yi nisa da barin ƙofar gidan yasa ta rufe ƙofar gami da komawa ciki.

Jiki na rawa ta nemi guri a wurin da abun sallarta yake ta zauna, ledar farko ta fara kwance wa, ganin jini ajiki yasa ta fara tunanin shin wa zai aiko mata da nama mai uban yawa haka?.

Jitai kawai zuciyarta na rawa dan haka da azama tasa hannu ta yaga ledar ciki tare da ware idanun akan abinda take tsammanin naman ne!!!

Caraf idanunta ya sauka akan abunda ya ɗimauta ta, ko gama tantance abunda yake cikin ledar ba tai ba ta saki ledar jikinta ya ɗauki tsuma haɗi da ƙarkarwa, bugun zuciyarta ya nin ninka na da, take numfashinta ya dinga season, lokaci guda kuma ta silale ƙasa sumammiya.

Sanyin iskar damunar da ake ciki ne ya dawo da ita daga doguwar suman da tayi, sosai ƙura ta baɗe ta.

A hankali ta buɗe idanunta saboda yadda taji ƙasa a saman idanunta, ƙoƙarin yunƙurawa ta fara yi tare da jingina da bango kafin ta zauna.

Ko da ta zauna tunanin ta shiga yi "shin ma me ya ɗauki hankalinta har tai barci a guri?"

A firgice ta miƙe tsaye tamkar ba mai tsohon ciki da zata iya haihuwa a koda yaushe ba, sai da ta tattaro jarumta kafin bakinta ya iya faɗin "innalillahi wa'inna ilahirraju'un!!!" lokacin da tai arba da fuskar jaririn da aka guntile masa kai gefe guda kuma ga hannu nan da aka guntule daga jikin gangar jikin, daga ƙasa kuma ƙafafunsa ne guda biyu wanda kowacce banda jini babu abinda ke zuba a jikinta,sai alokacin ta fahimci jaririne akai masa gunduwa gunduwa.

"Na shiga uku!!!, me nai muku? su waye ku? waya aiko ku? me na tsare muku!!!!, dan Allah kada....."

Dakyar ta haɗeye maganar sakamakon nocking ɗin da taji anyi.

"Ke dalla ki buɗemin tunda ba gidan ubanki ba ne" ya faɗa muryar nan cike da bala'i.

Cikin matsanan cin tashin hankali ta daddafa ta miƙe, da kyar take iya ɗaga ƙafa saboda gaba ɗayanta ba ta cikin hayyacinta.

"Wallahi baki buɗe ƙofar nan ba, ki ka sake na ɓalleta Inna shigo sai na ɓaɓɓalla ki dan ba ruwa na da wani nauyi cikin ki kwakwarfe ki....."

Jinta buɗe ƙofar yasa shi yin shiru tare da shigewa ciki har yana mangare ta.

"Ke baki san kurar da na baro a lungu ba shine ki ke ƙoƙarin sai ta ƙariso har maboya ta ko, dalla ki rufe ƙofar?" da idanu kawai take binsa har ya wuce ta.

"Kan uban can, ke zainab uban meye wannan?, 'yar babyn roba kika yanka ko kuwa mutum ce" sam ta kasa magana don gaba ɗaya ma ji take kamar ba'a duniyar take ba.

Ido ya shiga murjewa don gani yake kayan cajin da ya afa a ɗakin 'yar caras bai sake shi ba, shi yasa sam bai gani da kyau.

Fuskarsa ya shiga mari don tabbatar da cewar dagaske ɗan mutumne ko kuwa dai kayan cajin ne ke haska masa hakan, hannu ya kai ya ƙara mirgina ledar, cikin tashin hankali ya kalli Zainab dake tsaye kamar an dasa ta yace.

"Ke a gidan ubanwa kika samu gawa?, so ki ke in ƙare a gidan ɗan kande, to wallahi baki isa ba, wai ba magana nake miki ba ki ke kallona da idanunki irin na mayu"

Cikin rawar murya tace da shi "Ai na ɗauka kai aka kawo wa?"

"Wa?, ƙarya ki ke wallahi, yo da wannan bala'in ai gara in koma daba ayi kamen dani nasa duk tsiya bazan yi sati ba" sai yanzu wani irin kuka ya ƙwace mata.

"Wallahi kabiru wasu ne suka kawo a mashin, bansan su ba, bansan daga Ina suke ba"

"Kan uban can, mahaukayar ina ce ke da za'a kawo miki yankaken jaririn ki ƙarba?, kinga bama wannan ba na rantse da Allah sai dai ki san yadda zaki da shi, dan wallahi legasma ƙasan gada tai min kaɗan, jar'uban" ya faɗa lokacin da yake ƙoƙarin shiga ɗaki.

Sake raushewa tai da wani uban kuka jin furucinsa, to idan ya gudu ita ya zata yi?.

Abinka da ƙungurumin ɗan barikin da dama ba'abin arziƙi gare shi ba, ya fito da uwar bakkonsa a hannu yana ƙoƙarin fita.

Kamar an hakaɗo ta haka ta ƙariso gare shi ta durƙushewa tana faɗi.

"Dan Allah kar ka tafi kabar ni, wallahi in ka tafi basan a halin da zan tsinci kai na ba, kaji tausayina kabiru, ka sani duk a yadda kake, duk rintsin daka faɗa bazan iya tafiya na barka ba, dan Allah karka tafi ko don abin da ke cikina"

"Zainab! Zainab!!,Zainab!!!, sau nawa na kira sunanki, sau uku ko, to ko ba lanƙaya min ke akai ba sai na barki, bare kuma lanƙaya min ke akai, dan haka idan 'yan ɗari ne a cikinki bana so, na bar miki, dama kinsan ni ba ƙaunar cikin nan nake ba, kinga gyaramin in wuce tun kan ƙwalawa su zo yin ram dake su haɗa dani ki cuce ni da ƙuruciya ta in ƙare a bursin"

Ganin da gaske tafiya zaiyi yasa ta ƙanƙame shi ta nai masa magiyar yaji tausayinta.

Suna cikin wannan halin aka bugo ƙofar gidan, gaba ɗayan su sake kiɗemewa suka yi, a gigice ya hanƙaɗata baya yana faɗin.

"Wallahi ƙarya ne, ni zaki gogawa muguwar ƙaddararki, to bada Kabiru ba wallahi, kinga tafiya ta, kuma na sake ki saki uku ke in ana saki hamsin to nima nai miki"

Katanga ya kama zai haura sai ya hango kalil ne da kwanon abinci a hannu yana kwankwaso ƙofar, katagar ya saki don dama taga taga yake kamar zai faɗo, ƙofa ya nufa ya buɗe tare da arar ta kare ya nausa.

Irin hankaɗar da yayi mata yasa ta sakin wata mahaukaciyar ƙara, a firgice kalil ya ƙariso gare ta, kwanon tuwon da ya kawo mata ya aje agefe yana faɗin

"Dukan ki yayi ko anty Zainab?, kiyi haƙuri ki tashi ki bar shi da Allah"

Dakyar take numfashi saboda wuya da azaba ga kalmar kabiru ta ƙarshe tai barazanar tarwatsa kwakwalwar kanta.

"Dagaske ka sake ni?, nashiga uku ni! nashiga uku ni zainab rana zafi inuwa ƙuna, dama na mutu na huta daganin wannan baƙin ciki"

"Anty ki tashi, nasan kina jin yunwa ga abinci na kawo miki"

"Kalil, kai kaɗai kake sona daga kai sai ya sadeeq, nagode da ƙaunarku gareni ka tafi gida mutuwa zanyi, mutuwa zanyi wallahi kalil"

"Anty baza ki mutu ba bara inje in kira hajiya"ya faɗa yana mai fita da uban gudunsa.

Nan nauyan abu ne ya tsaya mata a ƙirji, ga uban kokawar da take tayi da numfashinta da yake ta ƙoƙarin ƙwacewa, tana cikin wannan halin mararta tayi wata irin murɗawar da sai da numfashinta ya ɗauke na wucin gadi, cikin matsanancin hali ta ɗaga hannunta da ta dafe mararta dashi tace.

"Ya Allah kai ne buwa yi gagara misali, kai ka halicci tsanani sannan ka halicci sauƙi ya Allah kayi ikonka akan wannan jarabawar da ta sake kutsowa rayuwata, ya Allah idan mutuwa hutu ce a gare ni ya Allah ka ƙarɓi rayuwata in huta da wannan kaddarori rayuwar"

Murƙususu ta shiga yi tamkar zata zauce ta cigaba faɗin

"Ya Allah baiwar nan taka ce wace ta taso acikin azabtacciyar ranar da har yanzu bata samu ko da inuwar mutum ta kare ta ba, ya Allah kaimin ɗaukinka"

Mu haɗu next page don Jin cikakken littafin Rana zafi....

Taku oum fu'ad

***

Follow for more pages

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.