Free chapter · Read without an account

Chapter 97-98

by Amanarcool · RAMIN ƘARYA...

💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫



_WRITING BY AMANARCOOL_✍️



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



Page 97&98


__________"Hajiya kamar yadda na gaya miki munsan inda Abbakar yake, kuma yana nan cikin ƙoshin lafiya, sannan yarinyar ma dana ke tunanin ita ce ƴar da Zainab ta haifa mun ganta da idonmu ni da Musa ɗin".

"Munir sai ƙunbiƙunbiya ka ke yi mini ka fito fili ka yi mini bayani yadda zan fahimta".

"Hajiya ki kwantar da hankalinki za ki ji sauran bayanin daga baya, wannan ma na faɗa miki ne ganin yadda ki ka ɗaga hankalin da tunanin inda za a nemu Abbakar ne".

Sosai Zainab ke kuka, Fatima na rarrashinta da ba ta haƙuri. Duk da tasan an zalunceta da yawa. Sharifa sai matsar ƙwalla take yi.

Abba ya yi shiru ya kasa magana, sai bin kowa yake yi da ido, ya ɗakko wayarsa ya yi danne-dannensa ya ajiye wayar.

Sai bayan da Turai ta gama fayyace komai wani irin tsoro ya shiga, ta ji hanjin cikinta na ƙullewa, tasan ita ma ba barinta za a yi ba. Dan haka ta miƙe tsaye babu kunya ta nufi hanyar barin falon.


"Dawo tsohuwar munafuka gidan uban wa zaki?". Maimuna ta faɗa cikin tsawa, jiki ba ƙwari kamar an sulala karas haka Turai ta dawo tare da yin zaman ƴan bori a gurin. Maimuna ta ci gaba da magana.


"Allah ya isa tsakaninmu daku wallahi ba za mu taɓa yafe muku, kuma Allah ba zai barku ba sai kun wulaƙanta tun a nan duniya, wane irin zalince ne a raba uwa da ƴarta? Ta haifi ƴarta a raye ku a ɗakko matacce a yi mata canje da shi saboda tsabar zalunci, Saratu kin bani mamaki, kuma ban yafe miki ba yadda ki ka sa na uzzurawa boyar Allah, kullum cikin kawo mini ƙorafi ki ke yi akanta, ki ka sa bana ganin farinta ko kaɗan. Yanzu duk irin halaccin da Musa ya yi miki da irin abin da zaki saka masa da shi kenan? Ya aure ki kina da yaro, kuma ya yarda ki zo masa gida da yaronki, daga baya ki ka ɗakko ƴar ƙanwarki duka ya haɗa su ya riƙe su tamkar ƴaƴansa, amma ki aikata masa wannan aikin saboda baƙin kishi da baƙar zuciya da ki ke da ita. Ke baki haifa masa ba, kuma wadda aka haifa masa ɗin ki ka nisanta shi da ita. Duk hakan bai yi miki ba, ki ka koma zubar mata da ciki, wannan wace irin zuciya ce dake haka?".


Cikin Mami ta fara magana "Don Allah kuyi haƙuri ku gafarce ni sharrin shaiɗan ne, da kuma zigar muguwar ƙawa da Allah ya haɗa ni da ita".


Da sauri Turai ta ce "Wace ni kuma? Ai ƙarya ki ke yi Saratu, dama can baƙin halinki ne, ina ga wani lokacin har laifina ki ke gani idan ina faɗar kyawawan halayen Zainab".


"Ku rufe muna baki azzalumai kawai". Maimuna ta daka musu tsawa.


Norking ɗin ƙofa aka yi. Izinin shigowa suka yi, mai gadi ne ya shigo da sallama, ya gaisheda mutunen dake falon sannan ya ce wa Abba "Alhaji ƴan sanda ne suka zo gasu nan a ƙofar gida".


"Je ka shigo da su" Abba ya bashi amsa.


Mamaki ne ya cika su, yaushe Abba ya kira ƴan sanda?.


Hankalin Turai ba ƙaramin tashi ya yi ba, Mami ta zube a gaban Abba tana bashi haƙuri da yi masa magiya, amma ko kallon inda take bai yi ba, babban abin da ya ƙara ɗaga mata hankali shirun da ya yi mata ya ƙi magana, tasan wannan shirun ba alkhairi ne a gare ta ba. Ƴan sandan suka shigo har cikin falon. Da hannu Abba ya nuna musu Turai da Mami ya ce "Ku tafi da su sai na zo".


Ɓare baki Turai ta yi ta fara ihun kuka, Mami haka.


Maimuna ta ce "Matsiyatan banza, ku je can ku girbe abin da kuka shuka". Ƴan sanda suka tasa ƙeyarsu gaba suka bar falon da su. Mudan ya ji baƙin cikin abin da uwarsa ta aikata sosai hakan ya sa bai ji damuwar tafiyar da aka yi da ita sosai ba.


Hajiya Maimuna ta yi ta zage-zage da tsinewa su Mami, sannan ta nemi yafiyar ta akan irin abubuwan da ta yi mata a baya. Ta dubi Abba ta ce "Musa tun ɗazu ka yi shiru baka yi magana ba".


Sai a lokacin ya nisa ya ce "Hajiya mamaki ne da tsoron Allah suka danne mini zuciya har na kasa yin magana, ina mamakin abin da Saratu ta aikata mini ne, yanzu ba ta iya duba tarin alkhairaina a gare ta ba, ta iya cuta mini ta hanyar hanani ganin jinina, wannan ai ba Zainab ce ba ta ƙauna ba ni, wato tafi so kullum na ƙare a bauta mata ita da yaran ta?". 


"Hmmm mutum ai bari da mutum inda ka ganshi". Cewar Maimuna


Abba ya kuma cewa "Wai me yasa idan mutum zai aikata ba daidai ba baya tunanin cewar komai daren daɗewa sai gaskiya ta bayyana? Yanzu gashi duk muguntar da ta ƙulla da irin ƙarya da tugun da take yi lokaci ɗaya Allah ya bayyana gaskiya. Dama shi ramin ƙarya ƙurarre ne. Komai daren daɗewa gaskiya za ta yi halinta, yarinyar da aka hanani gani ta ƙarfi da yaji aka nisanta ni da ita, sai gashi Allah ya bayyana mini ita ta inda ban yi zato ba". 


Da sauri Ammi ta ce "Alhaji don Allah a ina ka ganta ne? Mu je yanzu ka kaini in ganta don Allah". Ta yi maganar tana kuma fashewa da kuka.


Janyota ya yi jikinsa ba tare da ya yi la'akari da jama'ar dake gurin ba, ya ce "Please stop crying Madam, in sha Allah zan kai ki ki ganta, ki daina wannan kukan yana ɗaga mini hankali, kuma kinga ba ke kaɗai ba ce".


"Dole ne nayi kuka, yanzu taya kake tunanin rana tsaka za muje muce musu yarinyar da suke yi wa kallon ƴarsu ba ta su ba ce? Ai abin akwai rikitarwa ba lallai ne ma su yarda ba". "A'a Zainab ki daina wannan maganar ai dole ne su bamu ƴar mu, idan ma sun nuna yi mana gardama sai mu maka su kotu, ai ance yarinyar tana da shaida a jikinta irin na Zainab ɗin, sannan idan ta kama ko gwajin jini ne ai sai a yi". Cewar Hajiya Maimuna


"A'a Hajiya abin ba zai kaimu ga haka ba, a halin yanzu yarinyar nan fa surukarmu ce, tana aurenmu ɗan". Abba ya faɗa, yana kallonta. "Kamar ya bangane ba? Wai me yasa kuke yi mana nuƙu-nuƙu ne? Ku fito fili ku gaya mana abin da ke faruwa".


Gyara zama Abba ya yi ya fara yi mata bayanin komai, dama can ta san da zancen auren Amina, bai ɓoye musu komai ba, har haɗuwar su da Amina asibiti da zuwan da suka yi gidan, ganin da suka yi wa su Mama a gidan. 


A mugun firgice Momy ke kallon Dady da Sharifa da mamakin ina Sharifa ta haɗu da ita har ta ƙulla ƙawance da ita. Duk da ta ce mata ta yi ƙawa amma ba ta yi tunanin irin wannan ba ce, sannan ga wata sabuwar magana da ta ji ana yi wadda koda wasa Munir bai faɗa mata cewar ya haɗu da tsohuwar matarsa ba, lallai za ta ci uban Sharifa tunda aka haɗa kai da ita aka munafunce ta.

Sharifa ma zabura ta yi, dan ta fahimci cewar Afnan ce ɗiyar Ammi, lokaci ɗaya ta ji tausayin su Mama yadda taga suna son Afnan ya za su ji idan aka ce ba ƴarsu ba ce?.


"Allah mai iko, ina ƙara jinjina girman ƙudirar Allah, yanzu cikin ikonsa da buwayarsa ya haɗa ƴaƴanku waje ɗaya har auratayya ta shiga a tsakanin su, lallai duk wanda ya yi gangancin shiga hurumin Ubangiji ya tabka babbar asara. To yanzu ya kuke ganin za a yi ne?". Dady ya ce "Mu bari zuwa gobe za mu samo mafita".


 Ammi dai banda kuka ba abin da take yi, da ƙyar samu ta yi shiru. Suka ci gaba da jajanta lamarin. Daga ƙarshe Dady suka yi musu sallama suka tafi, tun a hanya ya san cewar yau akwai magana daga yanayin fuskar Fatima da ya gani. 


*******


Yau aka kawo kayan lefen Zaliha, kaya ne dai gasu nan kala biyar ne, sai ƴan kayan shafe-shafe da turaruka, duka kayan ba masu tsada bane, a cikin akwati ɗaya. Zaliha ta yi ihuuu da gunjin kuka hadda ƙoƙarin tada aljanu, Baba Umar ya samo ƙatuwar bulalarsa ya ce zane su zai yi, tana ganin haka ta miƙe ta shige ɗakin Hajara tana cigaba da kukanta, Hajara ma yau babu kalan zagin da ba ta yi ba. Sannan ga abin mamaki yanzu kawu ya daina ɗaga hankalinsa akan auren, abin duk ya bi ya taɓarɓare mata.



Baba ya yi mamaki da Mama ta gaya masa cewar ɗan abokin Alhaji Musa ne Afnan ke aure. Ya yi mamaki sosai saboda Gwaggo ta gaya masa ko ɗan waye aka aurawa Afnan a ƙauye, a lokacin data gaya masa ya ji babu ɗaɗi a ransa, saboda kai tsaye ta ce masa ruwan idon Afnan ya ja mata auren shege, daurewa kawai ya yi tare da fatan Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi. Amma kuma yanzu Mama ta zo masa da wannan zancen.


Baba Umar ma Inna Bilki ta gaya masa cewar iyayen mijin Afnan masu kuɗi ne sosai.


Gwaggo ta kira ƙauye ta ƙara sanar dasu batun aure Zaliha saura kwana uku. Tana zaune Hajara ta zo ta ƙare mata cin mutumci, ƙala Gwaggo ba ta ce mata ba, har ta gama ta tafi murmushi ta yi ta ce "Hmmm ba dai baki da kunya ba? Za ki gane baki da wayo tunda ke ma yanzu kin bi layin waɗan nan mata, ke yanzu an kusa a rufe miki bakin tsiwar nan".


*****


An kai ruwa rana tsakanin Momy da Dady akan rashin sanar da itan da bai yi ba.
Haƙuri ya bata, tare da nuna mata ya karɓi laifinsa, kunyar ta ne yasa bai faɗa mata mata.


Ta rutsa Sharifa a ɗaki ta zage ta tas, sai da ta yi kuka sannan ta fita. Sosai Momy ke jin kishi akan mijinta, tasan tunda har ya ga tsohuwar matarsa kuma hadda yaro tsakanin su, babu fashi mayar da ita zai yi. A daren da ƙyar ta iya bacci saboda kishin dake cin zuciyarta. 


Ammi ma da ƙyar ta yi bacci, saboda damuwa da tunanin yadda ƴarta za ta dawo gare ta.

*****

Washe gari ya kama saura kwana biyu auren Zaliha, yau ne kuma jama'ar ƙauye suka zo domin a yi sauran shirye shiryen bikin da su. Mama ta sanar da Afnan batun auren Zaliha da Daudu, har cikin ranta ba ta ji ma Zaliha daɗin auren ba. 


Ta sanar da Umma da Haidar batun auren, Umma ta ce su ranar auren sai ta shirya Haidar ya kaita a yi bikin da ita. Haidar zai yi magana kenan yaga kiran wayar Dady. Ɗauka ya yi tare da yin sallama.


Dady ya ce "My son kuna lafiya? Ina Ummanka da ƴata?".


Ya ce "Alhamdulilla suna lafiya Dady barka da wannan lokacin". Yana cewa Dady Umma ta haɗe rai.


"Ma sha Allah, ka gaisar mini da su, nasan ko na ce ka bawa Ummanka waya ba karɓa za ta yi ba, sannan ina son ka shirya anjima zamu zo ka kaimu gidansu matarka, kuma tare da ita matar taka nake so a yi tafiyar, saboda akwai abin al'ajabin da zaku ji wanda zai yi matuƙar baku mamaki".


Haidar ya amsa da "To Dady sai kunzo". Ya kashe wayar yana kallon Umma da mamakin me yake shirin faruwa kuma?.


Amanarcool ✍️ 
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.