Free chapter ยท Read without an account
10
_*NA YI SAKE....!*_๐
๐ '''DA DAMA TA'''
FREE BOOK ONE.
*E.W.F*
Mrs bb
Mom muhseen.
Watt pad name
Humaira3461
๐ ฟ๏ธ.....17&18
Duk da cewar na daina shashshekar kukan amman ruwan hawaye basu daina kwarara daga cikin idanuna ba, saboda jikina ya riga yagama mutuwa da kalaman Daddy, tsawon lokaci bai fara magana ba yana ta kallona kafin daga bisani yaja numfashi yana jin gina da allon gado, cikin sanyin murya ya sake ambatar sunana.
"Bahiyya"
Da rawar murya na sake amsa mashi da cewa, "Na'am Daddy"
"Ina son ki kula mun da kanki da kuma jalila, da ina nan da ban nan domin duk duniya bakida wata yar uwa ta jini kamarta, sannan komi Badaru da marawiyya zasu yi akaina da dukiyata don Allah Bahiyya ki zama mai kauda kanki kina jina?, Badaru da marawiyya komi ya faru dani sune sila, ba zai yuwu kisan komi ahalin yanzu ba, amma lokaci na zuwa zaki sani,ko kin sani bance kiyi musu komi ba, duk da bakida abunda zaki iya masu face ki barsu da mahaliccinsu, shine yasan yadda zai ya hukunta su, Abu guda zan iya sanar dake ko biyu shima don ki zaka shaida ta uku ko bayan raina,"
Jikina wata irin kerma yake da sauraren kalaman Daddy, tsoro tashin hankali sun baibayeni da zuciyata, jinake kamar zata fito waje saboda bugawae da take mun, hawaye jage-jage ga fuskata, na kasa furta komi sai kuka nake kasa-kasa.
"In baki daina kukan nan ba Bahiyya bazan fada ba"
Nasaka hannu ina share fuskata amman abanza, hawayen basu tsaya ba nace "Daddy kukan shi keyin kanshi ba nice nakeyin sa ba."
Shi kanshi wani irin rauni yakejin yana shigarsa, tausayinta da tausayin rayuwar da zatai nan gaba inbabu shi yake, ba uwa ba uba babu wasu dangi masu sonka.
Jiyai kamar kwalla zata zubo masa yai saurin maidasu yana cewa cikin karyayyar murya, "Bahiyya dake da Jalila kuka kadai ne jinina, UMAIMA DA KHALEESAT BA NINE UBANSU BA..............."
kamar yadda mukejin saukar aradu haka naji wannan maganar,wani irin bugawa zuciyata tayi da saida na dafe wajen, bai bani damar magana ya cigaba da cewa cikin wata kararyayyar murya wacce bantab'a jinsa da ita ba.
"Ban saka ran zan k'ara wasu kwana ki Bahiyya nan gaba, duk kuwa raina ba hannuna yake ba amma yana yin da bake jin kaina inajin kamar lokacina yayi, na hana Saheeb ya sanar dake ciwona ne saboda bana son ganin tashin hankalinki, amman yanzu dole ki sani tsawon shekara shidda kenan ina fama da ciwon zuciya mai tsanani, wanda zan iya cemiki Badaru da Marawiyya sune silar komi, yadda suka iya rabani da mahaifiyarki ba komi bane don sunga bayanki akan dukiyata, don haka Bahiyya don Allah komi zasuyi da dukiyata kisa musu ido.
Karki tanka dukkan abunda ya kamata nayi nayisa ta hannun lauyana da kuma likitana, don haka na ware miki wasu yan kudi da zasu iya taimaka miki nan gaba keda Jalila,ina rokon Allah ya kareku ya kuma kawo wanda zai jib'anci lamurranku............tari ne ya sarke shi wanda yana ciro hannunsa sai jini, kukan da nake bazan iya kwatanta muku shi ba, jikina kamar mazari na isa gareshi na rungumeshi ina kuka nama kasa cewa komi.
Bai daina tarin ba gashi yana son ya cigaba da yi mun magana, girgiza kaina kawai nake ina cewa, "Aa Daddy kayi shiru hakanan, don Allah kai shiru ka samu tarin ya lafa,"
Abun naga yafi karfuna dole na kira Dr cikin tashin hankali, alokacin la'asar tayi yadda yajini cikin wannan halin bai tsaya saurare ba ya kashe wayar.
*********
Kaff d'inmu muna asibitin da aka kwantar da Daddyn,anma hana ashiga inda yake saboda jikin yai tsanani sosai, saboda kuka muryata bata fita ko kadan, idanuna kamar jan kosai dana d'aga idona na kalli Ammah wani irin ciwo bakeji cikin zuciyata, ji nake da za'a bani wuka ko bindiga tsaf zan iya hallakata sai daga baya kila zanyi nadama, abunda bakeji akanta ita da Baba Badaru yafi gaban kwatance, yadda suka nuna damuwarsu da tashin hankalin su yabani mamaki, watau a haka gani suke ba asan komi kansu ba.
Taya Daddy zaice karna tanka?taya zanyi shiru da wannan abun da suka aikata koma ince suke kan aikatawa duk da bansan komiye ba, duk fitowar da Dr saheeb zaiyi sai sun tareshi da neman ba'asin ya jikin nashi,shi kanshi wani irin kallo yake masu saidai yace "da sauki" ya rab'asu ya wuce.
Mune har bayan magarib anan yaran sai kuka suke, sai suka koma bani tausayi saboda basuyi dacen uwa ba, kuma daga ranar da suka san gaskiya na tausaya mata don bansan ansar da zata basu ba.
Dr ne yake sanar dasu cewar kowa yana iya tafiya don ba'ason hayaniya kusada shi, yayi hakane saboda korar su Amma da Baba Badarun.
"Taya zamu tafi mubarshi ba kowa nashi a kusa dashi"
Cewar Ammah cikin fad'a, yai mata wani duba sannan yace "Bahiyya kad'ai ma ta isa"
"Bahiyya kuma?"
Suka fad'a tare ita da Baba Badaru, ya jinjina masu kai ya shige office d'insa yabarsu.
Kallon kallo kawai sukai ma juna kafin suka fara fita daya bayan daya,nabisu da kallon wulakanci ina adduar Allah ya tona asirin su, ya tozartasu ya wulakantasu.
Bayan tafiyarsu ne Dr ya fito yana kirana na tashi na shiga, lallashina yake tare da kwantar mun da hankali, hakan ya sake dawo da kukana sabo ina cewa.
"Dr idan na rasa Daddy nima mutuwa zanyi, shikadai ne gatana sai Allah, ya zanyi idan babu shi"
"Ki daina fad'ar haka, ba wanda yasan gawar fari sai Allah,kuma ciwo ba mutuwa bane sai kiga mai lafiya ya mutu yabar mai ciwon, kiyi masa addua kinji ko Allah zai tashi kafadarsa, bazan boye miki ba Yallabai yana cikin hadari, amma in sha Allahu zai tashi,kije ki zauna dashi kiyita masa addua na zabeki ne daboda kece kadai Mai kaunarsa har ranki."
Haka na kwana tare da Daddy ina sallah tare da roka masa lafiya, ko sau d'aya bacci bai daukeni ba hankalina amugun tashe yake, akwai tambayoyi da dama da nakeso nayi masa amma babu dama, don tunda aka kawosa bai farka ba ga oxygen ansaka masa ga wasu na'urori a jikin kirjinsa taya zan iya magana dashi a haka.
Dana kallesa zuciyata tsinkewa take na shiga toilet naita kuka idan na gaji infito in tusashi gaba ina kallo,a ahaka har gari ya waye aka kira asuba.
*********
"Abby nayi mafarkin Maah, ko zaka kaini na ganta please"
Gabansa ya fad'i shima d'in yai mafarki da ita ta rik'e kafarsa tana ta kuka, amma bazai ce ga dalili ba, shi yabar abunda akan dauke Amnat da yayi ne,kuma tsoro yakeji ya hadasu amnat tace bazata dawo garesa ba.
"Mafarki ba gaskiya bane angel kinji ko, ki share kawai maah dinki tana nan lafiya lau"
B'ata fuska tayi tana kallon Husna dake zuba musu abun breakfast, kamar zatai kuka tace "Ammi kice masa zanje, dana ganta zan dawo ni ganinta kawai zanyi"
Kallon juna sukai shida Husna, ta juya ga Amnat tana shafa kanta, "karki damu kinji ko Abbyn ki zai kaiki kiga Maah,amman kiyi mun alk'awari zaki dawo nan"
Ta washe bakinta "zan dawo Ammi nah"
"Yawwa KO kefa"
Daga haka bata sake cewa komi ba, ta zuba mata nata tafara bata,shi kuma yana ci yana kallonsu, taya zai kaita wajen Bahiyya? Shi yasan ko wacece Bahiyya, ammaa koma miye yafita iyawa ai.
Suka gama karya war suka fito waje wurin mota, Husna na rike da jikkarsa saida Amnat ta shiga motar sannan ta juyo garesa cikin natsuwa.
"Please"
D'an murmushi yayi saboda ya gane rokonsa take ya kaita d'in, ya jawo ta kusada shi yana riko kugunta yace "don't worry i will in sha Allah,hakan ya miki"
Ta d'aga kai sannan tace, "thank you I love u"
Murmushin mai kyau ya sake mata yana cewa, "that's my sweet wife, me too"
Tana tsaye har driver yajazu suka bar harabar gidan, ta koma ciki da tarin tunani akan mijin nata, ta sani ba zata tab'a samun soyayyar sa irin wadda yai ma matarsa tsohuwa ba, amman duk da haka bazatai giving up ba.
A hanya yaketa tunanin ya kaita yanzu ko yabari sai sun tashi sch, amman wannan lokacin shine daidai da zai iya fakewa da cewa makaranta zasu tafi, labari take ta bashi har suka iso unguwar.
Tun daga get maigadi yake sanar dashi ba kowa gidan ai, cikin mamaki yace "ina sukaje haka da sassafe?"
"Ai yallab'ai ne ya kwana asibiti babu lafiya suna can"
Hankalinsa yaji ya tashi yace, "subhanaallahi, wane asibiti ne don Allah sai mubiya"
Ya gaya mashi asibitin amma yace baisan dakin ba,a haka suka tafi yana ta tunanin Daddy meyasa meshi haka, Allah yasa ciwon ba sosai bane, don yana jinsa tamkar mahaifinsa na gaske har bada bazai iya mance alkairinsa ba.
Mom muhseenโ๐ป