Free chapter Β· Read without an account

19

by Aisha Abbakar Β· NAYI SAKE DA DAMA TA

*_NAYI SAKE....!_*πŸ’˜

     πŸ’˜ '''DA DAMA TA'''

Free Book one.

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

Mrs Bb

Mom muhseen.

Wattpad name

Humaira3461

πŸ…ΏοΈ.......35&36

Karfe tara na tashi nai mik'a tare da salati na sauko na nufi bayi don yin wanka,komi akwai a toilet d'in ba ka bukatar wani dafa ruwa akwai ruwan zafi dana sanyi zaka iya anfani da shower ko komin kwanka, irin dai bayin dakina na gida.

Ban jima ba nafito saboda inason magana da Dr bana so ya fita ban ganshi ba,a d'okance nake da koma wa gida b'angaren Daddy domin in tabbatar da mafarkin danai yake mun nuni da cewar ajiyar sa na nan ko aa,addua ta Allah yasa hakan ta tabbata, tunda har nai mafarki dashi akan wannan abun to hakika yana da mutukar muhimmanci fiye da tunani na.

Jalila na iske har tayi wanka ta shigo tace "Yaya ina kwana"

Ina tsane jikina da towel nace "lafiya lau jalila ya kwanan bak'unta?"

Tayi murmushi ta ce "Ai wannan qanwar Dr bata bari nai bacci ba surutu gareta wallahi Yaya"

Dariya kadan nayi nace "haka yai kyau zaku saba da wuri kenan,"

"Kinsan ma meke faruwa yaya?"

Na girgiza kai alamun ban sani ba,ina zama saman stool na bata hankalina tacigaba da cewa "wannan omar d'in fa school d'inmu ya gama mugune nak'in karawa, ba kadan ba nasha wuyarsa sadda aka basu prefect,munyi yar tsama sosai kafin su fita Daddy ya sha zuwa makarantar saboda dukan da yake mun,yanzu gani gidansu bansan ya zata kasance ba"

Murmushi nake ina shafa mai ina cewa, "yadda ya basar kema ki nuna baki ganeshi ba,baruwanki dashi in hanya ta had'aku gaidashi ki wuce hakan zai sa shima ya kama kanshi,don karma ya dauka alfarma yake miki kinzo gidansu zai iya ringa gaya miki magana"

"Shikenan Yaya zanyi hakan"

Shiryawa nai cikin wata doguwar riga ta atamfa brown da milk anyi mata d'inki umbrella ta bude sosai, saboda ina da fad'in k'ugu sannan daga sama ta d'an kamani saboda cikar Boob's d'ina, duk da yar ramar danai rigar bata wani yimun yawa ba.

"Wallahi Yaya d'inkin nan yana miki kyau umbrella na fiddoki"

Murmushi nai kurin ina dauko milk d'in mayafina na fesa mashi turare sai-sa sai-sa,nima na sanya on ready daman ina anfani da roll all na jiki,kamshi garai mai shiga rai na saka plat shoe Brown na dauki yar jaka itama.

"Yaya unguwa zakije ni?naga kinata shirin fita"

Inji Jalilar dake kallona,rolling nayi da gyalen wanda ya sakko mun sosai har bayana ya kuma rufe mun kirjina sosai shima, nace "gida zan koma akwai abunda zan dauko,sannan zanje gidan sakeena daga nan"

"Zanje yaya"

"Aa Jalila ki zauna ba dad'i sai suga kamar baki son zama dasu,nima dole ce ta kama fitar raina na bani ajiyar da Daddy yai tana nan zan je nasake dubawa"

Ta rausayar dakai tana cewa "shikenan Allah yakiyaye,amma zaki karya tukunna ko?"

Naja hannunta ina cewa, "muje to"

Waya ta nacire na saka ajikkar sannan muka fito,dai-dai fitowar Fareeda daga d'aki na karshe ita da ummi,ba wanda ya iya kallon mu cikin su,in bacin ma nai saurin basu hanya tsaf fareeda zata iya bankad'ata,jalila cikin jin haushi ta ce

"Yaya kina gani fa?"

Na ce "share su muje kawai"

Dining din kowa na nan banda jamil da Abba Dr ma bai fito ba, umma ce kurin sai yan matan da kuma mu sai omar, cikin sakin fuska muka gaidata tana tambayar ya kwanan bak'unta nace Alhamdulillah, suhaila ce ta iya cewa "Anty Bahiyya ina kwana"

Na shafa kanta ina jan kujera na xauna na ansa, "lafiya lau sai makaranta kenan"

"Ehy Anty Yaya Dr nake jira shixai saukeni"

Nace ma ummah" bai fito bane?"

Tace "eh amma inajin yana tafe, ummi fareeda baku gaisuwa ga junan ku?"

Kamar zasu mutu haka fuskokin su sukai, ummin tace "barka da safiya"

Atakaice nace "barka"

Fareeda kam k'irik'iri bata  tanka ba, omar ne yace mun "ina kwana"

Nima na ansa mashi Jalila ta gaishe su omar d'in kad'ai ya ansa, ummah dai bata ce komi ba,muka fara karya wa kowa da abunda ke ransa,nidai ina jinjina wannan zafin kai na wadannan yaran kodayake ai gidansu mukazo,amma koda mukazo gidansu bazan dauki wulakanci ba baruwana da harkar yarinya, inhar bata shigo gonata ba.

Muna gab da gama wa ya sauko daga sama bandai d'ago daga duken da nake ba ina shan tea,inajin yaran na gaidashi ya ansa cikin kulawa sannan ya gaida ummah, jalila ma ta gaidashi.

"Jalila ya kwanan bakon waje?"

Tana murmushi ta ce "lafiya lau YayaDr,saidai qanwarka akwai surutu bata bari nai bacci ba"

Duk akai dariya amma banda su Fareeda,yace "ai indai Suhaila ce saita koya miki surutunta don haka saiki shirya"

Ahankali bayan ya zauna gefena nace "barka da safiya"

"Patient barka kadai ya jikin,fatan komi dai-dai"

"Alhamdulillah"

Duk suka gama karya war omar zai fita fareeda tace "ka tafi da suhaila amotarka zanbi Dr ya ajeni wajen aiki"

Cikin bata rai yace "amma kinsan dai da friend's d'ina muke tafiya ke meyaci taku motar?"

"Bansani ba nidai nace kutafi tare"

"To bazanje..........omar!!!"

Ummah ta masa magana cikin yar tsawa kadan, "sa'arka ce tana fad'a kana fad'a, kaje da ita nace ni"

"To Ummah"

Yajuya rai b'ace yatafi,murmushi fareeda da ummi sukai ma juna,ummi ta mik'e tana cewa "ummah na wuce yau sai magriba zan dawo lectures din yamma zamuyi in munga ma C.A"

"Allah ya tsare adai kula sosai"

Daki tatafi dauko mayafi,saida nabari ya gama sannan nace "zanbika inje gida akwai abunda zan d'auko acan mai muhimmanci ne"

"Kutumar uba kibi wa?.........."

Fareeda ta rabka wannan zagi tana tsaye umma ta watsa mata kallo shima ita yake kallo,ni kam ko kallon ma bata isan ba jinai yace mun, "ok ba damuwa"

"Wallahi ni kuma inhar ita zaka dauka bazan je aikin ba,wannan ai iskan cine taya don taji nace zaka tafi dani shine don munafurci zatace itama zata bika, take tahau ta haya man.........Fareeda bana son iskanci banson hauka kina jina ko, motar ai ba wajen zaman mutum biyu kadai bane dole saike kad'ai zai d'auka ne?"

"Wallahi Zan shiga mota d'aya da ita ba,ita har ta isa na had'a kafad'ata da it...............Fareedaa!!!"

Dr ya daka mata tsawar da saida na toshe kunnena fashewa tai da kuka ta ruga dakinsu tabar wajen, dafe kai umma tayi tana cewa "kiyi hakuri Bahiyya"

Yak'e kurin nake nace "laaa ummah kibar bani hakuri ba komi wallahi"

"Tashi kuje saiyaa ajeki"

Tunda muka dauki hanya nida shi ba wanda yake iya cewa komi, ransa ab'ace yake ainun to nima d'in raina adagule yake, da alama wannan yarinyar ce zata kawo cikas d'in zaman mu agidan, don idan yau na jure jibi na jure gata najure,idan na jure na sati kona wata bafa kallai na iya jure na sauran watanni ba, dole na nema mana mafita nida Jalila wadda anan gaba zatai mana anfani.

Saida ya tsaya a bakin get d'in gidanmu sannan yaja iska ya fesar yace, "I'm so for what happen"

Ban kallesa ba na ansa da cewar "bakomi"

Na bud'e zanfita ya ce, "yaushe zaki dawo sai nazo na maidaki?"

"Karka damu daga nan akwai inda zanje kayi zamanka kayi aikin ka"

"To ki anshi wannan sai kiyi kudin taxi"

Na b'ata rai zan magana ya ce, "nauyina ne please ki tayani na cika alk'awari,bansan idona ya hararesa ba"

Murmushi naga yana yi kurin ansa nai nace "thanks"

Saida yaga shigata sannan yaja yatai,kallon gidan nake kurin don duka ko wata ba ai da rasuwar Daddy ba gidan har ya fara lalacewa, lallai uba agida babban ginshik'ine kuma karfaffan bango,tun a waiting falo nasan anyi bak'o gidan, kuma dama naga bakuwar mota a compound, ilai kuwa bakon ne saidai kirjina yai masifar bugawa saboda abunda nagane ma idona,zuciyata nan take tashiga kai kawo da sauri-sauri naji jiri na neman kayar dani.

Bakina da yake kerma naji ya furka "khaleesat!!"

Saurin dafa bango nayi saboda jirin dake neman kayar dani, khaleesat ce dare-dare bisa cinyar wani kato ta sakalo hannuwanta ta wuyansa fuskarsu a had'e da juna kissing suke bilhakki da juna,shi kuma ya rungumo k'ugunta,ko alama ma basu san da tsayuwata awajen ba.

Tunani na ya tsaya waje guda cak,na rasa ma abunda zanyi wani irin k'una da bakin ciki nakeji azuciyata, meke faruwa haka? Afalon gidan mahaifinmu wanda ko wata bai cika da rasuwa ba ake wannan bad'alar? Innalillahi wa inna ilahir raj'un.

Jikina na rawa na taka ina rangaji cikin falon,motsin da sukaji yasa afirgice suka saki juna ai kuwa ganina yai matukar furgitasu, zunbur ta mik'e daga jikinsa tana kauce kaucen fuska, shi kuma yai tsamo tsamo kamar kazar da aka tsamo a ruwa.

"Kunya kuka ji ko tsoro?ai bai kamata kuji kunyata ko tsorona ba,tunda bakuji kunya da tsoron mahaliccinku ba, khaleesat rayuwar da kika zab'arma kanki kenan? Koda yake banyi mamaki ba barewa bata gudu d'anta yai rarrafe,ban isa hanaki ba don haka bazance ki daina ba amma shawara daya zan baki don girman Allah in zakiyi abunki ba agidan nan ba, ubana tsarkakakkene kije wani wajen na daban, kai kuma tunda baka tsoron Allah kaje duniya zatai muku hankali,duk abunda kai ma yar wani sai anma taka,in qanwar wani kaima haka za'aima taka,in uwar wani kaimawa haka za'ai ma taka don haka ku taka ahankali"

Na rab'asu na wuce b'angaren Daddy ina budewa da key,hawaye na zuba saboda tausayin yaran nake har zuciyata basuyi dacen uwa ba,don da sunyi dacen uwar kirki hakan ba zata faru ba, wace irin rayuwace wannan kazamar rayuwa.

Ina kuka nake bi ahankali ina sake bincika d'akin har kujeru dai saida na d'aga na tara ma kaina muguwar gajiya,na zube kasa ina nishi ban samu komi a falon ba, saida na huta sosai sannan na wuce bedroom d'in.

Ina zuwa katifar gadon na hankad'a kamar almara naga wata yaga daga k'asan katifar,amma anbita an d'inke da zare baka tab'a cewa yaga ce, nima don ina zargin akwai abu wajen ne, jikina na rawa na soma kokarin bude wajen na kasa,naje na dauko key nazo ina farka wajen har Allah yasa na farka na bud'e,d'ago soson katifar nayi anan naci karo da ajiyar tashi, jikina na rawa na ciro su takaddu ne na gwajin DNA da akai mashi shida su umaima da khaleesat,sai kuma wani babban littafi mai cover hadda mab'alli ajiki an rubuta diary,jikkata na dauko da sauri na saka su aciki ko kayan ban tsaya gyarawa ba na fito ban iske su khaleesat ba nima ban tsaya ba nai waje, badan nayi alkawarin zuwa gidan sakeena ba da gida zan wuce kawai don zuciyata cike take da d'okin duba diary d'in nan,so nake inga meke ciki? meyafaru ?ina mahaifiyata? meya rabasu da mahaifina?taxi na tara nace dashi janbulo.

*Anan na kawo karshen NAYI SAKE DA DAMATA BOOK ONE, badan muyi koda rabin badak'alar dake ciki ba, domin akwai tarin abubuwa da mai karatu yake buk'atar ya sani,*

*_Shin meke cikin wannaan diary da Daddy yabarma Bahiyya?_*

_*me yake faruwa a idashen labarin haduwar Fa'iz da Bahiyya,shin wace ta'asar Bahiyya tai masa daya kasa mancewa?*_

*_shin mahaifiyarta tana raye ko ta rasu,in tana raye meya hana ta neman yarta tsawon shekara ashirin da biyar?_*

*_Baba Badaru DA Marawiyya (Ammah) zasu cinmma manufarsu kuwa? Shin mecece makomar su umaima da khaleesat_*

*_Fa'iz Zai cika wasiyyar Daddy na maida aurensa da Bahiyya? Ko kuwa Dr zai nasarar siye zuciyarta?_*

Uhmmm masu karatu karku bari abaku labari,karku bari ku zauna cikin tunanin ya za'ai kaidai hanzarta,k'ok'arta ka mallaki naka littafin kashi na biyu watau NAYI SAKE DA DAMATA BOOK TWO,ga duk mai son mallakar sa zai biya sassauk'an farashi watau 500 ta wannan asusun.

9034722970

Opay

Aisha Abubakar

Saika turo shedar biyan kudinka ta what's app da wannan no. ***

Sai najiku masoyana takuce har kullum mai kaunarku

Mom muhseen✍🏻😘😘

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.