Free chapter 路 Read without an account
Page 65
by Gimbiya Ayshu 路 馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰(GIDAN AURENA) BOOK 1.
馃尰馃尰MATSALAR GIDAN MIJI馃尰馃尰
(GIDAN AURENA)
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU馃挒馃挒馃挒
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION馃摎
GODIYA TA MUSAMMAN GA
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
*MATSALAR GIDAN MIJI (GIDAN AURENA)
*HAFSAT BASHIR
*MARYUDAH
*MIRRAH AMMIN LAYLAH
*UMMUKULSUM
*LIL SIS
*ABDOU MANZO MAIJIDAH
*CUTIE
*ESSSHA ALIYU
*FAREEY BABY(AUTAR MAMA)
*NABEELA IDRIS MUHAMMAD
*RASHIDAM006
*FATTUMA
*ZAFAFAN NOVELS
*LITTAFIN SOYAYYAH
BOOK 1: CHAPTER 129-130
___________________________Murmushi Mami ta yi ta ce"tashi ki zo daughter na,kyale ta".
Rungume ta Mami ta yi tana lallashin ta amman kasar zuciyar ta ciki yake da tunanin abinda Ummi ta ce,tabbas tana son a mata fashin baki akan wannan zanchan.
Wuri Ummi ta naima ta zauna tana dariya har da rike ciki.
Ba jimawa Jemeela ta shigo,tana yin ido hudu da Hauwa ta ji gaban ta ya yi mugun faduwa,haka kawai ta ji ba ta ji dadin zuwan ta ba wanda ta rasa dalilin hakan.
Fuska a yatsine ta karasa cikin parlor ta gaida Mami ba yabo ba fallasa ta nufi upstairs.
Ganin yan da take hada rai yasa Ummi ta zabga mata harara ta gaishe ta ciki-ciki.
Amsawa ta yi kamar wacce aka matsewa baki.
Binta da kallo ta yi har ta bacewa ganin ta,ji take kaman ta kamo ta ta shake ta ko ta huta da takaici.
Mami ta san halin Ummi tsaf,hakan yasa ta sakin murmushi ta ce"Ummiiiiiii,lafiya dai kohh!?,ya naga yanayin fuskar ki ya chanja,an miki laifi ne?".
Shiru ta yi ba tare da ta amsa ba sabida kunar da zuciyar ta take.
Hauwa dake ta zabga mata harara ne ta budi baki ta ce"bazai wuce ita da Jameela ba,kema kin san halin ta,sam ba ta da hakuri,ace mutun kaman zawo,ba dama ta dauke ido ko kawaici"...............
Zaro ido ta yi jin ta hada ta da zawo,kafin kiftawar ido da bismillah ta mike ta nufe ta tana huci.
Ihu Hauwa ta yi ta rungume Mami tana fadin"dan Allah ki cece ni Mami,wlh za ta iya nakada min duka".
Jalal da fitowar shi daga bathroom kenan ya yi saurin fitowa waje sakamakon ihun ta da ya ji,ganin abinda ke faruwa a down stairs ne yasa shi jan dan karamin tsaki ya ce"har yanzun dai bata girma ba,Allah ya shirya",ya fada tare da shigewa daki yana jan tsaki kasa-kasa.
Ba su suka bar gidan ba sai Yamma,Mami na ta son tanbayar Ummi gaskiyar zance amman ba hali.
Har bakin titi ta rakasu bayan ta musu sha tara ta arziki.
Bayan sun shiga napep Hauwa ta mikowa Ameen hannu akan ya zo amman yaki,kara rike hannun Mami ya yi yana girgizawa Maman shi kai alamun bazai je ba.
Murmushi Hauwa ta yi ta miko hannun za ta kama shi ya yi saurin rungume Mami yana dariya.
Rungume shi Mami ta yi ta ce"toh sai ku kara gaba,yau dai ya ce ba zai biku ba".
Murmushi Hauwa ta yi ta ce"ban zo mishi da kaya ba Mami".
Dariya Mami ta yi ta ce"shakurumin ki,indai kaya ne akwai su lodi-lodi,ku dai ku yi tafiyar ku Allah ya kiyaye hanya ya tsare".
Dan murmushi Hauwa ta yi ta ce"toh shikenan Mami,nagode".
Shafa fuskar ta ta yi ta ce"babu godiya a tsakanin mu daughter,ina kaunar ki sosai,ki gaida Maman ku kin ji".
Ummi ko ta kumbura ta yi famm,jira kawai take a taba ta ta fashe.
Dama Mami ta san hali hakan yasa ta kyale ta.
Zaune su ke da misalin karfe tara na dare a parlor suna hira,Jameela kuma tana yan latse虏 a waya ta ji Ameen ya ce"Daddy",a fusace ta dago ta ce"waye Daddy ka?".
Wani mugun kallo daga Mami har Jalal suka aika mata da shi,kai tsaye Jalal ya ce"ni ne Baban shi,ko ban isa na zama Baban shi ba?",ya fada yana kallan ta ido cikin ido.
Murmushi ta yi ta tabe baki ta ce"i banga alamun kai ka yi cikin ba,in kuma kana so ka ce min a yawon ta zubar aka same shi kuma".........
Marin da ya dauke ta da shi ne yasa ta yin shiru ba tare data shirya ba tana zare ido.
Mami da idan ta ya kada yayi jajir ta ce"dama mai hali baya fasa halin shi,mu zuba dake sai kin shaki abinda ba ki so,in kuma baza ki iya ba ki hadiyi zuciya ko ki daka barkono da citta",ta fada tare da mikewa tsaye ta dauki Ameen dake kuka suka bar parlor".
A ranar kasa barci ta yi tsabar takaicin furucin Jameela,ta saka wannan ta kwance ta saka wanchan ta kwance,tuno wani abu da ta yi ne yasa ta saurin mikewa zaune ta hade hannayen ta biyu tana murza su tana murmushi,Addu'ar ta daya shine Allah yasa abin da ta ji ya tabbata,inko haka ne sai ta fi kowa farin ciki,ganin ta cimma matsaya yasa ta kwantawa ta ja bargo tana Addu'ar samun nasara.
Kwance Jalal ya ke barci ya kauracewa idan shi,wani irin suya zuciyar shi take,da a ce wani ne ya gaya mishi abinda Jameela ta ce da bazai taba yarda ba,sai ga shi da kunnan shi ya jiyo,wai shi take kira da mazinaci a kaikaice,murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi ya ce"da badan katangar karfen dake tsakanin mu ba dana gwada miki Zina a muhallin shi",wani kuna zuciyar shi take,zai iya cewa tunda yake bai taba tsintar kan shi a irin wannan yanayin ba,ba'a taba bata mishi rai ba kamar yau,amman babu komi,sai ta kwashi kashin ta da hannun ta,ji yake kamar ya fashe da kuka ko ya samu sassaucin zugin da zuciyar shi take,ba shi ya samu barci ba sai gab da asuba.
Tun da suka tashi Ameen ya fara kananan kuka,Mami ta yi lallashi amman ya ki,ta bashi kayan ciye-ciye amman hakan bai sa ya bar kuka ba,da taga abin ba na karewa bane sai ta ce"za kaje wurin Mamin ka?".
Daga mata kai ya yi da sauri yana matsar kwalla.
Murmushi Mami ta yi tana goge mai hawaye ta ce"yi shiru ka ji my boy,yanzu za mu tafi".
Affan na jin za su fita ya makale musu,duk inda Mami ta bi yana bayan ta,dama ya ki zuwa islamiya wai cikin shi na ciwo,Mami na jin shi tasan karya ne,hakan yasa ta yi murmushi ta ce"ka ko yi gado,ashe kamannin ba na banza ba ne".
Sha daya da rabi Mami ta yiwa Jalal sallama,ko takan Jameela bata biba balle ta yi tunanin samun arzikin kallon banza balle na arziki,wani irin haushin ta take ji kamar ta shake ta har lahira.
Sosai Mama ta yi farinciki da zuwan su,sai nan nan take da ita.
Dariya Mami ta yi ta ce"ni fa ba bakuwa bace,na zama yar gida",ta karasa maganar ta tana dagewa Ummi gira,murmushi Ummi ta yi ta ce"haka ne Mamin mu.
Ba jimawa su Ummi suka tashi suka ba Mama wuri.
Suna cikin hira Mami ta ce"yaushe daughter za ta koma ne?",ta fada tare da kure Mama da ido.
Shiru Mama ta yi ta dukar da kanta kasa.
Murmushi Mami ta yi ta ce"ga dukkan alamu zanchan Ummi na da kamshin gaskiya".
Jin Mama ta yi shiru yasa Mami fadin"Maryam lafiya?,ya na ji kin yi shiru?,akwai wani damuwa ne?".
Murmushi Mama ta yi ta dauke hawayen dake idan ta ta ce"Hauwa ba ta da aure yanzu".
Wani irin farin ciki ne ya lullube zuciyar Mami,ji take kamar ta yi sujjadah a wurin,cikin alhini da rashin nuna jin dadi Mami ta ce"Allah sarki ban sani ba,yaushe hakan ta faru da ba'a gaya min ba".
Murmushin takaici Mama ta yi ta ce"wata biyar kenan".
Zaro ido Mami ta yi ta ce"ta gama idda kenan?".
Girgiza kai Mama ta yi tana share hawayen idan ta,ganin tana kuka yasa Mami lallashin ta ta ce"mai ya raba su".
Ajiyar zuciya Mama ta yi ta ce"hmmmmm,nan ta zayyane mata komi kamar yanda Hauwa ta fada ba tare da ta boye mata komi ba".
Kasa hakuri Mami ta yi,sosai ta yi kuka har da shasheka,abin ya mata ciwo sosai,ji take kaman ta kama shi ta nakada mai dukan da zai zama ajalin shi.
Bayan sun ci kuka suka lallashi kan su.
Share hawayen idan ta Mami ta yi ta ce"ina naiman alfarma a gun ki Maryam idan babu damuwa".
Shiru Mama ta yi ta ce"alfarma kumaaa!,ni i kin wuce alfarma a gurina,komai kike so ki fada zan miki shi insha Allahu matukar bai fi karfi na ba".
Shiru Mami ta yi sannan ta fara bata labari tun san da Jalal ya yi Aure har zuwa abinda ya faru jiya,cikin sanyin murya ta ce"sam Jameela ba ta da hali,ba ta da mutunci,hakan yasa na zo da kokon bara na gun ki da ki taimaka min,na yi kokarin yin wannan hadin a farko amman sai mijin ta na farko ya min shigar sauri,amman yanzu mun dawo muna bara a bamu ita dan Allah".
Murmushi Mama ta yi ta ce"babu komi,abin dubawa a nan shi ne Jalal,shin zai yarda?,baza'a chutar da shi ba?,baza'a shiga hakkin shi ba?".
Dariya Mami ta yi ta ce"hmmm! ba wani chutarwa ko shiga hakki,Jalal dina ya dade yana son diya ta tun kafin ta yi aure,sai dai a lokacin bai sani ba sabida babu jituwa a tsakanin su,ba dama su zauna wuri daya ba su yi fada ba,duk halin da ake ciki ina sane amman na zuba mishi ido dan naga iya gudun ruwan shi,na san yanzu idan na gaya mishi ba zai ki ba,illa ya karba hannu biyu,amincewar ki kawai muke bukata".
Dariya Mama ta yi ta ce"wuka da nama na hannun ki,duk yanda kika yi dai-dai ne,mu dai fatan mu shi ne muji alkhairi",ta karasa maganar ta tana dariya.
Murmushi Mami ta yi ta rike hannayen Mama tana mata godiya.
Bayan kwana biyu aka kawo kudin gaisuwa da komai na bukata sannan aka saka rana wata daya.
A daran Mami ta kira Jalal ta sanar mishi sai dai bata gaya mishi wacece ba.
Dagowa Jalal ya yi yana kallan Mami ba tare da ya ce komi ba,jikin shi ya yi mugun sanyi.
Shafa fuskar shi Mami ta yi ta ce"ka kwantar da hankalin ka son,bazan taba chutar da kai ba,na san insha Allahu sai ka fini farin ciki da zabin dana maka".
Girgiza kai Jalal ya yi idan shi cike taf da hawaye ya rike hannun ta dake fuskar shi ya ce"babu komi Mamina insha Allahu ni mai biyayya ne a gare ki,ina maraba da zabin ki",ya fada tare da mikewa ya fice daga dakin kukan da yake kokarin rikewa ya kufce mishi,dakin Hauwa na da ya shiga ya fada kan gado ya rufe kan shi da pillow yana kuka,shi kadai ya san kukan da yake",sai da ya shafe awa biyu a dakin kafin ya lallashi kan shi ya fice daga dakin idan shi ya yi jazir.
Yana shiga dakin shi direct ya wuce bayi ya yi wanka sannan ya daura alwala,bayan ya fito ya feshe jikin shi da tulare sannan ya zira jallabiya ya hau kan darduma ya fara sallah.
A ranar bai rintsa ba,washe gari da zazzabi ya tashi.
Tsaf Mami ta san damuwar shi amman ta share shi,ganin jikin yaki sauka bayan magungunan da ta bashi yasa ta dauke shi suka nufi Asibiti.
Tun daga ranar Jalal bai kara lafiya ba,yau lafiya gobe ciwo,ya rame ya yi baki,abinci ma bai iya ci sai Mami ta bashi.
Sossai wannan halin da ya shiga ya taba zuciyar Mami amman ba yanda ta iya,lokaci kadan ya rage kaman gobe ne.
Bayan sun tafi Mama tasa su Ummi suka kwashi kayan zuwa cikin uwar daka,bayan sun gama ta zaunar da su ta ce"an kawo kudin gaisuwar daya daga cikin ku kuma har an sa rana nan da wata daya".
Tuni Ummi ta sha ruwan jikin ta,ta yi tsuru-tsuru kaman an jefa ta cikin ruwan zafi.
Dariya Hauwa ta fashe da shi ta ce"sai matar Dr,Allah ya ja zamani ya kaimu lokaci",ta fada tana dariya har da faduwa kasa.
Murmushi Mama ta yi ta ce"Hauwa'u da ke nake,keh a ka sawa rana",ta fada tana nuna ta da yatsa.
A mugun rikice Hauwa ta mike muryar ta na rawa tana nuna kanta da yatsa ta kasa magana,durkusawa ta yi ta fashe da kuka da iyakacin karfin ta.
Shiru Mama ta yi tana bin ta da kallo,ko kadan ba ta yi yunkurin hana ta ba.
Dariya Ummi ta fashe da shi ta mike tana tikar rawa tana waka da baki.
Dakuwa Mama ta yi mata ta ce"zan ga ko dan ubanki baza ki yi aure ba,lokaci kadan ya rage miki,kema an kusa kawo naki,rawa bai ganki ba tukun,ki bari a kawo na ki sai kiji dadin taka rawa da kyau".
Ummi na jin haka ta yi mukus ta naimi wuri ta zauna ta buga tagumi,sam ba ta son ana mata maganar aure,gaban ta faduwa yake.
Cikin kuka Hauwa ta ce"mai yasa za'a min haka Mamaaaaa!?........,mai yasa za'a kuma min aure?,auren ma da wanda ban sani baaaaaa!......,mai yasa Mamaaaaaa!?.........,mai yasaaaa!?"........,ta fada tare da fashewa da kuka,cikin kuka ta ce"a fasa auren nan Mama bazan yi ba,ba ni da ra'ayin aure har abada,na gama aure a duniya",ta fada tare da mikewa za ta fice daga dakin taji muryar Mama ta ce"ki kalli cikin ido na ki gaya min kai tsaye,ni zaki watsawa kasa a ido?,ni zaki zubarwa da mutunci?",ficewa Hauwa ta yi daga dakin tana kuka.
Mikewa Ummi ta yi ta nufi Mama tana share hawayen idan ta ta ce"ki yi hakuri Mama,na san kin san halin Hauwa,wannan ba halin ta bane,zafin abinda aka mata ne ke damun ta har yanzu,ki yi hakuri dan Allah ki yi mata uzuri kin ji Maman mu",ta fada tare da fashewa da kuka ta fada jikin ta.
Rungume ta Mama ta yi tana girgiza kai idan ta cike da hawaye.
Tun daga ranan Hauwa ta rage walwala,abinci ma sai an matsa mata take ci,duk ta fige ta rame kamar kazar hausa.
Ana saura kwana biyar biki aka kawo akwati na gani na fada daya-daya har ashirin da hudu.
Ba karamin tsorata Mama ta yi ba da ta ga kayan,Hajiya ko har kwantawa ta yi a saman akwatin tana kukan murna,sai fadi take"jika ta ta yi goshi,daga saki sai aure,Allah nagode maka daka raba wannan auren ka kawo mana dan dumus-dumus,wai-wai inaga zan biki gidan ki,baza'a ci kayan duniya ba ni ba".
Hade rai Mama ta yi jin abinda Hajiya ta fada.
Harara Hajiya ta dalla mata ta ce"wasa fa nake ba zuwa zan yi ba,naga kin wani hada rai kaman hadarin daya hadu a gabas",ta fada tana turo dankwalin ta gaban goshi tana kunkuni.
Murmushi Mama ta yi ta ce"lallai Hajiya ta sauya,da dane da ta wanke ta tsaf har da gudunmuwar ruwan dauriya".
A bangaren Lubna cikin ta ya girma sosai haihuwa yau ko gobe.
Zaune ta ke akan kujera hannun ta rike da kugun ta dake mintsinan ta tun jiya,cige labe ta yi jin ciwon sai karuwa yake mai makon ya ragu,ganin ruwa na bin kafar ta yasa ta saki salati ta ce"na shiga uku fitsarin zaune na yi,inalillahi wa inna ilaihi raji'un ta fada tare da dafe marar ta tana nishi sama-sama,saurin lalabo wayar ta ta yi ta kira Sani,ba jimawa ya zo da mai a daidaita,ba bata lokaci aka nufi asibiti da ita.
Rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya.
Da misalin karfe 1:00 dai-dai aka daura auren"HAUWA'U MUAZU SA'ID DA ABDUL-JALAL ABDULKAREEM DANBATTA" akan sadaki dubu dari biyu lakadan ba ajalan ba.
Bayan an idar da sallah Jalal ya bi ta kofar baya ya sulale ya bar masallacin kafin a daura auren.
Tun safe ake abu daya amman haihuwa ya gagara,hakan yasa aka naimi ya saka hannu a mata operation,da farko kin yarda ya yi amman jin abinda likita ya fada ne yasa shi saka hannu tare da fatan samun nasara.
Ba bata lokaci aka nufi dakin theater da ita.
Zaune Sani yake yana ta Addu'a,wani irin kara daya karade asibitin ya saki ya dafe kan shi yana salati tare da kikkifta ido har ya sulale kasa yana shure-shure,chan kuma ya bar motsi.
Sai a lokacin Nurses suka karaso,da sauri suka dauke shi aka saka shi a kan gado aka nufi wani daki da shi aka fara ba shi taimakon gaggawa.
Alhamdulillah aiki ya yi kyau,Lubna da babyn ta suna cikin koshin lafiya sai dai bata farfado ba.
Sai da Sani ya shafe awa uku a kwance sannan ya farfado idan shi a kulle ya ce"baby..baby...baby,jin bata amsa ba yasa shi fadin Hauwa....Hauwa ki matso gare niiiiii,kai na na ciwo,ji nake kaman zai fashe",ganin sanbatun da yake yasa Dr ya yi mishi alluran barci,nan da nan barci ya dauke shi.
Bayan awa biyu ya farfado bakin shi dauke da salati,bin inda yake ya yi da kallo,cikin mamaki ya yi kokarin mikewa amman zafin daya ratsa shi tun daga kan shi har dan yatsar shi ne yasa shi dakatawa ya kalli inda ya ji yana mai zafi,nan yaga jini na zuba daga inda aka saka mishi cannula,alamun ya goce kenan,dagowa ya yi sakamakon turo kofar da aka yi.
Wata Nurse ce ta shigo hannun ta rike da tray,da sauri ta karaso ganin jini na tsiyaya daga hannun shi,cikin kwarewa ta gyara sannan ta tsaftace wurin,tana yi tana mai sannu,bayan ta kammala ta ce"congratulations sir matar ka ta haihu,an sami baby girl".
Cikin mamaki ya dinga bin ta da kallo,kasa shanye mamakin ya yi ya ce"matata kumaaa!?............yaushe ta samu ciki da har ta haihu ban sani ba?".
Dagowa Nurse din ta yi bakin ta a bude tsabar mamaki,shanye mamakin ta yi ta tattaro sauran jarumtar ta tana murmushi ta ce"wacce ka kawo da safe ta kasa haihuwa da kanta aka yi mata aiki",ta karasa maganar ta a dan tsorace.
Kura mata ido ya yi yana kokarin tuno lokacin da hakan ta faru,ganin ya kasa tunano komi ne yasa shi mikewa a hankali yana ganin jiri ya ce"muje ki kai ni wurin ta na ganta".
Tana murmushi ta ce"kai a'a ka huta ba yanzu ba,ka ga ba ka da isasshen lafiya".
Hade rai ya yi ya tuge cannula dake hannun shi ya ce"keh malama ban san shashanci zo ki kai ni inda matata take tun kafin na miki rashin mutunci",ya karasa maganar shi yana hararar ta".
Jiki na bari ta nufi bakin kofa.
Binta ya yi har bakin gadon da aka kwantar da Lubna.
Zaune take hannun ta rike da cup tana shan tea,tana ganin shi ta fara sakin mai murmushi.
Shiko ya hade rai yana zabga mata harara dan sam bai mance fuskar ta ba,bai ankara ba ya ji ta ce"ga gadon nan".
Bin gadon da take nuna mishi ya yi da kallo da alamun mamaki,fuska a hade ya ce"keh bana san shashanci,naga alamun hankali bai ishe ki ba,gun matata nace ki gaini ba gun wannan aljanar ba,meh hadi na da ita da zaki kai ni wurin ta",ya fada tare da bin dakin da kallo yana naiman inda aka kwantar da Hauwa amman sam babu ita babu alamun ta.
Salati Lubna ta yi ganin ta rasa lakanin ta,fashewa ta yi da kuka ta ce"shikenan na shiga uku na mutu na lalace asirina ya tonu",ta fada tare da fashewa da kuka da iyakacin karfin ta ba ji ba gani.
Bin ta da kallo duk mutanan dake dakin suke suna jiran karin bayani dan sam basu fahimce ta ba.
Cikin kuka ta fara bada labarin yan da aka yi ta aure shi da aikin da ta yi wurin raba shi da Hauwa da irin wulakancin da yayi mata da dukan da ta sha a hannun shi har zuwa dukan da ya yi mata na karshe wanda ya yi sanadiyyar zubewar cikin ta,tana jan nunfashi ta ce"a ranar yayar ta ta amshi takardar sakin ta,yau wata shida kenan cif",ta fada tana fashewa da kukan dana sani.
Durkushewa Sani ya yi ya fara rusa kuka kaman mace.
Baki na rawa Nurse Khadija ta ce"ni yanzun abinda ban gane ba shine ya aka yi asirin ya karye".
Dauke hawayen dake nuna tsantsar dana sani ta yi ta ce"bakomi bane face jikida,ya ce na yi anfani da abinda bazan cire ba hakan yasa aka yi komai akan jigida",ta fada tana kuka ta ce"na cuci kai na na zalinci kai na na chutar da Hauwa'u,dan Allah ku kira min ita na roki gafara ta kafin Allah ya dauki raina",ta karasa maganar ta tana gunjin kukan da ya yi sanadiyyar kwancewar dinkin da aka mata,nan da nan jini ya balle,da sauri Dr suka rufa a kanta ana kokarin shawo kan lamarin amman abin ya citura,nan Lubna ta amsa kiran ubangiji,rayuwa kenan.
Mikewa Sani ya yi jiri na dibar shi ya fice daga dakin,likita na kiran shi ya zo ya amshi jaririn amman kememe yaki,bai zarce ko ina ba sai gidan su Hauwa.
Cike kofar gidan su ya ke makil da mutane babu masaka tsinke,a haka Sani ya kurda har ya shige cikin gidan da mata suka cika shi ana ta hada-hada.
Da mamaki mata ke bin shi da kallo,nan wata mata da ta kasa hakuri ta yi magana,tana magana sauran matan suka dauka,jin hayaniyar mutane a waje ne yasa Mami da Mama fitowa,a kofar parlor Mama ta kusa cin karo da Sani,saurin ja da baya ta yi ta ce"malam lafiya?,mai ya kawo ka gidan mu?,ko abinda ka yi ne bai ishe ka ba ka zo ka Kara wani?".
Girgiza mata kai ya yi hawaye na zuba a idan shi.
Katse shirun Mami ta yi da fadin bashi hanya ya wuce.
Ba musu Mama ta matsa ya shige ciki.
Fuska a dake Mami ta roki mutanan dake parlor da dakin da su koma dayar dakin.
Ganin yanda Mama ta zauna yasa ta gane akwai sanayya a tsakanin su.
Cikin sanyi murya ta ce"kun sani a duhu,shi kuka ke tagumi mai ya faru?".
Dagowa Mami ta yi fuskar ta dauke da murmushin takaici ta ce"shine mijin Hauwa na farko".
Mami na jin abinda ta ce ta mike da sauri ba tare data shirya ba,cikin fushi ta ce"uban meh kuma ya kawo ka?",ta fada tana huci.
Hade hannayen shi ya yi yana kuka sosai,sai daya samu kukan ya tsagaita sannan ya labarta musu labarin komi kamar yanda Lubna ta ce.
Daga Mami har Mama an rasa wanda ya iya magana,sosai tausayin shi ya shige Mami amman aikin gama ya gama,da ace yazo kafin minti sha biyar da za'a iya yin wani abu a kai,amman yanzu ba hali.
Ko motsi Mama bata iya yi ba illa hawaye.
Ajiyar zuciya Mami ta sauke ta ce"ka yi hakuri son Hauwa ta maka nisa,an daura mata aure da wani".
A mugun razane Sani ya dago hannun shi dafe da kirgin shi yana kokarin magana tari ya turnuke shi,nan ya fara yin shi ba kakkautawa.
A rikice Mama ta mike ta dauko ruwa,ko kafin ta dawo ta iske baya motsi,sakin kofin hannun ta ta yi tana salati,Mami dake ta jijjiga shi ne ta dago ta ce"mun shiga uku,kar dai a ce ya mutu".
Kukan Mama ne ya karu,sallamar Hajiya ce yasa ta shanye kukan da take tana share idan ta,amman ina ta makaro domin ta riga ta gansu.
Cikin mamaki ta ce"kukan meh kike maryam?,mai ya faru?,ya nagan ku haka cirko-cirko kowacce da hawaye makale a ido".
Shiru Mama ta yi ta kasa magana,kukan da take kokarin danewa ya kufce mata.
Cikin rawar murya Mami ta mata bayani sama-sama,tun kafin ta kai karshe Hajiya ta mike ta fita waje fuska shabe-shabe da hawaye,ba jimawa ta dawo da matasa uku,nan suka fita da shi Mami da Mama suka bi bayan su.
Bin su da kallo mutanan tskar gidan su ka yi,ko wacce na jiran ta ji karin bayani.
Bayan tafiyar su Hajiya ta dawo ta ce"yaran yayan uwar Amarya ce,ku cigaba da aikin ku insha Allahu ba matsala".
Nan hankalin mutane ya kwanta aka cigaba da hada-hada,amman ba'a rasa yan gutsuri tsoma ba.
Duk abin nan da ake Hauwa bata sani ba,zaune take a tsakiyar kawayen ta tana gurshikan kuka,tun safe take kuka,an yi lallashin anman abi ya citura,ganin abin ba mai karewa bane yasa Ummi ficewa daga dakin,wani irin mugun haushin ta take ji,hakan yasa ta fita daga dakin,dan idan ta cigaba da zama a dakin ba shakkah za ta iya nakada mata mugun dukan da sai an rasa mai daura ta.
Bayan sallan Isha'i aka kai Amarya gidan ta,ba karamin mamaki Ummi ta yi ba ganin gidan da suka shiga,Allah-Allah take ta koma gida ta ji yanda aka yi wannan abin ya faru,tayama wannan abin ya faru?,tabdi akwai aiki a gaban Kuluwa,haka ta yi ta sake-saken ta ita kadai.
Da misalin karfe goma ango ya shigo hannun shi rike da laida,idan shi ya yi jazir kaman an barbada mishi barkono,dakin daya tabbatar na Amarya ne ya nufa ya tura kofar ya shiga tare da yin sallama kasa-kasa.
Jin muryar da ta yi ne yasa ta dagowa da alamun mamaki.
Ajiye laidan dake hannun shi ya yi ya karaso kan gadon ya zauna dan nesa da ita yana kokarin danne zuciyar shi.
Kokuwa Hauwa take da nunfashi ta dan ga dukkan alamu zargin ta nason zama gaskiya,bata gama zanchan zuci ba ya dage mata gyale suka yi ido biyu,hada baki suka yi wurin fadin whattttt!.
Cikin rawar murya ta ce"mai kake yi a daki na?".
Cikin mamaki shima ya ce"ke zan yiwa wannan tanbayar,mai kika zo yi a nan".
Hararar shi Hauwa ta yi cikin tsiwa ta ce"malam bana san wulakanci da rainin wayau,ka fitar min a daki,ko an ce maka nan gidan ku ne".
Bige mata baki ya yi yana hararar ta ya mike ya fice daga dakin.
Rike bakin ta ta yi ta bi shi da kallo har ya fice daga dakin.
Dakin Mami ya shiga ba tare da sallama ba,murya a sanyaye ya ce"ina dakin Amaryar yake Mami".
Mami dake hararan shi tun shigowar shi ne ta ce"ban sani ba,gidan ku,wa ya ce ka shigo min daki ba sallama,haka aka koya ma?".
Murya a sanyaye ya ce"yi hakuri Mami,ina wuni".
Ba tare da ta amsa shi ba ta ce"mai ya faru?".
"Mami dama dakin Amaryar ne naga kaman ban gane ba".
Dagowa Mami ta yi ta ce"ban gane ba,mai kake kokarin fadi".
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce"Hauwa'u na gani a dakin da kika ce min nan ne na Amarya".
Tsaki Mami ta ja dan duk a tunanin ta wani abu ne ya faru,a kufle ta ce"toh mai ya faru dan ita ka gani,dan Allah fita ka ban wuri bana san shirme,kuma idan ka kuskura ka mata wani abu wlh sai na saba maka ka ji na gaya ma".
Jingina ya yi da bango ya ce"toh Mami auren ta fah?".
Galala Mami ta yi tana kallan shi,chan kuma ta ce"da ba dan na san halin ka ba dana ce ka fara shaye-shaye,dama za'a daura maka aure da ita ne idan tana da shi",Jalal bana san rashin hankali fahhh!,wlh zan ci mutuncin ka,kuma ko da wasa ka nuna ba ka san auren sai na balla ka.
Murmushi Jalal ya yi har hakoran shi suka bayyana sannan ya fice daka dakin.
Bin shi da kallo Mami ta yi baki bude,bayan ya fita ta ce"gantalalle kawai,yana so yana kaiwa kasuwa,wlh ka kuskura ka yi wasa za kaga wasa".
Kasa tsayar da murmushin dake fuskar shi ya yi,ji ya yi gaba daya damuwar dake damun shi ya kau,ji yake kaman an mishi albishir da Aljanna.
Yana shiga dakin ya dauko darduma ya shinfida sannan ya fita daga dakin ba jimawa ya dawo hannun shi rike da tray da kaya a ciki,bayan ya gama saka kazar ya dago ya kalle ta tare da sakar mata lallausar murmushi ya ce"sauko mu ci Amaryar Abdul-Jalal".
Harara Hauwa ta zabga mai tana hade rai.
Ganin ya mike yana nade hannun rigar shi yasa ta mike ba shiri.
Kadan kawai ta iya ci ta sha yoghurt rabin cup ta mike cike da tarin tanbayoyi kunshe a zuciyar ta kuma ba halin tanbaya,gashi ko waya bai rako ta ba balle ta kira Ummi ta ji ko tana da masaniya,brush ta yi ta daura da alwala,bayan ta fito ta nufi drawer,sai data gama karewa night wears din kallo sannan ta dau wani dogon riga mai dan kauri ta kulle wurin,tana juyawa suka hada ido,harara ta zabga mai sannan ta shige bayi tana kunkuni.
Murmushi ya yi yana shafa kasunbar shi,tattara kayan wurin ya yi sannan ya saka sauran kazar a fridge,tana fitowa taga yana kokarin fita,hamdala ta yi dan duk a tunanin ta ya tafi kenan,shafa'i da wutiri ta yi,tana nan zaune taga ya shigo sanye da jallabiya.
Murya a sanyaye ya ce"tashi mu yi sallah".
Ni na yi nawa,yanzu ma na idar ta fada tare da mikewa tana kokarin daukar dardumar,rike hannun ta ya yi sannan ya ce"sallar godiya ga Allah za muyi,sabida haka ki natsu in ba haka ba ki ga kwanji na",ya fada yana murmushin mugunta.
"Turo baki ta yi tana kunkuni".
Dariya ya yi ya ce"mutun dai ya fito fili ya fada idan ba tsoro ba".
Bayan sun idar da sallah ya kama goshin ta ya yi Adduo'i sosai,yana sauke hannun shi ta mike kamar dama jira take.
Da sauri ta hau gado ta kwanta ba tare da ta cire hijabin ta ba ta ja bargo ta rufe har kan ta gaban ta sai faduwa yake,sam ta kasa yarda da abinda take gani,toh mai yasa Mama ta boye mata,ko da yake ita ta yi wawanci da bata tanbaya waye bane tun farko.
Bayan ya gama ya dau Al-Qur'ani ya fara karatu,sai da ya shafe minti talatin kafin ya mike ya fice daga dakin.
Hauwa na jin ya fita ta sauke ajiyar zuciya ta mika hannu ta kashe bulb din dakin ta bar dim light.
Har barci ya fara daukar ta ta ji an bude kofa,gaban ta ne ya yi wani irin muguwar faduwa.
Kunna wutar dakin ya yi ya bude drawer ya dau kayan barcin shi,bayan ya gama shiri ya feshe jikin shi da tulare sannan ya zagaya ta dayan bangaran ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya.
A hankali ya fara matsowa har ya karaso inda take kwance,bai yi wata-wata ba ya juyo da ita ta fada jikin shi,tana shirin ihu ya yi saurin hade bakin su,daga nan kuma labari ya sha bambam mai afkuwa ta afku.
Ana saura kwana biyu biki Jameela ta yi kaura ta bar gidan,dan idan ta tsaya har aka kawo Amarya toh zuciya zai iya dibar ta ta aikata aikin dana sani.
Bayan kwana biyu Sani ya farfado,tun da ya farka yake tsiyayar da ruwan hawaye,da sauri Ammi ta karaso gare shi idan ta cike da hawaye tana kwantar mai da hankali.
Murya a sanyaye ta ce"ka yi hakuri,hakika bawa bai isa ya tsallake kaddaran shi ba,ba kai kadai ke bakin cikin rasa ta ba har da mu,hakika mun yi rashin da zai yi wiya mu samu kamar ta,ka cirewa kan ka damuwa dan Allah,bana san na rasa ka ka jiii!".
Girgiza mata kai kawai ya yi idan shi na tsiyayar da ruwan hawaye.
"Ina jaririn da ta haifa?",sai a lokacin ya tuna da wata baby,shi ko sanin abinda aka haifa bai yi ba,ji yake ya tsani baby.
Bayan sati daya aka sallame shi,ba su zarce ko ina ba sai asibitin da Luban ta haihu,nan suka amshi babyn a hannun Nurse Khadija,sosai Ammi ta yi mata godiya tare da sa mata Albarka.
Bayan Sati daya Jameela ta dawo duk ta rame ta fige,a parlor ta iske Mami da Hauwa suna cin abinci a plate daya.
Bin ta da kallo suka yi har ta shige daki,tabe baki Mami ta yi tana murmushin mugunta,wani farin ciki ke nukurkusar ta.
Sai da Jameela ta yi kwana biyu a gidan sannan ta gane cewa Hauwa'u ce kishiyar ta,a ranar ba karamin tarzoma ta tayar ba,har kalanzir da ashana da dauko za ta kona gidan.
Tun da ta fara haukar ta Mami bata kula ta ba,amman ganin abin nata har da burbushin iskanci yasa ta nufe ta ba tare da tsoro ba ta dauke ta da mari,dai-dai nan Jalal ya shigo,bin su da kallo ya yi bakin shi dauke da tanbayoyi kala-kala.
Bai samu damar yin ko daya ba Mami ta ce"in dai har ni na haife ka Abdul-Jalal ina san ka saki wannan mahaukaciyar yarinyar yanzun nan",ta karasa maganar ta tana huci,in ranta ya yi dubu toh ya baci.
Dagowa ya yi yana kallan ta da mamaki,tabbas ran Mami ya baci tunda har ta iya kiran cikakken sunan shi,cikin sanyin murya ya ce"ki yi hakuri Mami dan All".......
Daga mishi hannu ta yi a fusace ta ce"bana san dogon zance,cewa na yi ka sake ta Kuma yan zunnan ba sai anjima ba,in kuma ban isa ba ne kuma toh sai in ji".
Jikin Jalal ne ya yi mugun sanyi,a hankali ya nufi step dan dauko paper da biro.
"Ina za ka je?",murya a sanyaye ya ce"biro da paper zan dauko na dawo".
Kwantawa Jameela ta yi ta rungume kafar Mami tana kuka da magiyar kar a sake ta baza ta kara ba amman fir Mami taki,ji take kamar ta take ta ta daina nunfashi gabadaya.
Da sauri ta mike ta nufi wurin Hauwa ta duka a gaban ta tana kuka ta ce"dan Allah ki taimake ni ki taimaki rayuwa ta kar ki bari a sake ni,ki taya ni rokon Mami dan Allah,na san zata saurare ki,na rokeki ki ceci rayuwar Aure na,wlh idan na bari aurena ya mutu kora ta za'a yi a gida ki taimaka min plsssssss!"...........
Mami dake ta jiran dawowar Jalal amman shiru kaman an aiki bawa garin su,kwala mishi kira ta yi tana fadin wlh na hauro saman nan sai ranka ya yi mugun baci.
A hankali Hauwa ta karaso in da Mami take ta fara tausar ta amman kememe Mami ta ki,kamar ma kara ziga ta take.
Ganin Jalal ya dawo yasa ta nufe shi da sauri ta anshe paper hannun shi ba tare da ya ankara ba ta yaga sannan ta fashe da kuka ta durkusa akan gwiwowin ta ta hade hannayen ta tana rokon Mami.
Ganin abinda ta yi ne yasa Mami kada kai ta nufi upstairs rai a bace.
Tun daga ranar Jameela ta sauko daga bushiyar kukar da ta hau,ba ta da aikin da ya wuce zaman daki,inko ta fita aiki bata dawowa sai shida,duk abin duniya sun taru sun mata yawa amman ba halin nunawa,haka nan ta hakura ta hadiye shi ta kora da hakuri.
Bayan wata daya da Aure Hauwa ta koma makaranta inda ta ke karantar medicine,zo kuga murna gun Hauwa ranar da aka tabbatar mata da ta samu Admission.
Cikin kwana biyu ta gama komi na clearance,abinka da masu kudi.
Bayan wata uku da Auren Hauwa aka yi bikin Ummi.
Da taimakon Allah Nurse Khadija ta gano gidan su Sani,duk juma'a sai ta zo gidan su duba jaririya,kuma bata zuwa hannu rabbana.
Ganin yanda take dawainiya da yarinyar yasa Ammi ta yi mishi tayin auren ta,ba dan ya so ba ya amince.
Bayan wata uku aka daura musu Aure,sosai Sani yake iya bakin kokarin shi wurin ganin ya faranta mata rai.
Bayan wata tara da Aure Hauwa ta haifi santalelen dan ta mai kama da Baban shi kaman ya yi kaki.
Ana saura kwana biyu suna Ummi ta zo gidan,sai nan-nan take da baby, dariya Hauwa ta yi ta ce"k ma dai kin kusa,zan ga irin rawar kafar da za ki yi idan kika haifi naki".
Hararar ta Ummi ta yi ta ce"bana san sa ido,ni dai ba ni da komi a toh".
Oho dai abu dai zai fito fili kowama ya gani,zanga ko alokacin maida shi ciki za ki yi.
Dariya Ummi ta yi ta ce"toh i sai ki bari ya fito da kan shi".
Ran suna yaro yaci suna Aliyu Hydar,anci an sha kuma an raba kyaututtuka sosai,mai jego da baby sun samu kaya sosai fiye da tunanin mai karatu.
Washe gari Ummi ta koma bayan sun gama shan kukan su,ga sha tara ta arziki da Hauwa da Mami suka bata.
Bayan wata hudu da haihuwar Hauwa'u Ummi ta haifi yan biyu,zo kuga murna gun dangi,musamman ma Hauwa,washe gari ta shirya saf ta nufi asibiti inda aka kwantar da Ummi,ba dan Jalal ya so ba ya yarda.
Ran suna yara suka ci suna Asiya da Hauwa'u amman ana kiran su da Ashraf da Ashfat,an raba kyaututtuka wanda ke dauke da sunan twins,wannan kuma gudunmuwar Jalal ne,duk abinda aka raba a ranar shi ya siya,hakan ba karamin daraja ya karawa Jalal a idon Ummi ba.
Bayan shekara daya Nurse Khadija ta haihu baby girl,ran suna ta ci suna Hauwa'u sannan aka mata lakani da Habibaty amman baban ta na kiran ta da sweetheart.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya a kowani bangare na wannan ma'auratan.
Bayan shekara goma
A yanzu Hauwa na da yara biyar da Ameen shida(Ameen,Aliyu Hydar,Juwairiyyah,Maryam,Jawahir da Muhammad Auwal).
Ummi na da yara hudu(Asiya da Hauwa'u,Mu'azu'Baffah' da Abdullah).
Jameela na da biyu Affan da Bilkisu.
Nurse Khadija na da uku(Hauwa'u, Muhammad Al-Ameen da Hafsat'Ummi').
Bayan Hauwa ta gama karatun ta aka bude mata katafaran Asibiti mai suna "MAJ SPECIALIST HOSPITAL".
A ranar ba karamin kuka Jameela ta ci ba,gashi ba halin yin wargi,haka nan ta hakura ta lallashi zuciyar ta da shaidan keta kawo mata tayi kala-kala.
A daran Jalal ya kawo mata takardun company da take aiki ya mallaka mata,sosai wannan abin da ya yi ya faranta mata har yasa ta cire komi a zuciyar ta.
Tun daga ranar Jameela ta sauko ta rike Hauwa da hannun biyu dan ta kula ita ce rayuwar mijin ta.
Zaune Hauwa ta ke a daki tana rike da Muhammad Auwal tana shayar da shi.
Jalal dake zaune a dayan bangaran ne ya ce"wai dan Allah baki gama ba?,a matse nake fahhh!,na kosa na yi ajiya yau".
Dariya Hauwa ta yi tare da mikewa ta ce"bari na kai shi gun Mami na dawo,ka cahchanci ka yi fiye da ajiya ma,makullin zuciya ta,muradin rai na,haske rayuwa ta,ina kaunar ka fiye da tunanin ka Abban Ameeen,idan babu kai babu ni,da kai kadai kawai zan iya rayuwa,kai ne nunfashi na"............
TAMMAT BI HAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH!!!
A NAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFIN NAWA MAI SUNA"MATSALAR GIDAN MIJI (GIDAN AURENA)BOOK 1,INA FATAN KUN ILMANTU KUMA KUN NISHADANTU.
ALLAH YA YAFE MIN KURAKURAN DAKE CIKI SANNAN YA BANI LADAN ABINDA NA FADA DAI-DAI YASA A ANFANA DA ABINDA KE CIKI AMEEN.
GODIYA TA MUSAMMAN GA MASOYA NA NA WHATAPP,WATTPAD,DA FACEBOOK INA GODIYA SOSAI GA SON DA KUKA NUNAWA NOVEL DINNAN.
ALLAH YA BAR MU TARE,KU CIGABA DA BIBIYAN ALKALAMIN GIMBIYA AYSHU.
BOOK 1 IS FREE AND BOOK 2 IS PAID,KAR KU BARI A BAKU LABARI,KU NAIMI NA KU.
BONUS 300
NRLM 500
COMPLETE 1000.
ACCOUNT DETAILS
BANK NAME:UBA
ACCOUNT NUMBER:2245462427
ACCOUNT NAME: AISHA MAARUF
EVIDENCE OF PAYMENT:***.
WHATSAPP ONLY BANDA CALL
SAI NA JI KU...
BY GIMBIYA AYSHU馃挒馃挒馃挒.