Free chapter · Read without an account
Page 4
•••SANADIN MAHAIFINA•••
Wattpad@SaNaz_deeyah
Arewabooks@sanazty
Facebook@Habibtyn Habibi
YouTube: ***
Tiktok: ***
KARAMCI WRITERS ASSOCIATION
[karamci tushen mu'amula ta gari]
Shafi na 4
Hannatu ce ta shigo ɗakin ta kalleshi murya ƙasa-ƙasa tace "Yaya kafin ta kirashi na kira nace dan Allah yace Mama ce ba lafiya, kuma ya nuna damuwa a tare dashi, dan haka na kashe matsalar. Yanzu kawo kayan in fita sai mu haɗu a waje in baka." Yaji daɗi sosai. Ya ɗauki baƙar ledar ya bata tare da cewa "Nagode Hanne" Karka damu" ta faɗa tare da zura ledar a Hijab ɗinta. Sai da tayi kamar mintuna biyu da fita sannan shima ya fita. A zaune ya tarar da Umma a falon. Zama yayi kusa da ita tare da faɗin "Umma na ɗan samu ƙarfin jiki, dan Allah ki barni naje ba daɗewa zanyi ba, kuma na daɗe ma ban leƙa waje ba, shiyasa nake son fita."
"Nayi waya dashi yanzu, naji alamun akwai damuwa ma a tare dashi, kaje ɗin amma ka kula da kanka"
"Insha Allahu." Ya faɗa cikin jindaɗi sannan ya tafi.
A ƙofar gida yaci karo da Hannatu. Ta miƙa masa ledar tare da faɗin "A gaida min ita, ace nayi kewarta sosai, insha Allahu idan Umma ta huce zan zo har gidansu sai a rakani gidan ta"
"Zan faɗa mata insha Allahu" ya faɗa yana murmushi. "To a dawo lafiya" "Allah yasa" ya wuce ita kuma ta koma cikin gida.
Gidan su Saminu ya fara zuwa lokacin ana ta kiraye-kirayen Sallar magrib dan haka sai da sukaje masallaci sukayi sallah sannan ya shirya, shima Saminu ya shirya sannan suka tari Napep zuwa The Royal Evenue Event Center inda anan ne za'ayi kamu.
*****
Hall ya cika damƙam babu abinda kakeji sai tashin kiɗa. Jannat da Khalil shigar blue sukayi, ita anyi mata irin gown ɗin nan ta amare Royal blue shi kuma shadda ya saka light blue. Sai ita kuma Safina ta saka White gown shima Ahmad shadda ɗinsa white. Ɗinkinsu iri ɗaya ne sai dai color ya banbanta su. Mazan kuwa Gethner ce a jikinsu. Kai kana ganin bikin kasan na manya ne. Kowa yayi shiga ta kece raini. Ƙawaye duk sun sha anko, sai kuma tsilli-tsillin mutanen da basuyi anko ba suma sun saka kaya ubansu. Mommy da Daddy kuwa suna daga gaba dan tables da ban aka ajje masu su da baƙinsu.
Biki ya ɗauki zafi an kira shahararrun mawaƙa sai baje basirarsu suke a gurin.
Ana ta hotuna wasu kuma na fili suna rawa. Da hannu Jannat tayi wa Farhan alama tazo. Ƙarasowa tayi ta ɗan sunkuya. "Farhan ya banga Sa'ad ba, ko bai kiraki ba?" "Ya kira yace min yana waje sai na bawa Jiddo ta kai masu guda biyar kamar yadda kika ce"
"Haba Farhan ke ya kamata kije da kanki fa" "Sis calm down zata bashi wallahi na bata fa"
"Okay" ta faɗa. Khalil ne ya kalleta Yace "Babe dance competition kin iya rawa kuwa ko ni ne zanyi winning?" Murmushi kawai tayi wanda ba har ciki ba, dan hankalinta yana can bakin ƙofa tana son taga shigowar su Sa'ad amma shiru.
Ta ɓangaren su Sa'ad kuwa ko da Jiddo taje da kallon wulaƙanci ta bisu dashi sannan tace "Wai wane Sa'ad a ciki ko kuwa masu gadin gurin ne ku?"
"Ke karki nemi ki faɗawa mutane magana" Saminu ya faɗa cikin ɓacin rai. Sa'ad yayi saurin riƙeshi tare da cewa "Ƙyaleta Saminu, taci darajar Jannat" "To dama idan bai ƙyaleni ba, ya zai yi dani, ko nayi kallar wadda zai iya bugu?" Murmushi Sa'ad yayi tare da cewa kece Farhan "Oho maka koma wacece ina ruwanka, gashinan guda ɗaya aka bani in baku, duk da dai babu class ɗinku a ciki" tana miƙa masa ta juya tayi shigewar ta.
"Wannan wane irin wulaƙanci ne, ni kam ba zan zauna nan ba dan haka tafiya zanyi"
"Haba Saminu ni kaina bani da lafiya yanzu haka wani jiri nake ji, amma nayi wa Jannat alƙawari dan Allah mu samu guri mu zauna ko ban samu shiga ba idan an fito sai in mata Allah ya sanya alkhairi, ta dai san nazo ɗin"
"To ni ka barni na tafi tunda ga guda ɗaya, kai ka shiga ni sai in koma"
"Kaima kasan ba zai wuyu ba tunda dai tare muka zo dole mu koma tare.
Guri suka samu suka zauna a gefe, suna gani ana ta shige da fice amma su babu halin shiga.
A cikin hall kuwa ganin da gaske ba su Sa'ad ne ya saka Jannat miƙewa. MC kuwa sai kurarata yake. Mommy ce ta taso da sauri ta ƙaraso gurin "Jannat ina zakije kin manta ke amarya ce?" Farhan ma da sauri ta ƙaraso gurin tace "Sis wai meyasa kika taso?" "Sa'ad yana waje jikina ya bani hakan, zanje in shigo dashi na san hanasu akai" "To ki koma yanzu Farhan zata dubo" Kallon Farhan ɗin tayi . Farhan tace "Indai suna nan yanzu zan shigo dasu dan Allah ki koma kar ki saka abin ya ɓaci"
Komawa tayi ta zauna, khalil ma nayi mata magana amma babu nutsuwa a tare da ita.
Farhan kuwa fita tayi ta fara laluben inda zata gansu. Can ta hangosu zaune tayi saurin ƙarasawa. "Kaine Sa'ad ko?" kallon ta yayi yaga kamar ma ya santa amma ya manta a ina ne. "Ni ne" ya bata amsa a taƙaice. "Dan Allah kuyi haƙuri ni Jannat ta bawa gate pass ɗinku sai na bawa wata, kuma wallahi wayana ne ya mutu ban san bazata baku ba dan Allah kuyi haƙuri, hankali Jannat ma gaba ɗaya ya tashi saboda bata ga Sa'ad ba" "Allah sarki Jannat" ya faɗa yana murmushi kafin ya sake cewa "Kece Farhan ko?" "Eh ni ce" "Okay. Ta kawo mana guda ɗaya kuma kinga bana shiga na bar abokina ba" "Hakane kuyi haƙuri yanzu dai gashi muje dai ko hankalinta ya kwanta" Karɓar card ɗin sukayi sannan suka wuce. Sai da suka bawa security sannan suka shiga. Sanyi Ac ne ya fara ratsa su suka fara ƙarewa hall ɗin kallo lallai abin na masu shine, irin decoration da akayiwa hall ɗin kai kace ba a Nigeria bane. "Muje nayiwa MC magana sai ayi maku hotuna ko?" "To ba damuwa" ya faɗa fuskanshi ɗauke da fara'a.
Ita kuwa jannat tunda ta hango shigowarsu take ta murmushin jindaɗi. Sai da Farhan tayiwa MC magana sannan ta dawo suka je tare da su Sa'ad aka kira Kibadash photographer yayi masu hotuna.
Suna ƙoƙarin sauka daga stage ɗin kawai yaji jiri ya ɗebeshi. Aikuwa a gurin ya zube. Saminu ya durƙusa ya fara jijjigashi. Aikuwa Jannat a sukwane ta taso ta ƙaraso lokacin kuwa an ɗagashi an fita dashi.
Farhan ce ta riƙeta, aikuwa ta fashe da kuka. Hall ya rikice aka hau surutu.
Ummu ce tazo ta riƙe ta tare da faɗin "Haba Jannat duk wanda kika gani anan dan ku yazo kije ki zauna zai tashi shima"
A dai-dai lokacin Safina da Mommy suka ƙaraso. "Meya samu Sa'ad ɗin"
"Wannan ya ɓata party kai...." cewar Jiddo.
Aikuwa Jannat da sauri ta fuzge tayi waje da ɗan gudu-gudunta, khalil ya rufa mata baya.
Har an saka shi a mota ta fito a ruɗe itama. "Jannat wai ina zaki je duk fa mutanen gurin nan sun zo ne dominki." Kallo Aunty Mamy tayi tace "Aunty Mamy dan Allah ki barni inje inga halin da yake ciki" tuni hawaye ya ɓalle a idonta, ganin hankalinta ya tashi sosai ne ya saka Khalil cewa "Bara mu bi bayansu Aunty, sai hankalinta yafi kwanciya" Ita dashi da Farhan suka bi bayan motar Abbas wanda a cikinta ne aka tafi a kai shi asibiti. Sai daya kira Abbas ɗin domin tuni sun ɓace masu. Yace sunyi asibitin Nassarawa. "Jannat dan Allah ki bar kukan nan kiyi haƙuri" Farhan dake bayan mota tayi maganar. Ɗan goge hawayen tayi sannan tace "Bikina yazo fa?" "Duk da haka komai ai muƙaddari ne" "Hmmm shikenan" Khalil dai ya kasa cewa komai har suka ƙarasa asibitin.
****
Yadda ta fito daga ɗakin a fujajan ya saka Hannatu saurin ɗagowa tana kallonta. "Umma lafiya?" hankalinta a tashe tace "Shiga ki ɗakko Hijabinki muje asibiti" Gaban Hanne ba ƙaramin faɗuwa yayi ba" "Umma asibiti kuma? Waye babu lafiya?" "Hanne yanzu ba lokacin tattauna zance, ki ɗakko tafi" "To Umma" da sauri ta shiga ta ɗakko Hijab ta fito. Suna cikin Napep Umma ta kalli Hannatu tace "Hanne yayanki ashe gurin bikin wannan yarinyar yaje? Kuma a gurin ya faɗi yanzu haka yana asibiti, Saminu ne ya kirani a waya" Gaban Hanne ba ƙaramin faɗuwa yayi ba. Shikenan abinda suke ɓoyewa ya bayyana.
Asibiti
Suna tsaye bakin ƙofa, Jannat sai kai da komo take. Khalil na daga gefe a jikin bango Farhan na zaune, sai su Abbas da Saminu suma a gefe a tsaye. Likita na fitowa duka suka ƙarasa gurinsa "Likita ya jikin nasa?" "Kaine ka kawo shi ya faɗa yana kallon Khalil. "Eh nine" "Muje office nayi maka bayani. Gaba ɗaya suka runguɗa zuwa office ɗin.
"Yana da damuwa sosai, wanda hakan shine ya haddasa masa ciwon zuciya, kuma idan har ba'ayi ƙoƙari wajen yin maganin damuwarsa ba to tabbas zai iya rasa ranshi." A zabure ta miƙe tsaye tare da dafe ƙirji. "A'a ba bazai yuwu ba, bazai rasa ransa ba, dan Allah doctor ku ceto rayuwarshi please" kallon ta yake cike da mamaki. "To ke naga yanayinki kamar na amarya ko shine angon naki? Ki zauna mu miki bayani mana" Khalil ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa "Jannat zauna please" tana goge hawaye ta zauna. Doctor ya cigaba da cewa "Muddin kuka barshi da damuwa to tabbas zai iya rasa ranshi, akwai magunguna da drip da muke buƙata aje a karɓa a pharmacy."
40 Minutes later.
"Bazan taɓa yafe miki ba Jannat Allah ya isa tsakanina dake, ashe sai da kika tilasta yaje bikinki, muguwa azzaluma kawai"
"Kada ki ƙara ce mata muguwa duk halaccin da tayi muku amma kuke kiranta azzaluma"
"Na faɗa mata me kika isa kiyi?"
"Sai in rama mata wallahi" Farhan ta faɗa cikin tsiwa.
"Farhan kada in ƙara jin kince komai, ki sani cewa ta girmemu kuma ta haifemu"
"Allah ya kiyaye in haife butulu irinku"
"Umma dan Allah kiyi haƙuri, kiyiwa Jannat kyakykyawan zato"
"Bazanyi ba, kuma wallahi Hanne idan kika sake magana anan sai na tsine miki"
A tsorace Hanne take kallonta, kuma kallon mamaki take mata.
"Idan har da gaske har cikin zuciyarki kina son Sa'ad, kuma kina son ceto rayuwarsa. To dole ki fasa auren wancan ki auri Sa'ad, idan kinyi haka shine zan miki kallon mai adalci kuma zan cigaba da sonki kamar da"
"Kada ki so ta sai me? Ai ba dole sai daku zata rayu ba, domin ku daga baya ta sanku dama can ba daku take rayuwa ba"
"Haba Farhan dan Allah ki daina wannan maganar. Kada ki manta mahaifiyar Sa'ad ce fa"
Farhan zatayi magana kenan, aka turo ƙofa aka shigo. Ganin su Khalil da Saminu ne ya saka Farhan cewa "Yaya Khalil dan Allah mu tafi gida"
Ajje magungunan yayi sannan ya kalli Jannat yace "Daddy yace muje gida yana son ganinmu" kallon Sa'ad tayi dake kan gado kamar gawa sannan ta kalli Umma da ko kallonta batayi. "Zaz....zam...zamuje gida Allah ya ƙara sauƙi"
"Amin ya rabbi" Hanne ta bata amsa.
"Yaya Khalil dan Allah kayi haƙuri da abinda ke faruwa na ruɗe ne."
Murmushi yayi sannan yace "Kada ki damu Jannat Allah ya bashi lafiya"
"Amin ya rabbi. Amma gaskiya mahaifiyarshi bata da mutunci" Farhan ta faɗa.
"Kada in ƙara jin kin cewa babbar mace bata da mutumci"
"Allah abin haushi ne da ita, bata da adalci"
"To ya isa haka" ita dai Jannat bata ce komai ba, domin ta shiga tashin hankali sosai.
****
Dukkansu su ukun suna zube a gaban Daddy. Safina, Jannat da Farhan. Sai Ummu da Mommy na zaune kan kujera. Khalil na daga gefen Daddy shima zaune a ƙasa.
Daddy faɗa kawai yake, ta inda yake hawa ba tanan yake sauka ba. Yana musu faɗan akan abinda ya faru da Sa'ad.
"Daddy kayi haƙuri"
"Ai dama sai kunyi abinku kuzo ku fara bada haƙuri, ke kin zama babbar banza ko?"
Nan ma shiru suka ƙarayi. "ke Jannat waye yaron da kika bi kina kuka dan ya faɗi, har kika ja mana surutu?"
Shiru tayi taƙi cewa komai "Tambayarki fa nake?"
"Abokina ne"
"Aboki?" kallon Mommy yayi yace "Kinji shashanci ko? To bazan lamunta ba. Jibi ne aurenki amma kina maganar wai aboki"
Cikin kuka ta ɗago ta kalli Daddy tace "Ni dai Daddy na fasa auren Khalil, Sa'ad zan aura" Wani ɓarin makauniya Mommy ta kai mata a fuska, tayi saurin dafe gurin hawaye gaba ɗaya sun wanke mata fuska. Safina ta taso daga inda take tare da riƙo Jannat ɗin. "Jannat har yaushe kika lalata tarbiyyar da na baki da har zaki iya kallon idona ki faɗi haka" Daddy yayi maganar cikin ɓacin rai. Cikin kuka ta miƙe tsaye tare da cewa "Matuƙar ba'a aura min Sa'ad ba, to sai na gudu na shiga duniya, ni bazan auri Khalil ba" tana gama faɗa ta ruga ta nufi ɗakinsu. Mommy da sauri ta miƙe zata bita Daddy ya dakatar da ita. "Ki barta kawai dani take zancen." kallon Khalil yayi wanda har a lokacin kanshi yana ƙasa. "Kayi haƙuri Khalil, kaje gida ka cigaba da shirye-shiryenka" sallama yayi musu sannan ya tafi. "Jannat har yanzu bata san waye mahaifinta ba, kuma wane ra'ayi gare shi, ni ne zata tashi ta bar wa guri ina mata magana ko" Ummu ce tace masa "Alhaji kayi haƙuri sha'anin yara sai haƙuri ai"
"Bazan lamunci wannan shashanci ba, ba a gidana ba."
*****
Tana kwance akan gado ta rufe fuskarta da pillow taji an turo ƙofa an shigo, bata cire pillow ɗin ba sai dai hawaye gaba ɗaya ya jiƙa inda ta rufe fuskar dashi. "Jannat tashi muyi magana" Safina ta faɗa tare da janye pillow ɗin ta ɗagota, aikuwa ta rungume Safina tare da fashewa da sabon kuka."
"Safina ko ba dan soyayya ba zan auri Sa'ad saboda ina tausayin halin daya shiga a dalilina"
Farhan ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "Gaskiya Sa'ad yana cikin mawuyacin hali, amma Jannat kin san babu yadda za'ai Daddy ya fahimceki, sannan kuma kema wannan abin da kikeyi ya nuna cewa kina son Sa'ad ko da baki furta ba, to yanayinki ya nuna hakan, a yanzu Sa'ad ya shiga wannan hali saboda yana ganin ya rasa ki, wane hali kike tunanin Yaya Khalil zai shiga idan ya rasaki, bayan kece muradin ransa, kun gina soyayya har ta tsawon shekara biyu, Sa'ad kuma fa? Baki ma san yana son ki ba sai yanzu"
Ƙurawa Farhan ido tayi ba tare da tace komai ba, sai dai har a lokacin idanunta a jiƙe suke da hawaye. Farhan ta cigaba da faɗin "Kiyi tunani Jannat, shi kunyi soyayya wane hali zai shiga idan ya rasa ki a dai-dai gaɓar da yake ganin zaku ci ribar soyayyar da kuka daɗe kuna ginawa"
Hannu ta saka ta sake goge wani hawaye daya zubo. "Ina son Khalil har yanzu da soyayyar shi a cikin raina, ina kuma tausayawa halin da Sa'ad yake ciki, Farhan kinaji likita yace Sa'ad zai iya rasa rayuwarshi" Kallon Safina tayi sannan ta riƙo hannunta tace "Safina bana son Sa'ad ya rasu ta dalilina, ku fahimtar da Daddy"
Hannu Safina ta saka tana goge mata hawaye "Jannat na fahimce ki, kuma na fahimci Sa'ad ma, domin yayi ƙoƙarin danne soyayyar ki tun kafin a furta na gane cewa Sa'ad yana sonki. To amma kina ganin Daddy zai yarda ya baki Sa'ad kada ki manta jibi ne ɗaurin aurenmu, ko Daddy ya amince sauran dangi fa?"
"Zan fahimtar dasu, dan Allah Safina ki taimaka min har raina inajin zafin abin"
"Okay calm down komai zai zama normal da yardar Allah"
"Amma Daddy" "Just relax, kiyi cooling mind ɗinki insha Allah zasu fahimceki" ta faɗa tare da janyota jikinta tana ƙara rarrashinta.
2 days later
Wani wawan mari Daddy ya ɗauke Safina dashi, sannan ya kaɗa mata hannu tare da cewa "Dama na daɗe da sanin ke kike zugata" Hannu ta saka ta dafe kuncin nata, kanta na ƙasa. Farhan da ke gefenta ta kasa ko ɗago kai ta kalli Daddy domin itama tsoro take kar ayi mata abinda akawa Safina.
Ajiyar zuciya Jannat ta sauke tare da cewa "Daddy na san ba zaka taɓa fahimtar halin da nake ciki ba, domin baka zama damu bare ka fahimcemu. Daddy ni dai na fasa auren nan wallahi ko da an ɗaura to bazan zauna ba. Sai dai ku nemeni ku rasa kawai" ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka.
"Yanzu har na haifi ɗan da zan riƙa faɗa yana musawa. Jannat har kinyi girman haka, ni zaki watsawa ƙasa a ido. To idan an aura miki shi ki mutu kinji, dan Allah washe gari a tashi a tarar da gawarki a gidan Khalil" yana gama faɗa ya fita ya bar su anan.
Ita da Safina gaba ɗaya rungume juna sukayi suna kuka.
Ƙofar gidansu Jannat cike yake damƙam da maza, ta ko wane ɓangare inda za'a ɗaura auren Safina da Ahmad da kuma Jannat da Ibrahim Khalil. Kowa ka gani a gurin yana cikin fara'a ne. Khalil da Ahmad baki yaƙi rufuwa. Yayinda Daddy kuwa yana ta karɓar baƙin da suka halarci ɗaurin auren.
Guri yayi shiru an fara sanarwa ana shirin ɗaura aure kenan. Jannat ta ƙaraso gurin a sukwane.
*Masu karatu a Arewabooks Please a rika haɗawa da following dina🥹*
SaNaz Ce✌️