Free chapter · Read without an account
15&16
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 16/7/2024.....✍️📚🌹
For information 0816139058 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________15🔥
Ai a dubu ɗari gimbiya Zunaira ta miƙe zaune daga kwanciyar da take jin Mama Haulat ta ambaci sunan Yah Jaish.
A hanzarce ta sauƙo kasa daga saman gadon, da gudu Wolf nata ya rufa mata baya, ɗan karami da shi gwanin ban sha'awa.
"Haulat je ki ce mashi ya shigo". Momma ta faɗa cikin sanyin murya, sai dai fa ita ma voice ɗin nata akwai kaifin mulki a tattare da shi, dama kuma ai dole a samu haka, uba sarki, kaka sarki, sannan miji sarki, ai mulki ya gama bin jininta, fin haka ma za'a samu a tattare da ita, izza da isa take da taƙama a jininsu yake, bare dama su fa modarawa sun yi kaurin suna na wuce misali wajen nuna isa, izza da kuma zuciyar bala'i, jininsu a tafashe yake, basu yafiya kuma basa ɗaga ƙafa, amma fa sai an taɓosu, haka kawai basu faɗa.
Miƙewa Mama Haulat ta yi tare da nufar waje bayan ta amsawa mommar da "Toh ranki ya daɗe Allah ya kara tsawon rai tare da nisan kwana farar mace mai farar zuciya".
Ko sannu momma bata sake cewa ba, da alama ita ma dai so silent ɗin ce, alamu sun nuna gadon shiru shiru su Jaish suka yi.
Gimbiya Zunaira kuwa tana fitowa parlourn bata nufi kowa ba sai wajen yayan nata, sai sakin uban murmushi take yi tamkar wadda aka yi wa albashir da kyautar gidan aljanna, baiwar Allah tana masifar son ƴan uwan nata, haka suma suna masifar kaunarta sosai.
Tana zuwa ba tare da ta yi mashi magana ba ta faɗa jikinsa tana ƴar dariya har gaf teeth nata dake a tsakanin kyawawan fararen hakwaranta suka bayyana.
Kyakkyawar hannunsa ya kai ya shafa kanta kafin ya ce. "Where's your hijab?". Ya yi maganar can kasa kasa.
Tana mai cigaba da sakin ƙayatattcen murmushin nan nata mai kara fito da tsantsar kyanta ta bashi amsa da.
"Na manta da shi a bedroom na Momma, ai tsabar murnar na zo na ganka ne yasa na manta, ina su mai ran karfe da su Yah Omar?".
Shiru ya yi mata yana kallon face nata yadda take zuba murmushi, yana bala'in kaunar kanwar nan tasa, baki ma ba zai iya faɗar son da suke yi mata ba, saboda tana da kyan zuciya kamar dai Mommarsu Gimbiya Rahilarh kenan.
"Auta wato Jaish kawai kika kallah a parlourn ko?".
Cewar Aunty MieMie.
Kwanciya ta yi a saman kirjin yayan nata tana faɗin.
"Aunty MieMie yanzu fa Yah Jaish shi ne sabo, ke ba ɗazun da muka baro wajen uncle Abbas na je wajenki ba? Shi kuma Yah Jaish yanzu ya kai almost 2 weeks fa ban ganshi ba, ki bari na gama ganinshi sai na zo wajenki".
"Kina da gaskiya".
Cewar Yah Jawad.
Mama Haulat ce ta katsesu da cewa tana neman izinin yin magana.
Daga Jaish har Jawad babu wanda ya amsa mata, ko kallon in da take ma basu yi ba, su fa idan na ƴan uwansu ba to kowa a ƙasƙance mara galihu suke kallonsa.
"Haulat me Momma ɗin ta ce?".
Cewar Gimbiya Aunty MieMie kenan.
"Yanki ya daɗe ta ce Yah Jaish ɗin yana iya shigowa".
Jinjina kai kawai Aunty MieMie ta yi ba tare da ta sake ce mata ko sannu ba, sai dai ta ɗaga mata hannu alamar zata iya tafiya ta basu waje.
Da gudu Wolf ɗin Auta ya zo ya haye jikin Jaish ɗin shi ma, ya manne da auta gam abinsa.
"Ɗagani na tashi baby".
Cewar Yah Jaish.
Da sauri ta miƙe tsaye rike da ɗan Wolf nata dan su bashi damar ya miƙe ɗin shi ma.
Tashi ya yi cikin nutswa ba tare da ya sake yin magana ba ya nufi katafaren kofar da zata sada shi da cikin bedroom ɗin. Da ido Jawad da Aunty MieMie suka bishi, basu ce da shi ko ubban ba, kuma basu da niyar tashi su bi bayansa, da alama su ba ganin Momma suka zo yi ba, sun rako shi ne kawai, kuma sai suka kyale shi ya shiga shi kaɗai, dan ɗa da uwa akwai sirri a tsakaninsu.
Komawa jikin Aunty MieMie auta ta yi ta haye saman laps nata tare da kwanto da kanta a saman shoulder ɗinta tana murmushi.
Da ɗan karfi Aunty MieMie ɗin ta ja dogon hancin nan nata har sai da autar ta ce. "Wash Allah na Aunty MieMie kin cire mun hancina".
"Dama ai hancin naki ya yi tsawo sosai, gara na rage maki shi". Aunty MieMie ta bata amsa.
Ɗan kawar da kai Jawad ya yi yana faɗin. "Aunty MieMie baki nemi zaman lafiya ba, ki rasa hancin wanda zaki rage a gabaɗaya gidan nan sai na babyn daddy?".
Ya kai karshen maganar yana miƙewa tsaye saboda call ɗin da ta shigo mashi cikin wayarsa a yanzu. Karar wayar kawai ya ji, tun bai duba ya ga wanene mai kiran nasa ba ya miƙe kamar yasan mai kiran nasa already. Kofar fita daga parlourn ya nufa, da yake kofofin da naura suke aiki kuma suna amfani ne da motsin ɗan adam, yana zuwa wajen kofar ta buɗe kanta da kanta.
Waje ya nufa ba tare da ya ce da Aunty MieMie ko uppan ba. Yana fitowa suka haɗu da Gimbiya Chuchu da ta fito daga cikin elevator a yanzu, ita ma wajen Momma zata je, dama renon Mommar ce ita, shiyasa kuka ga ta fi shaƙuwa da Gimbiya Zunaira sama da kowa a cikin gidan, a part ɗin Momma ta saba zama time da take karama, da ta girma ne ta koma part ɗin Akka, sam bata son zama a wajen mummy wato mamarta sosai, baiwar Allah da alama zama da Momma mace mai farar zuciya ne yasa ita ma take da saukin kai duk da bata kai Zunaira ba.
Kamar dai kullum aikin da aka saba, tana fitowa daga cikin elevator ta fara ɗaukar kyakkyawar fuskarta a hoto da wayar Fanan da yake a hannunta, idan baku manta ba Yah Jawad ɗin ya kwace nata wayar, hoto dai ba zata fasa ɗauka ba, abin ya bi jininta, ita da ko barci ta tashi sai ta kashewa kanta hotuna kala kala bare kuma ace ta yi wanka ta yi kwalliya, ai abin ba'a magana, shi ne har da aro wayar Gimbiya Fanan.
Tana aikin ɗaukar hoto tana tafiya, sai turo ɗan bakin nan take tana canza style kala kala, sam bata lura da mutun yana zuwa ba, da yake yanayin takalmar kafafunsa smooth shoes ne, irin na yawo a cikin gidan nan, suna da laushi sosai ta yadda sam basu kara idan mutun yana tafiya, hakan yasa sam bata ji tahowarsa ba.
Shi kuwa tun da ta fito daga cikin elevator yake kare mata kallo, ta canza shigar da yake a jikinta ɗazun izuwa wasu haɗaɗɗu kuma tsadaddun kayan, dama ita ƴar wanka ce, ga masifar san kwalliya, kamshi da kuma gyaran jiki kamar me.
Sai tinkarosa take yi kallonta na a kan screen ɗin wayar, sam bai kauce mata daga hanya ba kuma bai yi mata alamar tasan mutun yana gabanta ba.
Karo suka yi ta bugu da faffaɗar kirjinsa a in da wayar Fanan ɗin ta faɗi ƙasa saman beautiful tiles ɗin, ji kake tas karar wayar.
A razane ta ɗago da kallonta izuwa kansa, dan taga wanenen?. Shi kuwa ɗaure fuska sosai ya yi tamkar bai san me ake cewa sakin fuska ba bare murmushi.
Ganin shi haka yasa ta yi wani irin ja da baya, murya na rawa ta fara cewa. "Kayi hakuri Yah Jawad wlh ban ganka bane, kuma......".
Bata kai karshe maganar ba ta dakata sakamakon wani kallo mai kama da harara da ya watsa mata, shi dai bai san ya zai yi da Chuchu da Sarina a kan waya ba, su biyun nan idan suka rike waya sai sun baka haushi, bare ma ita chuchu mayyar hoto da videos, kana zaune baka sani ba sai dai kaga ta ɗaura maka camera a fuska tana yi maka video kamar ka aiketa, ita kuma Sarina mayyar chatting ce, shi ne yasa Yah Jawad ɗin ya kwace wayoyinsu ɗazun, sai kuma gata dana Fanan ta karɓo, kai Allah mai iko, yanzu haka idan ya karɓi na Fanan ɗin ma anjuma na Mummy ko Momma or Akka zata ɗauko, na Akka kuwa bai isa ya kwace ba, dan bala'in tsohuwar nan ba iya ta zai yi ba! Zaman ka lafiya kada ka bari Akka ta kamaka ka yi laifi, idan hakan ya faru ka shiga talatin, ta in da take shiga ba ta nan zata fita ba, ta iya faɗa. Irin dai faɗa na normal tsofaffi da jikokinsu.
Shiru ta nutsu tana muzurai kamar wata maras gaskiya, sai wani ƴan kame kame take yi. Shi kuwa ya kafeta da ido yana tunani wai me zai yi ya raba yaran nan da cutar waya ne? Dan wayar ta zama cuta a garesu.
Kunsan idan ana kallon mutun duk sai ya rasa nutsuwarsa, ko da kuwa kallon mutunci da soyayya ake yi wa mutun yana rasa nutsuwarsa bare kuma kallon neman kalar hukucin da za'ayi wa mutun, ai kunsan dole Gimbiya Chuchu ta tsargu ta rasa nutsuwarta sosai.
"Wayar waye wannan?".
Ya tambaya calmly kamar mai ciwon baki.
"Am.....inm...... Wayar Aunty Fanan ce..."
Tana magana words ɗin suna rarrabewa saboda tsoro.
Miƙa mata hannunsa ya yi akan ta bashi wayar ba tare da ya sake yin magana ba.
Jiki na kerma ta tsugunna kasa ta ɗauko mashi wayar tare da miƙo mashi ita.
Bai kai ga karɓa ba call ya sake shigowa wayarsa da take a cikin aljihunsa, kira ta ɗaya da ta biyu duk sun katse, yanzu na uku ne ya shigo.
Burus ya yi da call ɗin da ta shigon ɗin, ya kai hannunsa ya karɓi wayar da Chuchun take miƙa mashi, sannan ya ce. "Anjuma ki sameni a bedroom ɗina".
Yana gama faɗar hakan yasa kai zai wuce ta.
A hanzarce ta matsa ta bashi hanya. Wucewa ya yi ba tare da ya sake kallon in da take ba.
Tsayuwa ta yi tana bin bayansa da kallo ranta a cike tab da takaicin abin da yake yi masu na kwace masu wayoyi ya hanasu sakata su wala, ji take kamar ta je ta ja kunnen nan nasa ko zata huce takaicin da yake a cikin ranta.
"Allah Yah Jawad ɗin nan ya iya mugunta".
Ta faɗa a fili tare da murguɗa baki kafin ta wuce ta nufi kofar shiga parlourn Momma. Shi kuma Jawad elevator ya hau zuwa second step.
A ɓangaren Jaish kuwa, ɗan bakin nan nasa a ɗauke da sallama kasa kasa ya shigo cikin bedroom ɗin na Momma.
A wannan karon bata a saman bed nata, ta sauko kasa samar shinfiɗin alfarma da ake yi wa gimbiyoyi a cikin bedroom nasu dan hutawa, yanayin shinfiɗin kamar da gashin ɗawisu ake yinsu, amma kuma ba gashin ɗawisu bane, carpet ne na alfarma da ake kyarasa haka kamar da gashin ɗawisu, ga bala'in laushi, sai tashin kamshi yake yi, sannan an zuba mata throw pillows manya manyan a saman shinfiɗin, dan kishingiɗa aka zuba mata su idan zata kishingiɗa sai ta yi amfani da su, ta fito a ainahin cikakkiyar gimbiyarta, alkyabbar yana kara fitar mata da kyanta sosai.
Kusa da wani throw pillow dake a gabanta Jaish ya ƙariso ya zauna a saman shinfiɗar da take ɗin kenan.
"Sannu da hutawa Momma".
Ya faɗa kansa na'a ƙasa yana kallon shinfiɗar, dama na gaya maku muguwar kunya ke gare shi, sam baya son haɗa idanu da mutane.
Gyara zamanta ta yi a in da ta kara dakewa a cikin alkyabbar.
"Jaish ka dawo lafiya? Ya gajiyar hanya ya kuma ka baro mun su Abbana?".
"Kowa yana lafiya Momma, and suna gaisheki sosai".
Bawan Allah ko part nasa bai leƙa ba, yana dawowa kawai iyayensa ya fara buƙatar gani, sune sama da komai a garesa, baya wasa da su kuma bi haɗasu da kowa ba, idan ba ya zo ya gansu ba ko wanka ba zai iya zuwa ya yi ba, shi ne yasa ya fara da fada ya duba daddynsu sannan ya taho wajen Mommansa, a kullum idan ya dawo daga tafiya haka ko daga office sai ya bisu ɗaiɗai ya fara duba suna cikin aminci kafin ya tafi ya je ya yi abin da zai yi.
"Ina amsawa ina Omar?".
Ta yi maganar tana kai hannunta saman kyakkyawar bakin gashin kansa, a hankali ta fara shafa kan nasa tana saka mashi albarka.
"Baka je part naka ba ko?". Ta sake jefo mashi wata tambayar tana mai do da kallonta a saman kyakkyawar face nasa.
Nisawa ya yi kafin ya bata amsa da. Omar yana gidan uncle Rahab babban yayanta kenan, sai ku ya ɗaura da cewa. "Ban je part nawa ba, ai kinsan ba zan iya zuwa ko'ina ba har sai na zo na ganki".
"Allah ya yi maka albarka my son, ina alfahari da ku".
Da amin ya amsa mata kafin ya ce. "Momma kina lafiya ba wata matsala in wuce part nawa?".
"Lafiyata lou Alhdulillah nake, amma da ka je gidan Yah Rahab ya kasami su Jannat?".
Shiru ya ɗan yi na a kallah one mint kafin ya ɗago da kallonsa ya ɗan kalli face nata kaɗan, sannan ya sake sunkuyar da kan nasa ƙasa, sai ƙoƙarin tuna su waye kuma su Jannat a duniyar nan yake yi? Amma ina ya kasa tuna su waye su, dan bai ma san da su ba a duniya, ƴaƴan uncle ɗin nasa ne da shi bai ma san da zamansu a duniya ba, su kuwa sun san da shi, har ma sun saka shi a cikin zuciyoyinsu, dan muguwar farin jinin ƴan'mata ke gare shi sosai, duk in da ya shiga sai ya shiga can cikin zuciyoyinsu, amma shi sam baya kula kowa. E babbar magana kenan, lallai Jaish ka cika cikakken ɗan duniya, ƴaƴan uncle ɗin nasa ne ma bai sansu ba.
"Ba dai su ma su Jannat ɗin baka sansu ba kam?".
Ta yi maganar tana aikin kallon face nasa da ya wani sunkuyar da kai ƙasa.
"Momma i don't know them". Ya bata amsa yana kai hannunsa ya riƙo nata guda ɗaya a cikin nasa.
Shiru ta yi a kan maganar su Jannat ɗin, dan tasan fin haka ma zasu aikata, dama ta yi sa'a suka san uncle Rahab ɗin kenan, kaɗan daga aikinsu su ce basu san sauran uncles ɗin nasu ba.
"Mommana zan iya tafiya?".
Yana magana ya ƙoƙarin cire mata wani dankareran tsadadden diamond ring da yake manuniyar yatsarta, zoben ya kama mata yatsa sosai ne, har ya fara cin namar jikinta.
"Meyasa zaka cire mun? Zoben Ummiee na ne fa".
"Ummm shi ne yasa kika ki cirewa har ya fara cin maki namar jikinki ko? Tom ni dai ba zan iya ganin shi yana ƙoƙarin cutar mana da ke na barshi ba, zan cewa Ummiee ta aiko maki da wani, dan nasan nata daban ne".
Ya kai karshen maganar tare da zare ring ɗin a hankali cikin dabara ta yadda ba zai yi mata zafi ba, tamkar ma bata san an cire ba, duk da kuma yake ya kama jikinta.
Murmushi kaɗan ta yi a cikin zuciyarta tana ƙara godewa Allah da ya bata ƴaƴa masu matuƙar kaunarta har haka, sun san farincikita ko bata gaya masu ba, haka zalika sun san bakin cikinta ko bata bayyana masu ba, sun san abin da take so da wadda bata so.
"Momma zan je na yi wanka na ɗan yi barci, inason gobe na fita office da sassafe, kinga almost 2 weeks bana nan, so yakamata na je office gobe dan naga me ake ciki".
"Jaish barci yamman nan fa bashi da kyau, idan ka yi shiri yanzu zaka tashi da ciwon kai".
"In Sha Allah zan kiyaye, but now am feeling to much of sleeping, zan yi kaɗan kin ji mommata?".
Ya yi maganar in a low voice sosai!.
"Tom shikenan, ka kula sosai Allah ya yi maku albarka".
Da Ameen ya amsa mata kafin ya miƙe tsaye rike da ring ɗin nata, sannan ya nufi kofar fita da wannan taku nasa cikin nutsuwa haɗe da fadanci. Da idanu ta bishi har ya fice daga cikin ɗakin, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana mai kara godiya ga Allah a cikin zuciyarta.
Yana fitowa ya iske Aunty MieMie da Gimbiya Chuchu and Zunaira suna ta hirarsu, Yah Jawad baya wajen, tamkar zai tambayi Aunty MieMie ina Jawad yake? Sai kuma ya fasa tambayar yasa kai kawai ya wuce ba tare da ya bi ta kansu ba.
Ita ma Aunty MieMie bata ce mashi ko uppan ba, dan tasa da wuya ya amsa mata, Gimbiya Chuchu dama saboda ance mata yana cikin ɗakin ne yasa ta nemi waje a parlourn ta zauna, dan haka yanzu yana fita ta yi maza ta miƙe ta nufi cikin ɗakin da murnarta. A hanzarce auta ta miƙe ta rufa mata baya, suka bar Aunty MieMie ita kaɗai, gyarawa ta yi ta kwanta a samar sofar tare da fito da wayarta ta fara latsawa.
Dai'dai Jaish zai shiga cikin elevator wasu kyawawan ƴan samari suka fito daga cikin elevatorn, kyawawa ne sosai, da gani ba tambaya ƴaƴan Gimbiya Rahilarh ne, wato Momma. Ƴan samari ne da basu fi 13 years ba a duniya, kana ganinsu kaga twins, saboda tsannin kamannin da take a tsakaninsu ta yi yawa, ba zaka iya banbantasu ba, idan ka gansu ma zaka ce mutun ɗaya ne, dan fa komai sak suke kama.
Suna ganinsa suka ɗan ja da baya suna mai risinar da kai.
"Good afternoon Yah Jaish, ka dawo lafiya?". Suka haɗa baki wajen faɗar hakan.
Tsaresu da idanu ya yi ba tare da ya yi magana ba. Nan take suka sha jinin jikinsu suka fara ƴan kame kame.
Obaid ne ya ce. "Wajen momma zamu je dama". Sai kace an tambaye shi, tsabar tsarguwa ce kawai, da gani sun aikata wani abin da ba dai'dai ba, dan wlh idan kana neman ƴan rigima ƴan haɗa cakwakiya fitinannu marasa jin magana idan ka samesu kai kam ka gama komai, su ɗin number one ne a harkar rashin jin magana, sam basu son zaman lafiya, idan ƴaƴan sarakuna suka zo neman auren Gimbiya Sarina da Fanan, to da su Gimbiya Sarina take haɗa baki su kulla munafurci su kori ɗan sarkin, yanzu sau uku ƴaƴan manya manyan sarakuna daga masarautu daban daban suna zuwa neman auren Sarina ɗin, amma duk ta haɗa baki da su Obaid ɗin ta kori samarin, a cewarta babu class nata a cikinsu, suna da wani uncle mai suna Taheer kanin Mama wato matar king ta biyu, wannan uncle Taheer ɗin mutun ne mai izza da ji da kai bala'in girman kai na wuce misali, tun yana ƙarami yake cikin masarautar, yana nuna isa da zafin rai, ga jarumta, amma duk da haka sai da ranar su Obaid suka kusa saka shi kuka, kuma har yau babu wanda ya gane su suka yi mashi wannan ɗanyen aikin, kuma Sarina ce ta saka su, dan uncle Taheer ɗin yana bata haushi, yana takura mata da faɗa akan ta yi sallah ta dai'na taɓa waya, shi ne nan ta je ta sanya wata kuyanga daga cikin masu yi mata hidima ta ɗebo mata wani irin azabbabben mai mai zafi da aka rubuta rob a jikinsa, ɗan iskan zafi ke gare shi, haka ta kawo mata, saboda rashin imani ta saka su Obaid suka san ta yadda suka yi suka zubawa uncle Taheer ɗin wannan rob ɗin a towel da zai goge fuskarsa idan ya yi wanka, haka kuwa aka yi, dama ga shi jajir da shi kamar tsada, ai kuwa yana goge fuskarsa da towel nan ya kara yin wata uwar ja fuskar tasa, nan take face ɗin nasa ta yi ruɗu ruɗu kamar wadda ya sha marika a hannun maza irinsu commander ZAFAR, kan ka ce me idanuwansa sun yi jajir kamar jini, fitsari ne kawai bai saki a wando ba ranar, saboda azaba, sai da ya kwanta a gadon asibiti, saboda rub ɗin tana da azaba sosai, ga shi sun zuba dayawa a jikin towel ɗin.
Ƴan albarkar ƴaƴa har yau ba wanda ya iya gane su suka yi wannan aika aikar, sun iya haɗa sharri kamar ba jinin gimbiya Rahilarh ba su kam, babban abin haushin kuma muguwar shiga rai ke gare su, wlh idan ka gansu sai sun yi mugun burgeka, ka ji duniya kana kaunarsu, ga shi kuma idan suka yi laifi aka kamasu to fa ba za'a taɓa iya banbance wanene ya yi laifi a cikinsu ba, saboda tsananin kamar da suke yi, sai su yi ta rai'nawa mutane wayo, wannan ya ce wannan ne, wannan ma ya ce wannan ne, haka suke ruɗar da mutane.
"Me kuka aikata?".
Shi ne tambayar da Yah Jaish ya wurga masu.
Kallon juna suka yi, a tare suka haɗa baki wajen cewa.
"Yah Jaish bamu yi komai ba, daga part ɗin mummy fa muke"
Sam bai yarda da maganarsu ba, dan yasan hali, yasan basu zama shiru, basa ji, auta da take kanwarsu 11 years ma tana nan nutsatsiya kamar wata waliyiya, amma banda su, ba dan ba dan ba da na ce waɗan nan renon shaiɗan ne.......😅
"Idan na ji kun aikata wani abin Allah sai jikinku ya gaya maku".
Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya shiga cikin elevator abinsa.
Tsayuwa suka yi a wajen har sai da suka ga tashin elevator, sannan suka kalli juna suka kwashe da dariya a tare kamar wasu munafukai, tamkar masu aljanu a tsakar ka.
Dariya harda rike ciki suka yi, tamkar basu ne yanzu suke muzurai a nan ba. Sai da suka yi mai isarsu sannan Omaid ya ce.
"To mu idan ma mun yi laifi za'a iya gane mu ne? Ai ƙwaƙwalwar Star ne da mu, ba tunanin boss muke da shi ba, dan boss ne yake da ɗoɗaɗɗen ƙwaƙwalwa, a film kullum cikin rashin nasara yake saboda tunaninsa na banza, kullum shi ake kashewa ba actor ba, kafin mu yi abu sai mun yi tunani irin na actor, sai mun nemo hanyar da baza'a taɓa gane mumuka yi ba".
Dukar wasa Obaid ya kai mashi a shoulder ɗinsa yana faɗin.
"Amma kasan dai Yah Jaish and Yah Jawad they're acting like actors ko? Suma ba tunanin boss suke da shi ba, tunanin actors ke gare su, wlh tun da sun dawo sai mun kara dogon tunani ta yadda zamu rinƙa zulle masu".
(Ka ji wani zance, wai masu 13 years ne zasu yi wa mai 25 years wayo😂 kai jama'a su Obaid basu da kirki, kaɗan fa suka samu gadon kaifin ƙwaƙwalwar King Zuhair, amma har suke ƙoƙarin yiwa manyan kai waɗan da su suka gaji ƙwaƙwalwar da gaske wayo fisabilillahi 🤌😂 lallai kuna ruwa, mu muna gefa idan suka riƙeku zaku san cewa tunanin actors kuke yi, amma fa da gaskiyarsu, suna da kaifin basira sosai wlh, sun iya saka mutun a tarko su zulle su barshi)
"Kai Obaid mu wuce ciki hai, kada Yah Jawad ya isko mu a nan, kasan dai tun da ka kalli Yah Jaish ya wuce to Yah Jawad yana bayansa, dan kasan basu rabuwa, kullum suna a tare".
Ya kai karshen maganar tare da wucewa izuwa wajen kofar shiga cikin parlourn Mommar. Da sauri Obaid ya rufa mashi baya, suna sanye ne fa da fararen jallabiyas tas kamar wasu limaman masallacin jumma'a, amma kun ji irin tsiyar da suke surfawa!.
Yah Jais kuwa kai tsaye cikin wani luxury part ya nufa, idan kun ji ance luxury ai ƙarshen haɗuwa kenan, baki ba zai iya faɗar haɗuwar ba, ya ji komai ya more rayuwa wadda duk min girman burin ɗan adam aka bashi nan to sai ya mance da cewa a duniya ma yake.
Akwai kuyangu biyu dattijawa da suke kula da part ɗin nasa, sune suke yi mashi gyare gyare da komai da komai, ɗayar ta fi manyata, dan zata kai 45 years a duniya, ɗayar kuma bata da wani girma sosai, bata wuce 35 to 40 years ba, sun san kan aikinsu sosai, kasancewar sun sansu da balai'n son tsafta yasa suke zagewa su yi aiki babu kakkautawa, ko'ina sai sun gyara, su goge su sake gogewa, dan sun san idan Jaish ya sami datti komai ƙanƙantarta to fa bala'i ne zai tashi ya tsaya a cikin gidan, hakan tasa basu wasa kuma basu ƙasa a gwiwa wajen ganin sun yi aiki yadda yakamata, shiyasa part ɗin take tamkar sabuwa, komai very very clear gwanin ban sha'awa, ga uban daddaɗar kamshin da yake tashi tun daga dosowar mutun part ɗin zai bule shi.
Komai na cikin part ɗin launin milk color ne, sai ɗan ratsin ash a jikin tsadaddun curtains ɗinsa.
Bed da yake kwanciya duniya ce guda, abu kamar ba za'a mutu ba, irin wannan daula.
Yana shigowa kuyangun suka zube ƙasa a saman gwiwowinsu suna kwasan gaisuwa tare da zuba mashi kirari na ɗan sarki jikan sarki takawarka lafiya toron giwa, zaki kake kafi karfin kananun namun dawa, irin dai kirarin da ake yi wa Barde suke yawan yi wa ƴaƴan nasa ma.
Ko kallon in da suke bai yi ba bare asa ran zai yi magana, cikin luxury bedroom ɗinsa kawai ya wuce abinsa, sai a lokacin ya tuna da cewa ya bar laptop nasa a cikin mota, dama kayan sakawa kam baya tafiya dasu, dan Dubai gida ce a wajensu, kamar yadda yake da part nasa a cikin masarautar nan tasu da komai da komai, to haka yake da shi a can masarautar kakan nasu ma, so idan ya tashi tafiya Dubai ɗin baya ɗaukar ko tsinke na kayan sakawa, tafiyarsa kawai yake yi, haka dawowa ma.
Raba kansa da kayan jikinsa ya fara yi daga shiga cikin bedroom ɗin, waɗan nan kuyangu nasa sun iya gyara, katafaren bed ɗin nan nasa ya sha shinfiɗa ta alfarma ta wata dankarariyar luxury bed sheets, ga wata haɗaɗiyar duv mai girma sosai, idan ka haye saman bed ɗin nan ma ai ba za'a gane da mutum a wajen ba, saboda girmansa ga laushi over.
Haɗaɗɗen toilet ɗinsa ya nufa dan ya yi wanka, tas ya cire kayan jikinsa ya rage daga shi sai short, yana da kyan surar jiki sosai kamar shi ya yi wa kansa.
Bayan ya yi wanka cikin kayan shan iska ya shirya, ya yi wa kayan matuƙar kyau sosai, singlet ce and short, sannan ya haye saman katafaren bed nasa yana wani lumshe idanu, sai zuba kamshi yake yi, ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.
After some hours.
Babbar parlourn King Zuhair, wajen da suke haɗuwa su ci abinci kenan.
Hayaniya ne yake tasowa a cikin parlourn ba kaɗan ba, tun daga nesa suke ta aikin kace na ce. Gabaɗaya su Momma suna a saman haɗaɗɗen family dining table nasu dake dining room a cikin parlourn, abincin dare suke ci, King bai fito ba tukun nan, yana cikin bedroom nasa, Jaish da Jawad basu wajen, daga Momma, Mama, Mummy, sai su Sarina, Fanan, Zunaira, Chuchu, Aunty MieMie, Aneesa ƴar Mama kenan, Akka ma bata kai ga ƙarisowa wajen ba, tana part nata, sai Obaid da Omaid da suma suke wajen.
A dukka faɗin girman KINGDOM OF POWER kuyanga guda ɗaya king Zuhair ya aminta da ita da ta kula masu da shashin abincinsu, kakkarfar macece mai jini a jikan nan, idan ka ganta sai ka rantse da Allah ta karɓi horo waje commander ZAFAR, irin matan nan ne da ake cewa mace mai kirar maza, gata doguwa samɓal, akwai kuyangu biyu da suke tayata aiki irin goge goge kitchen da sauransu, ita kuma ita kaɗai aka yardanwa da ta yi masu girki, sannan ita kaɗai take serving nasu abinci.
Amma abin da baku sani ba shi ne, ita fa Gimbiya Rahilarh ranar da king yake ɗakinta ita take yi mashi girki da kanta, hakan yana ɗaya daga cikin abin da yasa yafi sonta, saboda tana nuna mashi cewa yana da kima da girma tare da daraja a idanunta, tana nuna mashi cewa ya fi mata komai a duniyar nan, kunsan maza da shegen sun respect, nan take king ya zama mata kamar baby, ga shi dai zaki ne a waje, amma a cikin gida wajen Gimbiya Rahilarh ba'a magana, na yi shiru kada su jini a miƙa ni wajen commander ZAFAR ya ragargaje mun baki na rasa na shan Maltina mai sanyi.
To wannan kakkarfar kuyanga mai suna Zubaida ita kaɗai ta samu damar iznin shigowa cikin parlourn king ta yi serving na family, sun aminta da ita sosai, so abin da ya tayar da hayaniya a dining room ɗin yanzu ba komai bane fa ce rigima a tsakanin Mama da Momma, Mama da Momma sam basu shiri, basu haɗuwa inuwa ɗaya, tamkar wuta da audiga suke, Mamma izzar bala'i ke gareta, ga shege nuna isa da iko, sai ta nuna kamar ita ce uwar gida ta fi kowa iko a gidan, kuma ba ita ba ce uwar gida Mummy mahaifiyar Gimbiya Aunty MieMie ce uwar gida, amma da yake a tare king ya auresu sai mamar take ganin ai babu abin da Mummyn ma ta fita da shi, so ita ma uwar gida ce, dan haka dole a sanyata a tsagin da za'a sanya Mummy. Kun san fa uwargidaye daban suke, koma ina za'aje azo sune ke da gida, ko rabuwa ka yi da uwargidanka wlh baku rabuba, in dai kuna da yara to ko zaka mutu ita ce kai, ko ka saketa ita ke da iko da kai, ka jira girman yaranta kawai malam kasha mamaki......😅
Shiyasa ake son murza kambun uwar gida, dan a gaskiya ita ɗin daban take musamman idan ta haihu a gida, ai hajiyata ki ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ki sha kuruminki tare da bin ƴaƴan nan naki da addu'a, duk wadda zata zo wlh daga baya ne, ko ya sakeki kece shi idan bai sani ba wahalar kawai ƴaƴan su girma ne! Mama dai ta dage ita ma uwar gida ce........ Allah mai iko 😅
Amma kuma Mama basu taɓa yin rigima da mummyn ba sai da Momma, saboda mummy mace ce da ko ka yi abu ma bata ɗaga idanu ta kalle ka, sau da dama Mamar tana takalarta da faɗa, amma ko kallon in da take bata yi, ita kuma Momma ainahin jinin Modarawa ne kada ku manta, basu barin kota kwana, hakan yasa bata bari idan Mama ta yi mata abu, abin a jininsu yake, kada kuga laifinta ku fara bincikar tarihin modarawa ku ji, basu yafiya.
Abin da ya faru yanzu bayan sun zauna a saman table za'a fara cin abinci, sai Momma ta ce da kuyanga Zubaida ta zuba mata abinci kafin king ya fito, ta zaɓi kalar da take so a zuba mata, da yake mama sarkin neman magana ce, sai ta yi maza ta ce ai ina a matsayinta na babba bata bada damar kowa ya ci wani abin ko abinci ba har sai king ya fito ko ruwa bata bada izinin a sha ba, yadda kuka san ita ce ta ajiye kowa da yake a saman table ɗin, shegen son girma ke gateta.
Jin haka yasa Gimbiya Aunty MieMie ta sanya baki, dan ita ma irin king ce, ba'a tauye hakkin wani a gabanta ta yi shiru, sai ta ce. "A'a Mama, Momma fa tana son cin abinci, kin sani ne ko yunwa take ji sasoi? Kuma ai shi daddy bai ce idan mun hau saman table mu rinƙa jiransa ba, mu ne nan muka ɗaurawa kanmu jiran nasa da muke yi kullum, dan haka idan wani yana jin yunwa yana da damar da zai ci abinci kafin dad ya fito, Zubaida ki zubawa Momma abin da ta buƙata yanzun nan ba tare da ɓata lokaci ba umarni nake baki!!".
Shikenan daga yin wannan magana Mama ta tada bala'i wai Aunty MieMie ta rainata dan ba ita ta haifeta ba! To daga nan ne fa abin yake ƙoƙarin zamar masu faɗa, dan kusan dukkansu sarakan zafin kai ne, Mummy ce kawai so silent da bata saka masu baki a cikin hayaniyar tasu ba, amma Momma ma ta saka baki, dan ta ce bata ga dalilin da zai sa Mama ta ce bata bada izinin a zuba mata abinci ba, wacece ita? Ko Mummy da take uwargida ran gida ma bata isa ta hana su cin abinci wai dan king bai fito ba bare kuma ita Mama, bata isa ba!! izza+izza ne yake aiki a nan.
Mama dai ta ce ta isa har ta yi yawa, dan haka dole a bi umarninta ko anki ko anso!!. Toh fa, dama ai ita da Momma ba'a shiri sam, basu haɗuwa waje guda!!.
Ita dai kuyanga Zubaida an sakata a cikin code, ga umarni gimbiya Aunty MieMie da kuma Momma sun bata a kan ta zuba masu abinci su ci, ga kuma umarnin da Mama ta bata na kada ta yarda ta zubawa kowa komai har sai king ya fito..... Wannan shi ne cakwakiya, tana tsaka mai wuya baiwar Allah, ta rasa zancen waye zata bi!.
Ga shi King kuma ya ce shi da kuyanga Zubaida kawai ya yarda, ita kaɗai zata rinƙa yin serving nasu abinci, babu wasu kuyangun da zasu zo masu kan abinci, baiwar Allah Zubaida tana ganin rayuwa, ita kaɗai take aikin zubawa wannan ta zubawa wannan, idan bata yi sauri ba su hauta da faɗa musamman Gimbiya Sarina da twins Obaid and Omaid sun fi kowa rashin kirki a cikin gidan......
Familyn king sun fara nasu kala kalar tsiyar, bari na haɗa kayana sai zuwa gobe muga ya za'ayi da wannan rikici na Mama da Momma, ga Kuyanga Zubaida dai a cikin wani hali, duk wanda bata bi umarninsa ba ta shiga uku, to ita ya zata yi da ranta kenan? Izza sam bata yi ba a rayuwa 😌
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 17/7/2024.....✍️📚🌹
For information 0816139058 Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________16🔥
Momma dai ranta ya ɓaci sosai, hakan yasa ta miƙe da nufin ta bar parlourn dan ma kada su yi ɓatattciya, kuma ta sanya a ranta idan ta fita daga cikin parlourn nan ta dai'na cin abincin a wannan dining room ɗin kenan, sai dai wani, dama saboda mijinta take zuwa part ɗin nasa, shi ya tsara wannan tsari na a rinƙa haɗuwa a part ɗin nasa ana cin abinci.
Bata kai ga motsawa daga in da take ba suka ji gyaran murya daga bayansu. Ko basu juya ba sun san wannen, kuma sun san halinsa fa, shi ɗin ba uba bane mai wasa, baya ɗaukar wargi, yana da wasa da dariya da ƴaƴan nasa, amma baya taɓa bari su wuce iyaka, ba sai na sake faɗa ba kun san shi da zafin rai ga iya adalci!.
Jin gyarar muryarsa yasa kowa ya nutsu tsit, dama can basu saba irin wannan kace na ce ɗin ba, bama sa yi, yau ɗin ma Mama ce ta tada wannan balli, kamar wadda aka yi wa wani laifi ta zo zata huce a kansu, shi ne ya kunna wannan wutar, amma fa da gasken gaske mama da Momma basa shiri, basu zama waje guda, sai dai basu kace na ce a tsakani, iya dai kiyayyar ce kawai da harare hararen juna sai ɗan abin da ba'a rasa ba, sai kuma time to time idan sun haɗu Mama ta yaɓawa Momma ɗin magana.
Ƙarisowa cikin room ɗin King ya yi, jikinsa na'a sanye da jallabiya fara kal, sai zuba uban daddaɗar kamshi yake yi kamar anyi ɓarin turare a jikin nasa.
Saman dining chair ɗin aka ware mashi mai kwalliyar sarakuna ya zauna, komai nasa daban yake, harta bed nasa mai ɗauke da tambarin sarauta ne, saboda fa mulkin kingdom of power mulki ne mai matuƙar karfin gaske, suna da karfin iko da muryar faɗa a ji a duniya, ba mulki bace ta kananar kai, ba sa a ƙarƙashin kowa, sai dai ma jiga jigan masarautu dake a ƙarƙashinsu suna mulkarsu, kuma dole ayi masu biyayya! Idan ba haka ba commander ZAFAR ya busa busoshin yaki a tashi ƙasa! Wasu masarautu ma ba dan Allah suke yi masu biyayya ba, dan tsoron horarrun jiga jigan dangerous warriors nasu suke yi.
Komawa Momma ta yi ta zauna ranta duk a ɓace.
A gaskiya King Zuhair kyakkyawan balarabe ne na gasken gaske, da ya cire wannan rawanin naɗin sarautar tasa sai tsantsar kyan nasa ta bayyana, ai dole ma ƴaƴansa su yi gadon kyau, ga dimple nasa gwanin birgewa, kaɗan zai ɗan motsa bakinsa kuga ta lotsa, ga shi jajir da shi kamar Akka, yadda kuka san ku taɓa shi jini ya zuba, madarar kyau ce babu mix!.
Kallon Mummy king ɗin ya yi ba tare da ya yi magana ba. Kamar tasan me yake nufi ta ce da kuyanga Zubaida ta fara serving na kowa, kowa sai ya faɗi abin da yake da buƙata ta zuba mashi, abinci ne kala kala sun fi kala goma sha biyu a saman katafaren table ɗin, ga kuma kayan fruits, kun dai san yadda cimar gidan sarauta take? Duniya ce guda saman table nasu a yayin cin abinci, kaga abubuwa kala kala. Kowa ya nutsu tsit daga fitowar King, hakan ne zai kara tabbatar maka ƴaƴan nasa ma masu tarbiya ne, kuma sarauta mai karfi aka bugawa ta gasken gaske!!.
A yanzu Jaish da Jawad sun dai'na zuwa parlourn cin abinci da su king ɗin, a cewarsu mata sun yi yawa a wajen, damunsu da surutu suke yi, bare ma idan Aunty MieMie ta baro part nata ta shigo nasu, duk sai ta ishesu ta saka masu ido, shi ne yasa suka dai'na cin abincin ana, kai masu nasu a cikin part nasu kawai Kuyanga Zubaida take yi. Da yake kullum suna a tare sai yazama a cikin part ɗin Jaish kuyanga Zubaidar take zuwa ta jere masu abinci, kuma idan ta gama da su King zuwa take yi ta yi serving nasu Jaish ɗin ma baiwar Allah.
Yanzu ma haka ta hau serving nasu kowa yana faɗin abin da zata zuba mashi, kamar wata engine haka take aiki, yadda kuka san bettery aka saka mata, abinku da ta saba, abin ya bi jikinta!!.
Kowa ta yi serving ta tura mashi sai ya ɗauki spoon ya fara ci a nutse, masu zaɓar kasassun nama an tea ma suna fama da wukar yanka namar suna kaiwa baki, Obaid da Omaid a al'adarsu kafin su fara cin abinci sai Obaid ya bawa Omaid first spoon nasa, shi ma Omaid ɗin ya ɗeba ya basa a baki, haka suke, dan haka a yanzu ma abin da suka yi kenan kafin su fara cin abincin.
Zunaira dai tana a kusa da daddynta tana shan kankana sarkin son fruits, ga abinci nan tasa an zuba mata, amma ta zauna tana shan fruits ba tare da ta ci abincin ba.
Ita kuwa hajiya gorgeous Queen namu kuma fashion babynmu wato Gimbiya Aunty Chuchu, ta tasa abinci a gaba, kaɗan kaɗan take ɗeba tana kaiwa bakinta, hankalinta sam baya a tare da su, tana can ta afka duniyar tunanin abin da Yah Jawad zai yi mata da ya ce ta same shi a cikin bedroom nasa, tsoronta ɗaya kada ya yi mata faɗa, tasan dai baya duka kasafai, sai ka yi mashi laifi goma bai ɗaga hannu ya daki mutum ba, amma kuma ya iya bada punishment ga shegen iya faɗa da tsawa, ita kuma ta tsani faɗar nan a rayuwarta, gara mata ma a zaneta da a yi mata faɗa, to shi ne ta afka duniyar tunanin abin da zai yi mana.
Sarina sarkin yanga yauki da iyayi sai cin abinci take yi tana wani kwaɓe fuska, kanwar Yah Jawad ce, kuma ita ce ma mai bi masa a wajen haihuwa, tana da 19 year a duniya, sai kanwarta Fanan mai shekaru 17 years a yanzu, ita kuwa Aneesa ƴar mama shekarunta 15 years, shekara ɗaya ta bawa Chuchu. Ita ma fa Aneesa ba tayar baya bace, ta iya faɗa ga tsantsar nuna isa da izza, hakan yasa basu shiri da Gimbiya Sarina ko kaɗan, dan duk sarakan ji da kai ne, kunga kuwa ai ba zasu zauna inuwa guda ba.
Momma, mummy and Mama dukka kuyanga Zubaida ta yi serving nasu na abincin da ransu yake so, dukkansu sun ɗauki spoon and salad knife sun fara cin abincin a nutse.
Shi ma King ya fara cin nasa abincin a nutse.
Sai a yanzu kuyanga Zubaida ta samu damar sauke nannauyar ajiyar zuciya, dan ta samu ta gama zubawa kowa abin da yake buƙata, sai ta ɗan koma gefe ta tsaya, tana jiran masu cewa ta zuba masu ruwan sha ko kuma wani drinks ɗin, ko dai ta yanka masu fruits da sauran aikin da suke sakata a lokacin cin abincin nasu, duk cikin gidan Gimbiya Zunaira ce kawai bata saka kowa aiki, da kanta take yi komai, sai dai idan sun ganta zata yi aikin ne su yi maza su kwace su yi mata, amma ita ko fruits ɗaukar wuƙa take yi ta ce zata yanka da kanta, sai dai su kwace su yanka mata, ba zaka taɓa jin ko da sunan wasa ta ce wance or wane yi mun abu kaza ba, sam bata da girman kai kamar ba jikar cikakkun modarawa ba!.
BARI MU LEƘA SU KAMRAN WATA KILA KAFIN MU DAWO SUN KING SUN GAMA CIN ABINCIN!!.
🏞️FOREST🏞️
KING OF THE FOREST. Aikin gyaran namar ya kammala tas, sannan ya miƙe ya shigarwa da Mammarsa ciki kamar dai yadda suka saba.
Bayan ya jibge mata su a madafarta ya fito ya nufi wajen da yake yin wanka. A gurguje ya yi wankar nasa ya fito, kayansa da ya saba sakawa na sakar audiga na gonarsu da Mammarsa take saƙa masu ya ɗauko, zuciyarsa cike pam da tunanin su pretty, ita kuma Mamma zuciyarta a cike pam da tunanin me ya kawo mayaƙa cikin wannan daji da har suka farmaki Kamran ɗinta? Kenan hakan na nufin basu da nisa da Masarauta ne ko yaya?.
Abin ya yi mugun bata mamaki ne, yau tsawon shekaru 25 zuwa 26 tana cikin wannan daji! Bata taɓa ganin mayaƙa ba sai yau, tana dai ganin manya manyan maharba suna giftawa time to time, suma tana kan jima bata gansu ba, bayansu kuma bata ganin kowa, sai dai idan hanya ta kwacewa wani ya afko cikin dajin bisa rashin sani. Wannan abin ya ɗaure mata kai kuma ya bata mamaki!.
Fitowa tsab tsab cikin shigarsa mai kyau king of the forest ya yi, ya kara kyau sosai Kamran, sai dai daga ganinsa ba tambaya kasan tabbas yana da yare, dan yanayin fatar jikinsa dama shi kansa, yanayin su Mamma san basu yi kala da larabawa ko Hausa fulani or turawa ba, sai Allah sai kuma mammar tasa ce kawai suka san su ɗin ƴan wace ƙabila ce or daga wasu duniya suke? Nasan kowa a ransa yana tunanin me ya kawosu wannan dajin? Ina mahaifin Kamran tun da dai mace bata haihuwa ita kaɗai? Ni kai'na PRINCESS TEEMA waɗan nan tambayoyi shi ne a cikin rai'na, a wannan daji aka haifi Kamran, kuma da alama tun kafin a haifesa Mamma tana cikin wannan daji, ta yi rayuwa mai tsawo a ciki, to kenan before a tare suka yi rayuwa mai tsawo da baban Kamran ɗin har suka haifesa? Me yasami baban nasa? Ina ƴan uwansu? Idan ita Mamma bata da ƴan uwa to shi baban nasa fa? Ina nashi ƴan uwan? Kun ga dai Mamma jaruma ce, da alama kuma kamar yadda take bawa Kamran training ita ma haka aka bata horo a cikin wannan dajin, to waye kenan? WAƊAN NAN AMSOSHIN ALƘALAMIN PRINCESS TEEMA CE KAWAI ZAI IYA WARWARE MAKU SHI KU DAI KU KASANCE A TARE DA NI, BA ZAKU YI DANASANIN BIBIYAR WANNAN LABARI NA RAWANIN ZALINCI BA IN SHA ALLAH, ZAKU ILMANTU, KU WA'AZANTU, IN FAƊAKAR DA KU, KU NISHAƊANTU MATUKA, AKWAI ABUBUWAN DA IDAN MUKA SHIGA CIKIN LABARIN ZAKU SHA MAMAKI!!.
"Mamma, Mammaaa, where are you?". Cewar Kamran ɗin kenan.
Tana daga zaune a gefen bakin bed nata tana tunani a kan warriors ɗin nan ta amsa mashi da.
"Here I am, what happened? Why kake nemana?".
Yaye labulen sakar dake a bakin kofar ɗakin nata ya yi, kasancewar babu mai yi mashi aski a cikin wannan dajin hakan yasa gashin kansa take da yawa, sai dai mammarsa tana rinƙa yanke mashi tsawon gashin da wuƙa, saboda ya rage yawa kada ya rinƙa takura mashi.
"Mamma i want to go to somewhere here, ba zan jima ba, only 1 hour is okey for me na dawo gida".
Bin shi da kallo kaɗan ta yi kafin ta ce. "What about your food? Waye zai ci maka?".
"Oh Mamma na manta da abincin ne, to zan ɗauki abincin na tafi da shi, dama wani babban kogi na gani mai ruwa sosai a cikinsa ta ganganren can, so the place is very very beautiful, can zan je in yi bule a cikin ruwa".
Tun da ya fara magana tasan karya yake yi mata, domin tasan gaskiyarsa da kuma karyarsa, bai saba yin karya ba shiyasa idan ya yi dole a gane, a haka ma fa wai ya yi kasa da kansa baya son ta kalli cikin idanunsa, dan yasanta da kaifin ƙwaƙwalwa, so baya son ta gano shi, sai dai ya makaro, ita ta haife shi ta kuma renesa tsawon shekaru ashirin da biyar yanzu, dole ta iya gane shi ciki da waje.
Amma sam bata nuna mashi cewa ta gane karya yake shirga mata ba, sai ma ta ce ya je ya ɗauki abincin nasa ya tafi, ta kuma yi mashi hakan ne ba dan komai ba sai dan ta jima tun ɓatar su twins bata gansa cikin farinciki da annashuwa ba sai yau, tun shekaru goma baya da maman twins ta ɓace mashi ya koma wani irin so silent over, daga e sai a'a kawai yake haɗa shi da mamar tasa, ya dai'na sakewa suna hira, ya shiga damuwa sosai ta yadda mammar tasa duk kaifin basirar nan tata ta kasa iya shawo kan damuwar tasa.
So yau ta ga yana cikin annashuwa tare da farinciki, bata son ta ɓata mashi wannan farinciki da ya jima bata gani a saman fuskarsa ba, duk da cewa bata san murnar me yake yi ba, amma dai tasan Kamran ba zai taɓa yi mata abin da zai ɓata mata rai ba! So koma me silar shigarsa farinciki a yau tana maraba da shi, kuma ba zata yi abin da zai kawar masa da farincikin ba, shiyasa ta bar shi ya je duk in da yake so, tasan jarumi ne sosai shi ɗin, so zai kula da kansa.
(Kada fa Mamma ta yi mana wayo, ta yi mana mage mai kwanciyar ɗaukar rai ta bi bayansa ta je ta raba shi da su pretty mu shiga uku💔😥 ni nasan halinta sarai😥)
A hanzarce ya amsa mata da okey Mamma, kafin ya wuce ya nufi cikin wajen madafar tata ya ɗauko abincinsa a cikin wani mazubi mai kyau, sannan ya fito tare da ƙara kwala mata sallama daga bakin kofa akan ya tafi.
Tana daga cikin ɗakin ta ce mashi take care.
Daga haka ya fice daga cikin ƙogon, sam bai nemi Rocky ba, dan yasan yau Rocky yana can yana ta fama da cin nama, so ba kula shi Rockyn zai yi ba, gara mashi kawai ya yi tafiyarsa.
Kai tsaye wajen su pretty ya nufa, sai daɗi yake ji a cikin ransa. Cikin nutsuwa a hankali ya shiga cikin wajen nasu, dan yana rike da abincinsa a hannu, kada ya yi ya zubar da abincin.
Kwance ya iskosu a saman bed ɗin nasu, pretty tana karanta wani littafi wanda sai Allah sai kuma mum ɗinta tare da alkalamin PRINCESS TEEMA ne kawai yasan a ina suka samo wannan littafin, ga littafin dai na addu'oe ne.
Jin motsin mutun yasa pretty ta ɗago kai, ɗan wannan ɗagowa da ta yi yasa kumatunta suka ɗan motsa, hakan ya bayyanar mata da kyakkyawar dimple nata da ya ƙara bayyanar da kyan fuskarta.
Ganin shi ne yasa ta yi saurin miƙewa zaune tana binsa da waɗan nan idanun nata masu jefa bawan Allah cikin ruɗu ya kuma rasa nutsuwarsa.
"Pretty motsin me nake ji haka ne?".
Cewar Sweetie dake kwance.
"Wannan mutumin na ɗazun ne ya sake dawowa".
Ta bata amsa tana mai zuro ƴan kyawawan fararen kafafunta kasan gadon.
Yunƙurawa Sweetie ɗin ma ta yi ta miƙe zaune tana jin wani irin babu daɗi a cikin ranta, yau karo na farko da ta ji zafin ciwon makantarta, da sam bata damu da dole sai idanunta sun buɗe ta kalli abu ba, saboda a cewarta to ko idanun sun buɗema ai daga mum ɗinsu sai pretty kawai zata gani, wadda kuma ta saba ganinsu kullum, amma yau an sami sabon mutun wadda bata sani ba kuma bata taɓa ganinsa ba, kash ba halin ta ganshi, abin ya yi mata mugun ciwo yau, har ga Allah tana son ganin wanene shi ɗin.
A saman wata dutse mai ɗan girma kaɗan dake cikin wajen Kamran ya zauna yana faɗin.
"How's your body Sweetie?".
Kamar zata yi kuka, har idanunta sun ciko da ruwan kwallah na rashin gani ta amsa mashi da. Alhdulillah.
Maimaita kalmar Alhdulillah ya yi kafin ya maido da kallonsa a kan pretty dake ta faman kallon kwanon abincin dake hannunsa, bata taɓa ganin irin kwanikan ba, shi kuma bai taɓa jin kalmar Alhdulillah ba, so dukkansu da abin da suke mamaki a yanzu.
"Let's go now ko?". Cewar pretty sarkin sauri.
"Go to where?".
Ya tambaya yana mai da kallonsa a kan littafin da suke karantawa. Allah idanun Kamran suna da matuƙar kyau sosai, sai ma idan yana kallon abu, sai kaga idanun suna ɗaukar hankali sosai.
"Neman wannan mutumin da mum ta ce mu nemosa, you forget that you said zaka taimaka mana to fine him ɗazun ba?".
Har wa yau pretty ce ta bashi wannan amsa.
"Yeah i will going to help you ku same shi, but now ku zo ku ci abincin Mammata".
Da sauri Pretty ta mayar da kallonta a kan Sweetie dake faman girgiza kai alamar su ba zasu ci abincin ba, dan basu yarda da shi ba, kuma da alama mum ɗin su ta ja masu kunne a kan mutane, dan ga shi sai ɗari ɗari suke yi da shi, sam basu saki jiki da shi ba.
Ganin Sweetie tana girgiza kai ba tare da ta yi magana bane yasa pretty ta ɗan shagwaɓe fuska kamar zata yi kuka ta bashi amsa da.
"We can't eat".
A shagwaɓe ta yi maganar. Hakan ba ƙaramin kara mata kyau ya yi ba, duk sai ta sa Kamran ya ji wani irin bawan Allah.
Why?. Ya tambayesu yana mai do da kallonsa a kan Sweetie, dan ya lura ita ce mai sanya Pretty yin abu, idan ta ce ba zasu yi abu kaza ba to Pretty ma ba zata yi ba, idan kuma ta ce za su yi abu, to Pretty zata amsa su yi.
Ita ce babba kamar yadda ya yi tunani tun farko, kuma ta fi Pretty tunani da nutsuwa, and then ita tun ainahi bata cika fita waje ba, koda yaushe tana a tare da mum ɗinsu lokacin da mum ɗin take nan, hakan yasa ta fi Pretty sanin abubuwa sosai, and kuma kafin mum ɗin su ta ɓace kullum tana gaya masu cewa Pretty ta bi Sweetie sau da kafa, idan ta bita tamkar ita mum ɗin ta bi, duk abin da Sweetien ta ce mata to maza ta yi shi, hakan yasa kuka ga idan Sweetie ta ce a'a, to Pretty ma zata ce a'a.
"We can't eat your food be cause we don't know you, kuma mum ta ce kada mu yarda da kowa, kada mu yi magana da kowa, ko mutun ya yi mana magana kada mu amsa, sai dai ta ce mana akwai mutun ɗaya da idan muka ji zuciyarmu ta yarda da shi to mu yarda da shi, dan mai taimako ne, and kuma ta ce lallai mu nemo wani wanda ya taɓa taimaka mata a dajin nan". Cewar Sweetie kenan.
"If that's the case then why kuka yi accepted nawa time da na shigo nan? Why kuka yi magana da ni? Kenan kun karya maganar mum ɗinku? Ba ta ce kada ku yarda da kowa ba? Kada ku yi accept nawa sai wannan da ta ce ku nemo, why ni kuka yarda da ni?".
Sweetie ɗin ce ta sake amsa mashi da. "Bamu yarda da kai ba, and we didn't accept you, kawai bamu da yadda zamu yi ne?".
Yana ƙoƙarin sake yin magana Pretty ta riga shi da cewa.
"Ni dai ina ji a jikina kai ne wanda mum ta ce mu nemo, and kuma zuciyata ta yarda da kai, please don't play with our heart, idan kai ne wannan mutumin tell us, idan kuma ba kai bane please nan ma ka gaya mana, ni dai har cikin rai'na i really accepted you".
Haƙiƙa hakance, ta yarda da shi, ita ma Sweetie ɗin har cikin zuciyarta ta yarda da shi, kawai ita Sweetie da yake ta fi Pretty dogon tunani sai ya zamana bata son gaya mashi cewa sun yarda da shi, a ƴan kananan shekarun nan nata wai zata bari ne sai taga gudun ruwansa sannan ta gaya mashi cewa ta aminta da shi, yarinya mai wayo. Shegen wayo ke gareta kamar me!.
Tun a karon farko suka ji ya kwanta masu a cikin zuƙatansu, kuma kuwa kunsan Kamran yana da shiga rai, and then ko dan kyan zuciyarsa da son taimako dole a so shi, kada ku manta haɗuwarsu ta farko ma taimakon Pretty ya yi, badan shi ba ai da yanzu babu ita ta mutu, kunga kuwa ko dan wannan taimako da ya yi masu dole su ji suna son shi, and kuma dole su fara tunanin ko shi ne mai taimakon da mum ɗin su ta gaya masu? Sau da dama suna ganin maharba suna giftawa ta cikin dajin, idan sun gansu ɓuya suke yi dan kada su gansu, haka mum ɗinsu ta koya masu, kada su yarda wani ya gansu, su rinƙa ɓuya idan suka ga mutane, to a takaice dai duk maharban da suke gani suna giftawa basu taɓa jin koda mutun ɗaya daga cikinsu ya kwanta masu a cikin zuciyoyinsu ba sai Kamran ɗin, hakan yasa suka fara tunanin ko dai shi ne mum ɗinsu ta ce su nema?.
"I can't play with your hearts Pretty, not even you, ni bana cutar da kowa ko mai ƙanƙantar cuta, so feel free with me, yanzu dai ku zo ku ci abincin Mammata sai mu fita waje neman mutumin ko?".
Kallon Pretty Sweetie ta yi tana jiran ta ji me ƴar uwar tata zata ce.
"Okey zamu ci, amma ba'a gabanka ba, sai ka fita waje". Cewar Sweetie ɗin.
Da okey ya amsa masu kafin ya miƙe ya miƙowa Pretty abincin. Sai da ya ji wani irin shock da bai taɓa ji ba a jikinsa na haɗuwar hannayensu wajen karɓar abincin. Amma sai ya daure ya nufi hanyar fita daga cikin wajen.
A wannan karon sam yaki yarda ya juyo su haɗa idanu da ita, dan ɗan taɓa hannunta da nasa hannun ya yi bisa kuskure ma tasa ya ji kamar ba shi ba, dan haka sai ya yi ficewarsa kawai abinsa.
Yana fita Pretty ta kalli ƴar uwar tata kafin ta fara magana a nutse.
"Sweetie Allah wannan mutumin shi ne Mum ta ce mu nemo, na ji hakan a jikina, dama kin ji mum ta ce idan mun gansa zamu ji zuciyoyinmu sun yarda da shi, to ni dai na yarda da shi, ban san ko ke baki yarda da shi ba".
Nisawa ta ɗan yi kafin ta amsa mata da cewa. "Pretty na fiki yarda da shi, zuciyata ta aminta da shi, amma kada mu yi sauri, mu jira mu gani, kinga mum ta yi mana kashedi sosai a kan yin abu cikin gaggawa, gaggawa aikin shaiɗan ne, duk kuma wanda ya yi gaggawa a kan abu sai ya tabka danasani".
"Hakane, to amma Sweetie idan dai har kin yarda da shi kema why not ba za mu bashi saƙon da mum ta ce mu bashi idan muka ganshi ba? Kawai na ɗauko mu bashi, nasan ya manta mum ne shiyasa ya ce mana ba shi ba ne muke nema, amma tun da mum ta ce saƙon yana ƙunshe da abubuwa dayawa masu girmaa cikinsa kila idan muka bashi yana dubawa zai tuna da mum ɗin".
"Pretty kefa baki jin magana, wai ba yanzu na ce maki mum ta hanamu yin abu cikin gaggawa ba? Kina ji fa bai yarda cewa shi ne wanda muke nema ba, taya za'ayi mu ɗauki saƙon da mum ta ce mana sai lallai wannan mutumi da ya taimaka mata ɗin zamu bawa ki ce mu bawa wanda bai yarda shi ya yi taimakon ba? Kina son mu saɓa maganar mum kenan?".
"A'a bana son mu saɓa maganarta, dama dai kawai dan na ji ta ce idan mun ji ya kwanta mana a rai to shi ne, shiyasa na ce ko ya manta da mum ne idan muka bashi saƙon zai tuna".
Shiru Sweetie ɗin ta ɗan yi kafin ta ce. "A'a ba zamu bashi komai ba, ba zamu ma nuna mashi kamar an bamu wani abin mu bawa wanda muke nema ba, mu bari har sai ya amsa da bakinsa shi ne wanda muke nema, kuma sai ya rantse mana da Allah".
(Ni kuwa na ce idan ya san Allah kenan ba! To fa ga shi shi Kamran ya ɓoye masu shi ne ya taimaki mamarsu dan wani dalili nasa na kansa wadda bai bayyana ba, ga shi su kuma mamar tasu ta basu saƙo su bashi, ko saƙon menene?.....🤔 Wannan sai alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana kawai zai warware maku wannan cakwakiyar, ku dai cigaba da bibiya, bamu fara komai ba, sai a gaba zamu yi ainahin shiga cikin labarin cikin labarinmu, yanzu duk muna faro foundation!!. Amma kuma fa da gaske idan bai gaya masu shi suke nema ba ba zasu taɓa bashi wannan saƙon ba, to fahhhhhhhhh)
"Tom shikenan Sweetie yadda kika ce haka za'ayi, yanzu ya zamu yi da abincin da ya bamun nan?".
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Jeki ki juye shi a cikin bowl, ki dawo mashi da kwanonsa, mu ba zamu ci abincinsa ba, na ce mashi zamu ci ne kawai dan kada ya yi wani mummunar tunani a kanmu, ko kuma ya ja baya da mu ganin kamar bamu yarda da shi ba, na nuna masa zamu ci ne dan ya kara sakin jiki damu har mu gane wanenen shi mu kuma san idan shi ne wanda muke nema".
(Ka ji yara kanana da shegen wayo da kaifin ƙwaƙwalwa, kai Sweetie akwai dabara, wai ta nuna mashi zasu ci ne dan ya kara yarda ya saki jiki dasu, wai ƴan 10 years ne suke ƙoƙarin yiwa mai 25 years wayo fisabilillahi 🤌😂 to mu dai namu ido, a buga game ɗin mu gani!!.)
Haka kuwa aka yi, suka juye abincin nasa suka ɓoye da sunan sun cinye, sannan Pretty ta nufi waje dan ta kira shi a kan ya zo sun gama cin abincin.
Mu ɗan koma baya kaɗan, a lokacin da Kamran ya fito daga cikin wannan ramin, ya nufi samar wata bishiya kwantatciya ya zauna, irin waɗan nan itatuwanne da suke fitowa a kwance, zaku gansu kamar waɗan da aka kwantar, amma haka Allah yaka halittarsu, a kwancen suke. So ya nufi saman wannan itaciya ya zauna yana ta tunanin Pretty, har cikin zuciyarsa yake son yarinyar nan, tana da shiga rai, sai dai idanunta suna tsorata shi, dan bai taɓa ganin irinsu ba! Yau ga jarumi Kamran yana tsoron wani abu, bai ji tsoron giwa ba! Bai ji tsoron zaki ba!! Bai ji tsoron Damusa da macizai ba, bai ma san menene tsoron ba sai ga shi yau ya sani kuma yana tsoron kallon cikin sexy eyes ɗin Pretty, tab lallai akwai cakwakiya nan gaba.
A hankali ya fara jiyo motsi daga ɗan nesa da in da yake zaune, Allah yasa bai yi zurfi a tunanin Pretty da yake yi ba kunnnuwarsa suka iya tsinkayo mashi sautin motsin.
Jin hakan yasa ya yi maza ya haura saman itacen dake kusa da wannan wanda yake a tsaye, ya ɓuya a cikin ganyayyaki ta yadda shi zai iya kallon su wanenen ko kuma menene mai nufo in da yake, amma su ba zasu iya kallon shi ba, ya shige cikin ganyayyaki.
Shiru ya lafe a jikin itacen yana jiran yaga su wanenen?. Ya jima a haka har ya fara tunanin sauƙowa ya je ya duba menene a wajen ƙoramar, dan har lokacin bai dai'na jiyo wannan motsi ba, ga shi a in da yake daga saman itacen baya iya hango komai, saboda dogayen ciyayi masu sunkuru da kuma bishiyoyi sun rufe wajen. Hakan yasa baya iya hango me yake motsi a wajen ƙoramar, sai ya yi tunanin bari ya sauƙa ya lallaɓa ya je ya leƙa.
Sautin karar haniniyar dawakai da ya dira mashi a cikin kunnuwarsa ne yasa sai ya fasa saukar, ya zuba idanu yana jiran yaga ta ina zasu ɓullo mashi.
Can kamar minti uku da jin haniniyar dawakan sai ya fara jin sautin takun tafiyarsu suna tinkaro ta wajen da yake. Kara ƙanƙame itacen ya yi tare da kara lafewa a jikinta ya ɓuya da kyau ta yadda ba zasu iya ganinsa ba, sai dai shi ya gansu!.
Bayan wani ɗan lokaci suka bayyana a tsakiyar wajen. Wasu jiga jigan zataran warriors ne har guda takwas, sun horu sosai, dan sun fi waɗan da Kamran ɗin ma ya yi faɗa da su ɗazun, waɗan nan manya manya ne gasu da tsawo da kiɓa, duk da suke zaune a saman ƙosassu kuma lafiyayyun dawakansu hakan ba zai hana ka gane cewa e lallai tabbas cikakkun jarumai ne na kin ƙarawa ba, suna dai sanye da kayan yaki irin dai na jikin waɗan can warriors ɗin da Kamran ɗin ya kashe ɗazun, har wa yau fuskokinsu hular kayan yakin nasu ya rufe shi ba'a iya ganinsu, da alama daga masarauta ɗaya suka fito da mayakan da Rocky yake watandarsa da su.
Zaro idanu sosai Kamran ɗin ya yi yana kallonsu, abin ya yi mugun bashi mamaki na ganin wasu mutane irin waɗan da ya kashe ɗazun, tambayar kansa yake yi kenan suna dayawa a cikin dajin? Kenan dama suma a cikin dajin suke? Ko yaya abin yake?. Bawan Allah bai taɓa ganin mutane irinsu ba, bai san cewa shigowa suke yi dan neman wani abin da su kaɗai suka san shi ba kuma suka san dalilin da yasa suke nemansa.
Sai dai kuma babban abin ban mamaki da waɗan nan warriors ɗin shi ne, idan suna tafiya suka ci karo da mutun sai su far mashi, babu abin da ya yi masu kawai zasu hallakasa saboda tsabar zalunci da ya yi masu yawa, kun dai ga yadda suka farmaki Kamran ɗazun ko? Ba dan Allah yasa yana da karfi shi ma suka gwabza ba ai da kashe shi za su yi, babu dai abin da ya yi masu bawan Allah, to haka suke, ko maharbi suka ci karo da shi a wannan daji sai sun far mashi sun kashe shi babu gaira babu dalili, sai kace waɗan da aka turo su kashe duk wanda suka gani a hanya, ni kam ma wai daga ina suke zuwa ne? Akwai cakwakiya sosai my people.
Suna zuwa dai'dai in da wannan itaciya da Kamran ɗin yake kai suka ja birki suka tsaya, kamar sun san da akwai mutun a wajen, tun da suka shigo arear wajen kuma suke hira, dan a hankali hankali suke kaɗa dawakan nasu ba da gudu ba, hakan ya basu damar suke zuba hira a tsakaninsu, sai dai kash suna magana ne da wata yare na daban wadda shi Kamran sam baya jin me suke faɗa, ya so ya ji zancen da suke yi ko zai iya fahimtar su waye su? Amma ina bai taɓa jin irin wannan yare nasu ba sai yau.
Kamar daga sama Kamran ɗin ya hango kofar ramin da su pretty suke ciki yana motsi, alamar za'a buɗe wajen a fito kenan, a dai'dai lokacin ne Pretty ta nufo wajen zata fito ta zo ta kira shi a kan ya zo sun gama cin abincin....... Tashin hankali da ba'a saka mashi date!.
Wani irin zaro idanu Kamran ɗin ya yi tamkar idanunsa zasu fito su faɗi ƙasa, tunani yake yi idan Pretty ta fito tabbas kasheta zasu yi, shi kuma da bai shiryawa yaki ba, ko wuƙarsa da yake fita da ita yau ma bai ɗauko ba, saboda zumuɗin ya zo wajensu ya mantata a gida.
Waɗan nan shegun warriors da suke kamar wasu dodannin nan wlh cikin minti ɗaya tsab zasu hallaƙata mana Prettynmu, babu imani ko miskala zarratin a tattare da su, wasu bujumaye da su, waɗan nan idan ka gansu ma sai ka rantse da Allah suna cin namar bil adama, saboda yanayinsu babu imani tamkar duwatsune a cikin kirazansu ba zuciya ba, ko shi kansa Kamran ɗin a yadda yake ɗin nan ya kuskura ya sauko cinye namarsa ɗanye zasu yi bare kuma Pretty ƴar firitu da ita da ko cinyeta suka ce zasu yi namarta ta yi masu kaɗan.
Kamran dai bai gama razana ba har sai da ya ga Pretty ta buɗe wannan kofar tasu tana ƙoƙarin fitowa waje, daga in da yake yana iya kallonta, dan har ta fara fitowa waje, kuma suma warriors ɗin tsab zasu kalleta tana fitowa, saboda suna fuskantar ta wajen da take ɗin ne, ita kuma da yake bata san komai ba sai ta yi yunƙurin fitowarta kai tsaye kamar yadda ta saba, har ma da karawa da saurinta dan ta fito ta kira Kamran...........
Wayyo Rocky yana can yana watandarsa bare mu ce ya kawo masu agaji, yau take sallarsa ai ba zai kula Kamran ba, Wayyo ni kai'na kada waɗan nan azzaluman su cinye mana Pretty ɗanyarta fa......💔😥
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍