Free chapter · Read without an account
54
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 13/9/2024.....✍️📚🌹
For more information *** Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________51🔥
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼
KINGDOM OF POWER 💪🔥💘
"Jannat lafiyarki kuwa?". Akka ta sake faɗa cike da damuwar son sanin me ya sami jikar tata ta zunduma ihu haka.
Dawo da kallonta a kan Akkar ta yi, a hankali ta sake satar kallon dressing room ɗin, da farko kamar zata gaya mata gaskiya, amma sai wani tunani ya faɗo mata a rai, tunawa ta yi cewa to idan har Yah Jawad zai gudu ya ɓuyan wa Akka bai kamata ta gaya mata cewa yana nan ba, yin hakan zai sanya ya ji babu daɗi. Wannan tunani yasa ta dawo da kallonta kachokam kan Akkar.
"Akka babu fa abin da ya sameni, ji nayi ne kamar wani abin ya shiga mun cikin rigata yana tafiya, shiyasa na yi ihu"
Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke daga in da yake tsaye, sanyi sosai ya ji tana ratsa zuciyarsa, ba ƙaramin daɗi ya ji da bata faɗi gaskiya ba, sai albarka yake saka mata a cikin zuciyarsa.
Matsowa kusa da ita a hanzarce Akkar ta yi, riƙota ta yi tana faɗin bari ta duba cikin rigar tata ta gani kada ya zamana akwai wani abin a ciki ya ji mata ciwo, ko ya cutar da ita.
Ƙanƙame rigarta ta yi bata son Akka ta kalle mata tula tulanta, mamaki ne ya kama ƴar tsohuwan. "Jannat lafiya? Ki bari na duba mu gani".
Girgiza kai ta fara yi. "Akka ni ba sai kin duba ba, koma menene ya tafi, kuma ma babu komai a ciki ni ce na ji kamar da akwai wani abin". Ta faɗa tana turo baki.
Haba da yake Akka sarauniya ce wajen iya magana, tuni ta fara sababi. "Ah ah ah lallai Jannat, ƴan nonuwar naki ne baki son in gani ko menene?" Nan fa ta fara jero mata kan cewa ai ba ita ba su Aunty MieMie duk taga nasu bare ita, dan haka sai ta duba..........😅
Dariya ne ya so kubcewa Jawad dake laɓe cikin room, yana jiyo duk abin da suke faɗa, yau yaga ikon Allah, yarinya da kayanta Akka ta ce sai ta duba, duk sai ya ji haushi za'a kalle mashi abin da shi ma bai taɓa kalla ba, wai shi ya zai yi da Akkar nan ne? Mata idan ka nuna baka son abu sai ta ce sai ta yi shi, ita fa idan taga kana kin abu ka ce baka so, sai ta ce rashin gaskiya ka kullah a wajen, dan haka sai ta ce sai ta gani!!.
Jawad dai bai ji daɗin hakan ba, dan yasan ran Chuchunsa zai ɓaci sosai, babu wata budurwa da take tasowa wadda zata so a kalle mata abinta, bare ma idan tana da kunya, wannan dabi'a ce ta mata, a jininmu yake.
Ita kam Akka ta kafe sai ta duba cikin rigar, ita kuma Chuchu taki yarda har da kukanta, ran Jawad ya ɓaci sosai, kamar ya kifawa Akkar nan mari yake ji, sai dai ba hali, ya suka iya da ita? Ai dole sai hakuri.
Da Akkar ta ga da gaske kuka Chuchun take yi da hawayenta, sai ta kyaleta ta koma cikin toilet dan dama wanka zata yi, tana shirin farawa kenan ta jiyo ihunta, so sai ta koma kawai tana yi mata sannu haɗe da surutun Chuchu na ɓoye mata ƴan nonuwa.
Tana shiga cikin toilet ɗin ya fito da sauri, ransa a ɓace saboda sanya mashi beb ɗinsa kuka da tsuhuwar nan tasu ta yi. Ya ɗaure fuska kamar hadari.
Yana zuwa in da take ya riƙo hannunta tare da ɗauka mata school back ɗinta dake saman gadon Akkar wadda ta ajiye da kanta. Ya riƙo hannunta tare da nufar kofar fita. Har lokacin ƴan siraran hawaye suna bin saman ƙuncinta.
Kai tsaye part ɗinsa ya wuce da ita ba tare da ya ce mata ko uppan ba, ya kuma yi sa'a bai ci karo da kowa a hanya ba har ya isa part ɗin nasa, kasancewar da safe ne kowa yana can yana ta faman aikin shiryawa, masu zuwa school suna nasu shirin, masu zuwa office suna nasu, masu yin breakfast suna fama, kowa dai yana room nasa yana abin da yake yi.
A bakin bed ɗinsa ya zaunar da ita tare da ciro handkerchief mai kyau daga aljihunsa, ya zauna saman bedside drawer, a gefenta ya ajiye mata jakarta kafin ya kai hannu a hankali ya fara goge mata hawayen nata.
"Am so so sorry my sister, duk ni na ja maki yin kuka da sassafen nan, kyale Akka hai ki dai'na kuka ba zata gani ɗin ba". Ya faɗa ƙasa ƙasa.
Ƙasa ta yi da kanta, kunyarsa take ji sosai saboda ya ji yadda suka yi da Akka, ga Akka bakinta babu full stop ta rinƙa kiran sunan tula tulan a tsiraransu, abin ku da tsoffi sam bata wani sakaya sunan ba, ta rinƙa ambatarsa ba kakkautawa, wannan dalilin yasa Chuchun ta ji tana bala'in kunyar yayan nata, dan ya ji komai.
Shi ma ya fahimci kunyarsa take ji, sai ya kawar da zancen da cewa. "Yau na kai ki school da kai na ko?". Ya yi maganar yana ƙurawa jikinta ido, gani yake kamar gizo idanunsa suke yi mashi, kamar kuma da gaske ne bata sanya vest a ciki ba, kuma bata sanya bra ita.
Yana son ya tambayeta kuma yana jin fargabar yadda zata ɗauki abin, tsoro yake ji kada ta kalli hakan da wata manufa ko kuma ta fara gudunsa ko dai ta fara jin kunyarsa sosai. Idan ɗaya daga ciki ya faru ba zai ji daɗi ba!.
Wani tunani ne ya faɗo mashi cikin ransa, idan ya tashi daga office ya je ya yi masu shopping na vest dayawa ita da Auta, sai ya bawa Autar ya gaya mata kada su sake saka kaya ba tare da sun saka vest a ciki ba, wannan ce tunanin da ya yi, yanzu haka sam ransa bai so ta tafi school a haka ba, amma ba yadda zai yi, idan ya ce zai yi mata magana a yanzu to tabbas zata haɗa maganar da abin da Akka ta yi mata ta kwaɓesu, daga haka zata fara ja baya da shi.
Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e ya kaita school da kansa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Kin yi breakfast ne?".
Kai ta girgiza mashi alamar a'a. Waya ya ɗauko ya kira kuyanga Zubaida a kan ta kawo mashi kayan breakfast yanzu. Yana ajiye wayar ya hau janta da hira dan ta saki jiki ta mance da abin da Akka ta yi mata ta koma walwalarta.
Ba'afi minti biyu da kiran da ya yi wa kuyanga Zubaida sai gata ta iso baki ɗauke da sallama. Izinin shigowa ya bata ba tare da ya kawar da kallonsa daga kan Chuchu dake ta faman murmushi ba, har ya mantar da ita kuncin da take ciki, ya sanyata farinciki.
Saman carpet ya yi mata umarnin ta ajiye mashi abincin, a hanzarce ta karɓi umarninsa tare da aiwatarwa.
Bayan ta fita ne ya ce da Chuchun ta zo su je su yi breakfast a tare. To ta amsa mashi da shi, hannunta ya riƙo suka nufi wajen kayan abincin.
Zama ya yi tare da zaunar da ita a kusa da shi. Cup mai shake da coffee mai zafi ya ɗauko ya kai mata bakinta. Ba musu ta buɗe baki ta fara karɓa. Wayarsa ce ta fara kara daga cikin aljihun coat ɗin jikinsa. Hannu yasa ya ciro wayar tasa.
Yah Rizwan, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Cigaba da bata coffee ɗin ya yi yana haɗa mata da pepper soup na kaza mai bala'in daɗi. Cike da kaunar yayan nasa ya ɗauki wayar yana kuma mamakin kiran da yayan nasa ya yi mashi da sassafe haka.
"Assalamu alaikum Yah Rizwan barka da safiya". Ya faɗa cikin nutsuwa, yana magana yana yanko tsokar kazar yana cusa mata a baki. Ta saki jiki sai ci take yi abinta.
"Jawad ka tashi lafiya?". Rizwan ya tambaya, daga jin muryarsa kasa yana kaunar ɗan uwan nan nasa sosai, sannan muryarsa da alama damuwa matuƙa a tattare da ita.
Da lafiya lou Alhdulillah ya amsa mashi da shi, sannan ya ɗaura da cewa. "Yaya ya naga ka kirani da sassafe haka? Ko dai akwai wata matsala ne?".
Sai a lokacin Chuchu ta ɗago idanu tana kallonsa jin ya ambaci matsala.
Daga ɗayan ɓangaren ya amsa mashi da. "E akwai matsalar babba ma kuwa, amma ba ita ce tasa na kiraka ba, na kiraka ne dan naji ya ka kwana? Ya kuma ka tashi? Jiya ban samu ishasshen barcin kirki ba, saboda tunaninka".
Miƙawa Chuchun cup ɗin coffee ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye ya nufi hanyar fita yana faɗin. "Matsala kuma Yah Rizwan? To matsalar me? Meyake faruwa?"
Bin shi da kallo ta yi har ya ficewa ganinta. Cigaba da cin abin nata ta yi tana tunanin to matsalar me aka samu kenan?.
After some minutes ya dawo cikin ɗakin fuskarsa babu annuri ko kaɗan, da alama Rizwan ɗin ya gaya mashi wani abin da ya ɗaga mashi hankali sosai, jikinsa duk ya yi sanyi sosai kamar ba shi ba. Kusa da ita ya koma ya zauna yana faɗin. "Jannat ci abinci da wuri na kai ki school akwai in da zanje".
Cikin sanyin murya ta ce. "Yah Jawad kai fa? Ba zaka yi breakfast ɗin ba ne?".
Kai ya gyaɗa mata alamar e ba zai ci ba, sannan ya ɗaura da cewa. "Sauri nake yi, ki ci da wuri in kaiki school ke dai, idan na dawo daga in da zan je zan yi breakfast ɗin".
"Yah Jawad meyasameka naga fuskarka ta sauya haka". Ta faɗa tana kallon face ɗin nasa.
Babu komai ya amsa mata da shi, sannan ya fara ƙoƙarin kiran number Jaish domin su gaisa su kuma yi magana, dan basu yi wayaba, ya so ya kira shi tun farkawarsa daga barci, amma bai samu dama ba, ya sha'afa.
Ringing wayar ta yi har ta katse ba'a ɗaga ba, duba time ya yi a danƙareriyar watch dake hannunsa. 7:05 am, yakamata ace Jaish ya tashi barci yanzu ai. Ya faɗa a bayyane tare da sake gwada kiran number.
A karo na biyu ma ba'a ɗaga ba. Knocking na kofar ɗakin da aka yi ne ya ja hankulansu shi da ita izuwa bakin kofar. Kasa ƙasa ya furta wanene?.
Daga wajen kuyangarsa ta amsa mashi da ita ce, tazo tana son fara yin aikinta ne na gyaran ɗaki. "Ki je sai anjuma ki dawo". Ya faɗa yana dawo da kallonsa a kan wayarsa da call ya shigo ciki yanzu.
Mammie, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗauki call ɗin, yana sonta, ya ɗauketa kamar uwa, saboda yana ganin cewa tana son su kuma ta rike su kamar ƴaƴan cikinta.
"Good morning Mammie". Ya faɗa cikin sanyin murya.
Tana daga zaune saman sofa a fatafaren parlournta, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, kamar kullum tana cikin haɗaɗɗen kwalliyar nan nata na alfarma, ga ruwan madaran gwala gwalai da ta zuba wuya da hannu, ta fito a hamshakiyarta, ta ko'ina dai bata da makusa sai bakar zuciyarta, kyakkyawar macece ga iya ɗaukar wanka, sai dai kash, kyan ɗan macijine. Daga gefenta wata hamshaƙiyar budurwace take zaune mai tsananin kama da ita, daga gani ba tambaya kasan kanwarta ce, dan sun yi kama sosai, yarinyar ba zata wuci 25 to 27 years a duniya ba, ita ma kyakkyawace, ga shi ta iya ɗaukar wanka kamar Mammie ɗin, yanzu haka ta sha wanka, duk wanda ya kalleta sai ya sake waigowa ya kalleta, da alama abin ya samo asali ne, duk yadda aka yi ainahinsu ƴan son gayu ne sosai.
"Morning Jawad how was your night?". Ta faɗa tana kallon kanwar tata.
Bayan ya amsa mata sai ta ce. "Kafin ka tafi office ka sameni a parlour mu ɗan yi magana".
Da okey kawai ya amsa mata, katse kiran ta yi tana bin kanwar tata da kallo. "Aliyah lafiya kike cunkushe rai haka?".
Kara tunɓune fuska kanwar tata ta yi kafin ta ce. "Aunty ba dole na turɓune fuska, ni ban san ya zan yi ba, saboda King nake zuwa gida nan, amma har in je fadarsa in gaishesa in fito baya ɗaga idanu ya kalleni, kuma ni ina matuƙar sonsa Aunty"............. Tashin hankali kenan, yau ake yinta, ita King ɗin da kansa ma take so ba ƴaƴansa ba, lallai wannan ta ɗebo da zafi, kai bama da zafi ba ta ɗebo mai tafasa!!.
Wani irin zaro idanun Mammaien ta yi, tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa. "Amma dai Aliyah baki da hankali! Ko dai kin sha wani abin ne yau kafin ki zo gidan nan! King Zuhair ma kike magana ko wani King ɗin da ban sani ba?!". Cikin tashin hankali ta yi maganar.
Kara turɓune fuska sosai ta yi. "Aunty idan ba King Zubair ba wani King muke da shi mai power a ƙasar Tunisia? King Zuhair nake magana a kai mana, kuma shi nake so, shi nake burin aura, In Sha Allah kuma ni ce cikon matarsa ta huɗu! Da ni zai rufe kofa, ko ana ha maza ha mata wlh sai King ya aureni!!". Babbar magana!.
"Aliyah lallai mutuwa kike nema, wlh idan baki yi hankali ba a ɗanya ƴaƴansa zasu cinye namarki, wai ke Aliyah ni da nake nan ina ta faman yadda zan yi in ga King auri Jahiz ɗan autan su King ɗin, shi ne bashi da aure, bai taɓa yin aure, matashi saurayi ne mai jini a jika, ga shi shararren mai kuɗi, duk duniya ta san shi, ya fi Abbas fa kuɗi nesa ba kusa ba, ke in takaice maki ma wlh zai iya fin King Zuhair ɗin ma kuɗi, ga shi sabon jini, shararrene da duniya dukka suna san shi, shi ba iya ƙasar Tunisia ne kawai aka san shi ba, duniya gabaɗaya ta san shi, shararren ɗan kwallo ne da yake bugawa Real Madrid, ke kanki kin san da haka, kin san Jahiz ganinsa da ido ma ba abu bane mai sauki, ko a cikin family na kusa kusa ba kowa yake samun damar ganinsa ba, ni kai'na da nake matsayin matar yayansa ma idan ya zo gidan nan ba samun ganinsa nake yi ba, idan kinga na gansa to yayansa yana nan, nan ne zai shigo wajen yayan nasa, a nan nake samun damar ganinsa, kuɗi iya kuɗi yana da shi, ga shi sabon jini matashi, me kuma zaki buƙata....."
Katseta Aliyah ta yi da cewa. "Sarauta! Yana da sarauta ne? Duk kuɗinsa a banza idan ba shi da mulki, burin mulkar ƙasar Tunisia nake da shi ni ba kuɗi ne a gabana ba, burina in yi mulki, in zama mai faɗa aji, dan haka yasa nake son zama mace ta huɗu da zata rufe kofa a zuciyar King Zuhair....." Tashin sense!!.
"To idan mulki kike so ai magajin masarautar zaki ci burin ki aura, magajin wannan powerful seat ɗin zaki kwaɗaitu da son aura, ga Ramish! Ga Bilal! Ga Suraj! Ga Jaish! Sannan ga Aryan! Ɗaya daga cikinsu yakamata ki zaɓa ai, dan sune zasu gaji wannan kujera mai matuƙar power da karfin ikon, in dai burinki ki zama mai faɗa a ji a faɗin ƙasar Tunisia ne to ɗaya daga cikinsu zaki buƙata........"
Kara kwaɓe fuska ta yi tare da wurgawa Aunty tata wani irin kallo mai kama da zargi. "Gaskiya Aunty kanki baya kawo wuta sam sam, ni fa ba ce maki na yi ina son in auri wanda zai yi mulki a nan gaba ba, so nake na haifi wanda zai yi mulki a nan gaba, kina tunanin ko na auri ɗaya daga cikin ƴaƴan King zan samu yadda nake so ne? Gaskiya Aunty sam baki tunani mai kyau, ai ko na auri magajin kakkarfar kujerar izza buƙatata bata biya ba, dan dai ke da kanki kin san ƴaƴansa ba masu juyuwa bane, baki isa ki juyasu yadda ranki yake so ba! Amma idan kika auri uban kika haifi naki ƴaƴan, ko ba yanzu ba nan da shakaru 20 zuwa da 25 zaki zama yadda kike burin ki zama, zaki zama mai karfin iko, a duk lokacin da aka ce ɗanki ne a saman wannan the most powerful seat ɗin, sannan ya sanya powerful Crown a kansa, ai kinga daga nan zaki murza kambunki son ranki a faɗin ƙasar, amma idan kika biyewa ƴaƴan nan nasa sai su ce maki basu son sarauta kamar dai Yah Abbas, kin ga shi ma ya ce maki baya sha'awar sarauta, to nasan ƴaƴansa ma yadda suke shararrun ƴan bokon nan ba wani mulki da za su yi, shiyasa bana son na auri magajin mulki, nafi son na haifi magaji wadda ko ya ce baya son ya yi mulki zan tursasa shi dole ya yi, sannan shi Jahiz da kike magana kada ki manta bashi da gadon mulkin nan a yanzu, dan King yana da yara, da bashi da yara ne sai kaninsa ya hau kujera........"
Kallon tsab Mammie ta yi mata. "Lallai Aliyah kin girma, waye ya ce maki Jahiz bashi da gadon mulki? Yana da shi mana, idan su Ramish suka kekashe ƙasa suka ce basu da ra'ayin mulkar ƙasar Tunisia ai dole idan King ya tsufa Jahiz ya karɓesa tun da Abbas baya ra'ayi".
Cike da rashin respect a maganar tata ta furta. "Aunty koma dai menene ni magajin nake son haifa, magajin da ko baya son mulki zan tursasa shi yi dan cinmma burina, dan haka ni King Zuhair ne burina, shi nake son aura!".
"Aliyah King Zuhair ya fi karfinki, Jahiz shi ne zaɓin da na yi maki, dan haka ki dai'na maganar King!!".
Cigaba da wurga mata kallon zargin ta yi, a ƙule ta ce. "Aunty saboda kema kina da burin auran King Zuhair ɗin shi ne kike son hanani ko? To ki bari mana kowacce ta gwada sa'arta, a cikinmu duk wadda ta samu nasarar mallakarsa ai shikenan duk ɗaya muke, ni dai ba zan hakura da burina kuma muradina ba"............... Tashin sense, lallan yanzu KINGDOM OF POWER zai kama da wuta, na ce ba my people's mu gayawa Aliyah wacece Momma ne ko dai mu bari ta Momma ta gwada mata karfin jinin Modarawa?🤔 Tab kuna tunanin da Momma King ya fara aura ma zai kara aure ne? Ai da ba wannan magana kuma kun sani, hmmm Hajiya Aliyah momma kam dai'dai take da zamaninki, ga Mama a gefe, sannan ga mummy, uwa uba ga su Ramish, wai kuna tunanin su Ramish zasu yarda King ya auri wadda suka girma ne?🤔 Gaskiya akwai rikici a wanan gida ba kaɗan ba.
"Aliyah ni kike gayawa ina son auran King Zuhair? A yaushe muka yi hakan dake?". Ta yi maganar cike da mamaki tana kuma zaro idanun.
"Kina mamakin ya aka yi nasan burinki ne Aunty? To bari ki ji ranar da kika je gida ina jinki ke da mama kuna magana a kan ke dama ba Yah Abbas kike so ba, King Zuhair kike so, dan burin mulki kike da shi, kuma ko za'a mutu ko za'ayi rai, ko rai nawa zaki iya salwantarwa domin ki auri King ki haifi maganin Crown of Kingdom of power!!".
Kara zaro idanu sosai Mammie ta yi, bata taɓa tunanin bayan mahaifiyarsu akwai wadda tasan da wannan magana ba, sirrinta ne kuma burinta!.
"Aunty ki dai'na yin mamaki fa, kuma ki dai'na ƙoƙarin hanani mallakar abin da zuciyata take so, Crown na kingdom of power rawani ne da kowani basarake yake burin samunsa, kujerar mulkin kingdom of power kujerace da jiga jigan sarakuna masu karfin iko suke fatan su zauna a kansa, masarautu ba adadi ne a ƙarƙashin wannan masarauta, duk wani karfin ikon mai karfi a faɗin ƙasar nan dama maƙota ƙasashe duk a ƙarƙashin King Zuhair suke, a haka kike son nayi wasa da wannan dama? Sanin kanki ne fa shiga in da King Zuhair yake ma ba ƙaramin abu bane, ke kanki kin san ko da yatsa ka nuna gate na farko na shigo cikin masarautar nan sai an datse maka hannu, duk wani karfin iko da isa tana nan! Wlh kamar yadda kika ce ko rayuka nawa zaki iya salwantarwa domin ki mallaki King, ni ma hakance, zan iya aikata komai dan na mallakesa, dan haka da ni dake lokacin buga wasa a tsakaninmu ya yi, kowacce ta gwada sa'arta kawai....." E lallai akwai cakwakiya ba kaɗan ba!.
Tana kai karshen maganar ta miƙe fuuu abayar jikinta na ja a ƙasa ta nufi waje, bata zame ko'ina ba sai family part ɗin King, kai tsaye wajen mummy ta nufa, dan ita mummy ƴar baruwa na ce, kowa nata ne, kowa ya zo gidan hannu bibbiyu take tarbansa, shiyasa suke sonta, tana da hakuri haɗi da kawaici, ainahin mahaifiyarta ƴar Nigeria ce, kuma ita ba yar kowan kowa ba ce, tana da taimakon mutane da kuma saukin kai sosai, ba kamar Mama da Momma ba, ku kunsan Momma tana da kyan zuciya, wargi ne kawai bata ɗauka! Iadan ka kawo mata ba dai'dai ba yanzu zata nuna maka cewa jinin Modarawa ne yake gudu a jikinta. Mama kuma sai ka rasa me matar nan take so a duniya, sai bala'in masifar tsiya, ga ɗan banzan kishi na masifa.
Da kallon mamaki Mammie ta bi Aliyah har ta kurewa ganinta, mamaki da al'ajabi ya hanata yin magana, tunani take yi wai yaushe Aliyah ta girma da har take cewa su ƙara ko wacce tata ta fisheta?. Ita ma fa Mammien ba wata babba bace take wani cewa yaushe Aliyah ta girma, Aliyah ɗin ce fa mai bi mata a wajen haihuwa, kada ku manta Sarina ce ƴarta ta farinta, so ita ma ba wata babbar mace can can bace, iyayi ne kawai.
Wayarta ta ɗauka tare da miƙewa ta nufi cikin bedroom ɗinta tana faɗin. "Dani kike yi Aliyah, yaushe ma aka haifeki da har zaki ce mu ƙara akan muradina? Ke har kin isa ina son abu kuma a yunwace nake da na cinma burina a kansa ki ce kema kina son shi? Wlh ba'a haifeki ba! Tsab zan gyara maki zama, zan gwada maki banbancin shekaru..."
Ta kai karshen maganar tata tana zama a gefen bed ɗin nata, dai'dai lokacin kuma wadda take kira a waya ya ɗauki kiran. "Misalin karfe 1 dare mu haɗu a in da muka saba haɗuwa". Shi ne abin da ta gayawa wanda ta kira ɗin. Tana gama faɗin hakan ta katse kiran tare da buga uban tagumi tana tunani.
(Ni kam na ce uncle Abbas da King sun ga ta kansu, shi yanzu uncle Abbas kenan ya Mammie zata yi da shi tun da ta ce yayansa take so? Shi kuwa King yaga ta kansa kowa son shi yake yi, bawan Allah bai ma san ana yi ba, momma ki shirya ga kishiyar karfi da yaji na dole nan Aliyah tana zuwa, zaki tashi daga amarya 😅 Mama kuma kishi zai karu😅 family part ɗin King zai kama da wuta, 🔥 mummy baiwar Allah dai babu ruwanta, da rabon za'ayi yaki ba kaɗan ba, da rabon su Ramish zasu yi kisan kai ko na ce kashe kashe😅 hmmmm KINGDOM OF POWER kuma yanzu nasu wasan zai fara🔥 ina commander ZAFAR sai ku shirya, ni dai bari na tafi Nigeria gidansu Zainab dan jin ya ake ciki).
GIDANSU KHADIJAH 😥💔
Hakura maman Zainab ta yi ta karɓi wannan ɗaki da Hauwa ta zaɓa mata, a ciki ta kwana, bakinciki kamar zai kasheta, ta fara danasanin zuwanta sabon gidan nan, dan bakinciki kala kala Hauwa take kunsa mata, tsabar mugunta dan ta kuntata mata ma da daddare tasa baban Zainab ya sanyata ta yi masu girkin dare, har da gaya mata kalar abincin da take son ta girka masu Hauwar ta yi.
Idan ran maman Zainab ya yi dubu to ya ɓaci, amma haka ta daure ta yi girki tare da taimakawar su Khadija, ita kuwa Hauwa tun yamma da ta gaya mata ga abin da zata yi masu, suka ci wanka ita da baban Zainab ɗin suka nufi kasuwa, ta tasa shi a gaba wai sai dai su je ya karɓi komai nasa daga hannun Sadiq, haka ya shirya suka tafi, maman Zainab ta yi girki tare da su Khadija.
Sai can wuraren karfe 9 na dare su Hauwar suka dawo, a lokacin maman Zainab sun kammala girki ta zubawa su Khadija sun ci nasu, ita ma ta ɗan tsakuri kaɗan ta ci, bakinciki ya hanata cin abincin na kirki, so kaɗan ta tsakura.
Tana gama cin abincin bayan sun yi sallar mangariba da isha'i ta wuce ɗakinta ta kwanta, su Khadija ma suka wuce nasu da Hauwa ta basu suka kwanta, Zainab ta yi addu'ar barci ta kwanta, ita kuma Khadija ta ɗauro alwala, dan kwanciya bai ganta ba iyayenta suna cikin masifa.
Maman Zainab tana kwanciya sai ga kiran Sadiq ya shigo cikin wayarta, haka kawai ta ji gabanta ya faɗi da ganin kiransa. Ɗauka ta yi cike da fargaba. A hankali ta yi sallama kamar mai jin tsoron wani abin ko wadda bakinta yake ciwo.
"Assalamu alaikum Maman Zainab na manta ban gaya maki ba ni fa ina hanyar Kaduna, da farko massages naso in tura maki, amma sai dai nace bari kawai na kiraki". Cewar Sadiq ɗin.
A zabure ta miƙe zaune a tsakiyar gadon, zaro idanu waje ta yi. "Sadiq me zaka je yi a Kaduna? Kuma sai ka tafi baka sanar da ni ba? Yanzu da ka tafi ya kake son na yi da rai'na? Da waye zan yi shawara? Waye zai rage mun raɗaɗin da yake damuna a rai'na?! Ina kake son na sanya rayuwata na ji daɗi? Mutuwa kuke son nayi ne?". Tana magana wasu zafafan hawaye suna biyo ƙuncinta.
"Ki yi hakuri maman Zainab, dole ce tasa na tafi, amma kinsan ni ma ba zan so rabuwa dake a irin wannan hali da kike ciki ba, shiyasa nace maki da farko sms naso in yi maki ba kira ba, saboda kada na ji kukanki, da ina turo maki sms zan kashe wayata, amma ki yi hakuri Allah yana tare da ke!!".
"Sadiq to me yayi zafi da zaka tafi ka barni? Kana da wata ƴar uwa a duniyar nan biyu na ne? Ko dai ka dai'na sona ne". Cikin raunin murya haɗe da karyewar zuciya ta yi maganar.
"Ko ɗaya maman Zainab, ban dai'na sonki ba, yama za'ayi na dai'na sonki? Ai ba zai yiwu ba, yanayi ne yazo da dole na yi nisa dake, idan ba haka ba zan iya aikata kisan kai wadda kema kanki ba zaki so na yi hakan ba, ba zan iya jurar cin kashin da suke yi maki ba, baban Zainab ya zo kasuwa da yamma, ya karɓi komai da komai nasa, mun yi lissafi da shi da Hauwa, komai ya fita yadda yakamata, kuma mun yi a rubuce yasa hannu na sa hannu a kan na mayar mashi da komai ɗinsa, shi ne naga ya dace na koma gida in je in kula da mama".
Magana ta gaskiya ba hakance tasa Sadiq ya bar garin Kano ya kama hanyar Kaduna ba, abin da yasa shi ne, wani irin mummunar cin mutunci baban Zainab da Hauwa suka yi mashi a kasuwa, ga lissafi sun yi dallah dallah amma Hauwa ta ce da baban Zainab karya ne ya saci wasu kuɗaɗen, wai ba zai yiwu ace iya wannan ribar kawai aka samu a shagon ba, gudun irin haka fa yasa Sadiq ɗin yake ciyar da su maman Zainab ɗin da kuɗinsa, harta su maman Haidar idan suka zo kasuwa a kan basu da abincin ci daga aljihunsa yake cire kuɗin ya basu, duk dan kada ya taɓa naira biyar ɗin baban Zainab, amma da yake Hauwa makirace, kuma tana jin haushin marin da ya yi mata, sai da ta sa baban Zainab ya ci mutuncinsa a bainan nasi, ya yi mashi kaca kaca, shi kuma Sadiq ga shegen zuciya kamar ɗan kuturu, hakan yasa ya haɗa kayansa ya nufi gidan iyayensa in da zai bugi kirji yace ya isa a can, har police Hauwa ta ce baban Zainab ya kira su zo su tafi da Sadiq ɗin, da kyar masu shagunan kusa da su suka bata hakuri ta hakura, mata kamar wata kanwar shaiɗan. Wannan shi ne a takaice abin da ya faru a tsakaninsu da yasa Sadiq ɗin ya bar Kano, yaki gayawa ƴar uwa tasa gaskiya ne kawai dan baya son ya ɗaga mata hankali, baya son kara mata zafi a kan zafi, shiyasa ya ce mata sun yi lissafi lafiya lou!!.
Sosai maman Zainab ta rinƙa kuka, sai hakuri yake bata ita kuma tana yi mashi magiyar ya dawo dan Allah, daga shi sai su Khadija take gani ta ji daɗi a rayuwarta, sune kaɗai suka rage mata, sune kaɗai farincikinta a yanzu.
Duk magiyar da ta yi mashi ya kafe a kan lallai shi ba zai dawo ba, ta yi hakuri kawai, daga ƙarshe dai ya bata hakuri tare da kashe wayarsa ya yi switch off ɗinta mai gabaɗaya dan ma kada ta sake kiransa.
A wannan daren dai sai da barci ya kasance ɓarawo ya saci maman Zainab, nan ma har wuraren karfe 2, bakinciki da ɓacin rai ya hanata rintsawa baiwar Allah.
Washegari da safe haka ta farka idanunta a kumbure luhu luhu, saboda kuka da ta sha ga kuma rashin barci, tana farkawa ta fito kuma Hauwa ta ce lallai lallai ita zata yi masu kayan ƙarin kumallo, rai a ɓace ta ce ba zata yi ba, baban Zainab ya ce ta yi ko ranta ya ɓaci.
Danne zuciyarta ta yi ta girka ba dan ta so ba, yau dai su Khadijah basu je school ba, dan basu taho da uniform ɗinsu sabon gidan ba, ga shi yau jumma'a, so basu taho da uniform ɗin da suke amfani da shi ranar Friday ba.
A takaice dai babu daɗi suka yi ƙarin kumallo a gidan, duk wanda ka gani ransa a cunkushe banda Hauwa da take cikin farinciki, ranta fes, sai daɗi take ji tana kuntatawa maman Zainab.
Da misalin karfe ɗaya na rana tana zaune a parlour ita da su Khadija, Zainab tana kallo a Tv, Khadija kuma ta buga uban tagumi kamar yadda mamanta ta yi.
"Mama ina kawu Sadiq ne? Ba zai zo gidan nan bane?". Cewar Zainab.
Wani irin ƙululun bakinciki maman ta ji ya taso mata. "Khadija tashi ki je ɗakina ki ɗauko mun wayata bari na gwada numbersa ko yanzu kam zata shiga, tun safe nake gwadawa bata shiga".
Da to Khadija ta amsa mata.
Bata kai ga miƙewa ba sai ga Hauwa da baban Zainab sun fito. Yana shirye cikin wata haɗaɗɗiyar shadda chocolate color, ya yi kyau sosai, da alama masallacin jumma'a zai je, ita ma Hauwa ta ci kwalliya cikin abaya brown color.
Gaisuwa Khadijah ta ɗagawa baban nata, a takaice ya amsa ba tare da ya bi ta kanta ba ko ya ɗaga idanu ya kalleta ba. Zata wuce cikin kenan ya ce. "Khadija ki shirya Hauwa ta ce lallai yau a ɗaura aurenki da Haidar bayan mun sauko sallar jumma'a, dan haka ki shirya su Maman Haidar zasu zo su ɗaukeki".
Wani irin kuka Khadijan ta fashe da shi mai matuƙar tsuma zuciyar mai sauraro, da gudun gaske ta afka cikin ɗakin maman nata, wani irin jan numfashi da take yi cikin kuka sai ta baka tausayi, kamar zata haɗiyi zuciya. Da gudu Zainab ta tashi ta bi bayanta.
Ita kuwa Hauwa wani irin murmushin mugunta take ta faman saki. Miƙewa tsaye maman Zainab ta yi, cikin wata iriyar murya da ba zaka iya fassara halin da take ciki ba ta furta. "Baban Zainab kada ka yi wannan kuskuren, wlh billahi Haidar ba zai aura mun ƴa ba, kada ka bijiro da abin da zai sanyaka yin danasani, wlh a kan farincikin ƴaƴana na yarda komai ya faru, zan iya barin maka gidanka a kan wannan aure".
Hauwa ce ta ce. "To me laifi dan yarinya ta auri ɗan uwanta na jini? Kyamar dangin nasa kike yi ne? Amma kuma ke kin haɗa jini da shi ko?......"
Cikin ɗaga murya tare da zafin rai haɗi da ɓacin rai maman Zainab ta ce. "Hauwa ban kasa dake ba, a wannan gaɓa idan kika saka mun baki a maganata zan ci uban, wlh wlh wlh idan kika sake saka baki a maganar nan babu uban da ya isa ya dakatar da ni daga sumar dake a cikin gidan nan, sai na yi maki dukan uwar ala tsine, ke sai na yi maki abin da wlh ke da kanki ba zaki iya gane kanki ba, kin san halina bani da full stop idan aka kureni, in dai ba so kike hajiya ta haifi wata Hauwar ba, ki sake saka mun baki shegiya mai kama da kazar mayu".
Juyowa ta yi ta kalli baban Zainab ɗin. "Honey ka tafi masallaci abinka, kada ka dakata kowa, idan an ɗaura auren ka kirani ka sanar da ni". Cewar Hauwa. Ta yi hakan ne kuma dan tana tsoron maman Zainab, tana tson sake yi mata magana, amma tana da bakin yin magana da baban Zainab ɗin kam ai, a ranta kuma ta ƙuduri niyar yau sai an ɗaura auren nan ko dan taga ya maman Zainab zata yi.
Kai Hauwa dai anyi sheɗaniya makirar mace.
Sa kai baban Zainab ɗin ya yi zai wuce ya fita ba tare da ya ce da maman Zee uppan ba, ko kallon in da take ma bai yi ba.
A ɗari maman Zainab ta sha gabansa tana faɗin. "Kada ka haɗa wannan aure, zaka yi danasani".
Wani irin mari ya zabga mata wai dan ta sha gabansa, rai a ɓace ya daka mata tsawa ta bashi hanya ya wuce.
Ɓacin rai iya ɓacin rai yau ranta ya ɓaci, dama ga baƙincikin tafiyar Sadiq, sannan ga bakincikin da ya ƙunsa mata da safe na sanyata ta yi girki da ya yi, ga na jiya da daddare, sai abin ya haɗu ya yi mata yawa, yanzu kuma ga marin da ya dalla mata, sannan ga future yarta da yake ƙoƙarin lalatawa ta hanyar aura mata Haidar, ta ƙuduri niyar ba zata bari hakan ya faru ba!!.
Hauwa dake tsaye a bayansa kaɗan ne ta ce. "Yes honey, wlh ka kyauta da ka mareta, kai sa'arta ne da zata tare maka gaba?".
A wani irin kaunace maman Zainab ta ɗauketa da wani irin wawan mari wadda sai da ta ga wani haske ya gifta a gabanta idanunta, yau ɓacin rai ya rufewa mmn Zee ido. Cakumo wuyar rigarta ta yi da nufin ta yi mata ɗan iskan duka. Baban Zainab bai bari hakan ta faru ba ya fara ƙoƙarin kwatarta, wasa wasa yaga idan bai saka karfi ba ba zai iya kwatarta ba.
Cikin fushi yasa kafa ya kwashe kafafunta sai ga mmn Zee a kasa rigijib, har lokacin kuma bata saki wuyar Hauwar ba, a tare suka yi ƙasar, ta ƙanƙame wuyar tata kamar mage a saman ɗan siririn reshen bishiya da idan ta sake saza faɗo, kunga dole ta ƙanƙame da kyau. To haka maman Zainab ta ƙanƙame wuyar Hauwa!.
Mari baban Zainab ɗin ya sake kai mata, daga karshe ya fara haɗa mata da duka, Hauwar ma ta fara kai mata duka domin ta kwaci kanta, ta ji shaƙa shegiya, ta ji kamshin lahira, dole ta fara kai duka dan ta samu ta tsira da ranta.
Dukan da baban Zainab yake kai mata ne ya yi mata tsananin zafin da yasa ta saki Hauwar, a guje ta miƙe ta nufi kitchen, sabuwar wuƙa ta ɗauko wadda ba'a taɓa amfani da shi ba, dan komai na cikin kitchen ɗin sabbi ne. Da gudun gaske ta yi kansu da wukar faɗi take yi yau ko sama zata haɗu da ƙasa sai ta kashe Hauwa, sai dai duk abin da zai faru ya faru.
Sanin halinta da balai'n bakar zuciya yasa Hauwar ta ruga a guje ta yi ɗakinta. Da mahaukacin gudu ta rufa mata ba, kamar wata mahaukaciya haka maman Zainab ta zame masu, hauka take yi masu kamar wadda take da aljanun kukar buluhi a kanta.
Da gudu baban Zainab ya bi bayansu. Ihu Hauwa ta fara yi tana kewaye ɗakin dan ta ceci rayuwarta, ita kuwa maman Zainab yadda kuka san bata san menene hankali bama yau, binta take yi kawai tana faɗin. "Yau idan kinga baki mutu ba to ni ce nan na mutu, shegiya mugun iri, ina kika ce ke shaiɗaniya ce? To ki tsaya dan ubanki, yau sai dai hajiya ta haifi wata Hauwar!!"
Sai kewaye ɗakin suke yi, a hau gado a sauka, duk maman Zainab sai farfashe abubuwan cikin ɗakin take yi. A haka baban Zainab ya iskosu, da gudu ya yi ƙoƙarin shiga tsakaninsu dan ya rabasu, ai kuwa maman Zainab zata cakawa Hauwa wukar sai ta caka mashi a tsakiyar cikinsa wajen cibiya. Dama da Hauwa taga ya shigo sai ta tsaya a saman gadon, dan tasan zai tare mata, shi ne maman Zainab ta nufota da wukar, zata caka mata shi kuma ya shiga tsakani.
Nan take jininsa ya fara yin wani irin tartsatsi kamar wutar welder, ga wukar ta cakesa har can cikinsa, gabaɗaya kaifin wukar ta lume a cikin nasa. Kan kace me ya zube ƙasa a kan gadon, jini ne yake zuwa kamar an buɗewa ruwa hanya.
Wani irin mahaukacin ihu maman Zainab ɗin ta saki tare da yin kansa tana kiran sunansa, ita kuwa Hauwa waje ta nufa a guje kamar mahaukaciya tana kurma nata ihun.
Da gudu su Khadija suka fito daga ɗakinsu jin irin ihun da mamansu take kurmawa, kai daga jin wannan ihu kasan bana lafiya ba, dan ihu take kurmawa tamkar maƙoshinta zai ɓalle, sai ambatar sunansa take yi.
Gwanin ban tausayi shi kuma sai shure shure yake yi kamar wadda ransa yake fita, ƙafafunsa sai kaɗawa suke yi, ko'ina na jikinsa kakkarwa yake yi, harta gashin kansa sai da suka mimmiƙe tsaye, wani irin zara zaran jijiyo ne suka fito ɓaro ɓaro a hannunsa zuwa ƙafafunsa har gaban goshinsa da kuma wajen wuyarsa, wahala ta fito da su, nan take ya yi wani irin fari kamar ba shi ba, har lokacin jini na feshi kamar wutar welder, haka zalika har lokacin yana ta shure shure, idanunsa sai juyawa sama suke yi, bakin ciki sai ƙoƙarin ɓacewa yake yi, wani irin zufa dake tsastsafo mashi yana wanke ko'ina na jikinsa sai ya baka tausayi, fuskarsa kamar an watsa mashi ruwa, ya jike sharkaf da zufa, kayan jikinsa duk sun jike da zufar azaba!!.
Ai Khadija na leƙowa taga abin da yake faruwa sai ta yi waje da gudu domin ta kira mutane su zo su taimaka masu kada babansu ya mutu, ita kuwa Zainab ta yi kansa da gudu tana ihu, Hauwa kuma sai Allah kaɗai yasan in da ta nufa...... Tashin sense!!! Akwai matsala fa my people's😥💔
Shin baban Zainab zai mutu ko zai rayu? Ina Hauwa tsohuwar makira? Ya makomar maman Zainab?.
Zuciyata ba zata iya jurar ganin tashin hankalin da waɗan nan ahalin suke ciki ba, bari dai na leƙa Dubai muga me yake faruwa a can, my people's yanzu littafin RAWANIN ZALINCI zai fara ɗaukar 🔥 dan yafi karfin ɗaukar zafi sai dai wuta, mun dai kusa isa ga RAWANIN ZALINCI da gaske!.
Second to the last page of book 1 my people's. 💘🔥
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍