Free chapter · Read without an account
55
🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡
❤️🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)
🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻
❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 14/9/2024.....✍️📚🌹
For more information *** Whatsapp me only!!.
🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
E____________52🔥
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🕊️🌼🕊️
ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥
A karo na biyu ma wahala Leesharh ta sha sosai wajen neman mai kai abinci, sai dai kuma bata ci nasara ba har yanzu, sake dawowa cikin ɗakinta ta yi, a bakin gado ta zauna, uban tagumi ta buga tana tunanin mafita, mahaifinta ne kawai a ranta, shi kaɗai take tunawa, ta ci burin yau ta yi magana da shi.
Sallamar Sharifat a cikin room ɗin ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka. Da kallo ta bita, ta kasa iya amsa mata sallamar, dan hankalinta baya a jikinta, duk ta yi la'asar.
Kusa da ita Sharifat ta zauna, cikin sanyin murya ta ce. "Leesharh Yah Guyson ya gaya mun kin yi kuka a kan wani abin ya shiga maki cikin ido ko?".
Kai ta gyaɗa mata alamar e haka ne. "Eyya sorry, amma kuma dan wani abin ya shiga cikin idanun ki hakan doesn't mean sakacin masu aiki ne, i told Yah Guyson kada ya ce laifinsu ne, kada a hukuntasu, be cause yau rana ce ta taro, baki dayawa sun zo, a wajen shige da fice ma za'a iya samin kwari ai".
Da sauri ta amsa mata da. "Yauwa Sharifat, even me abin da na gani kenan, please ki rarrasheshi kada ya ce za'a hukunta masu aikin nan, please ya yafe masu".
"Leesharh tell me the truth, what's wrong with you? I already saw many problems in your eyes, so please feel free and tell me!".
Tsuru tsuru ta yi da idanu, yanzu me zata ce da Sharifat? Ta tambayi kanta da kanta.
"Leesharh from which country you came here?". Ta sake jefa mata tambaya, Sharifat tana zargin ko Leesharh tana kewar iyayenta ne yasa take shiga damuwa haka, kamar dai yadda Guyson ya yi hasashe ɗazun, suna ganin yarintarta sosai, suna ganin bata kai a rabata da iyayenta ba, shiyasa suke yawan tambayarta ko tana kewar iyayenta ne, basu ma san ita Leesharh ai ta jima rabonta da iyayenta ba, idan da sabo yanzu ta saba da kaɗaicinsu.
"Am from Nigeria". Ta bata amsa a takaice, ta yi maganar kuma kanta na'a ƙasa tana kallon ƴatsun hannunta. "Do you mean Nigeria African?". Ta faɗa tana zaro idanu alamar mamaki.
Kai ta gyaɗa mata alamar tabbatarwa daga Nigeria take. "From Nigeria you came here because of work? Kai dole ki yi missing na parents naki, dole ki shiga damuwa, but why your parents zasu yarda su barki ki zo nan aiki? Su ba zasu ji kewarki bane? And su basu ga akwai nisa bane?". Tana maganar still mamaki ne sosai a saman face ɗinta.
Shiru ta ɗan yi mata, kamar zata fashe da kuka take ji, zuciyarta na yi mata zafi, Sharifat ta taɓo mata in da yake yi mata kaikayi, ta tuna mata da iyayenta, duk sai ta ji wani irin.
"Sorry ko Leesharh, dole ki rinƙa kuka na kewar parents ɗinki, in saya maki waya ki rinƙa magana da su dan ki rage damuwa da kewa?".
Sai a lokacin ta zaro nata idanunta da suka girmewa na Sharifat a girma, idan ta zarosu kamar ka ruga a guje. Ko me ta tuna sai kuma ta ɗan yi ƙasa da kai.
"Leesharh meyasameki kuma? Is there any problem again?".
Kai ta girgiza alama a'a babu komai. "Leesharh talk to me now! should I buy phone for you? Saboda ki rinƙa kiran parents ɗinki, I don't want to see you always crying and worried".
A takaice Leesharh ta ce mata. "I don't have anyone in my life, I don't have a mother and i don't have a father, they're not alive, they're all dead". Ta faɗa kamar zata yi kuka, kuma ta gaya mata hakan domin Sharifat ɗin ta rabu da ita da zancen saya mata wayar nan, kada ta zo ta saya mata waya hakan ya zame wa babanta babbar baraza, dan masu nikaf basu bata damar yin amfani da wata waya ba bayan wanda suka bata, shi ma kunji sun gargaɗeta a kan kada ta kuskura ta kira kowa da shi, so hakan yasa ta ce bata da har da uba, ni da ku mun san iya mamanta ce kawai bata raye, amma ta haɗa harda babanta dan tsira daga wajen Sharifat kada ta saya mata waya. Tasan cewa duk abin da zata aikata a kan mahaifinta masu nikaf zasu ɗauki fansa, idan ta yi kuskure babanta ne zai ji a jikinsa! Hakan yasa take taka tsantsan sosai!.
Wani irin mugun tausayinta ne ya kama Sharifat ɗin na jin cewa bata da iyaye, Allah sarki duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, ji ta yi zata yi ƙoƙari ta ɗauketa kamar yar uwarta dan ta rage mata raɗaɗin rashin iyaye, da yake ita da Guyson akwaisu da zuciyar zinari na tausayi sosai, ga hakuri kamar damo, basu da faɗa kuma basu son hayaniya, kowa ya zauna da su sai ya ji yana tsananin kaunarsu, saboda kyawawan halayensu.
Ɗan matsowa ta yi ta rungumeta tana yi mata sannu a kan rashin iyaye. "As from today i am your sister kin ji? Sorry ko?". Ta faɗa tana mai kara jin tausayinta sosai.
Ita ma Leesharh ɗin duk jikinta ya yi sanyi, tana jin kaunar Sharifat ɗin tamkar ƴar uwarta na jini, saboda kauna da ta nuna ma, duk sai ta ji bai kamata ace ta yi abu komai ƙanƙantarsa dan ta cutar da bayin Allah nan ba, ita tama rasa a wani matsayi zata ajiye Sharifat da Guyson, babu ruwansu da girman kai, mahaifinsu yana da murya mai karfin faɗa aji kuma dole ayi abin da ya ce a faɗin ƙasar, ga ɗimbin dukiya da shi kansa bai san adadinsu, ga matsayi a siyasance, sannan ga matsayi a sarauce, ga tarin masu kaki kala kala a ƙarƙashinsa, duk wata kaki a faɗin ƙasar bata isa ta motsa ba ba tare da izininsa ba, karfin iko gare shi ba kaɗan ba, amma su Sharifat duk basu ɗauki hakan a bakin komai ba, abin duniya bata damesu ba, basu ɗaurawa kansu girman kai ba, Guyson kam ma ai shi ta ko'ina ma jinin mulki ne yake gudana a jikinsa, ta sama da ta ƙasa, amma babu ruwansa da girman kai ko kyamar talaka, yana son kowa da zuciya ɗaya.
A can wajen walima kuwa. Tun da suka je wajen Guyson yake ta ƙoƙarin dannar twins Obaid and Omaid, shi Omaid ma ya hakura ya barwa cikinsa abin da yake tunani dan gane da Leesharh, dama shi kun san ya iya takunsa. Obaid kuwa sarkin bakar zuciya, sai cika yake yana batsewa, shi lallai lallai dole sai Guyson ya yarda Leesharh criminal ce, har da wani cewa su basa hasashen abu kuma ya zama karya. Shi kuma Guyson ya ce sam ba zai yarda a kan ita mai laifi bace kuma abin zargi, saboda shi baiga laifin da ta yi masu ba, kuma shi ba zai yarda ya zargeta ba, ya kafe masu a kan lallai ita ɗin mai gaskiya ce, sune kawai basu sonta.
Tun da suka shigo wajen yayyun nasu suke yi masu kallon tuhuma except Abu Abdussalam da ya buƙaci su zo kusa da shi su zauna ya yi kewarsu, Abu Abdussalam yana bala'in kaunar Momma da King Zuhair, shiyasa yake kaunar ƴaƴan nasu.
Kusa da shi suka zauna cikin manya manyan ministoci da ƴan majalisu, Guyson yana ta gefen damansa, su kuma ta gefen hagu suka zauna, basu taɓa raba wajen zama, duk in da ka gansu a tare suke, kai su basu raba komai ma ba wajen zama kawai ba, in dai ba zaka basu abu a tare ba gara ma ka barshi, dan ɗaya ba zai karɓa ya bar ɗaya ba.
Abbie ne ya ce. "Guyson where's Ramish?" Ya yi maganar cikin kwararriyar laraɓcinsa, yare biyu Abu Abdussalam yake ji a duniya, daga turanci sai larabci.
Cikin sanyin murya haɗe da nutsuwa ya ce. "Abbie wai kansa na yi mashi ciwo, he can't come here, dan kara mashi ciwon kai za'ayi da surutu, so ya kwanta".
Kallon Bilal Abbie ya yi. "Jeka duba mun shi, Dr Raj ka kula da lafiyarsa sosai".
Da okey suka amsa mashi kafin su miƙe su nufi hanyar fita. Tun da suka miƙe maza da mata kallonsu suke yi, ba dai haɗuwa ba kam, sun fito ba'a magana, kyau iya kyau. Shi kuwa Rizwan ya kafa kansa a kan waya yana chatting da Chuchu, sai zuba mata kalaman soyayya yake yi, ita kuma sai narke mashi take yi!.
Bayan anci an sha, kowa yasan da cewa lallai yau Abu Abdussalam empire ya zo, biki aka yi na girma da girmamawa, rakuma har biyar ma'aikata suka gasa, nama kamar hauka, da nama na magana yau da ya yi a gidan Abu Abdussalam, drinks da ruwa suma da sai sun yi magana, abinci kala kala, a yau ba wata ma'aikaciya ko ma'aikacin masu yin girki waɗan da basu ji a jikinsu ba, yau sun sha aiki sun kuma wahala, jiki duk ya yi tsami.
Rera karatun Alkur'ani mai girma manyan baki suka fara yi, kun san fa larabawa akwai iya rera ƙira'a, Abu Abdussalam ne ya buƙaci da a yi karatu sosai kafin a tashi daga taron. Duk wanda zai yi karatu saman stage yake hawa, abin ya yi tsari sosai ya kuma bada ma'ana, sannan ya ƙayatar matuƙa.
Lokacin da Guyson ya fara rera kira'arsa sai da gabaɗaya jama'ar cikin hall ɗin suka bar abin da suke yi suka zuba mashi idanu, tsantsar madarar kyau suke gani, ga zakin murya kamar me, karatu yake rerawa cikin kwanciyar hankali cikin suratul Yusuf, yadda yake fitar da kowani baki, kowani gunna sala sala yake fitar da ita, baya mance wasali ko yaya, dai'dai yake zayyanosu ga nutsuwa matuƙa a tattare da shi sai ya tafi da imaninka, dama ga yaran Momma da bala'in farin jini kamar su suka bawa kansu.
Wasu kyan da Allah ya yi mashi suke gani, wasu kuma kyakkyawan arab hairnsa suke gani, dan fa kunsan gwani ne wajen iya gyaran gashi, ga shi ɗan wanka, wasu daga cikinsu kuma wankarsa suke kallo, wasu zazzaƙar voice ɗinsa ne ya tafi da imaninsa, wasu kuma yadda yake rera karatun cikin nutsuwa ne ya tafi da imaninsu, yaro mai farinjini, dayawa daga cikin manyan bakin nan sun kwaɗaitu da son samu ɗa kamar sa, ji suke yi dama ace ɗansu ne.
A hankali zazzaƙar muryarsa ta fara rikiɗewa daga yadda ya faro karatun cikin zaki da nutsuwa zuwa muryar mai kuka, da kaɗan da kaɗan fararen idanunsa suka fara rikiɗewa izuwa ja saboda kukan, siraran hawaye ne suka fara bin kyakkyawar farar kumarunsa, ba komai ya ja hakan ba kuma face sanin fassarar surar da yake karantawa da ya yi, zuciyarsa tana kara jinjinawa girman Allah, jikinsa har tsuma yake yi yana kerma a lokacin da yake karanta gudurorin Ubangiji da ya yi ta yi wa annabi Yusuf. Kukansa kara tsananta ya yi lokacin da ya zo in da aka raba annabi Yusuf da mahaifinsa, sanin fasarar surar tasa shi kuka sosai da yake karantota.
Guyson bai kai 17 years ba a duniya, amma Allah ya bashi baiwa ta ilimi fiye da tunaninku, ba boko ba ba Arabic ba, dukka akwai tarin ilimin a kansa, shiyasa yake da saukin kai sosai, saboda ya san girman Allah sosai, yasan duniya ba'a bakin komai take ba, a wajen Allah duniya kamar wuni guda ce. A ƴan shekarun nan nasa ya san farrasarar rabi da kwana na surorin dake cikin Alqur'ani mai girma, kun san larabawa fa ba baya ba wajen iya karatu, basu wasa. A bangaren littafan addini ɗan tahaliƙin nan ba'a magana, yasan dayawa daga ciki, ya haddace dayawa, kuma har yanzu bincike yake cigaba da yi yana kara nutsawa cikin karatun addini, yana ta ƙoƙarin ya haddace fasarar Alqur'ani gabaɗaya, ɓangaren bokon ma baya wasa, yanzu kunga ya kammala secondarynsa, jam zai rubuta kai tsaye ya shiga babban makaranta da kananun shekarunsa, shiyasa ƴan uwansa dukka suke sonsa, saboda jajircewarsa wajen neman ilimi.
Su Omaid kuwa, akwai tarin ilimin suma, amma sai shegen shakiyanci, iyashege, da tarin rashin ji, ga ɗan banzan shiga rai garesu kamar me, ga farin jini kamar su suka yi wa kansu, amma duk da hakan baya hanasu karatu, duk iskancin da suke yi basa wasa da karatu, dan idan suka kuskura suka yi wasa wlh zasu kwashi kashinsu a hannun idan su Ramish suka riƙe su, shiyasa kome zasu yi banda wasa da karatu kam. Kai in takaice maku labari gabaɗaya jinin King Zuhair babu jahili, sai dai ilimin wani ya fi na wani, wani ya fi wani kaifin basira, ga tafasasshen jini, dagiya da kafiya, jarumta da jajircewa, babu jahili sam sam! Suna da dagiya wajen neman ilimin boko dana addini basa wasa!.
Kukan Guyson a cikin hall ɗin nan yasa dayawan mutane kuka, masu raunin zuciya sun taya shi kuka, shi kansa Abu Abdussalam sai da idanunsa suka ɗan yi ja.
Kasancewar a nutse yake karatun sai ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya kammala. Yana kammalawa Abbien nasu ya miƙe ya rungumo shi tare da fara goge mashi hawaye, kabbara jama'a suka fara yi suna zuba mashi ruwan albarka sosai da sosai.
Omaid ne ya miƙe ya fara rera nasa kira'ar cikin suratul ma'ida, dama kun san su sarakan shiga rai ne, ga farinjini, nan take jama'a suka fara binsa dana mujiya, sai santin kyansa da muryarsa kusan irin na Guyson suke yi. Shi kam Omaid saboda dakiya da taurin zuciya ko ɗigon hawaye babu a idonsa, sarai kuma yasan fassarar surar da yake karantawar, amma akwai taurin zuciya, ko alamar hawaye ma babu a idanunsa, idanun suna bushe karau yake rera karatunsa har ya kammala, har lokacin kuma Abu Abdussalam bai saki Guyson ba, yana bala'in kaunarsa, duk da sun koma sun zauna yana ƙanƙame da hannunsa suna sauraron kira'ar Omaid ɗin. Bayan ya kammala Obaid ma ya miƙe ya fara rero nasa cikin suratul Maryam.
A wannan gaɓar ma sai da Guyson ya yi hawaye, saboda yasan fassararta, sosai kuma ya kara jin tsoron Allah matuƙa, sai goge mashi hawaye Abu Abdussalam yake yi. Shi kuwa Obaid da ya karanta surar ma idanunsa a bushe karau, Guyson sai sharar kwallah yake yi shi da ba shi yake karatun ba, mai karatun kuwa idanu a bushe karau, ga gashin idanun nasa zara zara a tsaitsaye na rashin kunya da rashin jin magana, kowa ya ga idanun Obaid da Omaid ya san akwai tarin rashin tsoro da rashin kunya game da mugunta a cikinsu, basu tsoron a mutu.
Bayan Obaid ya kammala karatun ne ƴaƴan manyan baki suka fara rero nasu.
A can cikin gida kuwa, Leesharh ta saki jiki sosai suna ta hira da Sharifat.
"Leesharh anata gudanar da abubuwa a wajen walima ni kuma ina nan a tare da ke, ki tashi mu je can mana? Kin ga ai sai mu yi hira a can ko?". Cewar Sharifat.
Make mata kafaɗa ta yi. "A'a Aunty Sharifat ni bana son zuwa, ban son shiga cikin mutane sosai, ki barni a nan kawai".
Gyara zama ta yi. "To shikenan Leesharh mu zauna tare a nan ɗin kawai ko? Mu cigaba da hirarmu ni ma na fasa zuwa duk da nasan Yah Guyson zai damu idan bai ganni ba".
Da sauri ta girgiza mata kai tana faɗin. "A'a Aunty Sharifat, kada ki sa ya ji babu daɗi, idan kin san zasu damu da rashinki a wajen kawai ki tafi".
Gyarawa ta yi ta kwanta a saman gadon tare da miƙe kafafunta. "Kawai mu cigaba da yin hirarmu Leesharh ba zasu damu ba, ai na gayawa Yah Guyson bari na je wajen ki tun lokacin da ya gaya mun kin yi kuka".
Okey ta amsa mata da shi haka suka cigaba da yin hirar duniya cikin nishaɗi abinsu.
Sun shagala da hirar duniya mai daɗi Sharifat ta dubi ɗan siririn diamond watch dake manne a hannunta. "Kai Leesharh karfe 7 ta yi bamu yi sallar mangariba ba! Sannan karfe 7: 30 dai'dai zan kaiwa Yah Ramish abincinsa da cappuccino, kin san shi bai yarda da kowa ba, bai yarda da ƴan aikin gidan nan ba, abincin da zai ci ma wanda yake girka mashi na musamman ne, bai yarda wata ko wani mai aiki ya keto cikin ɗakinsa ya kawo mashi abinci ba, garama idan da rana ne yana zaune a babban parlourn haka zai iya cewa a kawo mashi, nan ma sai idan yasan na tafi school ko bana kusa ne zai yarda wata ta kawo mashi abinci, duk wata ƴar aiki da kika gani a cikin gidan nan sai da Abbie ya aminta da ita kafin ta fara aiki, amma shi ya Ramish bai aminta da kowa ba sai ni da su Yah Rizwan, ke ni ina ganin ma kamar Ummie ma bai yarda da ita ba fa, dan naga baya wani sakin jiki da ita kamar yadda su Yah Rizwan suke yi".
Shiru Leesharh ta yi tana sauraron tun da ta fara maganar, wani irin sanyi ta ji yana ratsa mata zuciya, tsuntsu daga sama gasasshe! Ta sha wahala wajen neman mai kai mashi abinci cikin room ɗinsa, ashe dai tana tare da ita bata sani ba, wannan shi ne tsuntsu daga sama gasashe! Sosai abin ya yi mata mugun daɗi, har wani sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke.
"Leesharh tunanin me kike yi?". Ta yi maganar tare da ɗan taɓata. Ƴar razana ta yi tare da cewa. "Babu komai, amma meyasa Yah Ramish ɗin baya yarda da kowa?".
"Saboda ya ce yana da tarin makiya, kuma fa na gaya maki dukka masu aikin gidan nan daga maza har matansu amintattu ne, shi ne dai kawai bai aminta da su ɗin ba".
Shiru Leesharh ta yi tana jinjinawa kaifin ƙwaƙwalwarsa, yana da gaskiya, su suke ganin kamar dukka ma'aikatan gidan amintattu ne, shi da ya san da cewa ɗan adam yanzu ba a abin yarda bane, ya san kan duniya ai ga shi bai yarda da su ɗin ba, ita kanta Leesharh ai kunga ba amintatciya bace, ƴar leken asiri ce, ƴar ɓadda kama!.
Miƙewa Sharifat ta yi. "Bari na ɗauro alwala Leesharh, kema ki tashi lokacin sallah ya yi, ki yi sallah mu je ki rakani wajen Yah Ramish mu kai masa abinci, idan mun je sai ki jirani a kofar shiga part ɗinsu, dan idan kika shiga na shiga uku na, ba kowa yasan in da part ɗinsu yake ba a cikin gidan nan, kuma Yah Ramish baya son wata ma'aikaciya ta zo arear part ɗinsu, wai kyamar ƴan aikin yake ji, idan sun zo in da yake zai yi amai, so sai ki jirani a waje".
Sharifat baki abin magana, ta aminta da Leesharh ta saki baki sai gaya mata sirrin gidan take yi, bata san cewa Leesharh dai green snake under green grass bace, ƴar ɓadda kama kuma ƴar basaja. Rashin sani bai yi ba a rayuwar nan.
Okey ta amsa mata da shi, nan take ta ji kwarin jikinta ya dawo, wani irin daɗi ta ji ya kamata, duk yadda zata yi ta zuba mashi maganin nan yau sai ta yi, dole ta san yadda zata yi ta shammaci Sharifat ta aiwatar da aikinta.
Waje Sharifat ɗin ta nufa, ita kuma Leesharh ta nufi cikin toilet, alwala ta ɗauro tare da zuwa ta shimfiɗa dadduma ta tada sallah, bayan ta idar ta sanya hannu ta taɓa aljihun wandanta dan ta tabbatar maganin yana ciki.
Jin cewa yana ciki yasa ta saki cool murmushin da bata san lokacin da ya fito ba, faɗi take yi a cikin ranta shikenan da ta zuba mashi maganin nan masu nikaf zasu haɗata da babanta ta yi magana, yau tsawon shekara kusan biyu bata ji muryarsa ba, tana kewarsa sosai, tun lokacin da aka kaita prison ta kashe mamanta, tun ma kafin lokacin take kewar muryarsa, sun ɗan kwana biyu basu a tare, shiyasa take ɗaukin jin muryarsa, take begen hakan.
Sallamar Sharifat a cikin ɗakin yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka. Ɗago idanun nan nata ta yi tare da saukesu a kanta, rike take da katon luxurious tray, shake yake da kulolin abinci masu bala'in kyau da tsada, ga cup dake shake da cappuccino, sannan ga cup na coffee mai zafi a gefe, duk suna rufe da ƴan ƙananan plate na set ɗin cup's ɗin. Sai sauran snacks dake saman wani luxurious plate.
Zubawa trayn idanu ta yi tana kallonsa sosai, ayyana yadda zata zuba mashi maganin a ciki kawai take yi. Muryar Sharifat ɗin ce ya katseta da cewa. "Let's go Leesharh".
Miƙewa ta yi suka jera a tare.
Allah sarki tausayin maraicin Leesharh da Sharifat take yi yasa zata tabka kuskure ba tare da sanin ta ba, burinta ta ja Leesharh ɗin a jiki ta yadda zasu saba sosai, duk dan ta mantar da ita damuwar da take ciki na rashin iyayenta, tana son su saba sosai su zama kamar ƴan uwa, shi ne harda gayyatota ta rakata wajen ƴan uwanta. Hmmm bata san aiki dama ta zo yi a kansu ba, rashin sani ya fi dare duhu.
A tare suka tafi, cikin dabara Leesharh ta ciwo maganin daga aljihunta, ko tsoro bata ji ba, kamar mai son gyara zip ɗin wandonta haka ta yi ta buɗe ɗan gwalbar ganin. Sai da suka shiga wajen wannan ɗan hanya in da ta yi karo da mai aikin ɗazun ɗin nan, kun san wajen akwai ɗan duhu. Saboda jajircewa da karfin hali haɗe da ƙoƙari irin nata, ga taurin zuciya da rashin tsoro, cikin dabara ta kai hannu ta bude plate ɗin cappuccino ba tare da Sharifat ta jita ba, sai hira Sharifat ɗin take zuba mata, tana bata labarin kyan Yah Ramish ɗin.
A hanzarce ta zuba maganin kaɗan a ciki, ta sake zubawa a cikin coffee ɗin ma kaɗan sabosa ƙoƙari irin nata. Tana yi kirjinta na dukan tara tara, ita kuma Sharifat sai surutu take zubawa suna tafiya a hankali cikin natsuwa, saboda girman tray ɗin yasa bata ji an taɓa komai ba.
Kaɗan kaɗan ta zuba maganin kamar yadda suka umarceta, ta yi maza ta dunƙule kwalbar a hannunta kasancewar sun fito wajen haske. Fargaba da faɗuwar gaba ne ya kusa kasheta, zuciyarta sai bugawa da karfi karfi yake yi, da kyar ta haɗiyi yawun wahala, wani irin jan numfashi da ta yi har sai da tasa Sharifat ɗin ta ɗan ci birki tare da tambayarta lafiya kuwa?.
Cikin dakiya ta ce babu komai su je kawai, duk a ruɗe take, gabanta na faɗuwa, sai karanto addu'oi take yi dan ta ji sassauci a cikin zuciyarta...... Kai Leesharh ba dai karfin hali da dakiya haɗe da taurin zuciya ba, kai irin wannan ɗanyen aiki haka? Ko tsoron asirinta ya tonu bata ji yarinyar nan, idan ta sa kanta zata yi abu, to fa sai ta yi. Ashe ba'a banza masu nikaf suka ɗaukota ba, ashe sun san wa suka ɗauko, yo dama Allah na tuba mu jinin ƴan Nigeria ai fin haka ma zamu aikata ba tare da tsoro ko shakka ba, ai mu karfin halinmu tare da jajircewa a jininmu yake, dan haka kada ku yi mamakin idan Leesharh ta aikata fin haka, yauwa jininmu a tafashe yake, babu abin da baza'a samu a Nigeriarmu ba, mu ai ba'a isa a mana gorin komai ba ato...........🥱
(Jinjina gareki Leesharh jikar baba bola Ahmad tinunbu🥱 kina da karfin hali irin na jikokin tinunbu,🔥 kin ci lambar ya bo, dole villa ta san da zamanki, irinki ake turawa aikin soja🥱)
Cigaba da tafiya suka yi. Sun ɗanyi tafiya mai nisa kafin su kai bakin haɗaɗɗen katafaren part ɗin nasu.
"Leesharh ki jirani a nan ina zuwa". Ta faɗa tare da nufar cikin part ɗin. Ita kuma Leesharh ta tsaya a bakin stair case da ya yi ƙasa.
Shiru ta yi tana tunanin me zai faru idan bawan Allah Ramish ya sha wannan maganin?. Tana son buɗe hannunta ta kalli maganin, amma tana tsoron yin hakan, dan tana zargin wajen da take ɗin da akwai camera. A hankali ta fara jiyo takun sahun mutun yana haurowa saman stair case ɗin, kuma daga jin wannan taku kasan bana ƙananan yara bane. Wani irin tsoro ne ya kamata wanda yasa ta watsa a guje ta bar wajen, kai tsaye hanyar da suka bi suka zo ta nufa.
Ita kuwa Sharifat ta kaiwa yayan nata cikin parlournsa, yana zaune saman sofa, jikinsa na sanye da hoodie mai bala'in tsada launin milk color, ya sanya hular rigar a kansa, kasancewar hular rigar ta gaba akwai gashi gashi kamar jikin mage, hakan yasa ba'a ganin face ɗinsa da kyau, ya yi matuƙar kyau sosai a cikin kayan, sai dai kayan kusan kalar fatarsa ce. Kyawawan fararen ƙafafunsa na'a saman haɗaɗɗen carpet ɗin tsakiyar parlourn mai bala'in laushi, ya mike kafafun yana latsa waya, da alama shirin fita ya yi abincinsa kawai yake jira.
A gabansa saman center table ta ɗaura tray ɗin, cikin girmamawa ta ce "Yah Ramish ga abincin nan".
Ajiye wayar ya yi a gefensa, ba tare da ɓata lokaci ba ya kai hannu ya ɗauki cup ɗin cappuccino ya fara sha. Ita kuma Sharifat ta zauna a gefensa saman sofan da yake ɗin tana faɗin. "Yah Ramish fita zaka yi ne?". Da alama ta mance da cewa ta ajiye Leesharh a bakin kofa tana jiranta.
Kai kawai ya gyaɗa mata alamar e fita zai yi ba tare da ya yi magana ba. Cikin nutsuwa ya fara shan cappuccino. Ita kuma ta mayar da hankalinta kan Tv dake magana.
Tas ya shanye cappuccino kafin ya miƙe ya nufi cikin master room ɗinsa. Dawo da kallonta kansa ta yi tana son ta tambayesa ba zai ci abincin bane? Sai dai kafin ta tambayesa ya wuce cikin ɗakinsa.
Jiransa ta yi har sai da ya fito sanye da haɗaɗɗun takalma a ƙafafunsa, wayarsa ya zo ya ɗauka. "Ki barmun abincin a nan sai na dawo zan ci". Ya faɗa a sanyaye tare da nufar waje da sauri.
Kafin ta amsa mashi da okey ma ya fice. Sai lokacin ta tuna da cewa Leesharh na waje ga kuma Ramish zai fito, da sauri ta miƙe ta bi bayansa, dama dayawan lokuta idan ta kawo mashi abinci yin zamanta take yi a part ɗinsa, wani lokaci ma har barci ya ɗauketa, idan da daddare ne ta yi mashi barci a ɗaki sai lokacin da ya gama abin da yake yi sai ya mayar da ita room nata, idan su Bilal sun shigo kuma sai ya ce su mayar da ita. Magana ta gaskiya Sharifat tana son Ramish sosai, shi take burin aura, sai dai shi bai san da hakan ba, kuma babu hakan a gabansa, ita kuma ta kwallafa rai a kansa sosai, shiyasa take son zuwa in da yake, idan tana wajensa mantawa take yi da kowa da komai........,....... Lallai kuwa Sharifat tana kwale kwale, amma kuma idan ta ce shi take so anya zai iya yi wa Abu Abdussalam musu kuwa?🤔 Amma kuma ina tausayawa Sharifat gaskiya, dan son wanda baya sonta take yi, wanda ma bata isheshi kallo ba, kai suma dai da nasu cakwakiyar kunji my people's, mu fita harkarsu, kowa ma da nashi cakwakiyar a littafin nan, yanzu kuma kowa zai fara buga wasansa iya wasa, yanzu game zai fara, zamu ga winners, idan kun ji ana cewa tseren mutuwa to wannan cakwakiyar na cikin littafin nan ne, yanzu dai zamu afka cikin ainahin labarinmu da kuma cakwakiyoyinmu kala kala.
A ɓangaren Leesharh kuwa, tana watsawa a guje ta nufi hanyar koma ɗakinta. Dai'dai zata fita cikin wannan ɗan siririn hanya mai ɗan duhun suka ci karo da mutun, hakan yasa kwalbar maganin hannunta ya faɗi ƙasa ya fashe. Wani irin baya baya ta yi tana ƙoƙarin faɗuwa.
Da kyar ta iya riƙe kanta ta tsaya, goshinta ya bugu da nashi ne sosai. Kirjinta kara tsananta bugu ya yi saboda tsoro da tunanin da waye ta yi karo? Ga kwalbar maganin ya faɗi ya fashe, shikenan asirinta ya gama tonuwa, yanzu idan aka ga maganin kuma idan wani abin ya sami Ramish kashinta ya bushe!.
Shi kuwa Obaid da farko ya ɗauka da Sharifat ce suka yi karon shiyasa bai yi saurin dalla mata mari ba, sai da ta ɗan ja baya ya gane ba Sharifat bace, cikin fusata ya matso tare da sharara mata wani gigitattacen mari a karo na biyu wanda ya sanyata dai'na gane komai.
Wani irin azaba ya ji a ƙafarsa lokacin da ya matsa kusa ya mareta, ba komai ne yasa hanan ba kuma face taka kwalbar maganin da ya fashe ya yi, ƙafafunsa suna da laushi sosai, hakan yasa kwalbar ta yi saurin fasa mashi namar cikin tafin kafar tasa ta shige ciki. A hanzarce ya kai kallonsa kasa kan...............
To fa akwai cakwakiya, Ramish ya sha maganin nan! Ko maganin menene? Ga Obaid kuma ya kara dallawa Leesharh mari a karo na biyu! Da alama asirin Leesharh zai tonu! Dama kunsan Obaid yana zarginta, ya kuma kafe lallai lallai ita mai laifi ce abar zarga, ga kwalbar maganin ya faɗi ya fashe, bugu da ƙari ya fasa mashi kafa, akwai cakwakiya ba kaɗan ba, dama da Guyson suka ci karo ne, to da da sauki, amma Obaid fa, tab Leesharh kina ruwa wlh, sai dai muce Allah ya ceceki!..
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
FOREST🏞️ 🔥
Zaune Pretty take a cikin Raminsu tana daddaka ganye da wannan farar abin mai kama da lu'ulu'u nasu da suke daka, ita kuma Sweetie tana kan gado ta yi shiru tana tunanin Kamran.
Wani irin sauti Pretty ta ji ta bayanta yana fita suuuuu, sirrrrrrrr haka, da sauri ta juyo domin taga menene?. Ai kuwa tana juyawa suka yi ido huɗu da wani murtukeken kumurcin maciji bakin kirin da shi kwance a kusa da dutsen da Kamran yake zama idan ya zo. Macijin yana da girma sosai da sosai, ga shi bakin kirin.
Wani irin ihu ta kurma tare da miƙewa tsaye. Ihu da ta yi yasa macijin girgiza jikinsa ya kuma miƙe daga kwanciyar da ya yi, sannan ya yi wani irin kananannaɗa kamar ba lafiya ba, wannan maciji kamar ba maciji ba.
A guje ta miƙe tare da rugawa wajen ƴar uwarta, hannunta ta riƙo tana faɗin. "Tashi mugudu Sweetie, mun shiga uku maciji a ɗakinmu". Da karfi ta yi maganar cikin ihu.
Ai a dubu ita ma Sweetien ta miƙe, hannunta Pretty ta riƙe gam suka nufi waje da gudu. Ai kuwa macijin yana ganinsu ya rufa masu baya.
Da gudun gaske suka fito cikin ramin, sai jan hannun Sweetien take yi, baiwar Allah bata iya ganin komai sai yadda aka yi da ita. Gudu suke yi basu san ina suka nufa ba, shi kuma macijin da kyar ya fito daga cikin ramin, saboda hawace tana yi masu wahala, ko da ya fito babu alamarsu a arear, habawa Pretty sarkin tsoro tuni ya ja Sweetien suka bar arear wajen. Waige waige snake ɗin ya fara yi kamar yadda macizai suke yi idan suka bi mutun ko idan zasu yi mugunta. Ya fasa kai tare da ɗago kan yana nemansu.
Ganin babu alamarsu a wajen ne yasa ya kwantar da kansa ƙasa ya fara bin cikin ciyayi suuuuuuuu ya tafi.
Su kuwa gudu suke yi babu kakkautawa, basu fa san ina suka dosa ba bayin Allah, sai fincikar Sweetie pretty take yi suna tiƙar uban gudu.
Basu fargaba sai ganin wata bakar damisa suka yi a gabansu. Wani irin birki Pretty ta ja har sai da Sweetien ta kusa faɗuwa, a hankali ta fara ja da baya da baya. Suna ta zuba uban haki Sweetie ta tambayeta lafiya suka tsaya?.
Ƙasa iya yin magana ta yi, dara daran idanunta na'a kan hakwaran wannan damisa da yake ta faman buɗe baki. Ai bata san lokacin da ta saki fitsari a jikinta ba, zuuu fitsarin ya ganganro ƙasa, tana son ta yi kuka, amma ta rasa ina kukan nata ma ya tafi, wani irin kakkarwa jikinta ya fara yi kamar wadda sanyi ya kama, ji take yi shikenan yau kwananta ya kare.
Sai yau ta tuna da addu'ar da mun ɗinsu ta koya masu na idan sunga miyagu zasu cutar da su, sai dai ta ƙasa iya furta addu'ar ma. Sambatun Sweetie na tambayarta lafiya ne ya dawo da ita cikin hayyacinta.
Kuka ta fashe da shi mai tsananin sauti tare da cewa. "Sweetie mun mutu yau, damusa ce a gabanmu, baki ji gurnaninta ba? Mun mutu yau kam!". Tana kai karshen maganar ta kara sautin kukan nata.
Sweetie na ƙoƙarin yin magana kirjinta na dukan uku uku duk da ita bata kalli damisar ba, bata san ya take ba, amma ta tsorata, tana ƙoƙarin tambayarta damisar Kamran ne wato Rocky. Bata kai ga yin maganar ba damisar ta daka wani uban tsalle ta haykewa Sweetien wanda hakan yasa ta zube ƙasa hannunta dana Prettyn ya rabu, Prettyn ta saketa dan dole ta faɗi ƙasa a gefensu ita ma.
Ƙoƙarin capko wuyar Sweetien damisar ta yi, baiwar Allah bata gani sai ƙoƙarin kwatar kanta take yi, tana ta buge buge da hannunta.
Ganin hakan yasa Pretty ta miƙe tsaye, zuciyarta tafasa yake yi kamar an ɗaura dalma a wuta, jikinta na tsuma, da taga yadda Sweetie ke buge buge da hannu da kafa, ga shi jikin damisar ya rufe jininta ba'a iya ganinta sai hannu da kafar da take ta bubbugawa a ƙasa tana neman yadda zata kwaci kanta.
Ganin haka yasa Prettyn ta yi tunanin ko damisar cin namar Sweetien take yi, ta kara tsorita over! Jikinta na tsuma tana tsotace, nan take ta ji wani karfi ya zo mata, zuciya ba zata iya gani a kashe mata ƴar uwa ba, da wani irin mahaukacin gudu ta nufi damisar, ita kanta bata san ta nufe shi ba, jini ba wasa ba, tashin hankalin kada ƴar uwarta ta mutu ne yasa ta nufi damisar ba tare da saninta ba, bata san tana da karfin zuciya har haka da zata iya tinkarar damisa ba har sai da taga Sweetien a gaɓar mutuwa. Wani irin kukan kura ta yi ta haye saman bayan damisar ta fara kai mashi duka da ƴan hannayenta da basu wuce a kama a karya ba, duka take kai mashi har da su cizo, tana yi tana sambatu a kan ya rabun mata da ƴar uwarta, kada ya kasheta, wlh ita kaɗai kawai take da shi a duniya.
(Ni kam na ce ko yaushe damisa yasan duniya bare har yasan yar uwa kuma yasan ita kaɗai kike da shi a duniya? Jama'a ku taya jin abin da Pretty ke gayyawa damisa fisabilillahi 🤌 Allah sarki, duk wata zuciya mai imani ne ba zata ɗauki ganin a kashe mata nata a gabanta ba, barema su da suka taso a tare, basu da kowa, kullum suna manne da juna, suka kwanta ciki ɗaya kuma suka sha nono lokaci guda, ai fin haka ma Prettyn zata aikata)
Baiwar Allah ihu take tamkar maƙoshinta zai ɓalle, komai rashin imanin zuciya ta gansu a wannan hali sai ta tausaya masu. Wani irin girgiza damisar ta yi sai ga Pretty ta faɗo ƙasa tim.
Ɗago kai damisar ta yi daga kan Sweetien tana kallonta, duk ta farfasawa Sweetie wuya da faratunan hannunta, sai dai bata kai ga tsinke mata maƙogoro ba, har yanzu akwai rai a jikinta.
Ihu Prettyn ta sake kurmawa ganin jinin dake malala daga wuyar ƴar uwar tata, da karfi ta miƙewa tsaye, cikin dakiyar zuciya da ita kanta bata san tana da shi ba sai yau data ga bone, da Sweetie ta mutu gara mata ta rinkari koma wace iriyar masifa ce. Wani katon itace dake kusa da ita yashe a ƙasa ta ɗauko, idanunta ya rufe sosai, gadan gadan ta nufi damisar, a lokacin kuma damisar ta mayar da kanta kan Sweetie tana ƙoƙarin lamusheta.
Da karfi Prettyn ta daddage ta bugawa damisar itacen a kai. Hakan yasa ta ɗaga kanta sama ta saki wani uban gurnani mai tarwatsa ƙwaƙwalwale masu sauraro. Ita kanta Pretty sai da ta jefar da itacen ta sanya hannu ta toshe kunnuwanta, tare da runtse idanunta ta ɗan yi baya.
Wani irin dip da ta ji a kusa da ita ne yasa ta yi saurin buɗe idanunta. Damisar ce a gabanta, ta baro kan Sweetie ta tinkarota, shi ne ta yi tsalle daga kan Sweetien ta diro a gabanta hakan yasa ta ji wannan dip ɗin.
Sai a lokacin kuma ta dawo cikin hankalinta ta gane ashe fa damisa ce a gabanta, duk buga mata itace da ta yi bata cikin hayyacinta ne, tsoron rasa ƴar uwarta yasa ta yi duk abin da ta aikata. Yanzu kuma da ta juyo ta kanta sai ta fara tunanin mutuwa zata yi, nan take ta fara hawaye.
Cikin takun ƙatsaita damisar ta tunkarota. Habawa kafa me naci ban baka ba? Da wani irin mahaukacin gudu ta juya ta nufi barin wajen, da gudu damisar ta rufa mata baya, gudu take kamar walkiya, kamar zata tashi sama, tana gudu kuma tana ihun a kawo mata ɗauki.
(Gaskiya duk da sun ban tausayi a wannan waje, kuma na yi kwallah, amma wlh sai da Pretty ta sake bani dariya😅 dan ni kaɗai naga irin gudun da take yi kamar walkiya😅 Allah sarki gudun cetan rai😥💔 ko in da take kawa bata sani ba, yi take kamar zata fire sama kawai)
Ita kuma Sweetie jin damisar ta bar kanta ne yasa ta miƙe jini ba ɓulɓula daga wuyar tata, ta kai hannu ta rike wajen tana kuka gwanin ban tausayi, ga shi bata iya gani, haka ta bazama cikin dajin nan tana layi tana kiran sunan Pretty, kuka take yi sosai gwanin ban tausayi, sai kutsawa cikin dajin take yi ba tare da ta san ina ta nufa ko in take takawa ba.
Hanyar yamma ta nufa dan neman Prettyn tana kuka, ita kuma Pretty ta yi gabas ne, so kwata kwata ma basu haɗa hanya ba. Bata yi nisa a lalluɓen hanyar da take yi tana tafiya ba sai ga wasu jiga jigan zaratan matasan maza da mace ɗaya masu ji da lafiya sun sha gabanta, dukkansu sanye suke da fararen kaya tas except macen, kumma dukkansu suit ne a jikinsu, macen kuma wani irin kaya ne mai kama dana mayaƙa ta sanya, macece da a shekaru ba ba zata wuci 22 years ba, mazan kuma zasu iya haura 30 haka. Face ɗinsu da wani irin bakin fenti na zanen bakar damisa, ba zaka taɓa iya gane su wanene bane, maza ne majiya karfi madaka katti. Su goma ne cif sai macen. Daga sama har ƙasa su da gani kasan daga wani ɗaular suka fito, dan babu harkar karanta a tattare da su, sun jiku da naira, sai dai kuma babu alamar imani ko ɗigo a tattare da su, sannan babu annufi a kan fuskokinsu, duk yadda aka yi waɗan nan basu ƙunso alkhari ba!! Dan daga ganin yanayinsu kasan babu lafiya!.
Macen cikinsun lafiyayyar mace ce wadda da kallo ɗaya zaka yi mata kasan e lallai ta karɓi horo iya horo bana wasa ba, macece amma damtsen hannunta kamar na Assistant commander wato HOORAIN, daga ganin wannan mayakiya ce ko dai wani abin makamancin hakan. Macen ce ta matso ta ɗauki Sweetie cak ta saɓa a saman shoulder ɗinta, da alama nemanta ne ya kawosu cikin wannan daji, duk yadda aka yi sun san face ɗin Sweetien kuma ita suke nema, dan suna ganinta babu wata wata suka nufeta, duk yadda aka yi ita ce dalilin zuwansu wannan dajin. (Da alama Sweetie ce zata kai mu ga RAWANIN ZALINCI)
Gaba da ita macen ta yi, waɗan nan zaratan mazan suka rufa mata baya, da alama itace shugabansu, kuma itace karama a cikinsu, duk sun fita shekaru, amma yadda suke yi mata biyaya sun yi mubaya'a zaka gane e lallai duk yadda aka yi ta fisu matsayi. Gata jajircecciya, daga gani jininta a tafashe yake.
Tafiya suka yi da Sweetien ta hanyar da suka fito, sai sambatu take yi tana kiran sunan Kamran da kuma Pretty, Allah sarki bata ma san wanene ya ɗauketa ba. Su kuma sam babu wanda ya ce mata ko sannu a cikinsu, kuma ba kayan mayaƙa ne a jikinsu ba bare muce mayakan da suke nemansu su da mum ɗinsu ne suka kamata, ko dai su ne suka sake yin ɓadda kama da fararen suit? To lokaci ne zai nuna mana koma su wanene.
A ɓangaren Pretty kuwa, tana tsaka da tikar gudu wannan damisa ta daka wani uban tsalle da nufin ta sauka a kanta, sai dai bata kai ga yin hakan ba Kamran ya shiga tsakaninsu, dan kuwa hanyar da Pretty ta biyo hanyar kogonsu ne, yana zaune a saman dutsen a waje suna hira da Mammarsa ya jiyo ihu tun daga nesa, ko ba'a gaya mashi ba yasan ita ce, dan muryarta hadda ya yi mata. A ɗari ya miƙe Mamma na kiransa amma ina, ko kallonta bai yi ba, da gudun gaske ya nufi in da ake ihu, to kun ji yadda aka yi.
Ai kuwa yana shiga tsakaninsu damisar ta sauka a kansa, rigizib ya zube ƙasa. Habawa hayke mashi damisar ta yi, kokawa da ita ya fara yi yana ƙoƙarin kwatar kansa, ita kuma damisar da waɗan nan shegun faratu nan nata duk ta farfashe mashi fuska, so take ta damki maƙogwaransa ta tsinketa ta kashe shi.
Ita kuwa Pretty da bata san ma da cewa Kamran ya zo ba, cigaba da tikar gudunta kawai ta yi tana ihu, a tunaninta damisar na binta, gudu take yi sosai har ta bar yankin mai gabaɗaya, ta yi nisan kiwo.
Kamran kuma gabaɗaya damisar ta gama da shi, ko motsin kirki baya yi, duk ta farfashe mashi fiska jini na malala, tana ƙoƙarin capko wuyarsa da bakinta dan ta ƙarisa kashe shi kwatsam ba zato ba tsammani sai ta ɗaga kai sama ta kurma wani irin gurnanin azaba sakamakon wani irin kaifaffen wuƙa da Mamma ta caka mata a ciki.
Wani irin gurnani ta saki take da girgiza jikinta. Mamma dake tsaye a dake kamar wata commander mayaka ta fara kalla.
Ko alamar tsoro babu a fuskar Mamma, tana tsaye cikin jarumta, ko shakkar damisar bata ji ba, zuciyarta tafasa yake yi, wani irin bakinciki ta ji na jiwa ɗanta ciwo da damisar ta yi, burinta kawai ta zo su gwabza ta kashe banza, dan ita ba yau ta fara faɗa da damisun dake cikin wannan dajin ba, kafin Kamran ya girma ta sha gwagwar maya kafin su shafa mata lafiya, so Mamma ta wuce tunaninku, ita kaɗai tasan wacece ita kuma me yake ranta.
Kanta damisar ta yi cikin zafin nama. Ai kuwa bata yi wata wata ba ta sunkuya ƙasa tare da daba mata wata kaifaffiyar wukar a wuya wajen maƙogwaranta. Kun san damisa da zaki taurin rai ne da su, basu mutuwa ta daɗi, dan haka suka fara kokawa da Mamma babu kakkautawa.
Ganin haka yasa Kamran ya lallaɓa da kyar da makyarkyata ya miƙe, yana ta layi ya fara nufar hanyar da take ta kudu domin neman Pretty, bawan Allah shi bama ta rayuwarsa yake yi ba, Pretty ce kawai a ransa. Ita kuma Pretty gabas ta yi, Mamma kuma na faɗa da damisa tana ƙoƙarin ƙarisa kashe ta, yau Rocky baya nan, su suke kwatar kansu da kansu, Allah sarki ga Sweetie dai an tafi da ita, ko su wanene?............ Wai yau ina wannan jarumin mai irin idon su Pretty wanda yake kawo masu ɗauki kullum ne?😥💔
To wannan shi ne sanadiyar rabuwar waɗan nan bayin Allah da suka shafi tsawon lokaci a tare, Sweetie, Pretty, Kamran, shin zasu sake haɗuwa? Ya Kamran zai yi idan aka ce yau babu Pretty? Anya zai iya cigaba da rayuwa? Kun san kaunar da take a tsakaninsu fa! Shin Kamran zai je neman babansa? Wanenen ma shi? Wacece Mamma? Ina mum twins ta tafi ta barsu a cikin wannan dajin? Su waye su Pretty? Suwaye suke neman rayuwarsu? Su waye suka biyo mamansu time da take da cikinsu? Meyasa su kaɗai ake da buƙata ban da mamarsu? Meyasa lokacin da aka biyota waɗan da suka biyota cikin nata kawai suke da buƙata? Ina babansu? Ina baban Kamran? Waye wannan jarumi mai irin idon Prettyn?
DUBAI. Menene makomar Leesharh? Shin asirinta zai tonu? Maganin me Ramish ya sha? Shin zai cutu da gaske?. Idan Allah yasa Leesharh ta gama aiki shin masu nikaf zasu cika alkawarin da suka ɗaukar mata na haɗata da babanta kuma su mayar da ita kasarsu? Shin da gaske Leesharh ita ta kashe mahaifiyarta? Idan ita ce menene dalili? Wacece ita ma? Ya makomar tsakaninta da Obaid a yanzu?
GIDANSU KHADIJAH. Menene makomar maman Zainab? Baban Zainab ya mutu? Ina Hauwa? Idan baban Zainab ya mutu ya maman Zainab zata yi? Zata tsira kuwa? Kisan kai ta yi kenan? Hukuma zasu barta?.
KINGDOM OF POWER. Nan ba sai na yi magana ba, cakwakiyar dake ciki ya wuce tunaninku, abin ya wuce zatonku.
Shin da gaske Sweetie ce zata kaimu ga RAWANIN ZALINCI? Suwanene waɗan da suka ɗauketa? Ina kuma zasu kaita?.
Amsoshinku yana step two, yanzu zamu afka cikin labarinmu, kada ki bari a baki labari, labari ne da yazo da salo na daban, zalinci, cin amana, hainci, cutarwa, zanba cikin aminci, tauye yarda, tauye hakki, cin hakki, cin zarafi, mugunta, keta, da kuma zazzafar soyayya mai cike da kaddarori haɗi da nasarori da kuma fafutukan cikar buri. 500 Naira kacal kuɗin karatun littafin RAWANIN ZALINCI from step one to end, da 500 naki zaki cigaba da karatunsa cikin aminci da kwanciyar hankali, trust me ba zaki taɓa yin danasanin karanta littafin RAWANIN ZALINCI ba, zaki ilmantu matuƙa, zaki nishaɗantu matuka, zaki wa'azantu matuƙa, ku kunsan yadda alƙalamina yake, akwai tarin abubuwa a tattare da shi, ba sai na ɓata bakina wajen sake gaya maku ba.
Duk wadda ta shirya biyan kuɗin karatun littafin RAWANIN ZALINCI zata tura kuɗinta ta wannan account ɗin 1882812910 Musa Fatima Zahra access bank. Sai ta tura mun shaidar biya ta nan. ***, kina biya zaki afka cikin tafiyar nan, ayita dake, kada ki yarda a baki labari!!.
TAƁA KA LASHE STEP TWO🔥💔😥
KAMRAN AND MAMMA.
"Kamran idan ka sake magana a kan babanka zaka mutu, mutuwa kuma mafi muni a rayuwa, kamar yadda ka taso baka san kowa ba, sai ni, to haka zaka riƙe ka manta da duk wasu tunanin banza".
"But Mamma why? I want to know my father ko da kuwa hakan ce zata zama sanadiyar numfashina na karshe, just tell me where's he? Ni zan je in da yake koda kuwa ya fi wuta zafi dole na tunkaresa!! Na kusancesa!!".
Tsawa ta daka mashi mai sauti, cikin fusata, idanunta sun kaɗa sun yi jajir, jijiyon kanta har wani mimmikewa suka yi, da alama ranta ya kai kololuwa wajen ɓaci, har wani huci take yi kamar zakanya. "Kamran ina gaya ma zaka yi mutuwar walaƙanci in dai ka sake yin magana a kan babanka! Kai ba mutun ne kamar kowa ba! Kai ba kamar sauran mutane kake ba! Kai na daban ne, farautarka ake yi kamar yadda ake karautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana! Zaka mutu idan ka fita! Zaka mutu kamar dabba! Dan haka ka tsaya a in da na tsayar da kai!!".
"Mamma i can't! I can't gaskiya! Idan kuma kina son na bi maganarki so tell me who I am?! Where's my father and my family?! Why are you hiding our life anytime?! Am tired! Am tired Mamma! I want to see my father and my family, cos I can't stay with you again! Tafiya zan yi na nemo babana and Prettyta even wannan shi ne ganina dake ta karshe!".
Tashin hankali kenan, ɗan tsokaci a tsakanin Mamma da Kamran kenan, menene dalilin Mamma na hana shi sanin tarihin babansa bayan ya buƙaci sani? Waye shi? Ina mahaifin nasa yake? Meyasa take cewa zai mutu idan ya sake yin magana a kan babansa? Meyasa?!!.
SWEETIE.🔥
"Ɗago idanunki da kyau ki kalleni, sannan kuma ki yi mun shiru, a nan ba'a son hayaniya, kada ki bari a jiyo ki".
Shiru dole ta yi ba dan ta so ba, sai dan tsoron irin muryar da ta ji anyi mata magana da shi, tabbas wannan murya da ta ji ba muryar wasa bace, kuma da alama babu imani a tattare da mai wannan murya ko ɗigo.
"Ina Spender yake? Shi kawai muke da buƙatar ki bamu, kina bamu zamu sakeki, mu bamu da bukatarki a nan wajen!". Wannan murya ce ta sake katseta da faɗin hakan.
Su waye su? Meyasa suka ɗauketa? Menene Spender? Ina kuma yake? Me zasu yi da shi?.
Murya a dashe saboda kukan da ta rinƙa sha tun safe, murya ya dashe, da kyar ta iya furta. "Menene Spender?".
A fusace Delisha ta ɗaga wannan katakon hannu nata zata zabga mata mari, dan a ganinta Sweetien ta raina masu wayo ne, ta isa tace bata san Spender ba? Ba zai yiwu ba dole ta basu yau, abin da suke haukace suke nema, nemansa suke yi kamar hauka, kuma sun san yana wajenta, sama da shekaru biyar suna nemanta, da kyar suka ganota, sun sha bakar wahala a nemanta, amma ta nuna masu bata ma san shi ba? Tama isa?!!.
Tana ƙoƙarin sauke mata wannan katakon hannun nata a saman lallausan kumatunta kwatsam ta ji hannun nata ya sage a saman iska bai ƙarisa kai saman kumatun Sweetien ba.
Yar karar azaba ta saki kafin ta furta.............
Kai kai kai taɓa ka lashen ya isa haka my people's, sai dai mun haɗu a step two kawai, akwai cakwakiya over. Hanzarta ki biya kuɗin karatu dan ki morewa ganin wannan cakwakiyar!.🤸💃💃
Ƴan Niger kuma ban barku a baya ba, ku mun magana ta wannan numberta ɗin dan na gaya maku ta yadda zaku yi naku payment ɗin. ***
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi 👏
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍